Showing 66001 words to 69000 words out of 185789 words
kuma ba ta ta'ba cewa bata gamsuwa ba sai ke sarkin jaraba ko."
Hawaye suka zubo min nace." Alhaji wannan Wace irin magana ce ni kake kira da jarababbiya.''
Yace."To idan ba ita bace me yasa zaki sani a gaba kina min kuka okey kina so na jigata kaina a kanki ko? na yini a kasuwa ina nema da daddare sai na 'kare a gindin ki ko ? to ni ba haka nake ba idan nayi sau d'aya shikkenan na gamsu matata Murja bata da matsala dani .
Wani irin kallo nake masa ina mamakin maganganunsa wato dai Alhaji Nura yaudarata yayi Ashe bashi da mutunci dama."? Zuciya tace "Aa Sa'ida ke kika cutar da kanki yanzu da Khalid kika aura ai bakin ki alaikum zai cika miki mara ya dauke miki dukkanin bukatunki.
Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi ya juya min baya ya rufe jikinsa da bargo babu abinda ya dameshi baccin sa kawai yake.
A tsananin bukace na matsa kusa dashi ina dan shafa jikinsa, ya juyo da saurin gaske ya ture ni da fad'in " Sa'ida bafa ki isa kisa nayi abinda banyi niyya ba ni na gaji ki kyale ni nayi bacci na huta gajiya."
Sakato nayi da baki ina kallonsa yaja tsaki mai karfi ya koma ya kwanta.
Shuru nayi a zaune a gadon ina sa'kawa da kwancewa, nafi karfin rabin a wa a zaune ina tunani shin ya za'ayi na warware wannan gagarimar matsalar da nake fuskanta. Hakuri kawai na bawa kaina na cire abin daga raina na mike da mataccen jiki na shiga bandaki na tsarkake kaina har na fito daga toilet din gabana bai daina tsut-tsut ba babu shakka har yanzu gurin bai daina bukatar a gaji ba.
Ban kwanta kusa dashi ba sai na dauki fillo na ajiye kasan kafet na kwanta na takure jikina cikin hijab ina addua akan Allah yasa bacci ya dauke ni......Cikin ikon Allah kuwa bacci mai nauyin gaske ya dauke ni.
Sai wajejen shida na safe na tashi, lokacin shi tuni ya fice daga dakin na dinga mamakin yanda akayi bai tashe ni nayi sallah ba. a sanyaye na mike na shiga bandaki wanka nayi a gurguje na daura alwala na fito sai da nayi sallah tukkuna na shirya jikina gabad'aya auran Alhaji Nura ya fice min daga raina, gefan gado na zauna na kunna waya ta ina dube dube so nake na kira k'awata Hauwwa na fada mata halin da nake ciki ko da akwai shawarar da zata bani....Ina kokarin kiran wayar ta Khalid ya kira babu kwari na daga wayar gami da sawa kunnena.
"Auntyna kin tashi lafiya." A sanyaye nace."Lafiya Khalid." Yace."Ya na jiki wani iri ko baki da lafiya ne."? 'Kwallah ce take kokarin zubo min na daure nace."Lafiya ta lau." Yace."Okey ki bawa Gwaggo mu gaisa a gurguje zan fita gurin wasa ne." Nace."Khalid Gwaggo tana bacci." Jim yayi kafin yace." Tunda nake banta'ba ganin Gwaggo na bacci da safe ba a daidai wannan lokacin take zaman kad'i tana sauraran redio aunt Sa'ida ko dai da akwai abinda kike 'boye min."?
Nace."Khalid Gwaggo ba ta jin dadi ne shiyasa tana karya kummalo tasha magani ta kwanta bacci ya dauketa." Cikin jimami yace."Allah sarki Gwaggo ki gaishe min da ita idan mun fito daga wasa zan sake kira." Nace."Tom shikkenan." Kokarin kashe wayar nake ya shigo dakin cikin dakakkiyar shaddar galila kamshin turaransa ya game ko'ina har ya karaso inda nake ban dauke idona daga kansa ba cikin zuciyata nace"A zahiri cikakken mutum amma a bad'ini malalaci ne.
