Showing 117001 words to 120000 words out of 185789 words

Chapter 40 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24207

ne ya rage a daura min aure bana tsammanin zan iya watsa mijin mahaifiyata 'kasa a ido.............."Salamu alaikum." Sallamar da muka ji itace ta sanya muka dawo nutsuwar mu. Baito ce da Jamila suka shigo gidan Baito sakin baki tayi tana kallon mu tare da tallafe ha'ba, ita kuwa Jamila ido jawur ta wuce gurin Ummatu fuuuuuuu! kamar tashin Iska.





_Nagode kwarai da adduarku masoya ciwon kai da sauqi sai dai dole ku cigaba dayi min uziri har zuwa lokacin da zan warware ina fata da yardar Allah na gama muku littafin nan kafin azimi a yanzu dai ina shan magani wannan pege din ma dauriya ce ganin kun damu da yawa yasa nayi typing din Ina rokon Ubangiji Allah ya 'kare mu da lafiya wannan zafin da muka shiga Allah kasa mu wuce lafiya NAGODE da Alfarma????_




*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*





*70&71*
Tunda ya shiga d'akinsa ya kulle bai fito ba sai da yaji kiran sallar magariba ya bude dakin ya fito yana ya mutsa fuskarsa lokacin su Baito sun dade da tafiya sai Ummatu a kicin tana aikin tuqa towon teba. ganin fitowarsa yasa ta bishi da kallo cikin kulawa tace.''Wai dama tun dazu kana cikin dakin."? Sumar kansa ya shafa a hankali yace."Eh ina ciki bacci ne ya daukeni.'' Ya fadi hakane domin ta kyaleshi da tambaya, tace." Sai kayi sallah kazo ka irin abincin da kake so nayi maka.
Yana kokarin daukar buta yace."To shikkenan nagode Ummana." Bandaki ya shiga ya fito ya tsuguna yana daura alwala ta kalleshi da fadin."Ya jikin naka."? Yace."Da sauki." Tace."To Allah ya kara afuwa ina fata dai kaji maganata ta dazu." Yace."Kada ki damu Ummatu insha Allahu zan kiyaye." Taji wani irin dadi a cikin zuciyarta juyawa tayi ta cigaba da aikinta shi kuma ya nufi massalaci.

Tare suka shigo gidan da mahaifinsa. Kawu ya tsaya suna magana da mahaifiyarsa shi kuwa da sauri ya shige gurinsu.....hakan sai duk ya basu mamaki! amma dai duk basu kawo komai ba a cikin ransu....Gwaggo ta cigaba da bawa Kawu Iro Labarin irin halin da Khalid din ya shiga a lokacin da ya samu labarin auran Sa'ida da Aminu.....Kawu Iro ya dinga girgiza kansa yana mamakin al'amarin Gwaggo tace."Wallahi Ibrahim sosai na tsorata da ganin yaron nan yana aman jini hakika ba karamin son Yarinyar nan yake ba don Allah Ibrahim kayi wani abu kai domin ceto rayuwar yaron nan.

Kawu ya girgiza kai da fadin."Gwaggo wane abu zanyi akan Al'amarin nan aski yazo gaban goshi dole khalid yayi hakuri bashi da rabo dama aman jini kuma ina ganin kamar shi ya d'orawa kansa tunda bashi da tawakkali."

Tace."Ibrahim idan kana nunawa Khalid kiyayya sai naga kamar ba kai ka haifeshi ba ya za'ayi yaron nan ya dorawa kansa ciwo yanda aka yaudareshi ina ganin zai iya yanke jiki ya fadi saboda tashin hankali.

Kawu Murmushi yayi yace."Gwaggo mu dai har kullum za'bin Allah muke nema saboda haka dukkanin abinda ki kaga yana faruwa daga Allah ne Khalid kuma duk abinda nake nunawa a kansa 'kauna ce ta janyo haka saboda haka ki daina cewa bana sonsa.

Tace."To ai shikkenan dama nasan ba zaka ta'ba fahimtar maganata ba Ubangiji Allah ya bashi lafiya." Ya amsa da ameeen yana kokarin shiga gurinsu.



