Showing 132001 words to 135000 words out of 185789 words
fada hakane bani da wanda zan kaiwa matsalata ya saurare ni sai ke da kika haife ni To inaso na sanar miki da cewa tsayin watannin aurena da Yaya Aminu wata mu'amular aure bata ta'ba shiga tsakani na dashi ba gabadaya bashi da kuzari bashi da girma irin na maza haka nake zaman hakuri har aka kawo wannan lokacin da na kasa hakuri nazo na sheda muku koda taimakon da zakuyi a matsayin ku na iyayenmu tunda nima nayi iyakacin bakin kokari na akan matsalar."
Ido ta tsira min tana girgiza kanta daka ganin yanayin ta al'amarin ya bata mamaki! "Sa'ida yanzu tsayin wata hudu da kwanakin auranku babu wata mu'amula ashe."?
Kaina na daga mata hawaye na kokarin kwace min." Tace."Amma al'amarin ya bani mamaki mutuka kuma babu kama ko kad'an to shin me yake damun wannan yaron haka."?
Nace."Wallahi nima ban sani ba gashi baya son shan magani dan har zuwa nayi gidan Gwaggo Uwale taje can kauyen daburau ta samo masa magani amma sau uku kacal yasha yace a zubar dashi ba zai kara amfani dashi ba."
Ummu Habiba tace."Ai to hakan ba zata yiwu ba dole ya nemi magani domun rayuwa ba zata ta'ba tafiya a hakaba wace macace zata zauna dashi a haka babu shakka dole yau mahaifinsa yasan halin da ake ciki domin yasan matakin da zai dauka.
Nace."Ummu ni wallahi da Ya bani hadin kai a gida babu wanda zaiji ko ya gani tunda dai wannan maganar ta sirri ce be kamata a fad'a ba amma duk kokari na akan hakan be samu ba gabadaya ma yanda na fahimce shi matsalar bata damunsa."
Ummu tayi shuru tana nazari kafin tace."Ko shiyasa ya'ki aure ne saboda yasan bashi da lafiya." Nace."To ina jin dai hakane manufarsa." tace."To ai shikkenan Allah yayi mana magani kuma naji dadi da baki rufe maganar ba kika fito kika fad'a domin a san matakin dauka saboda haka kada ki damu insha yau idan Alhaji ya dawo zan isar masa da maganar." Ajiyar zuciya na sauke da fadi."To shikkenan Umma Allah yayi mana magani." ta amsa da "Ameeen Ya Allah."
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*84&85*
Koda Alhaji Shamsu ya samu labarin abinda yake faruwa sai ya rasa bakin magana yayi shuru yana mamakin al'amarin da kyar ya iya d'aga kansa ya kalli inda nake zaune kaina a kasa yace."Sa'ida ina neman gafara a gurinki a bisa wannan al'amari da ya faru wallahi dana san yaron nan yana da matsala da ban tilasta ki auransa ba ni duk abinda yake faruwa ban sani ba bani da labari shi bai fada min ba kuma mahaifiyarsa ma haka saboda haka kiyi hakuri da wannan al'amari nasan anyi miki laifi amma mutukar al'amarin nan ya zama da akwai cutuwa a ciki to zan sanya Aminu ya sawwake miki sai kiyi auran da hankalin ki zai kwanta."
Umma Habiba ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye tace."A'a Alhaji ba za'ayi gaggawar yanke hukuncin rabuwa ba kamata yayi shi Aminun ya nemi magani domin a duniya babu cutar da bata da magani amma kada kace zaka raba auran."
Yace."Habiba yaron nan ya bani mamaki mutuka wato ashe yasan yana da dauke da lalura irin wannan amma bai ta'ba zama tare dani munyi maganar ba to Habiba ta yaya za'ayi rayuwar aure babu wannan mu'amular akwai cutuwa a ciki dole a raba auran.
Murya na rawa nace."Aa Alhaji ka dai kira shi kayi masa magana ya mayar da hankalinsa gurin neman lafiyarsa nima bana so a kashe min aurena ina tausaya masa halin da yake ciki.
Kallona yayi yana girgiza kansa yace."Sa'ida hakika ke 'yar halak ce kuma hakika ke din matar rufin asiri ce duk namijin da yayi dace da samun mace kamar ki ya samu jin dadin duniya ina rokon Allah yayi miki albarka ya azurtaki da 'ya'ya masu albarka kuma insha Allahu kamar yanda kika bukata cewa ba kya so a raba auranki da Aminu to bazan raba ba amma dole duk inda magani yake yaje ya nema kuma yatsa tsayin daka gurin amfani dashi."
