Showing 87001 words to 90000 words out of 185789 words
alkairi."
Gwaggo tace."Ni dai baki ji nace komai ba akan maganar ko."? Nace."Eh banji ta bakin ki ba Uwale naji dama tunda naga tana kallona nasan da magana a bakinta.
Tace."Ke kin ga Sa'ida da girma na da komai ba zaki tsaya a kaina kina gaya min maganar banza ba tun kafin a haifeki nasan Allah da ma'aiki kuma aljanna dai babu wanda yake da tabbacin samunta kowa hasashe yake saboda haka wannan wa'azin ya isa haka."
Murmushin takaici nayi na shiga dakin ina fad'in "Uwale gaskiya daci gare ta shiyasa kike ganin kamar inayi miki rashin kunya to tunda abin hakane ke kadai zakiyi yawon malamanki amma kada ki sake zuwa kija Gwaggo ki kyaleta taji da abinda yake gabanta."
Gwaggo tace."Ke bana son rashin kunya ya isa haka.'' Uwale na 'yar dariyar dubura tace."Aa Gwaggo ki kyale ja'ira ta cigaba da fad'a min magana yanda ranta yake so."
Gwaggo tace."Uwale kiyi hakuri dan Allah kin san halin d'an yau ba'a iya masa duk abinda mutumin da zaiyi sai su kushe su kawo nasu suce lallai shine daidai."
Uwale tace."To ai shikkenan tunda bata so a kai sunanta inda za'a taimaka mata sai tayi ta zama a gida tana tsotsar tsamiya." Gwaggo murmushi tayi da fad'in "Ko kuma ta dinga had'a kafad'a da kafad'a dani ba." Uwale na kokarin mikewa tace."Aikuwa dai ni yanzu tafiya gida zanyi naje na huta bari na kwance buhun na baki kayan miyan.
Gwaggo tace."Uwale dole fa na rage miki wani abu bana so ki kwashe kayanki kiyi min gwaninta dasu." Uwale tace."Ai ni nayi niyya ba rokana kikayi ba saboda haka dan Allah ki daina wata magana." Gwaggo tace."To shikkenan nagode kwarai da gaske.
Bayan tafiyar Uwale na kalleta tana harhad'a kayan gabanta nace."Wallahi Gwaggo kiyi hattara ki raba kanki da Uwale domin ta riga tayi nisa.
Tace."Sa'ida ashe dai maganar nan bata mutu ba." Nace." Gwaggo magana bata mutu ba dole na fada miki gaskiya." Tace."Amma dai tunda take maganarta ba kiji na amincewa bukatar taba ko." Girgiza kaina nayi. tace."Ai nima kawai jinta nake da kunne mu rabu lafiya amma ni me zai kaini gurin wani malami bayan ina da rabbissamawati shi kadai zan daga hannu na rokeshi ya amsa min."
Nace."Alhamdulillah Gwaggo naji dadin wannan magana taki ita kuma Uwale Ubangiji Allah yasa ta tuba ta gane hanya mai kyau." Ta amsa da ameeen Ya Allah Uwale kenan sarkin kyauta ki duba kiga uban kayan miyan data bani.
Nace."Ai dama hakane Dan adam tara yake bai cika goma ba ni kaina na sheda kyautar matar kuma tana kaunar ki sai da wani lokacin ni bana kaunar abotar ku sabida munanan halayenta." Tace."Hakane addua kawai zamu cigaba dayi mata akan Allah ya shiryeta ta gane hanya me kyau." Nace."To Allah ya shiryeta." ta amsa da ameeen ya Allah.
To haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau da dadi gobe babu na kammalah iddah na samu nutsuwa alhamdulillhi kuma gurin aikina sun kar'bi uzirana babu abinda zance da kawata hauwwa sai dai addua domin ta taka muhimiyyar rawa a cikin rayuwata.
Ranar asabar da safe na samu Kawu da maganar komawa ta aiki. jim yayi na 'yan mintina kafin yace."To shikkenan Sa'ida ban 'ki maganarki ba amma ki bari na samu babanki Alhaji Shamsu mu tattauna maganar.
