Showing 141001 words to 144000 words out of 185789 words
Azzalimi mugu lusari kawai."!!
Cikin zafin zuciya yace."Ni kike zagi saboda baki da mutunci ko."? Ina kuka nace."Ai kai ka janyo yanzu ya kake so nayi da rayuwa ta wallahi na gaji sai ka sake ni nagaji da wannan masifar."
Tsaki yaja yana kokarin saka rigarsa yace."Ba zan sake ki kai tsaye ba sai kinje kin samu wanda ya had'a auran da maganar in yaso shi sai ya sake ki da kansa."
Yana gama maganarsa ya mike da niyyar shiga bandaki.....Da sauri na tare gabanshi A jigace nace."To ni yanzu ya kake so nayi da rayuwa ta ka tayar min da hankali wallahi ba zan iya bacci ba sai ka biya min bukatata."
Murmushin takaici yayi yace."Dame zan biya miki bukatar ki bayan ke duk wani wasa baya gamsar dake dole sai shige ki ni kuma bani da wannan lafiyar sai kiyi hakuri duk wani kokari da zanyi miki nayi amma baki gamsu ba saboda haka kada na kara jin kin zage ni idan kika kara sai na miki abinda baki taba tsammani ba." Ture ni yayi ya shige toilet din ya barni a durkushe a gurin ina kuka bakin ciki da takaici.
*BAYAN SATI UKU*
B'angaren khalid kuwa yana ta k'okari domin ya hadu da manyan yan wasa na kasashen wajen kamar Irin Nymar,C-ronaldo,messi dasu sargio ramos.kuma Yazaka Kamar shine Gwarzon shekara Domin shi ciwo musu ball masu yawa kuma ya lashe kyaututtuka na gwarzantaka da hazaka.kamar su
*(world foot boller)* duk a Kokarin sa kuwa an ciwo wasanni kamar su *CHAMPION,LEANGUE*
wannan kuma duk ta faru ne sakamakon Adduar iyaye da take ta bibiyarsa.
khalid sun shirya tsaf domin dawo wa gida cikin nasara inda suka sauka a legos, labarin samun nasarar sa kuwa tuni takewaye kano da kewayenta Gwaggo kullum bakinta kamar gonar aduga saboda tana samun labarin abinda yake faruwa da Khalid din ta bakin abokinsa Salim Kullum tana cikin farin ciki gami da yi masa adduar dawowa gida lafiya......B'angaran Ummatu da 'yan uwanta kuwa Allah-Allah suke ya dawo gidan da yake duk talakawa ne sun samu labarin makudan kudin da ya samu sai kowanne yake jiransa ya dawo ya samu rabonsa , Jamila sai girman kai take tana iyayi wai masoyinta ya zama gwarzon shekara sai ta dauki kanta ta ajiye can nesa tana ganin ita yanzu tafi k'arfin tayi mu'amula da k'awayenta na cikin unguwar tasu itama ta damu ya dawo gida domin ayi auransu kamar yanda aka tsayar da magana.
Vip gruop #600.
Normal #400
Accont number... 0542382124....Binta umar gtbank...idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*91*
'Yan uwan Aunty Murja hankalinsu ya tashi sosai a lokacin data shiga gidan da takardar sakin a hannunta babbar yarsu mai suna Hajiya Mairo ta rufe ta da fad'a sosai ta inda take shiga ba tanan take fita ba tace lallai akwai babban dalilin da ya sanya mijin nata ya yanke mata irin wannan hukuncin. Aunty Murja na share hawaye tace."Wallahi Hajiya ni ban san komai ba kawai yazo ya rufe ni da fad'a daga karshe ya bani takardar saki uku tare da fadin albarkar haihuwa ce tasa ba zaiyi sharia dani ba saboda haka kada na kuskura koma gidansa."
Hajiya Mairo tace."Kin dai janyo mana abin kunya Murja Allah yasa ba zargin da jama'ar gari suke miki ba ya samu labari ba ko kuma ya gani da idonsa."
Murja na kuka tace."Haba Mairo wace irin magana ce wannan? wane kuma zargi jama'ar gari suke min babu sata ballantana maita."