Umma Habiba tace."Eh dama hakan shine maslaha a tsakaninsu Ubangiji Allah ya bashi lafiya kamar ko wane da namiji." Cikin alhini da damuwa ya amsa da ameeen ya Allah."
Tunda na shiga motar naga fuskarsa kamar hadari nasha jinin jikina, a sanyaye nace."Yaya Aminu ya kasuwa da Jama'a."? Shuru yayi min a zafafe yaja motar muka bar gurin.
Sunkuyar da kaina nayi gabana na fad'uwa! wato saboda mahaifinsa yayi masa fad'an gaskiya yake jin haushi na akan gaskiya ni ina ganin idan da mutunci ban cancanci wannan sakamakon daga gurinsa ba tunda duk abinda nake saboda da lafiyarsa nake babu laifi domin iyayensa sun san halin da yake ciki.
A haka muka isa gida kamar kurame! yana gama parking ya bude motar da sauri ya fita barni a ciki....Na jima ina mamakin al'amarin kafin na fito da sanyayyan jiki nabi bayanshi.
Kasa shiga dakina nayi na yanke shawarar bin sa dakinsa, tsaye na sameshi da towel a jikinsa wanka zai shiga sai kawai ya daga min hannu a fusace yace."Ki fita ki bani guri bana bukatar ganin ki a dakina tunda dai ke kin kasance mace mara sirri."
A sanyaye nace."Yaya Aminu kada kayi min mummunar fahimta dan Allah ka tsaya ka fahimce ni."
"Sa'ida babu wata fahimta da zanyi miki nagode da abinda kikayi min."
Rai a 'bace nace." Yaya Aminu laifi ne dan mahaifinka yasan lalurarka kada fa ka manta shine silar samuwar ka a duniya me yasa kake 'bacin rai akan yaji matsalarka."
"Ki rufe min baki munufaka kawai tunda nake ban ta'ba samun sa'bani da mahaifina ba sai ta dalilin ki dama bani nace ina sonki ba tilas ta min akayi idan kika takura min zan iya sawak'e miki babu lallai babu dole."
Wani irin gumi ne ya shiga yanko min na dinga kallonsa ina mamakin furucinsa ashe dama alkairi yana zama sharri! ban ta'ba tsammanin shima yana da mugun hali ba sai yau.
"Yaya Aminu na fahimci kai baka san abinda ya dace ba kuma kana da son kanka da yawa a wannan rayuwar da kake ciki duk kudin ka da kima da mu'kamin ka wace macace kake tsammanin zata zauna da kai da mugun halinka da lalurarka to gaskiya ni na gaji da wannan masifar taka nima zaman hakuri nake idan rabuwar itace alkairi meye a ciki."
"Kada dai kice zaki zage ni ranki zai mummunan baci yanzu yanzu." Cikin fushi yayi maganar, hawaye na share na juya da sauri na fita daga dakin ba'kin ciki kamar ya dagargaza min zuciyata.
Yau kusan kwana goma kenan baya yi min magana ko gaishe shi nayi baya amsawa abinci kuwa idan na ajiye haka nake dauke abuna daga ya dawo daga kasuwa zai shiga daki ya kulle kansa sai dai kuma na fahimci yana shan magani amma na asibiti ne sabida nagansu akan drowar d'akin shi.
Gajiya nayi da zaman gabar na sameshi a d'akinsa yana shirya kudi a cikin akwati na samu kujera na zauna a nutse nace."Yaya Aminu barka da asubah."
Shuru yayi min bai amsa ba, nace."Kayi hakuri dan Allah babu kyau gaba gashi Azimi zamu shiga idan muka cigaba da irin wannan zaman to ibadar mu za tayi rauni Allah da mala'iku zasuyi fushi damu saboda haka naji ni mai laifi ce a gurina kayi hakuri ka yafe min."
Kallona yayi babu sassauci a tare dashi yace."Wallahi kada ki kuskura ki sake fita da sirrin gidana ban amince kowa sake jin matsala ta ba cikin kuwa harda iyayen da suka haife ni bana bukatar suji idan zaki zauna dani a haka ki zauna idan ba zaki zauna ba ga hanya nan a bude."
Hak'ika
Bai ta'ba 'bata min rai irin yau ba sai kawai na mike tsaye rai a bace nace."To sai me? babu d'a babu jika zaman me zanyi dole ne? kabar ganin kana da kud'i to ni ba sune a gabana ba kwanciyar hankali ce a gabana kudin ka na banza ne domin basa gabana zan tafi inda nafi wayo sai ka biyo ni da takarda sai me? idan mun rabu kanka kayi wa." Ina k'are maganata na juya da sauri zan fita daga dakin. tare hanya yayi fuska a tur'bu ne yace."Ni kike d'agawa murya Sa'ida."? Murya na rawa nace."Yaya Aminu duk abinda nayi maka kaina ka janyo mai yasa ba zaka tsaya mu fahimci juna ba? me yasa ba zaka tsaya mu kashe matsalar mu ba duk fa abinda nake saboda da kai nake amma saboda gadara! ka dinga fad'a min dik maganar da ranka yake so to shikkenan na hakura da zama da kai babu lallai babu dole a rayuwar aure."
Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ke da kan ki kikayi wa mahaifina al'kawari cewa zaki cigaba da zama dani da lalura ta me yasa kuma yanzu kike wannan maganar." Dauke kaina nayi nace."Ai kai ne naji kana wata magana wacce bata dace ba shiyasa na nuna maka cewar idan mun rabu d'in bawai zan tagayyara bane watakila ma Allah yayi min kyakykyawan sakamako." Yace."To duk dai magana ta wuce magani dai naje asibiti sun bani gashi can ma ina kan amfani dashi insha Allahu za'a a dace kiyi hakuri raina ne ya 'baci."
Ajiyar zuciya na sauke tare da ratse shi na wuce na barshi a tsaye a gurin gabadaya al'amarinsa ya fice min daga rai.
Saura kwana uku a dauki Azimi Yaya Aminu ya k'are shan maganin asibitin da yake amfani dashi ganin bashi da niyyar komawa asibitin sai na yanke shawarar yi masa magana sai kawai yace dani ranar litinin zai koma asibitin nace.''To amma dai kana gananin sauyi ko."? shuru yayi min sai da na sake magana yace."Ni babu wani sauyi da nake gani kullum jiya i yau." Wani k'aton abu ya tokare min a kirji Nace."To ai sai kayi musu bayani idan kaje ko kuma kawai kayi na hausa shine daidai." girgiza kansa yayi yace."Aa ni duk magungunan hausan nan ban yarda dasu ba zan dai cigaba da neman maganin asibitin.'' Fita nayi daga dakin ba tare da na sake masa magana ba Yaya Aminu mugun d'an taurin kai ne wannan lalurar tashi dole sai an hada da maganin gargajiya sam na bature ba zaiyi ba amma ya'ki amincewa.
Kwanciya nayi da waya ta a hannuna cikin rashin zuciya na sake nemo number yaron so kawai nake naji muryarsa ko naji sanyi a cikin raina haka kawai kwana biyu yaron ya tsaya min a raina yanzu gabad'aya hankalina na kansa ina ganin a gurinsa kad'ai zan iya samun abinda nake bukata.
Wayar ce ta katse bai dauka sai na rubuta masa text hade da magiyar ya daga waya ta......Ina kokarin sake kiransa sai ya kira, hannuna na karkarwa na daga wayar tare da sata a kunnena murya na rawa na kira sunansa.
A dakile yace."Ya akayi ne matar manya kwana biyu kina ta kiran waya ban amsa ba wai shin ma a ina kika samu number na."
Ajiyar zuciya na sauke nace."Khalid ni kake wulakantawa ko."? Girgiza kansa yayi yace."Haba dai big aunty ai ke kinfi karfin wulakanci a gurina lokacin da kike kiran waya ina busy ne shiyasa ya kike ya maigidanki ina fatan kuna lafiya.''?
A sanyaye nace."Kowa lafiya Khalid.'' Yace."To Alhamdulillah ina fata dai lafiya ko."? shuru nayi ina nazari akan maganar dake raina.
"Auntyna ke nake saurare fa." A sanyaye nace."Khalid ina alkawarin mu."? kai tsaye yace."Wane alkawari kuma."? shuru nayi na minti biyu kafin nace."Maganar magani mana ina so ka bani number mai maganin zamuyi magana dashi tunda naji kace maganinsa yana da kyau."
'Yar dariya yayi yace."Auntyna ni da bana najeria ina zan samu number wani mai magani kina nufin har yanzu a cikin matsala kike."?
Kwanciya na gyara a gadon nace."Eh har yanzu a cikin matsalar muke muna ta maganin asibiti amma ya'ki yi."
Shuru yayi na minti biyu kafin yace."Aunty Sa'ida wannan sokon mijin naki ki rabu dashi ba namiji bane mace sunan shi zaman me kike a gidanshi kina k'waruwa." Kawai sai na tsinci kaina da fad'in."Khalid kana so ayi ta lissafa min aure ko? ko kuma kai zaka aure ni."?
Miskilin murmushi yayi yace."Aa ai ni kinfi karfina aunt 'Kashin ki bana yara bane na manya ne ni ba zan aure ki amma nasan kina rabuwa da wannan shashashan zaki samu wanda zai auranki."