Gaishe shi nayi ba tare dana kalleshi ba, ya amsa yana duba agogon hannunsa da fad'in "Dawa kike waya ne."? Gabana ne ya fad'i ! nace" Khalid ne."? Jim! yayi yana kallona da fad'in "Menene zai kira ki da sassafe haka."? Nace." Wai yana so su gaisa da Gwaggo ne." Yace."Ita Gwaggon bata da waya."? kaina na daga masa.
Ya wani 'bata rai da fad'in "Kada ki kuskura ki sake d'aga wayarsa a cikin gidana." Kai tsaye nace "Sabida me."? yace." Tambaya ta kike."? na kalleshi ido cikin ido nace."Eh." girgiza kansa yayi yace."Yaron nan fa nasan mun had'a takara dashi gurin neman auranki to mai zai sanya na zuba ido na barki kina mu'amula dashi."
Cikin takaici Nace."Alhaji da kuka had'a takara da Khalid wa na za'ba a cikin ku."? 'Kirjinsa ya nuna da hannu da fad'in "Ni kika za'ba."
Nace."To meye naka na kishi da damuwa Khalid dan uwana ne na jini ba zaka rabamu ba."
Rai a 'bace yace."Yanzu dai nasan kin san da cewa a karkashina kike ko."? Nace."Eh yace."To idan na isa kada ki sake daga wayar yaron nan." cike da d'umbin mamaki nake kallonsa. ya girgiza kansa da fad'in "Ni zan tafi kasuwa." shuru nai masa. yayi murmushi wanda shi kadai yasan manufarsa ya kama hanya ya fita daga dakin ya barni cikin d'umbun mamakin sa.
Bayan fitar sa na jima
ina sa'ke-sa'ke kafin na yanke shawarar kiran Hauwwa a waya idan da hali tazo mu tattauna domin a gaskiya ina bukatar mai bani shawara akan wannan gagarimar matsalar
Jin yanda nake magana a sanyaye yasa itama tasha jinin jikinta tace."Sa'ida lafiyarki kalau kuwa.'' Nace."Hauwwa lafiya ba lafiya ba dan Allah idan an tashi kizo zamuyi magana."
Tace."Sa'ida kina ganin babu matsala ko? bana so ina zuwa gidan mata biyu gudun zargi kin san dai yanda rayuwar nan take wata matsalar tana iya faruwa ace ni ce''
Nace."Haba Hauwwa wace irin magana ce wannan me zai faru da har sunanki zai fito dan Allah kizo babu damuwa Aunty Murja tana da saukin kai.
Tace."To shikkenan idan an tashi zan shigo." nace."Okey to ina sauraranki."
Kashe wayar nayi na ajiyeta kan mirror na futa falon, shuru babu kowa da alama yaran sun tafi makaranta tunda litinin ce. gurin cin abinci na nufa naja kujera na zauna wato dai nice bare a gidan nice wacce bata da mutunci da galihu ban isa a zauna tare dani a ciki abinci ba tabbas badan kada na cutar da kaina da yunwa ba to da babu abinda zai sanya na zauna naci abincin gidan amma babu komai karshen wata na dauki albashina zan sayi komai nawa na dinga ciyar da kaina wannan shawarar na yanke a cikin raina.
To har na gama breakfast din Aunty Murja bata sauko ba sai kawai na yanke shawarar hawa saman na gaisheta.
Na jima a bakin kofar ina knocking kafin naji motsinta ta bude kofar dakin muka had'a ido da juna.
Fuskarta a sake tace."Aa Sa'ida kece ashe shigo mana." Kasa shiga nayi sabida nauyi tana sanye da wani gajeran wando da riga mai kamar breziya da madauri a wuya nonowanta duk a waje bayan ta ma haka.