Hajiya Mairo tace."Kinga Murja maganar ta isa haka yanzu zan kira Saminu a waya yazo ya kira Mijin naki domin muji dalilin da yasa ya sake ki."
Murja gabanta ya tsananta faduwa sai taja bakinta tayi shuru tana zazzare ido.
Alhaji Saminu ya shigo gidan Hajiya Mairo duk ta zayyane masa abinda yake faruwa hankali a tashe ya fito da wayarsa ya nemo number wayar Alhaji Nura domin ya kirashi su tattauna."
Kiran duniya Alhaji Nura yana gani yaki dauka Alhaji Saminu jiki a sanyaye ya kashe wayarsa yana kallon 'yan uwan nasa yace."Da alama mutumin nan a fusace yake kuna dai ji na kira wayarsa yafi sau biyar bai daga ba babu shakka ruwa baya tsami banza.'"
Hajiya Mairo tace." Gaskiya ne maganarka Yanda Alhaji Nura yake ganin kima da mutuncin mu babban abu ne zai sanya yaki dauk'ar wayarka."
Alhaji Saminu ya kalli Murja da tayi tsuru-tsuru jikinta dik yayi sanyi yace."Hakika Murja kin cutar da kanki duk da ban san abinda ya hadaki da mijinki ba amma jikina na bani cewa kece mara gaskiya insha Allahu ba zanyi zuciya ba zanje har kasuwa na sameshi domin mu tattauna maganar.
Tace."Dan Allah kada kaje masa da wata magana kawai ka rabu dashi tunda ko kaje gurinsa ba gyara auran za'ayi ba tunda saki uku yayi min saboda haka kawai ka kyaleshi kawai wanda ya zalinci wani Allah zai saka masa." Yanda ta fadi maganar zaka dauka tana da gaskiya. gabad'ayansu sai jikinsu yayi sanyi da maganarta.
*BAYAN KWANA BIYU*
Murja ta dinga kiran wayar Hajiya Aziza tana gani taki d'auka sai al'amarin ya dinga bata mamaki dama tana so ta kira ta ne domin ta fada mata cewa auranta ya mutu text ta tura mata cewa tazo gidansu ta same ta tunda an share zaman makoki.
Hajiya Aziza ta bata amsa da cewa ita yanzu tana Abuja sai dai idan ta dawo." Murja jikinta ya mutu ganin irin wulakancin da aminiyarta ta take mata.
Shiryawa tayi ta nufi can gidan mahaifiyar Tsohon mijin nata domin ta duba 'ya'yanta....Koda ta shiga gidan lokacin Yusura tana bakin gate tana aiki sai ta 'bata fuska ciki-ciki ta amsa sallamar ta dauke kanta.
Tace."Yusura kina gani na amma kin dauke kanki me yake faruwa ne."? Yarinyar ta share hawaye masu zafi tace."Mommy bana son kallon fuskarki kin cuce ni." Da gudu ta ruga cikin gidan.
Murja gwiwarta tayi sanyi salo-salo tabi bayanta, Hajiya Dayyiba tana zaune a falo Yusura ta zube a jikinta tana gurshe'ken kuka.!
Da sauri ta dago ta tana fadin."Yusura lafiya menene? kafin ta rufe bakinta Murja ta shigo da sallama a bakinta.
Hajiya da kyar ta amsa sallamar ta dauke kanta.....Murja babu kuzari ta zauna kan kujera a sanyaye tace."Hajiya sannu ina wuni ya gida da yara."?
Ba tare da ta kalleta ba ta amsa. tace"Me ya kawo ki gidan nan."? Murja baki na rawa tace."Nazo ganin yara na ne."
Hajiya Dayyiba tayi mata wani irin kallo rai a 'bace tace."Tur da uwa irinki Murja Allah ya shirye ki idan zaki shiryu.''
Murja tace."Hajiya me nayi da zaki dinga la'antata kada fa ki manta kema kin haifa."
Tace."Eh na haifa amma bana fata zuria ta ta dauki irin munanan halayen ki Murja munyi nadamar hada zuria dake ."