To har wajan tara da rabi na dare Khalid bai leko inda muke ba Gwaggo hankalinta ya tashi ta kalleni da fadin."Sa'ida anya kuwa lafiya kinga yaron nan har yanzu bai shigo ba ko dai yana can a kwance a d'aki ciwon nasa ya tashi.


A sanyaye nace."Kije ki duba ki gani." Yunkurawa tayi ta mike ta kama hanyar fita tana fad'in."Ai dole naje na duba shi.


Lokacin data shiga gurin samun sa tayi a kusa da mahaifiyarsa suna hira.......Ganin ta shigo yasa sukayi shuru....Tace."Khalid ashe lafiyarka lau ina can ina zaman jiran ka ka shigo kaci abinci shuru baka shigo ba nace bari nazo na duba ka."


Cikin kulawa yace."Gwaggo ina nan muna hira da Ummatu abinci kuma na riga naci amma ki ajiye min d'umame."? Jiki a sanyaye tace."Yau kuma a gurin Uwarka kayi ra'ayin cin abincin."?

Murmushi yayi bece komai ba Ummatu tana 'yar dariya tace."Gwaggo yau yana so ya faranta min rai ne a matsayina na Uwarsa ni kuma sai na samu damar zaunar dashi ina masa nasiha akan rayuwa.

Gwaggo na k'ok'arin juyawa tace."Eh ai kam kin kyauta Rabi ki cigaba dayi masa nasiha." Tana gama maganarta ta fita daga gurin jikinta duk a mace babu shakka akwai abinda Surikar tata take shirya mata.


Haka muka kwana ni da Gwaggo cikin tunane tunane mara dad'i da ma'ana......Da safe cikin kayan motsa jiki ya leko dakin a maimakon ya shiga kamar yanda ya saba sai kawai ya dogare a bakin kofa hannunsa rike da labule yace."Gwaggo kun tashi lafiya."? Tace."Lafiya lau Jarumi ya karfin jiki."? Murmushi yayi yace."Naji sauki sosai gashinan ma zan fita atisaye." Tace."To masha Allah kafin ka fita ka shigo ka karya kummalo tukkuna.

Yace."Gwaggo a yanzu dai bana bukatar wani abu sai bayan na dawo." Baki a sake muke kallonsa....ya kalle ni babu yabo babu fallasa yace."Auntyna kin tashi lafiya."? Nace."Lafiya lau ya jikin ka."? murmushi yayi be amsa min ba ya saki labulen dakin ya bar gurin.


Shuru dakin yayi na minti biyu kafin ta kalleni a sanyaye tace."Sa'ida Rabi ta kitsawa yaron nan mugun nufi akan mu ko bakya ganin abinda yake sai kace dodanni ya'ki ya zauna a inda muke."

Nace."Nima tun jiya na fahimci hakan amma bana so ki tayar da hankalin ki gwaggo ki kyaleta don Allah duk rintsi bata isa ta sanjawa towo suna ba.''


Gwaggo tace."Aikuwa dole sai na zauna dashi munyi magana idan ma uwarsa ce take zuga shi sai ya fada min." Murya na rawa take maganar....Tausayi ta bani na girgiza kaina gami da fadin." Komai dai yayi farko yana da karshe Gwaggo idan kin kwantar da hankalinki Ummatu bata isa ta raba soyayyar dake tsakaninki da Khalid ba.

Hawaye ta share ba tare da tace komai ba ta dauki jug din kunu tana tsiyayawa a kofi....Mikewa nayi na fita domin nayi wanka da wuri nake so na fita gidan Hauwwa domin cigaba da gyaran jikina.


Tsaf na gama shiryawa na zauna ina karyawa in ban da hirar yaron babu abinda take min gabadaya duk ta d'aga hankalinta kan abunda yake ni dai lalla'bata nake yi akan kada bayan fita ta daga gidan ta takali Ummatu da wata rigimar sabida na riga nasan halinta da rashin hakuri ita kuma Ummatu idan ranta ya 'baci ta mayar da martani suyi ta hayaniya a gida mak'ota na jinsu hakika ina masifar jin takaicin abinda sukeyi.