Na tsaya daga bakin kofar da fadin"Dama naji shuru baki sauko ba nace bari nazo mu gaisa." Murmushi tayi tace."Kin ga ni wallahi tunda nasha maganin mura ya kashe min jiki nake ta bacci mijinki ma ban san lokacin daya fita ba."
Nace."Ayya sannu Allah ya sawa'ke." ta amsa da "ameeen da fad'in " Ki shigo mana." cikin ya'ke nace"Aa aunty zanje nayi ayyuka a dakina ne anjima idan na gama sai nazo muyi hira."
Tace."Tom shikkenan babu damuwa." sallama nayi mata na sauka ina kokarin shiga dakina naji sallama da sauri na juya domin na dauka Hauwwa ce. wata hamsha'kiyar mata ce taci kwalliya har ta gaji kana kallonta kasan naira ta zauna..
Nace"Sannu da zuwa hajiya." ta amsa fuska a sake tana min wani irin kallo kafin tace."Kece amaryar Murja ko.''? nace."Eh nice amma ke d'in 'yar uwarta ce ko dan naga kuna kama."
'Yar dariya tayi tace"Haka mutane suke fada Aa Murja ba 'yar uwata bace ta jini 'Kawata ce dai." Nace."Ayya sannu da zuwa tana sama sai ki hau ki sameta."
Tace."Okey babu damuwa.'' Juyawa nayi domin bude dakina naga ta bini da kallo tana murmushi, al'amarin ya dinga bani mamaki! irin murmushin da Aunt Murja takeyi min matar ma irinsa take........Gefen gado na zauna abun na cigaba daure min kai.
'Karfe biyu shaura Hauwwa ta karaso gidan, bayan mun gaisa ta dinga bina da kallo tana girgiza kanta kafin tace."Sa'ida kwana biyu kacal naga duk kin sanja kin wani hargitse dan Allah me yake damunki.'?
Ajiyar zuciya na sauke nace."Hauwwa matsala mai girma nake fuskata a gidan nan." Zama ta gyara tana kallona, idanuwa na suka ciko da ruwan hawaye na shiga bata labarin abunda ke faruwa.
Kanta kawai take girgizawa kafin tace." *AI GA IRINTA NAN!* Sa'ida babu irin shawarar da ban baki ba akan mutumin nan kika rufe idonki kika aureshi gashinan kwana biyu kacal ya nuna miki akuyanci me ake da auran irinsu Alhaji Nura kayan ba'kin ciki da takaici ai wallahi gwara na auri 'karamin yaro na raine shi nasan komai rintsi ni zan mora amma duba dan Allah kwana biyu da yin aure kin zama tamkar wata zautacciya."
Nace."Hauwwa dan Allah ki bar wannan maganar Alhaji Nura fa lafiyarsa lau tsabar iskanci ne da wulakanci yasa yake min haka tunda ai na fad'a miki hujjarsa ta 'kin sakin jiki dani saboda kada na haihu bayan sun tsara rayuwarsu shi da matarsa."
Tsaki taja tace."Eh ai na fahimta mayaudarin banza da wofi kawai to ke yanzu wace shawara kika yankewa kanki ko kina nufin a haka zaki cigaba da zama da sha'awa."
Nace."Shine ai na kira ki domin ki bani shawara."
Shuru tayi na minti biyu kafin tace." Sa'ida ki rabu da mutumin nan shine alkairi a gare ki ni dai wannan shawarar ita zan baki."
Gabana na wani irin fad'uwa nace."Hauwwa wace irin magana ce wannan? aure kwana biyu ki fadi irin wannan maganar gaskiya bata dace ba ki bani shawarar arziki mana."
Dariya tayi tace."Duk wata shawarar da zan baki bayan wannan take wallahi idan kika cigaba da zama da mutumin nan zuciyarki sai ta buga irinsu suna nan da yawa masu kashe matansu da bakin cikin su."
Shiru nayi ina kallonta tace."Idan kuma kinga ba zaki rabu dashi ba to sai ki dauki tsatstsauran mataki a duk lokacin daya kusance ki sai ki hana shi tunda zalinci baya barin sa ya biya miki bukatar ki."
