Showing 171001 words to 174000 words out of 185789 words

Chapter 58 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24206

yau sati biyu kenan da daurin auran Sa'ida tare da Dan uwanta Khalid."


Alhaji Nura gumi ne ya tsinke masa ya cire hularsa yana firfita da ita kamar mara hankali yace." Ya za'ayi ayi min haka? Yarinyar nan fa ni take so tayi min alkawarin komawa gidana domin ta kula min da 'ya'ya na mai zai sanya ka tilasta mata auran d'anka wannan ai rashin adalci ne."


Kawu ya dinga kallonsa yana mamakin maganarsa........Alhaji Nura ya cigaba da cewa ." Wannan yaron naka mara kunya kwata-kwata bai dace da kamilar mace irin Sa'ida ba saboda haka duk yanda zanyi sai nayi na ruguza auran da kuka daura."

Kawu na 'kokarin magana Muryarsa ta bayyana a gurin ya jima da zuwa gurin basu sani ba......."Kai wane irin wawan mutum ne bagidaje mara hankali da nutsuwa."
Gabadaya suka juya da sauri suna kallonsa.

Rai a masifar 'bace yace." Ka jima kana kira na da mara tarbiya shin kai d'in menene sunanka? Kana gadara da dukiya ko? to inaso na sanar maka da cewa a yanzu idan nayi Ra'ayi ba zaka koma gidan ka ba zan sa a daure min kai har karshen rayuwarka."
Kawu ya daga masa hannu da fadin."Ya isa haka kowa ya bawa zuciyarsa hakuri.'' Khalid shuru yayi sai wani irin huci yake yana jin kamar ya shaqe wuyan Alhaji Nuran ya had'a masa jini da majina bai ta'ba ganin mutum mai mugun naci kamarsa ba.

Kawu ya kalleshi da fadin." Alhaji idan rai ya 'baci ba'a sauran yanke hukunci ya kamata kayi mana uziri sannan kuma ka dauki kaddara komai kaga ka samu a duniya dama rabonka ne idan kaga baka samu abu ba to dama baka da rabo saboda haka sai kayi hakuri ka barwa Allah al'amarinsa.

Gumin goshinsa ya goge rai a bace yasa hularsa ya bude motarsa da karfi yaja Kawu yayi saurin matsawa yana kallon ikon Allah sai da ya bar gurin ya juyo yana kallon yaron nasa yana tsaye bakin kishi ya cika masa rai idanuwansa sunyi jajawur.

Yace." Yau shigowar dare kayi kenan."? ajiyar zuciya ya sauke yace."Eh kasa hakuri nayi sai da safe ina so naga Gwaggo ne." Yace." To babu laifi nima yanzu nan na fito daga gurin nata. Yana kokarin shiga kofar yace."Bari a gurguje na shiga mu gaisa Allah yasa ba tayi bacci ba." Kawu yace." Bana tsammanin hakan."


Gwaggo na gyangyad'i ya shiga ya sameta, kamshin turaransa taji da sauri ta bude idonta tana kiran sunansa.

Kusa da ita ya zauna yana gaisheta ta amsa cikin kulawa tace."Kwana uku ina lissafe baka zo inda muke ba."

Yace."Nayi tafiya ne Kuyi hakuri yanzu dawowata kenan na kasa hakuri na shigo na duba ku." Tace."Jarumi za kayi tafiya amma babu labari ko baka bukatar adduarmu."?

Yace." Gwaggo kuyi hakuri nayi laifi tafiyarce babu tsammani ina fatan na sameku lafiya." Tace."Lafiya kalau alhamdulillhi Ya iyalin naka."?

Yace." Duk suna nan kalau." Tace." To masha Allah sai ka tashi ka tafi gurinsu su ganka kada ka shiga hakkinsu."

Yace." Tom ki bani abinci naci." Girgiza kanta tayi tace."Aa babu ruwana ba zan baka abinci ba mai girki taji haushina.

Yar dariya yayi yace." Gwaggo bana sha'awar komai sai abincin ki kawai ki bani idan da akwai."

Jim tayi tana nazari tace." Bari na baka kadan idan kaje gida sai ka 'kara wani."