Nace."To shikkenan Kawu ina saurare." Yace."Insha Allahu zan kirasa a waya duk hukuncin da ya yanke a kanki sai kiyi hakuri kinji ko."
A sanyaye nace."To Kawu." Mikewa nayi babu kuzari a jikina nayi masa sallama na fita daga gurin.
Kwana biyu da faruwar haka ya same ni a dakin Gwaggo ina yanke farce na muka gaisa a nutse yace."Sa'ida mun tattauna magana da Alhaji Shamsu yace kiyi hakuri akwai tunanin da yake akan ki sannan yace yana son ganin ki gobe kije gida ki sameshi zaku tattauna wata magana.
A sanyaye nace."To shikkenan Kawu insha Allahu gobe da wuri zan shirya na tafi." Yace."To babu laifi Allah yasa alkairi ne." Na amsa da ameeen ya Allah." har muka gama magana Kawu ya bar gurin Gwaggo ba tace uffan ba kad'in lagwaninta kawai take.
Muryar Uwale mukaji tana sallama tsaki naja a zuciya nace."Allah yasa alkairi ne ya kawo ta....Gwaggo ta gyara mata gurin zama a kusa da ita ta zauna suna gaisawa.
A nutse na gaisheta na dauki wayata ina dubawa......Ta kalleni tana mirmushi da fadin."Sa'ida gurin ki nazo fa."
Kallonta nayi da mamaki a tare dani.....Ta cigaba da cewa"Wani babban kamu nayi miki na mijin aure Alhajin burni ne mutumin mai kudin gaske ne shine yake neman 'yar duma dumar mace wacce bata ta'ba haihuwa ba kyakykyawa mai cika da kwarjini irin naki sai kawai kika fad'o min a rai na garzayo domin na sheda miki halin da ake ciki Sa'ida hakika kika auri mutumin nan kin huce takaicin duniya kudi ne dashi dan a yanda nake jin labari ma ashe shine shugaban babbar kasuwar nan ta *kwari* ko wane dan kasuwa a bayansa yake.
Gwaggo cike da farin ciki tace."Ikon Allah Uwale hakika naji dadin wannan labari dama hausawa suna cewa wani hanin ga Allah baiwa ne."
Na dinga kallonsu ina gyada kaina kafin nace."Uwale ta nan kuma kika 'bullo."? Sakin baki tayi tana kallona, nace."To bari kuji komai kwad'ayin ku ba zanyi auran dalili ba saboda haka kije ki nemo masa wata amma ba Sa'ida ba.
Jiki a sanyaye Uwale ta kalli Gwaggo da fad'in "Kinga yarinyar nan tana nema tayi mana bu'kulo ko."? Gwaggo ta ajiye makad'in hannunta rai a bace take kallona tace." Yanzu Sa'ida azo miki da irin wannan alkairin ki mayar dashi sharri wai me yake damun ki ne."
Murya na rawa nace."Gwaggo kada ki sake kisa maganar Uwale a ranki zaki fuskanci bacin rai mai tsanani na fad'a miki ni ba neman kai nake da kaina ba Insha Allahu Allah zai fito min da mijin da ya dace da rayuwata amma ni ba zanyi auran dalili ba.
Dakin yayi shuru bayan na gama maganata Uwale a sanyaye tace."To ai shikkenan Sa'ida tunda kina mana bakin cikin zuwa hajji da umara sai ki zauna ki cigaba da tsotsar tsamiya."
Nace."Har da lemon tsami zan tsotsa ba zanyi auran dalili ba.
Gwaggo cikin takaici da jin haushi tace."Kinga Uwale idan muna da rabo komai hassadar mai hassada sai mun sauke farali saboda haka kije ki cigaba da bincikawa a cikin 'ya'yan 'yan uwa insha Allahu za'a samu wacce za tayi masa."
Uwale tace."Aikuwa yanzu zan bazama insha Allah bazan koma gida ba sai an dace." Mikewa tayi tana gyara yafan mayafinta.