Nace."To kinga wannan shawarar ita zan duba a cikin shawarwarin ki amma maganar kashe aure sam bata taso ba."
Tace."Tom shikkenan sai ki kwada ki gani mybe idan kikayi masa butsu ta wannan hanyar zai dinga dogon zango a kanki tunda kin ce lafiyarsa lau ba rashin kuzari bane wulakanci ne irin nasa.
Murmushi nayi nace."Hakane Hauwwa Alhaji Nura ragal yake kawai 'keta ce nima kuwa zan gwada masa tawa." Dariya tasa ta bani hannu muka tafa.
Sai da tayi sallah la'asar muka ci abinci sannan tayi shirin tafiya, tare muka fito falo wanda yayi daidai da saukowarsu daga sama.
Nace."Hauwwa ki tsaya ku gaisa da aunt Murja ko." Tace."Okey babu damuwa.
Muna tsaye suka 'karaso dukkaninsu fuskarsu a sake da walwala aunty Murja tace."Ashe kema bakuwa kikayi.''? Nace."Eh wallahi 'kawata ce Hauwwa gurin aikin mu daya."
Tace."Ayya Sannu.'' Hauwa ta amsa da "yawwa aunty ya gida ya yara."? tace."Alhamdulillahi." Hajiya Aziza na murmushi tace."Ai sai muje na rage miki hanya ko."?
Hauwwa tace."Nagoda hajiya amma nima ina da abin hawa.'' Tace."Okey to babu damuwa sai mu fita tare ko." Tace."Eh hakan yayi.'' Ta kalleni da fad'in "Sa'ida sai munyi waya kenan amma yaushe zaki koma gurin aiki."? Nace." Insha Allahu sati na sama." tace."Tom shikkenan Allah ya bamu alkairi." Nace."Ameeen ya Allah nagode k'awata." Aunt Murja tace."Muje mu taka musu." bayansu muka bi kowacce ta shiga motar ta suka fita daga gidan muna daga musu hannu da fatan alkairi.
Tare muka koma gidan ita ta hau sama ni kuma na bude dakina na shiga ina tunanin shawarar da na yanke akan abinda yake faruwa.
To yau ma dai ban san lokacin da ya dawo ba sai da na fito falo na same shi a zaune suna hira da ita ga yaran su suna wasa, tsabar haushi da takaici ya hana ni kulashi ballantana nai masa sannu da zuwa.
Gurin cin abinci na zauna naci na koshi na bar gurin ita kanta aunty Murjan haushinta nake ji sabida na gane itama fuska biyu gareta.
Sai da bacci ya soma daukata ya shigo dakin, na dinga kallonsa ina daga kwance har ya gama shirye shiryen sa yazo ya tsaya a kaina....."Sa'ida wacece tazo d'azu."? tambayar da yayi min kenan....Na mike zaune ina kallonsa ya sake maimaimata maganarsa." Wacece tazo gurin ki d'azu."? Nace."Kai waye ya fad'a maka wata tazo."? a fusace! ya daga min hannu da fad'in "Wace irin magana ce wannan a maimakon ki bani amsar tambayata sai kuma ki tambaye ni..
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
Nace."Hauwwa wai ko son yaron nan kike ne." ? tasa dariya da fad'in "Ai abun so ne yaro ingarma namiji mai 'kwazo ai wallahi ni idan na sameshi to bakina alaikum."
Na dinga kallonta ina mamakin maganarta ita kuma sai kyalkyala dariya take tana 'kara tabbatar min da gaskiyar maganarta...
*Littafin na kudi ne....kada ki saya ki fita dashi, idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing idan kika karanta baki biya ba ina bin ki bashi.....'yar uwa idan kina so ki biya ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal gruop#300...account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE**SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna min????*_
*45&46*
Raina ne ya 'baci ganin yanda yake daga murya sama kamar zai doke ni nace."Kayi hakuri dan Allah ni banga abin daukar zafi ba idan kana so kasan wacce tazo guri na sai kaje ka tambayi wacce ta fada maka cewa yau nayi bakuwa."