Shuru nayi ina nazarin maganarsa nasan magana yake fada min cikin magana amma ni yanzu idan Allah ya kaddara rabuwa ta da Yaya Aminu me zan kuma ci da auran irinsu Alhaji Nura babu dadi Shima Yaya Aminun babu dadi sai takaici da bakin ciki yaro k'arami zan aura na more rayuwata.
"Auntyna zan kashe waya ina da uziri." maganarshi ta katse min tunanin da nake na sauke masa wata zazzafar ajiyar zuciya a kunnansa........a kid'ime! yace."Wai me yake damunki ne magana d'aya biyu sai ki sauke ajiyar zuciya da nishi! ko mijin naki yana kusa dake ne."?
Murmushin takaici nayi nace."Kaga bana son rashin kunya Khalid." Ta'be bakinsa yayi yace."To shikkenan ni zan kashe waya ta." Da sauri nace."Kada ka kashe muyi hira ka d'ebe min kewa." Al'amarin ya dinga bashi mamaki da al'ajabi yau auntynsa ce ke muradin jin muryarsa lallai ta gane mahimancin sa.
"Babu kyau abinda za muyi a yanzu ni dake idan muka tsananta zamu shiga fushin ubangiji nasan kin sani amma kuma saboda tsabar son zuciya kina take gaskiya to ni na tuba nabi Allah da manzo ba zaki sani na sa'bawa Allah ba."
Kafin nayi wata magana ya kashe wayarsa, zaune na miqe ina duba wayar kamar me neman wani abu gabad'aya jikina yayi sanyi da al'amarin na kuma san abinda nake aikatawa haramun ne amma son zuciya da sharrin shed'an na nema yasa na kauce hanya. hawaye masu zafi na share ina girgiza kaina tabbas ba kowa ne ya janyo min wannan bala'in ba sai Yaya Aminu da ina samun biyan bukatata a gurinsa nasan da babu abinda zan nema a gurin yaron ballanatana ya fada min maganar da zuciyata zata yi zafi. ko da yake duk abinda ya fada gaskiya ne babu karya nice idona ya rufe na kasa gane daidai da rashin daidai.......
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*86&87*
A daran na jima ina mur'kususu da birgima a gadon kafin wani wahalallan bacci ya d'auke ni mai cike da mafarkai barkatai marasa dadi dasa damuwa, ban tashi da wuri ba saboda yanayin yanda jikina ya saki kasala da rashin kuzari duk sun dabaibaye ni wanka nayi na dauro alwala na fito sai da nayi sallah tukkuna a gurguje na shirya jikina na fita falon nasan yanzu watakila ya shirya domin fita kasuwa gashi ban shirya komai ba.
Ina kokarin shiga dakin nasa ya fito cikin shirin fita gefe na matsa ina d'an satar kallonsa Yaya Aminu cikakken namiji ne a zahiri duk mace zata so ace tana da miji kamarsa wannan lalurar tasa itace kawai tayi masa cikas amma duk inda ake neman cikakken namiji Yaya Aminu ya kai ya cika.
Kallona yayi yana gyara agogon hannunsa yace."Ina fata dai lafiya ko."? A kasalance na kalleshi da fadin."Lafiya lau me ka gani kake wannan tambayar." yana kokarin zuwa gurin cin abinci yace."Naga idanuwanki sunyi jawur ne."
Murmushin takaici nayi nace."Rashin bacci ne." tsayuwa yayi yana kallona da fadin."Me yasa bakya samun bacci." Girgiza kaina kawai nayi nace."Mu bar maganar domin tayar da ita zai janyo mana bacin rai." Jim yayi na minti biyu kafin yace."To Allah ya kyauta zo ki had'a min abinci zan fita."
"Wallahi yanzu zan shiga kicin din yau na makara.'' Wani irin kallo yayi min. na sunkuyar da kaina a kasa nace." Kayi hakuri dan Allah ka zauna yanzu sai nayi maka indomee da 'kwai."
Yace."Tunda kike dani kin ta'ba ganin naci indomee."? girgiza kaina nayi yace."To kada ki wahalar da kanki tunda kin fiso naci abincin kasuwa shikkenan."
Nace."Yaya Aminu tunda ka aure ni yau ne kawai aka ta'ba samun matsala kada kaji haushi kayi min uziri mana." Yace."Nayi miki uziri gobe ma ki sake bari na na fita da yunwa." yana gama maganarsa ya wuce ya barni a gurin. har ya fita ban dauke kaina daga bakin kofar ba mamaki sosai nake da al'amarinsa sam bai da wani uziri idan ba nasa ba bashi da adalci ko kad'an duk hidimar da nake masa rana d'aya nayi kuskure sai yaji haushi ya fad'a min bakar magana.