Hanya ta kama ta fita Gwaggo nayi mata fatan alkairi...........Gwaggo kwana tayi bata kula ni ba ko nayi mata magana da kyar take amsa min jefi jefi zata saki magana wacce idan nayi nazari a kanta sai na gane da ni take. murmushi kawai nake cikin zuciyata nake fadin ."masu irin halin Gwaggo ba zasu ta'ba zama da kishiya ba idan kuwa sun yarda zauna da kishiyar zata sha bakar wuya Gwaggo wata irin mata ce mai wani irin hali baudadde.
Da wuri na shirya nayi mata sallama ta dakatar dani wata leda viv ta miko min da fadin "Ki kaiwa mahaifiyar taki." Ledar na karba da fadin."Gwaggo menene a ciki." ? Tace."Ke dai ki kai mata meye naki na tambaya." Ledar na bude ina dubawa naga busassun kayan miya masu yawan gaske.....murmushi kawai nayi nace."To ni na tafi sai na dawo." Tace."Allah ya kiyaye hanya...........
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*60&61*
Kawu Iro shuru yayi a gurin tamkar ruwa ya cinyeshi gabadaya al'amarin ya daure masa kai ya rasa ma bakin magana shi kam ya rasa wane irin yaro Allah ya bashi. Gwaggo ta kalleshi da fadin"Ibrahim kayi shuru ka kasa magana." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yace."Gwaggo al'amarin ne ya daure min kai shiyasa kikaji nayi shuru na kasa cewa komai wato Khalid yayi hakane domin ya kashe mata aure ta fito daga gidanta shi ya aureta hakane ko ba haka bane." ? Gwaggo tace."Ato nima abinda nake zargi kenan.....Ummatu ta karaso gurun da fad'in "Dan Allah Gwaggo kuyi wa al'amarin nan kyakykyawar fahimta kada ku zargeshi da mummunar manufa tunda kun san dai maganar auransa da Jamila tayi nisa to mai zai sanya ya kashe auran Sa'ida wannan magana tuntuni ta mutu domin ya hakura ya kar'bi Jamila a matsayin matar auransa.
Kawu yace." Rabi ke kika haifi Khalid amma har yanzu baki san halinsa ba yaron mugun Hatsabibi ne." Cikin bacin rai yayi maganar....Gwaggo tace."Kada kayi masa baki Ibrahim ka daina kiransa da wannan suna addua za'ayi masa.
Yace."Gwaggo idan wannan ce manufar Khalid akan Sa'ida to ni mutukar ni na haifeshi ba zan lamunce masa auranta ba Allah zai kawo mata miji daidai da ita ta aura."
Jin abinda ya fada Yasa Ummatu jin dadi a zuciyarta gurin ta bari tana godewa Allah. Gwaggo jiki a sanyaye tace." Allah ya kyauta ya za'ba mana abinda yafi alkairi." amsawa yayi da amin ya kama hanyar fita yana kokarin fito da wayarsa.
Kofar gida ya zauna yana goge gumi hankalinsa a tashe ya nemo number wayar Alhaji Shamsu ya kirashi domin ya sheda masa halin da ake ciki.
Alhaji Shamsu hankalinsa ya tashi jin irin bayanin da Kawu Iron ke masa yace."Ibrahim na jima ban ji 'bacin rai irin na yau ba kuma banta'ba tsammanin Alhaji Nura zaiyi mana wannan wulakancin ba shin me yarinyar nan tayi masa da har zaiyi mata saki uku."?
Kawu ya goge gumi yana dawurwura hakika yana jin nauyi da kunyar fada masa dalilin da ya janyo sakin....Alhaji Shamsu yace."Ibrahim ka kwantar da hankalinka Alhaji Nura bamu ya tozarta ba kansa ya tozarta kuma abinda kayi wa d'an wani kaima sai anyi wa naka.
Kawu yace."Kwarai da gaske Alhaji maganarka haka take." Yace."Yanzu yanzu zan kirashi a waya dole ya fad'a min dalilin da yasa ya saki yarinyar nan domin hankalina gabadaya ya kasa Kwanciya inata tunani babu shakka ruwa baya tsami banza.
Jiki a mace Kawu yace."To shikkenan Alhaji duk yanda kukayi dashi sai ka kira wayata ka sanar dani."
Alhaji Shamsu yace."Insha Allahu zan kaji daga zarar mun tattauna magana dashi."
Sallama sukayi kowanne ya kashe wayarsa.