Murja fashewa tayi da kuka baki na rawa tace."Hajiya nifa har yanzu ban san meye laifi na ba sai zagi na kuke kuna aibata ni uwa uba anzo anyi min saki uku sakin wulakancin "
Hajiya Dayyiba tace."To meye amfanin zama dake Murja? ai kin zama annoba tunda kika aikata abinda Allah ya haramta saboda tsabar son zuciya ki haifi 'ya a cikin ki amma ki lalata ta sabida bakya jin tsoron Allah da Annabi."
Sunkuyar da kanta tayi kunyar duniya ta isheta tace."Ni fa Hajiya ban fahimci inda maganarki ta dosa ba na haifi yarinya a ciki na kuma ta yaya zan lalata ta."?
Hajiya Dayyiba tace."Kinga Murja ki tashi sawun ki a likkafa ki fice min daga gida bama bukar ki wa'innan yaran kuma da ana canza uwa to da sai mun sanja musu wata a madadin ki."
Murja ranta ya 'baci sosai tace."Hajiya zan tafi dama ai ba zama nazo ba tunda babu wata alaka a tsakaninmu sai ta haihuwa naji dadi sosai da baku isa ku sanja musu uwa ba dole dai nice uwarsu ko kun so ko kunqi ba zaku sanjawa towo suna ba.
Hajiya Dayyiba tace." To naji maganarki mara kunya kawai wacce bata tsoron Allah ki tashi ki tafi tunda kinyi abinda ya kawo ki." Mi'kewa tayi ta kalli Yusuran tace."Wato har dake a gurin shirya min makirci ko dan ubanki me nayi miki da har ake kira na da suna fasiqa."
Sunkuyar da kanta tayi a sanyaye tace."Mommy me yasa idan Mommy Aziza tazo gidanmu kuke hawa sama ku kulle kofa ku dade baku sauko ba ranar da Babanki ya rasu data zo gidan bakya nan shine tace nazo nayi mata tausa da muka hau saman sai ta rufe kofa ta tu'be min kaya na ta...........Kuka ne yaci k'arfinta ta kwanta kan cinyar kakarta tana girgiza kanta.
Murja zaman da'baro tayi a gurin wani irin gumi mai zafi ya shiga yanko mata bakinta sai rawa yake tana so tayi magana tsabar rud'ani ya hanata sai girgiza kanta take kafin wasu zafafan hawaye su shiga karakaina akan fukarta.
Cikin takaici da bakin ciki Hajiya Dayyiba tace."Kukan banza da wofi kike yi ai dama duk wanda ya bijirewa Allah sai ya gani a 'kwaryar cin abincinsa ke a tunanin ki abinda kuke aikatawa da k'awarki babu wanda zai fahimta to bari kiji idan kowa bai ganku ba Ubangijinku yana ganin ku kuma shine ya tanadi irin zabar da zaiyi muku a ranar lahira sabida haka tun wuri ki tuba ki nemi gafarar Allah akan abinda kika aikata."
Tana kuka na fitar hankali ta dinga kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Aziza ta cuce ni ta lalata min 'Yata na shiga uku na lalace."! Kuka take sosai tana sa bakin zani tana fyace majina sai wani irin gumi takeyi.......Yasir ne ya shigo da kayan Islamiyya a jikinsa ko da yaga Mahaifiyarsa tasa cikin halin damuwa bai nuna damuwarsa ba sai ma ya dauke kansa yana k'okarin wuce ta sai ta janyo hannunsu ta rungumeshi sosai a jikinta tana kuka da fad'in "Yasir ku gafarce ni dan Allah nayi muku laifi kada ku 'kullace ni kuyi min aikin gafara." Tana kuka ta janyo Yusuran ta rungume ta a jikinta sai hakuri take basu tana fyace majina.
Hajiya Dayyiba sunkuyar da kanta tayi tana kokarin mayar da hawayen idonta wannan wace irin kaddara ce? ko da yake dama duk wanda ya kaucewa dokokin ubangiji dole ya fukancin Fushin Allah ita kam ta rasa da wane ma'auni zata auna al'amarin bahaushe yana cewa son zuciya 'bacin ta. Allah kasa mufi karfin zuciyoyinmu ameeen.