Mayafi na yafa ina kallonta nace."To ni zan tafi sai na dawo." Tace."To shikkenan nima idan anjima zanje a lalla'be min kaina idan yaso da daddare sai na kunshe fafafuna da lallai."

Nace."Hakan nada kyau Amma Gwaggo don Allah ki dauki maganata kada bayan na fita ki takali Ummatu da wata maganar." Tace."Kije abinki babu abinda zai faru sai alkairi." Nace."To dama haka nake so naji.

Ina fitowa soro kira ya shigo wayata ina dubawa naga angona ne a nutse na daga wayar tare da sata a kunnena cikin nutsuwa muka gaisa yace."Ki fito gani a waje ki same ni."

Cike da mamaki nace."Yaya Aminu ina fata dai lafiya."? Murmushi yayi a nutse yace."Lafiya lau sai alkairi."

Ajiyar zuciya na sauke nace."Gani nan fitowa dama na shirya zuwa gurin gyaran jiki." Yace."Okey to ina sauraranki."

Wayar na kashe da sauri na kama hanyar fita..........Motar Ya Aminu abar kallo ce baga yara ba baga manya ba duk wanda yaga motar yasan za taja kudi masu yawa, yara-yaran dake tafiya makaranta suka dinga tsayawa suna kallon motar wasu har zuwa suke su shafa motar......Khalid da abokansa suka shigo layin jikinsu duk yayi 'kura da kasa......Faduwar gaba naji lokacin da muka hada ido dashi, da sauri na kauda kaina na nufi motar Yaya Aminu gilashin motar ya sauke fuskarsa a sake yace."Shigo mota mana....hannu nasa ina kokarin bude motar Khalid ya karaso gurin....kallonsa nayi gabana na faduwa bana so ya zubar min da mutunci a gurin wanda zan aura amma ga mamakina sai naga ya saki fuskarsa cikin nutsuwa ya mika masa hannu da fadin."Alhaji barka da Asubah." Yaya Aminu da sauri ya mika masa hannu da fadin."Barka abokina ya gida ya al'amura."? Ya amsa da komai "Alhamdulillahi." Yaya Aminu yace."To Allah ya taimaka." Ya amsa da "Ameeen tare da cire hannunsa a nasa ya bar gurin

Yaya Aminu ya kalleni da sauran murmushi a fuskarsa yace." Amma dai wannan d'an uwanki ne ko."? Nace."Khalid ne fa."? Yar dariya yayi yace." Ina zan san shi tunda ni d'in ba mazauni bane."

Nace."Hakane fa Yaron Kawu Iro ne." Yace."Eh shiyasa ai naga kuna d'an kama dashi." Dariya kawai nayi na bude motar na shiga.


Cikin kulawa yace."Sa'ida kin san wani abu."? Kaina na girgiza ina kallonsa yace."Wallahi tafiya ta kama ni zuwa india zan shigo da wasu kaya an jima nake sa ran tafiya amma bazan dade a can ba kada ki damu za'a daura aure kamar yanda aka tsara za kuma ki tare a gidanki insha Allahu sati biyu kacal zanyi na dawo."

Rau rau nayi da ido ina kallonsa nace."Me zai hana idan an d'aura auran na zauna a gida har ka dawo bana so na zauna ni kadai wallahi.

Hankici yasa yana goge min hawaye yace."Da haka na tsara amma Alhaji yace bai amince da hakan ba ya fiso idan an daura auran ki tare a gidanki idan yaso sai a turo miki wanda zai ta yaki kwana daga gidan mu."

A sanyaye nace."To shikkenan Yaya Aminu Allah ya kai ka lafiya ya kuma dawo da kai lafiya." Ya amsa da ameeen Ya rabbi dole sai kinyi hakuri da yanayin kasuwanci na Sa'ida."