Washe gari da safe Alhaji Shamsu ya zaunar da matarsa kafin ya fada mata abinda yake faruwa sai da yayi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ya sheda mata abunda ya faru da 'yarta.
UmmuHabiba fashewa tayi da kuka tana girgiza kanta take fadin."Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una Alhaji wannan wane irin wulakanci ne? saki uku a lokaci guda akan wane dalili ashe dama mutumin nan auran sha'awa yayi."
Alhaji Shamsu ganin hankalinta ya tashi tana kuka ya shiga rarrashinta yana bata baki har sai da tayi shuru tana goge fuskarta yace." Dama yanzu nake tunanin kiransa a waya naji bayani daga bakinsa domin tabbas akwai dalili mai karfi da ya janyo hakan."
Tace."Eh ai gwara ka kirasa a wayar yayi mana bayani muji abinda ya janyo wannan cin mutuncin.
Wayarsa ya dauka ya nemo number Alhaji Nuran ya shiga gurin kira.
Yana kokarin fita kasuwa kiran wayar ya sameshi ya fito da ita daga aljihu yana dubawa, ganin number Alhaji Shamsu yasa yaja tsaki! aunty Murja ta kalleshi da fadin"Lafiya dai.''? Yace.''Mahaifin yarinyar nan ne Sa'ida." shuru tayi bata ce uffan ba har wayar ta katse wani kiran ya sake shigowa.
Tace."Kayi hakuri ka dauka mana kaji abinda yake tafe dashi a yanzu dai ai babu wata magana tunda saki uku kayi mata."
Wayar ya daga yasa a kunnensa had'a da sallama.....Alhaji Shamsu ya amsa masa a nutse suka gaisa da juna kafin yace."Alhaji Nura wane gagarimin laifi yarinyar nan tayi maka kayi mata saki uku a lokaci guda."?
A tur'bune yace."Kana so kasan dalili kenan."? Da sauri yace."Eh ai sabida inaso nasan dalilin yasa na kira wayarka domin dai nasan babu shakka ruwa baya tsami banza."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Ai Alhaji kune da laifi kuma banta'ba tsammanin zaku munafurce ni ba ashe yarinyar nan sai da ta gama watsewa da lalattatun maza a waje ku rufe min na aureta.
Cike da mamaki yace."Wace irin magana kake Alhaji Nura ban fahimci inda ka dosa ba yarinyar nan Sa'ida da kima da mutuncinta muka aura maka ita."
Da sauri yace." Waye ya fada maka haka? bari ma dai na daina rufe maka magana a ranar dana kusanci yarinyar nan na gane ba budurwa bace fanko ce. lokacin dana turketa ina tuhumarta tana kuka ta kawo min wasu hojojji wanda suka kashe min jiki har na yarda da ita na cigaba da zama da ita, a kwanakin baya yaron da nake zargin shi ya lalata ta yazo har cikin gidana sabida tsabar cin fuska har cikin d'akina na same su nan ma raina ya 'baci sosai na nuna mata kuskuranta hakuri ta bani ta nuna min babu wata alaqa a tsakaninsu sai gashi jiya Dr Maryam likitan ta ta tabbatar min da gaskiyar magana kuma itama Sa'idar ba tayi musu ba akan abinda ake zarginta dashi al'amari ya fusata ni sosai kuma naji takaicin abinda kukayi min na ha'inci wannan dalilin yasa na yanke alaqar aurena da ita."
Alhaji Shamsu ji yayi gumi na tsatstsafo masa bakinsa ya bushe qamas da kyar yace."Alhaji Nura ka dai fad'i wata hujjar amma ba wannan ba yarinyar nan Sa'ida bata san ko wane namiji ba lafiya lau muka aura maka ita kadai kara binkice akan maganarka."
Alhaji Nura yace."Alhaji a yanzu dai babu batun tashin-tashina a tsakaninmu tunda dai na yanke alaqar data had'a mu shikkenan magana ta 'kare dan Allah kada ka 'kara kiran wayata kazo min da maganar Sa'ida na sake ta saki uku babu ni babu ita."
