Showing 30001 words to 33000 words out of 185789 words
magana dan na lura jikinta yayi sanyi da maganata.
Girgixa kaina nayi ina kokarin magana Umma ta shigo falon hannunta da farar leda cike da goro manya masu kyau Gwaggo da sauri tasa hannu ta kar'ba da fad'in " Kai amma naji dadi sosai Habiba Allah yayi miki albarka."
Umma Habiba ta amsa da "ameeen ya Allah." Ta fita daga falon.
Ledar ta kwance ta dauko daya ta 'bantara ta fara taunawa. Nace."Gwaggo Khalid ko ya kai *Dangwate* kud'i a duniya baya cikin tsarina yaje can ya auri daidai dashi nima na auri daidai dani magana ta mutu a gidan nan kada ki Sake yi min maganar Khalid."
Tace."Ai shikkenan Sa'ida tunda kinqi Khalid har kina kokarin yi masa sharri zanyi masa magana ya rabu dake tunda bakye kad'ai ce autar mata ba insha Allahu Allah zai bashi wacce ta fiki kyau da 'kuruciya."
Nace "Nima zan taya shi da adduar samun macan data fini."
Shuru tayi min ta cigaba da tauna goronta kallonta kawai nayi na gane maganata ta kashe mata jikinta, nace."Ko na kawo miki abinci."?
Girgiza kanta tayi tace."Bana bukata saboda inda na baro da akwai abinci." Nasan magana ta fad'a min a fakaice oho! ni dai na fad'a mata abinda yake raina sabida haka ita da Khalid din duk su shiga hankalinsu.
Tace."Khalid d'in ma gobe zai koma makaranta." Nace."Allah ya bada sa'a." ta amsa da "ameeen ya Allah."
Umma ce ta shigo dakin da fad'in "Gwaggo Alhajin ya dawo tashi muje nayi miki jagora ku gaisa." Da sauri ta miqe tana gyara yafan mayafinta suka fita tare.
Alhaji Shamsu yana zaune a kan kujera yana lissafi da wayar hannunsa sukayi sallama a dakin nasa....cikin kulawa ya amsa da fad'in"Gwaggo sannu da zuwa ga guri nan zauna."yafada yana nuna mata kujerar dake kallonsa
Gwaggo ta zauna kan kujerar tana amsawa tare da fad'in "Ai na jima a gidan ina jiranka da fatan ka dawo lafiya."? Yace." Lafiya lau gwaggo ai ban sani ba da tuntuni na dawo gidan sabida ke koda na shigo ma maigadi yake sanar dani zuwan Ibrahim bayan fita ta hakika banji dadin faruwar hakan ba."
Tace."Aikam dole kaji rashin dadi dan muma jiya haka muka kwana zuciyoyinmu Babu dadi wannan dalilin ne ma yasa shi Ibrahim dako sammako yazo gurinka domin ku tattauna magana sai kuma akayi rashin sa'a ka fita kasuwa shine nace to ni bari idan rana tayi sanyi sai nazo gidan na sameka mu tattauna maganar dan nazo tafiya da Sa'ida ne matarka Habiba tace lallai sai ka dawo ka bada umarni shine nace to komai dare kuwa zan zauna har ka dawo domin naji uzirinka akan yarinyar."
Alhaji Shamsu yayi gyaran murya yana kallonta ya riga yasan halinta 'yar taratsatsi ce yace."Hakane Gwaggo Sa'ida tazo gidan nan cikin halin damuwa tana kuka ta sheda mana abinda yake faruwa acan gidan al'amarin ya tayar min da hankalina sosai Gwaggo shi ai aure lokaci gareshi mai zai sanya ku tayar da hankalinku akan yarinyar nan har ku dinga d'ora mata lalura irin ta aljanu bayan haka kuma har a samu masu yi mata 'kazafi na zina wannan al'amari baiyi min dadi ba gaskiyar lamari raina ya 'baci dajin wannan magana shine dalilin da yasa ma na yanke hukunci kancewa ba zata koma gidan ba sai an kwana biyu kuma dole ne mu samu zama dashi Ibrahim din akan maganar yana da kyau ya jawa matarsa kunne ta guji jifan yarinyar nan da muna nan kalamai domin hakan bai dace ba."