Yace." To ki had'a min bari na shiga gurin Ummatu mu gaisa na fito." Tace." Tom shikkenan sai ki fito.


Da 'Kyar Gwaggo ta kore shi ya tafi dan bayan ya gama cin abincin kwanciya yayi kusa da ita tana bashi labarai sai dariya yake kyalkyalawa ganin dare yayi beda niyyar tafiya gida yasa tace ita kwanciya za tayi ya tashi ya tafi gurin iyalinsa da kyar ya tashi ya tafi cike da 'kaunarta a cikin ransa.


Sai da ya fara duba Jamila tukkuna ya nufi Gurin ta.

Duk da nasan yau zai dawo gida Ban yi tsammanin zai shigo inda nake ba wannan dalilin yasa ban zauna zaman jiransa ba na shige daki nayi kwanciyata.

Maganarsa kawai naji a kaina, da sauri na bude idona ina kallonsa, ganin fuskarsa a murtuke yasa gabana faduwa ni kam Allah yana jarrabata da masifaffun maza.

Zaune na mike a sanyaye nace." Khalid ka dawo ashe."? a dakile yace." Na dawo ina fatan kuna lafiya."? Nace." Lafiya kalau Ya hanya."? shuru yayi min kawai ya zuba min ido." Nace." Kana bukatar wanka na had'a maka ruwa."?
"A'a idan ina bukata zan shiga na had'a da kaina yanzu inaso nayi magana dake ne." Yanda yake magana a harzu'ke yasa na gane cewa lallai da tashin hankali ya shigo gidan.






*Kika karanta baki biya ina bin ki bashi.....Vip group #600...Normal...#400 Account... 0542382124....Binta umar gtbank.....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE**101*
Motsin shigowarsa dakin ne ya farkar dani na miqe zaune ina kallonsa ya a jiye lodojin dake hannunsa, ba tare da yace min komai ba ya nufi toilet kamar na tashi na bishi domin nasan wanka zaiyi na had'a masa ruwa sai wata zuciyar ta kwa'be ina jin tsoron iskancin yaron domin na lura da cewa idan yaga ina masa rawar jiki yafi wulakanci.

Ina zaune ina tunanin rayuwa ya fito daga bandakin daure da towel da karami a hannunsa yana goge jikinsa.

A nutse nace."Sannu da zuwa." Yana tafiya zuwa mirror ya amsa ba tare da ya kalleni ba.

Komawa nayi na kwanta tare da juya bayana, boxer yasa a jikinsa ya had'a da vest wacce ta matse shi kaina yazo ya tsaya yana min magana cikin gadara da Iko.

Zaune na mike ina kallonsa "Ki tashi ki bani abinci." Cikin jin haushi nace "Ka duba daining da akwai komai."

A fusace! yace."Kina nufin ni zanyi hidima da kaina kenan."

Nace."Kaga Khalid bana neman fitina cikin daran nan don Allah idan za kayi min magana ka daina d'aga min murya kana buga min tsawa ba sai kayi haka ba za'a san kai maigida ne."


"Anyi miki tsawar ko zaki mayar da martani ne."? Cike da mamaki na dinga kallonsa sai wani huci yake yana kumfar baki Nace." Akan na mari Jamila ka tsaya a kaina kake kokarin zagi na."

"Eh akan hakane me yasa ba zaki jira na dawo ba ki fad'a min na dauki hukunci da hannu na ko kuma zaman kanki kike."?

Murmushin takaici nayi da fadin." Naga kaji zafin abin abinda za'ayi yanzu kawai ka rama mata marin sai ka huce haushin ka."


Tsaki mai karfi yaja yace."Wannan shine na farko kuma shine na karshe wallahi mutukar kika sake fitar da hannu kika daki yarinyar nan sai na hukunta ki dake da ita dukkaninku Amanar ku a hannuna take."


Kwanciya kawai nayi na kyaleshi yana surutai "Kin raina min mahaifiya sam bakya ganin kima da mutuncin dangi na kina maganar duk sharrin su zai koma kansu me sukayi miki na sharri da har kike fad'in wannan maganar."?