A fusace! Yace."To sai me don ka saketa Alhaji Nura akwai maza a duniya da zasu aureta kuma wallahi ina mai tabbatar maka da cewa sai kayi nadamar abinda ka aikata."
Yana gama maganarsa ya kashe wayar sam baya bukatar sake jin wata magana daga bakinsa sabida yayi masifar 'bata masa rai."
Ummu Habiba kallonsa kawai take ko beyi mata bayani ba ta fahimci komai tunda wayar a hands free take.....Gumin goshinsa ya goge yace."Saboda kawai yana so ya rabu da yarinya sai yayi mata kazafin zina Habiba kina jin abinda mutumin nan yake fada akan yarinyar nan Sa'ida wai bai sameta da budurci ba to bai samu budurcinta ba me yasa tun farko bai fada ba sai yanzu da tayi watanni a gidansa ni nafi tunanin cewa ya gaji da zama da ita ne shiyasa ya shirya wannan maganar."
A sanyaye tace."Ni kaina al'amarin ya daure min kai kuma duk bayanin da yayi maka naji da kunnena dama can ba son Allah da annabi yake mata ba sha'awarta yake."
Ya dauki hularsa yasa da fad'in "Ai babu komai duk wanda yayi nagari kansa kiyi hakuri kuma ki cigaba dayi wa yarinyarki addua insha Allahu Allah zai za'ba mata abunda yafi alkairi a rayuwarta.
A sanyaye ta amsa da " Ameeen Alhaji nagode sosai da kulawar ka akan yarinyar nan." Yace."Habiba ni na dauki Sa'ida tamkar ni na haifeta saboda ina tausayawa maraicinta ina kuma kwadayin ladan kula da maraya sabida haka kada ki damu zan tsaya tsayin daka akan yarinyar nan."
Tace."To shikkenan Alhaji Allah ya shige mana gaba kai kuma abinda kakeyi na alkairi Allah ya baka lada." ya amsa da ameeen ya Allah yana kokarin fita sai ta mike a nutse tabi bayansa domin taka masa.
Koda ta dawo gidan dakinta ta shiga ta zauna kan kujera babu kuzari a tare da ita ta dauki wayarta number 'yar tata ta nema ta shiga gurin kira.
Lokacin data kira ina bandaki ita kuma Gwaggo bata iya da waya ta ba kira ta dinga kwala min da fadin na fito ana kiran wayata.
A gugurje na fito daga bandakin na ajiye butar hannuna, wayar ta miko min da fadin."Kinga har ta katse sai ki duba kiga ko wanene idan Khalid ne kada ki daga ki shareshi kamar yanda nake masa idan ya kira ni."
Murmushi kawai nayi ba tare da nace mata komai ba na nufi dakin da wayar a hannuna ina dubawa
Ganin number Ummana yasa da sauri na zauna gefan gado na shiga gurin kira da alama wayar tana hannunta domin sau daya tayi ringing ta daga, yanda naji muryarta a sanyaye yasa nima jikina ya mutu a nutse na gaisheta ta amsa tare da fadin."Ya mukaji da wannan abu."
Nace."Alhamdulillahi Umma." Tace."Kiyi hakuri kinji ko kowane mutum akwai irin kaddararsa kisa a ranki cewa dukkanin abinda ya faru da rayuwarki kaddara ce insha Allahu wataran sai labari."
Hawayen da suka zubo min na share murya na rawa nace."Insha Allahu Umma ki taya ni da addua akan Allah ya za'ba min abinda yafi alkairi."
Tace."Sa'ida addua kullum akanta muke Ubangiji Allah ya amsa mana adduo'inmu na alkairi." cikin sanyin murya na amsa da ameeen Ummana." Tace."Ki gaishe min da Gwaggo da kyau." nace."To zataji insha Allahu.'' Sallama mukayi da juna......Gwaggo ta shigo dakin tana fadin."Dawa kike waya ne."? Nace."Umma Habiba ce tace ma a gaisheki.''
Kallona tayi da fadin."Ita kuma a ina ta samu labarin abinda yake faruwa."? Nace."Watakila ko Kawu ya sanar da mijinta ne.''
Tace."Eh hakan zata iya yuwu wa Allah dai ya kyauta.'' cikin mutuwar jiki na