Gwaggo tace."To ai Alhaji Ibrahim ya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro inaso na sheda maka cewar duk yanda kake kaunar yarinyar ba kamar shi ba tunda Ubanta ne ya saki nono shi ya kuma ya kama kaga dole yayi kishinta ya kuma nunawa matarsa 'bacin rai dan yanzu maganar da nake maka Rabi tana gidansu tun jiya ya koreta daga gidansa yace mutukar ba Sa'ida ce ta dawo gidan ba to ya gama zama da ita."
Alhaji Shamsu yace."Subahanallahi Me yayi zafi Ibrahim zai yanke wannan hukunci." Ummah Habibatan tace."Nima haka na gani Alhaji Iro ya yanke hukuncin da bai kamata ba ai komai a sannu a hankali ake binsa."
Gwaggo tace."To ai shine nake so ku fahimta Ibrahim zai iya rabuwa da matarsa akan yarinyar nan to tun kafin hakan ta faru yasa nazo domin tafiya da ita."
Hankali a tashe ya dauki wayarsa da fad'in "Bari na kira wayarsa idan da hali sai yazo domin mu tattauna maganar a tsakanina dashi amma banji dadin wannan lamari ba."
Gwaggo tace."To shikkenan ai yanzu nasan ya dawo daga kasuwa idan ma bai dawo ba to babu shakka yana kan hanya.
Kawu Iro na adaidaita sahu kira ya shigo wayarsa ganin number Alhajin yasa da sauri ya daga suka gaisa a tsanake Alhaji Shamsu ya sheda masa uzirinsa....Kawu Iro yace."To babu damuwa Alhaji ganin zuwa insha Allahu." Wayar ya kashe ya umarci direban daya juya baya ya kaishi hotoro. Yace."Amma dai zaka 'kara min kudi ko."? Kawu Iro yace."Eh 'kwarai kuwa idan ma ka samu fasinja ka dauka." yace."to shikkenan.
Sai magariba Kawu Iro ya isa gidan kuma basu samu zama ba sai da suka gabatar da sallah tukkuna suka fito daga massalaci a tare wani 'kebantacan guri suka samu suka zauna suka sake gaisawa cikin mutumci kana suka shiga tattauna abinda ya had'asu.
Kawu Iro ya sauke ajiyar zuciya da fad'in "Alhaji ka kwantar da hankalinka insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba maganar mai d'akina kuma ni a ganina hukuncin dana dauka a kanta shine daidai kaga gaba zata kiyaye jifan yarinyar nan da wata mummunar kalma."
Alhaji Shamsu yace."Hakane Ibrahim to amma inaso dan Allah ka sake sanya ido akan yarinyar nan sannan idan da wani wanda kaga alamun da gaske yake sonta to kayi masa magana ya fito kawai domin hakan shine ya dace."
Kawu Iro yace."Insha Allahu hakan za'ayi akwai wani mutumin anan gaban inda muke yana son ta koga yanayin hidimar da yake mata to saboda haka idan na koma gida zan sameshi da maganar domin mu tattauna."
Alhaji Shamsu yace."To Alhamdulillahi Allah yasa sanya alkairi.'' Kawu Iro ya amsa da ameeen ya rabbi.''
To muna zaune a falo har gwaggon muna hira ya shigo. gwaggo tayi saurin fad'in "Ina fatan Ibrahim din yazo." Yace."Eh Gwaggo yazo ina fita da niyyar shiga massalaci na hangi zuwansa tare ma mukayi sallah masha Allah mun tattauna magana dashi ta fahinta saboda haka ke Sa'ida zaki koma gida magana ta wuce insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba sannan kuma Ibrahim ya sheda min cewa akwai wani mutumi da yake sonki a Cikin unguwar to nace masa yayi magana dashi idan da gaske yake sai yayi magana ayi abinda za'ayi."
Gwaggo har ta bud'e baki za tayi magana sai kuma ta fasa.
Yace."Gwaggo kamar akwai magana a bakinki." girgixa kanta tayi tace."Aa babu magana Alhaji." Ya kalleni da fad'in "Kinji hukuncin dana yanke ko."? Nace." Eh naji Alhaji dama nima inaso nayi masa magana kan cewa ya turo magabatansa ayi maganar aure idan da gaske yake."