Murja kasa hakuri tayi ta sake neman number wayar Hajiya Aziza domin ta nuna mata cewa ta fashe ta gane abinda yasa ta gudu daga gari saboda abun kunyar data tafka.....
Kamar ko da yaushe Hajiya Aziza taqi daga wayar Murja ta fusata! kawai sai ta shiga WhatsApp d'inta ta duba taga tana onile voice note tayi mata na rashin mutunci muryarta sai rawa take tace."Wallahi banta'ba tsammanin za kiyi min haka ba Aziza ashe babu amana yanzu ki rasa wacce zaki lalata sai 'yar cikina me zaki samu a jikinta me kika rasa a duniya wannan abun kunya dame yayi kama."
Hajiya Aziza a fusace! tace."Kinga Murja wannan shouting din ya isa Aa ya kike wannan maganar ne? yanzu ke har kin manta yaran da kika lalatawa rayuwa? ashe laifi ne don nayi sha'awar Yusura na kawar da kwadayi na a kanta meye a ciki? Sauran yaran da muke lalatawa ashe ba iyaye ne suka haife su ba." A fusace! tace."Kinga Aziza ki daina wannan maganar don na lura kina so ki kare kanki ne yanzu ke ba zaki iya kawar da kanki akan yarinyar ba sai ki dinga yi min wata maganar banza su yaran da muke mu'amula dasu ai ba dole mukayi musu ba sune suke kawo kansu da kansu kuma kudi ake basu sai me kuma."?
Aziza taja tsaki da fadin."To tunda kin kasa fahimta ta ni zan kashe waya ta domin ina da uziri." Rai a 'bace tace." Yar iska mutsiyaciya macuciya insha Allahu sai kinyi mutuwar wulakanci."
Hajiya Aziza ta fashe da dariya da fadin." Ni dake za muyi mutuwar kaskanci wallahi 'yar iska kawai dole ne ki girbi abinda kika shuka." tana gama maganarta tayi blocking din number ta taja tsaki!
Murja shuru tayi da waya a hannu abin duniya yayi mata yawa sai kawai ta fashe da kuka tana girgiza kanta yanzu wai ya za tayi ne? babu aure babu yara ga 'yan uwa da dangi sun juya mata baya jama'ar gari suna mata wani irin kallo wace irin rayuwa za tayi ne.? Gefan zanin ta tasa ta goge hawaye tana kiran sunan Allah a zuciyarta.
****
Tun ranar da mukayi sa'insa dashi bai 'kara yi min magana ba Na lura Yaya Aminu d'an gaba ne ban san me yasa ba laifi kadan sai yayi fushi yayi kwana da kwanaki bai kula ni ba, to wannan karon na gaji kullum cikin tashin hankali babu kwanciyar hankali ta aure sai bacin rai da damuwa ina ganin tun kafin dare yayi min na yanke wa kaina hukunci............Da yake tunda mukayi haka dashi ya sanja lokacin dawowa gida sai can dare yake shigowa kuma kafin na tashi ya fita yau dai na zauna a falo dole ya dawo akan idona domin ba zan kwanta ba sai naji matsayina a gurinsa.
Sai goma da arba'in da biyar ya shigo gidan Ganina a zaune a falo yasa yayi kici kici da fuska ya kauda kansa hade da kama hanyar dakinsa......."Yaya Aminu sannu da zuwa." Ko kallona beyi ba ya cigaba da kokarin bude d'akinsa.
Sai da na bari ya shiga dakin tukkuna na mike nabi bayansa.
Yana kokarin cire rigarsa na tsaya a gabansa fuskata a mugun hade......Rai a bace yace."Lafiya zaki zo ki sani a gaba."? Tsaki naja nace."Ina so naji matsayi na ne? ina so nasan zaman me nake a gidanka."
Shuru yayi min ya cire rigar tare da ratse ni zai wuce da sauri na tari gabansa na bude baki kenan zanyi magana ya gaura min mari!