Nace."Haba ai babu komai Yaya Aminu Allah ya baka halas d'inka." Ya amsa da ameeen ya rabbi......"Yanzu muje na ajiye ki a gidan gyaran jikin idan yaso daga can sai na wuce airport. " Nace."Tom shikkenan hakan yayi." Motar ya kunna yaja mukar bar gurin.


Koda na koma gida kasa fad'awa Gwaggo maganar nayi saboda na riga nasan halinta da nanata magana, sai a washe garin ranar ne da Kawu ya shigo yake fada mata halin da ake ciki aikuwa ta dinga surutai tana fad'in "Wannan wane irin d'aid'aitaccen aure ne.'' Tsabar bakin ciki da takaici ya hana Kawu cewa komai ya fita daga gidan yana mamakin halin mayafiyar tasa.

Ni kam ai surutan da take sai da ya janyo min ciwon kai kawai na haye gado tare da juya mata baya naci kuka na na koshi ina addua akan Allah yasa kada tayi wa al'amarin baki.


Sai da Khalid ya shigo sannan ta tsahirta da surutan da take ta kalleshi da fadin." Kai kuma sai yanzu kaga damar shigowa ka gaishe ni? ai na dauka an hana ka ka gaishe ni."

Yace."Gwaggo tunda na dawo daga sallar asubahi nake bacci sai yanzu na tashi ina fitowa naji surutan ki keda waye ne."?


Tace."Humm! Khalid dole nayi surutu wannan wane irin gantalallan aure ne da za'a d'aura shi babu ango a kusa wato kudi ya fi mutunci ko? duk wanda yaga haka zaice dama kudinsa muka gani muka bashi auran 'yarmu."


Yace."Nifa ban fahimce ki."? A nutse ta warware masa abinda yake faruwa....Yace."To ai ba laifi bane don anyi daurin aure babu ango a kusa sau tari hakan na faruwa kuma hakan ba yana nufin cewa aure bai d'auru ba aure ya dauru mutukar an d'aura shi akan tsari da shedu da kuma waliyyai sabida haka don Allah ki daina wannan surutan."

Gwaggo shuru tayi tana kallonsa mamaki dan'kare a zuciyarta tace."Khalid kai kake fadar wannan maganar kanka tsaye yaushe Allah yasa maka dangana haka."?


Murmushi yayi yace." Tuntuni Allah yasa min dangana Gwaggo ai na barwa Allah komai na hakura da Aunty Sa'ida tunda ba alkari ce a tare dani ba."


Zaune na mike ina kallonsa sam banji dadin maganarsa ba. kallona yayi na second guda ya dauke kansa agogon hannunsa ya duba da fadin."Ni zan dan fita gurin abokaina." Tace."To shikkenan sai ka dawo." Ba tare da yace komai ba ya bar gurin.

Kaina na sunkuyar kasa ina mamakin sadudar yaron ikon Allah lokaci guda yayi sanyi ya mikawa Allah lamarin duk tsananin kishi irin na Khalid wai shine yake musabaha da wanda zan aura hakika al'amarin ya bani mamaki mutuka.


To kamar yanda ango ya tsara al'amarin hakane ya kasance kwanasa biyu da tafiya kasar india aka daura auran kuma a ranar na tare a dan'kareran gidana dake Unguwar Jambulo gida gari guda komai na more rayuwa akwai a gidan Yaya Aminu jin dadi dai na duniya na sameshi sai dai fatan zaman lafiya Layuza da Karima 'kannansa su aka turo domin su taya ni zama kafin ya dawo naji dadin zuwansu sosai dama mun saba dasu tunda ina ziyaryar gidansu sa'i da lokaci, bamu da fargabar komai gidan tunda akwai matakan tsaro a gidan sosai akwai securities masu dagi da karninuka a Estate d'in.






*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*






*68&69*
'Kokarin cire kansa nake daga kan kirjina yana sake lafewa a cikin jikina har da sa hannu da zagaye 'kuguna. Baito ta shiga tafa hannuwa tana fad'in ''Iko sai Allah Khalid wane irin iskanci ne wannan ashe dama rashin lafiyar naka na karya ne akaje har gida aka d'aga mana hankali."?