Alhaji yace."To Alhamdulillahi hakan yayi kiyi masa magana shima Ibrahim din yayi masa sai ya dauki maganar da muhimmanci." Nace."To shikkenan Alhaji." hannu yasa a aljihu ya dauko kudi kimanin dubu biyar ya mikawa Gwaggo da fadin "Gashi kya sayi goro." Babu yabo babu fallasa ta kar'bi kudin dan Taji masifar haushin yanda yake nuna ikonsa akan Jikarta wai duk muna nan maganganun data ya'ba masa ba suyi masa zafi ba sai wani za'kal'kalewa yake.
Bayan fitarsa daga falon Ummah Habiba tace"Gwaggo bari na kawo miki abinci kici sai ku taf......tun kafin ta 'karasa tayi saurin katseta da fad'in "Bayan wanda naci d'azu kuma zaki sake d'ubga min wani Aa bana bukata tafiya za muyi." kana jin yanda tayi maganar kasan a fusace take......mi'kewa tayi tana gyara yafan mayafinta, nida Umma muka bita da kallon mamaki.
A cunkushe tace."To gimbiya ina jakar kayan naki take na d'aukar miki.'' Murmushi takaici nayi ba tare dana tanka mata ba na mi'ke Umma ma ta mi'ke tana 'yar dariya nasan ita da gwaggo ne....Hijabina na gyara na dauki jakar kayana na ri'ke ta ta'be bakinta tai tayi gaba tana surutai! Umma tace."Gwaggo ga mayafi da takalmi kayi amfani dasu."
Juyowa tayi tana kallon ledar hannunta murmshi tayi wanda be kai ciki ba tace."Habiba kin manta ni tunda jajayen sawuna bana yafa wani gyale idan ba na atamfa ba."
Umma tace."Kwarai hakane na manta wallahi to ki kar'ba dai ko kyautarsa sai kiyi.....Nace."Umma ki ajiye mayafin ki zaiyi miki amfani idan ta kar'ba ma munafukar matar nan zata bawa Uwale."
Umma ta ri'ke bakinta cikin mamaki tana kallon Gwaggo tace."GwaggoAshe har yau kina tare da Uwale."?
Da sauri tace." 'Kwarai kuwa ba kuma mai rabani da ita sai mutuwa." Tana gama maganarta tasa takalmanta ta fita ta barmu...Umma tace."Sa'ida ki cigaba da hakuri kinji ko watarana sai labari." Nace."Umma Insha Allah zan cigaba dayi nasan Allah yana kallo."
Ta mi'ka min ledar da fad'in " 'Karbi ki ri'ke mata tunda nayi niyya bazan fasa ba babu ruwanki da wanda zata bawa." ledar na kar'ba da fad'in "To shikkenan." sallama mukayi da ita tace."Lallai idan na fita na shiga d'akunan kishiyoyinta nai musu sallama.
Nace."To insha Allah zan shiga.
bakin gate na same su a tsaye ita da Baba Iro suna jiran fitowa ta ina ta kici-kici da jakar kayana yazo ya kar'bi jakar yana fad'in " Sai kiji da ledojin hannunki." Nace."Haba dai Kawu dan Allah ka ba kawo dik zan iya ri'kewa." Gwaggo tace."Au! ashe kayan naki suna da yawa tunda ga wasu nan a ledoji."
Nace"Aa wannan ledar taki ce su kuma wannan yanzu akayi min kyautarsu amma ni ba dasu nazo ba." hannu ta mik'a ta kar'bi ledar kayanta tayi gaba nabi bayanta ina mamakin 'karfin halinta.
Direba ya kar'bi jakar kayana yasa a bayan mota Gwaggo ta shiga ta zauna Kawu ya zauna kusa da direba ina kokarin shiga........Motarsa ta shigo gidan tsayawa nayi har direbansa yayi parking ya fito a nutse cikakken mutum kamili dogo ba'ki da kyau daidai misali saboda yanayin hutu da jin dadi yasa bakar fatarshi tayi wani freesh sai daukar ido take...... kwata-kwata Yaya Aminu baida izzah irin ta masu kudi dalilin ma da yasa kenan nake 'kara mutunta shi.