Dafe kunci na nayi ina kallonsa idanuwa sunyi jajawur! Yace."Baki san haushin ki nake ji ba ko."? Jikina na kyarma nace."Kana jin haushina kamar yanda nake jin haushinka wallahi na tsanake bana kaunar kallon wannan bakar fuskar taka."
Murmushi yayi yace."Duk na gane akan abinda yasa kike min rashin kunya kina so ki tunzura zuciya na sake ki ko."? shuru nayi ina kallonsa ya cigaba da cewa."To ba zan sake ki ba sai kin wahala a hannuna tunda ke baki da mutunci."
Hawaye na share nace."Komai abinka idan zamana ya kare da kai dole ka sake ni ai ba'a dole na gaji da zama da kai babu lafiya gashi baka san mutunci ba."
Ture ni yayi na fadi a gurin ya shige toliet din yana fadin."Hukunci saki a hannuna yake zanga wanda ya isa ya sani na sake ki."
Cikin mutuwar jiki na mike na fita daga dakin......Gefan gado na zauna ina kuka na dauki waya ta number Umma Habiba na nemo gabadaya na manta da dare burina kawai na samu wanda zai rarrashe ni Yaya Aminu so yake yasa zuciyata tayi bundiga."
Umma Habiba na kokarin kashe wayarta taga kira gabanta na faduwa ta daga........."Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! wannan kalmar ta fad'a hankali a tashe tace."Sa'ida ya isa ki daina kuka haka kiyi shuru kiyi min bayanin abinda ya faru shin fada kukayi da mijin naki."?
Cikin shaqewar murya tace."Umma na gaji da wannan masifar na gaji wallahi So nake ku raba ni da wannan wahala Yaya Aminu yana azabtar dani zuciyata daf take data buga saboda abubuwan da take had'iya."
Alhaji Shamsu ya miqa hannunsa da fadin."Bani wayar." Jiki a mace ta mika masa wayar yasa a kunnensa a nutse yace."Sa'ida yi shuru kinji ko ki daina kuka haka ya isa duk naji k'orafin ki kuma duk abinda kika ce Aminu yayi miki ba zanyi musu ba domin ba'a shaidar mutumin yau wannan auran dama ni tuntuni ya fice min daga raina saboda wannan gagarimar matsalar ba zan zama mara adalci ba insha Allahu ni zan tsaya miki akan hakkin ki Aminu zai sake ki kamar yanda kika bukata Allah yasa haka shi yafi alkairi."
Jikina ne kuma yayi sanyi sai tausayin mutumin ya lullu'be ni a sanyaye nace."Alhaji wallahi ba laifi na bane nayi dukkanin bakin kokari na al'amarin yaci tura Yaya Aminu yaki fahimtata kullum babu nutsuwa da kwanciyar hankali shiyasa kawai na yanke wannan shawarar domin ina ganin kamar itace maslaha."
Yace."Kwarai kuwa Wannan shine Maslaha kuma kinyi tunani mai kyau Sa'ida ba zaki kashe kan ki akan bukatar wani ba tabbas kinyi hakuri kuma kinyi namijin kokari akan al'amarin auranki duk wanda zai budi baki ya fadi laifin ki to yaso kansa domin ita gaskiya duk inda take sai ta tona kanta saboda haka kada ki damu kinji ko gobe da safe kizo gida da kayan ki." A sanyaye nace."Tom shikkenan Alhaji nagode sosai Allah yasa haka shi yafi alkairi" Cike da kulawa ya amsa da "Ameeen ya Allah." Kwanciyar rigingine nayi ina kallon rufin dakin......."Yanzu idan na rabu da auran Yaya Aminu wane irin namiji zan aura? Shin Sa'ida anya kuwa zaki samu nasarar auran wanda zuciyarki take hasashe."? Zuciyata ce take min wannan zancan.....Idona na rintse gabana ya shiga bugawa! kawai sai na tsinci kaina da addua akan Allah yasa Khalid ya dawo da soyayyarsa a gare ni........
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*92*
Da wannan tunanin bacci mai nauyi ya d'auke ni da asubah sai da na fara wanka tukkuna na dauro alwala na fito