Kaina ne naji yana wani irin ciwo nace."Don darajar Allah ka matsa daga kaina wannan masifar taka ta haddasa min ciwon kai Khalid bana son damuwa naji na amsa laifina shikkenan ko."?

Gurin ya bari yana cigaba da k'ananun maganganu cikin zuciyata nace." Tunda Allah ya riga ya had'a ni zama da mutum mara hakuri dole na dauki kaddara.


Can cikin bacci na na jishi a naniqe a jikina yana kokarin cire min rigar bacci.

Haushi ya turnuke ni Khalid bai da kunya ko kad'an ya gama cin mutuncin na amma yazo yana lalube ni.

Hannunsa na d'auke na matsa can karshen gado.....Janyo ni yayi ya matse a kirjinsa yana wani irin nishi........"Auntyna kiyi min taimako irin na jiya kinji ko."

Shuru nayi masa ina jinsa yana magana kasa-kasa sai kokarin cire min riga yake ina hana shi.

Murya na rawa yace."Kina so nasa miki karfi ko."? Uffan bance masa ba, ya mike zaune bedlamp ya kunna haske ya gauraye dakin. mikewa zaune nayi ina kallonsa gabadaya kammaninsa sun sanja idanuwansa sunyi jajawur.!


"Ba zaki amince min ba ko."? Yafada yana bina da wani mayataccan kallo.

Babu fara'a a fuskata nace." Ka tafi gurin Jamila tayi maka ni ina bukatar hutu a halin yanzu."


Rai a bace yace." Ba zanje ba kuma wallahi ba zaki huta ba kin janyowa kanki fushi na sai na kwana a kanki."

Cike da mamaki nake kallonsa wai sai ya kwana a kaina ko ayu ma ai yana sauka ya huta........Bedlamp din ya kashe kafin nayi wani yunk'uri ya turmushe ni 'karfi yasa min gabad'aya ya galabaitar dani saduda nayi na sakar masa jiki yayi abinda yake so amma shi yake kid'an sa yake rawar sa duk sonsa da nayi masa wassani qi nayi duk ya wani susuce yana kama hannuna yana d'orawa kan joystick d'inshi ina cirewa gabad'aya naqi nayi masa abinda yake so.

Jin haushin hakan yasa ya zage k'arfi a kaina ya dinga bugu na tamkar wanda Allah ya aiko shi da k'yar ya bar mu muka rintsa a daran.


Washe gari da safe a murtuke ya tashi gaisuwa ce kawai ta had'a mu ya shirya tsaf domin fita.....Kamar kada nayi masa magana sai da na daure nace." Zaka fita ba kayi break fast ba.

Yana gyara agogon dake daure a hannunsa yace." Ba zanyi ba."

"Kamar yaya ba za kayi ba."? Hannu ya d'aga min da fadin." Bana bukatar doguwar magana tunda nace ba zanyi ba sai a kyale ni ko."


Nace."To an kyale ka Cikin ka ne ba na wani ba." bai tanka min ba ya kama hanyar fita, kallo na bishi dashi mai mugun hali kawai. cikin zuciyata nayi wannan maganar.


Ya jima a gurin Jamila kafin ya nufi gurin taron da zasu gabatar na 'yan kungiyarsu ta Kano pillars taro ne mai muhimmanci wanda ya had'a manya 'yan siyasa hatta da maigirma Governor zai hallaci taron saboda mahimmacinsa........Wani wasan za'a buga a kasar Italy Khalid Lawali tare da Ahamad Musa sune zasu jagoranci kungiyar tasu wannan dalilin ne yasa mai girma governor ya zauna dasu da shuwagabbaninsu domin tattauna yanda al'amura zasu tafi cikin tsari.

Khalid da Ahamad sunyi alkawarin cewa zasu tsaya tsayin daka suyi wasa cikin kyau da tsari kuma insha Allahu zasu 'kara kankaro martaba da kima na Jahar Kano.....Wannan bayanin nasu ya faranta ran duk wanda yake zaune a gurin a take manyan masu kudi da 'yan siyasar dake gurin suka soma yi musu kyautuka na mussaman.