Fuska a sake ya 'karaso inda nake yace."Ranki ya dade dama kina nan."? murmushi nayi a nutse nace."Ina nan Yaya Aminu ya kake ya al'amura."? Yana min wani irin duba yace."Alhamdulillah wato dai ba zaki tambaye ni Iyali ba ko."?
Dariya na d'anyi nace."Yaya Aminu kenan to Ya Iyali." Cikin sigar tsokana nayi maganar ya amsa min da "Suna nan lafiya kalau kamar gaske.
Dariya nasa ina kallonsa shima sai yasa dariyar Gwaggo ta le'ko kanta da fad'in " Wannan kuma waye kike ta ya'ke masa baki."
Da Sauri nace."Yaya Aminu ne babban yaron Alhaji." "Au! koda naji." abinda ta fada kenan ta dauke kanta......Motar ya dafa cikin nutsuwa ya gaisheta ta amsa kamar bata so Ya mi'kawa Kawu Ibrahim hannu suka gaisa a mutunce, Ya dawo da hankalinsa kaina da fad'in "Tafiya zakuyi ne."? Nace." Eh wallahi."
Jim! yayi kamar da magana a bakinsa kawai ya basar yasa hannu cikin aljihu sabbin kudi ya dauko ya mi'ko min.
Nace."Dan Allah ka barshi." girgiza kansa yayi yace."Ki kar'ba mana ko katin waya kyasa ko." hannu biyu nasa na kar'ba da fad'in "Nagode Yaya Aminu Allah ya 'kara arziki.
A nutse ya amsa da ameeen to sai gani na biyu ko."? nace" Aikuwa dai tunda kai ganinka ha'bo ne baka zama a gari."
Yace."To ya za'ayi Sa'ida taurari na masu zagaye ne nima ba a san raina nake zurga zurga nan ba.
Nace."Hakane to Allah ya taimaka." Ya amsa da "ameeen tare da daga min hannu da sauri ya wuce cikin gidan......Ina shiga motar ta rufe ni da fad'a " Sa'ida wato kin mai damu marasa galihu ko kinga kudi duk kin gigice kin barmu zaune a mota to bari kiji wallahi komai abunki ba zaki sanjawa towo suna ba."
Uffan bance mata ba ta cigaba da sababi tana fadin" Yana fama da 'bakar fuska yazo ya tsayawa mutane to idan ma sonki yake sai dai yayi hakuri dan ba zaki aureshi ba ehe! ba naji ubansa na wata magana ba Kai Ibrahim kada ka kuskura ka tunkari Alhaji Nura da wata magana Sa'ida bata da miji sai Khalid da yardar Allah."
Nida Kawu Iro shiru mukayi mata uffan ba muce ba ta 'karaci surutan ta ta gaji tayi shuru tana gyangyadi. sai da muka isa gidan na tashe ta ta fito tana mita......Khalida dake can tsallaken gidansu Salim ya karaso gurin, hannunta ya ri'ke suka shiga gidan sai magana take masa 'kasa-'kasa...Yace." To shikkenan Gwaggo magana ta wuce zan fita daga harkarta. har daki ya kaita ya karkade mata shimfidarta ta kwanta tana mita wai kafafunta ciwo suke mata da sauri yace."Bari naje na siyo Roob sai na shafa miki a kafafun.
Yana kokarin fitowa daga dakin ni kuma ina 'kokarin shiga mukayi karo dauke kaina nayi tare da bashi hanyar wuce wa.....ba tare da ya kalleni ba ya fice daga gidan.
Tana mitar ciwon kafafu tana fama da redio sai shuuuuuu! takeyi ta'ki kamawa da alama batir din yayi sanyi, da 'kyar ta yunkura ta mi'ke tsaye da fad'in "Ai dole na fita na siyo batir." Da sauri na kalleta tana kokarin yafa mayafi nace."Gwaggo yau d'aya dai ai sai ki hakura kuma yanzu fa Khalid ya fita mai yasa bakice ya siyo miki batir din ba."
Tace."Sa'ida bana san takurawa Khalid bashi da kud'i shiyasa bance ya siyo min ba." Nace"Idan kika bashi kudinki zai siyo miki ba lallai sai da kud'insa ba.'' Girgiza kanta tayi tace."Bai zama lallai ya kar'ba." Nace." Ki daiyi hakuri da jin redion ki barwa gobe."