Wani irin kallo yake min yana girgiza kansa yace."Sa'ida ashe baki da kunya dama? ni kike fadawa wannan maganar?
Hawaye na share nace."Alhaji wace magana na fada maka mai zafi! al'amarin ne ai ya bani mamaki kuma banta'ba tsammanin aunty Murja fuska biyu gare ta ba."
Yace."Okey yanzu mai kike nufi."? kai tsaye nace."Ina nufin abubuwa da yawa." Girgiza kansa yayi kafin yace."Ni ban hana wani naki yazo gidan nan ba kawai dai sintiri ne bana so inace duka-duka yau kwanan ki biyu da tarewa a gidan nan mai zai sanya a fara yi min sallama a gida.
Fuskata na goge nace."Babu wanda zan hana shi zuwa cikin gidan nan tunda dai kasan ina da jama'a bayan haka kuma ina da 'yan uwa da dangi masu yawa saboda haka ni dik wanda yazo gurina ina maraba dashi."
Rai a 'bace yace."Ni kike d'aga wa murya ko."? shuru nayi yace."To bari ki ji abinda baki sani ba Murja da kike gani ta fiki 'yan uwa da dangi da jama'a amma saboda tana bukatar zaman lafiya dani tabi doka ta a kan dauki dogon lokacin kafin kiga wani dan uwanta a cikin gidan nan saboda haka kema yana da kyau ki kiyaye.
Nace." 'Karya take aunt Murjan." cike da mamaki yake kallona.
Na cigaba da cewa" D'azu itama ai tayi bak'uwa mai yasa bata fada maka ba saboda ita ta cika munafukace magulmaciya."
"Murjar kike kira da wannan sunaye." ? a hasale nace."Eh ita din fa ai ta amsa duka sunayen."
Rai a 'bace ya juya ya fita daga dakin. tsaki naja mai karfi da fadin"Mijin tace kawai."
Koda ya fita daga dakin kai tsaye bene ya hau ya sameta a kwance da wayarta a hannunta tana latsawa, ganin shigowarsa yasa tayi saurin kashe wayar ta ajiyeta ta mike zaune tana kallonsa.
Zama yayi kusa da ita rai a dagule! ta dafa kafadarsa da fadin "Abban Yusura ya akayi ne naga ka shigo fuska a 'bace."
Ajiyar zuciya ya sauke yace."Murja na lura yarinyar nan Sa'ida bata shigo gidan nan da sigar son zaman lafiya ba kamar ni zata tsaya tana jayayya dani akan hukuncin dana yanke a gidana saboda na kawo mata misali dake shine take zagin ki."
Murmushi tayi alamun abun bai mata ciwo ba tace."Sai hakuri Abban Yusura kasan ko wace mace da irin halinta wallahi nima yau haka ta yini tana yar min da habaici ban san meye dalili ba amma dai ka cigaba da hakuri da halinta.''
Yace."Ai kuwa zata gane kuskuranta Murja babu wata mace da zan aura ta taka martabarki ban nuna mata kuskuranta ba saboda haka na bar dakinta har sai na koya mata hankali."
Murmushin samun nasara tayi tace."Haba Abban Yusura kayi hakuri dan Allah ka koma dakin kaga amarya ce ka cigaba da rarrashinta.
Hannu ya daga mata yace."Murja kin san bana magana biyu ko saboda haka ki bar maganar kawai ni nake auran Sa'ida ba ita ke aurena ba dan haka zan nuna mata cewa ni cikakken namiji ne."
Tace."To shikkenan tunda kace haka sai dai nace Allah ya kyauta ya rufa asiri." shuru yayi bai amsa ba ya nata wani muzurai kamar gaske.
Nayi ta tsammanin dawowarsa dakin naji shuru cikin takaici da