Bai dawo gida ba sai gefin magariba Security dinshi ne ya bude masa mota ya fito takardun dake hannunsa ya miqa masa ya umarci shi da ya biyo bayansa. Motar ya rufe da sauri yabi bayansa da takardun a hannunsa.


A bakin kofar falo ya tsaya yaron nashi ya karaso inda yake ya kar'bi takardun tare da sallamar shi, har yayi nisa ya kira sunansa........"Chinedu." da sauri ya amsa tare da dawowa da baya. key din motarsa ya mika masa da fadin." Ka bude mota za kaga wani abu a daure a leda ka dauko min yanzu."

Da sauri ya karbi key din ya tafi. Shaf ya manta da sakon Gwaggo sai yanzu ya tuna dashi mybe ma abin ya lalace tunda ya kwana.

Tsayuwa yayi bakin kofar falon yana kallona, a nutse nace."Ka dawo." Shuru yayi min idonsa kuri a kaina dama ina sane nayi shigar k'ananun kaya na tamke fuskata had'e da fadin." Ka shigo mana ka tsaya a bakin kofa."

Ajiyar zuciya ya sauke a miskile yace."Babu oyoyo kenan." Kallonsa nayi ina mamakin rashin kunyarsa sai yayi abu ya nuna kamar beyi ba saboda biyan bukatarsa.


Gajiya yayi da tsayuwar ya karaso inda nake fulas din hannunsa ya ajiye min a gabana da fadin"Ga sa'kon ki inji Gwaggo tun jiya ta bani na kawo miki na manta sai yanzu na tuna."


Daukar fulas din nayi ina dubawa, dahuwar ta soma lalacewa amma dai idan aka gyara za'a iya ci saboda nasan muhimmancin abin yasa da sauri na shiga kicin domin gyarawa.


Zaune a falo na sameshi yana ta waya cikin zuciyata nace waya dai waya sam baya gajiya ko da yake dole hakan ta kasance dashi saboda yanayin sana'arsa.

Cikin dakina na zauna naci kazar a nutse kadan na rage ina sanya ran kafin na kwanta na cinye sauran.

Sai da nayi sallar isha'i na fito falon lokacin ya jima da fita zama nayi kan kujera da carbi karami a hannuna.............Sai da nayi zaman awa biyu da rabi ya dawo. kusa dani ya zauna naji yana kamshi turare ba irin wanda na san shi dashi ba turaran irin nawa ne da nake amfani dashi........Raina ne ya 'baci kishi ya sanya na dauke kaina daga kanshi.

"Wai me yasa kullum sai nace ki bani abinci ne."? Kallonsa nayi rai a bace nace." Kamar yaya? inace dazu kafin ka fita sai da nayi maka bisimillah kace baka bukata to me zai sanya na damu kaina da lallai sai kaci abinci."



"To yanzu ina bukata." cikin sassauci ya fadi maganar....a nutse na miqe na nufi gurin cin abincin baya na ya biyo yaja kujera ya zauna yana aikin latsa waya.


Ina had'a masa abincin na bar gurin domin bana so na zauna rai yazo yana 'baci.

Shirin kwanciya nayi cikin rigar bacci iya cinya pant kawai nasa ban sa breziya ba tattare gashin kaina nayi na had'e guri daya hula nasa na rufe kan na nemi guri na kwanta har yanzu kishin yarinyar na tsunkulin zuciyata.


Ina jin motsin shigowarsa dakin na rufe idona yayi dik abinda zaiyi ya gama yazo ya kwanta kusa dani yana ma'kale murya......"Big Aunty ki tashi na baki wani labari."

Share shi nayi yasa hannuwansa ya janyo ni jikinsa fuskarsa yasa a tsakanin wuya na yana min magana kasa-kasa.......Ganin yana so ya rinjaye ni yasa nace."Khalid don Allah ka barmu yau mu rintsa haba jama'a kai baka gajiya da abu d'aya ne."


"Aa Ni ba zan ta'ba gajiya dake ba kwanciyar hankalin ki kawai ki bani abinci naci."