"Aa ba zan hakura da jin taskar labarai ba." Hanyar fita ta kama cike da mamaki na bita da kallo maganarta naji a tsakar gida tana fad'in "Eh fita zanyi na siyo batir na redio na yayi sanyi ta'ki kamawa."
Muryar Kawu naji yana fad'in "To koma ki huta bari naje na siyo miki.'' Tace." To yawwa Ibrahim nagode Allah yayi maka albarka."
Dakin ta dawo ta zauna tana dai sake mummurd'a redion sai shuuuuuu take amma taki hakura.
Khalid ya shigo dakin da sallama a bakinsa itace ta amsa masa dan ni ko inuwarsa ma ban kalla ba....ya mika mata batir din da fad'in "Gashi Baba yace a kawo miki." kar'ba tayi ta fara sawa a redion ya zauna kusa da ita tare da mi'kar mata da 'kafafunta a nutse ya bud'e Roob din ya fara shafa mata. addua ta shiga yi masa kafin naji sun fara magana 'kasa-'kasa 'karamin tsaki naja na fita daga d'akin buta na dauka na shiga band'aki ina jin takaicin abinda suke.
"Gwaggo na fad'a miki fa magana ta 'kare zan fita daga harkata amma kuma ba zan daina so da kaunarta ba wannan nasan a jinin jikina yake......Tace." Kuma ka kwantar da hankalinka idan ka koma makaranta kayi karatunka lafiya maganar Alhaji Nura Gaibu ce.
Murmushin takaici yayi yace."Gwaggo qaddara ma Akawai aure a tsakaninsu to ni kuma mutukar ina raye sai na hanata jin dad'in aure wallahi."
Shuru tayi ba tace masa komai ba ya mike da fad'in "Ni zan tafi kallon ball." tace."To dan Allah kada kayi dare." yana kokarin fita daga dakin yace."Da wuri zan shigo gida insha Allahu.
Ri'ke da buta na fito daga band'akin santsin ruwa dana takalmin 'kafata yayi yun'kurin kayar dani salati nasa nayi saurin ri'ke kyauran bandaki dik da haka sai da nayi zaman da'baro a gurin. 'Kuguna ya buge sosai na rintse ido ina kiran sunan Allah.
Gurin ya 'karaso kawai naga ya sunkuya yana kokarin dauka ta....duk yanda naso dana hanashi kasawa nayi saboda naji jiki sosai jikina sai kyarma yake......har bakin kofar dakin ya ajiye ni ba tare da yace min komai ba ya juya ya fita daga gidan.
Jiki a sanyaye na bishi da kallon mamaki!
To washe gari da safe kadaran kadahan muka tashi gaisuwa ce kawai ta had'ani da ita sai da na shirya tafiya makaranta nayi mata magana, tace."Ba zaki tsaya ki karya ba ga ruwan kunu na d'ora a wuta."
Nace."Gwaggo idan na tsaya karyawa zan makara zan samu wani abu naci a ofis." Tace."Ai ke idan ba dan kina da kurman jiki ba to da tuni kin zabge kiyi ta zama da yunwa ko damuwa bakya yi."
Murmushi kawai nayi na gyara jakata dake kafad'a nace"Sai na dawo." tace."Allah ya bada sa'a." na amsa da "ameeen." Ina kokarin fita yana kokarin shigowa dakin baya na koma na bashi hanya ina d'an satar kallonsa yana sanye da 'kananun kaya ya goya jaka a bayansa kafarsa sanye da boot ya taje tarin sumar kansa sai kamshin turare mai sanyi yake.....babu walwala a fuskarsa yace."Auntyna barka da asuba." Ba tare dana kalleshi ba nace."Barka kadai ka tashi lafiya."? a tsanake ya amsa yana kallona da fad'in "Zan koma skull yau." nace."Allah ya bada sa'a." da sauri na fice daga dakin dan bana son wata duguwar magana a tsakaninmu.
Gwaggo kamar za tayi kuka haka sukayi sallama ta rakashi har soro tana ta zabga masa addua.....a daidaita sahun Salim ya shiga yana daga mata hannu shima yasan zaiyi kewar kakar