Ina kokarin magana Gwaggo ta fito daga dakinta ganin Baito a tsaye a kanmu tana surutai yasa tace."Aa Baito kada daga shigowarki kiyi wa yara kazafi shin me kika shigo kika tarar sunayi da har kike farfad'ar maganar da bata dace ba." Kallonta tayi cikin kumfar baki tace."Na shigo na tarar dasu rungume da juna kice kada nayi musu kazafi ki duba fa ki gani har yanzu yana kwance a cinyarta shin me hakan yake nufi.''?

Gwaggo ta juyo tana kallon gurin da muke....babu kuzari a tare dani na dauke kansa daga cinyata na mike na shiga daki raina a masifar bace da abinda Baito tazo tana yi.

Gwaggo tace."Saboda kawai tana rarrashinsa a matsayinsa na d'an uwanta sai ki fassara al'amarin da wata manufa Baito kada kice zaki watsa min zuria domin ni kaf ahali na babu mai mugun hali."

Baito na kokarin magana ya daga mata hannu a kasalance yace."Baito dan Allah a bar wannan maganar ta isa haka babu wani mugun abu da mukeyi da Auntyna kada kiyi mana mummunan fassara."

'Kwafa tayi da fadin."Ai shikkenan Khalid tunda ka mayar dani shashasha naga abu da idona amma ka 'karyata ni." Shuru yayi mata ransa duk a dagule ya tsani rashin fahimta irin na kakar tasa. Baito kofar Ummatu ta nufa tana surutai Gwaggo taja tsaki da fadin"Duk wani sharrinku sai dai ya koma kanku." Baito tana ji bata tanka mata ba saboda ta riga tasan duk masifarta Gwaggo ta dame ta ta shanye.

Kallonsa tayi da fadin."Khalid ya jikin naka."? Kansa na kallon kasan katifa yace."Da sauki Gwaggo wanka nake so nayi ko naji dadin jikina."

Tace."To bari na d'ora maka ruwan zafi kayi wankan sai kasha magani ko."? Yace."To shikkenan Gwaggo nagode." Da sauri ta nufi kicin domin ta hura wuta.


Gefan gadon Gwaggo na zauna kawai na tsirawa guri guda ido gabadaya na rikice na rasa wane irin tunani zanyi hakikanin gaskiya lamarin Khalid yayi masifar tsaya min a raina kuma banta'ba tsammanin cewa son da yake min yayi girman haka a cikin zuciyarsa ba aman jini gaskiya na tsorota sosai cikin zuciyata naji ina tausaya masa domin Allah ya jarrabeshi da son abu gashi kuma ga dukkan alamu ba alkairi ne a tare dashi ba da zaiyi hakuri yayi tawakkali ya mayar da al'amuransa gurin Allah sai yayi masa kyakykyawan tukwici amma gabadaya ya kasa hakuri da kaddara gashi yana nema ya janyowa kansa mummunan ciwo.

Hawaye na goge ina girgiza kaina lokaci ya kure maganar aurena da Yaya Aminu tayi nisa saura kankanin lokaci babu yanda za'ayi nazo da wata magana dole mu hakura mu barwa Allah ikonsa amma dole a cikin 'yan kwanakin da suka rage min na saki jikina da yaron na rarrashe shi ya kwantar da hankalinsa ina ganin idan nayi masa hakan zai dan samu sassauci.



"Kinga Jamila ki daina kuka da damuwa na fada miki mutukar ni na haifi Khalid to ba zai auri wannan tsohuwar guzumar ba duk wani abu da sukeyi daurin gindi suka samu a gurin waccar tsohuwar kuma na lokaci kad'an ne tunda ai saura kwana uku a daura mata aure kinga kuwa Khalid ko yaki ko ya so dole ya hakura da ita.


Jamila ta share hawayen fuskata murya na Rawa tace." Allah Ummatu ba kiji yanda zuciyata take zafi ba na rasa abinda yake min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login