Shuru nayi masa, yasa hannusa kan breast d'ina yana mutsikawa tsigar jikina gabadaya ta mike.....a kasalance nace." Ba zaka rabu dani ba kenan"

Cigaba yayi da abinda yake takaici ya ishe ni 'karfi nasa zan tureshi ya danne ni jikina ya hau ya kwanta gabad'aya ya sauke min nauyinsa.....Jajayen idanunsa ya tsira min na kauda fuskata daga kallonshi

Hannu yasa ya juyo da fuskar kasa-kasa yace." Ya labarin tsofaffin mazajen ki ina fatan yanzu kin bambamce aya da tsakuwa a tsakanin mu.

Shuru nai ina kallonsa yayi murmushi tare da lasar lips d'inshi fuskarsa daf da tawa ya fara kokarin kama baki na.

Babu yanda na iya haka na hakura na kyaleshi ya dinga jagwagwala ni sai da ya tayar min da dukkanin sha'awata gabadaya na rikirkice sai nishi nake ina rungumarsa wasu zafafan kesses ya dinga sakar min ina mayar masa da Martani Jikina ya riga ya jiqe babu abinda nake bukata sai biyan bukatata yanda ya rike wuta nima haka na rike sosai na rikita shi da salo na cikin fitar hayyaci ya dinga k'ananun hawaye yana sambatun surutai.


Washe gari cikin walwala da farin ciki ya tashi don be takale ni da rigima ba sai dai ni kuma gabadaya na kasa nutsuwa kishi ne ke damun zuciyata yau kwanaki na ya kare zai tare a dakin Jamila wannan dalilin yasa na kasa sakewa dashi wani irin haushin sa nake ji.

Koda dare da ya shigo domin yayi min sallama da 'kyar na kula shi, ya tsaya yana kallona da fadin." Naga tun safe kike da damuwa ko zaki fad'a min abinda ke damunki."


"Babu abinda ke damuna kaje kawai." qin tafiya yayi ya koma ya zauna wai lallai sai na fada masa abinda yake damuna.


Ganin ya damu yasa na sasasauta fuska da fadin." Na fada maka babu komai fa kada ka damu ajizanci ne irin na dan Adam amma ni babu abinda ke damuna."


Jikina ya matso yana kokarin rungume ni da sauri na matsa ina hararsa da fadin." Menene haka."? a kasalance yace."Sallama za muyi." Gurin na bari ya sake biyo ni yunkurin mi'kewa nayi ya mayar dani ya zaunar kan kujerar da karfi na zauna ina kallonsa da mamaki a tare dani.

Yatsansa ya d'ora saman le'buna na "Ki bani nasha wannan sweet din kafin na tafi." Kaina ne ya daure kawai na rasa abun cewa sai kallo. Cinyata ya zauna ya karkato da fuskata bai jira komai ba ya had'a bakinsa sa nawa..........Sosai yake sucking din harshena da le'bena duk ya wani gigice nasa hannu na cikun rigarshi fatar gefan cikinshi na mintsina da karfin gaske.

Saki na yayi yana kallona duk yayi wujiga-wujiga idanuwa sun zama tamkar jan gauta........"Ni zakiyi wa mugunta." a kasalance yayi maganar.

Hannu nasa na tureshi da fadin." D'aga ni don Allah duk kabi ka sagar min da gwiwa." Tashi yayi daga jikina yana shafa sumar kanshi yace." Wai menene a cikin bakin ki idan ina sha tamkar ina shan zuma."

Cikin kasala da tsananin sha'awa nace." Kan ka zaka tambaya." Kanshi ya shafa ido a lumshe yace." Eh wannan gaskiya ne ni zan tafi sai da safe." Ba tare dana kalleshi ba nace." Allah ya bamu alkairi." Ameen yace ya kama hanyar fita...Kallo na bishi dashi ina mamakin halayyarsa.




*Kika karanta baki biya ba ina binki bashi......Vip group #600....Normal group #400....Account... 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*102*
A daran ranar da k'yar na iya rintsawa (bacci ) saboda tsabar kad'aici da asubah da wata irin kasala da mutuwar jiki na tashi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login