Showing 51001 words to 54000 words out of 185789 words
shiga gida sai da ta tsaya gidan Lantana Dillaliyi tayi mata bayani kancewa idan tana son siyan katifar gado tazo ta gani.
Lantana ta kalleta da mamaki a tare da ita tace."Ke kuwa Rabi me yayi miki zafi zaki siyar da katifar gadon ki shin rashin ci ko rashin sha ne ya janyo haka."?
Ummatu a sanyaye tace."Ko d'aya Lantana wata 'yar matsala ce dani wallahi sabida haka nazo nayi miki tallah idan kina so kawai muje ki gani bana san doguwar magana."
Lantana ta yafa mahaifinta da fad'in "To shikkenan muje naga katifar." suka fito daga gidan a tare.
Muna zaune nida Gwaggo a tsakar gida muna hira gwaggo na gyara wake za tayi mana alala Ummatu da Lantana suka shigo.....Lantana cikin mutunci ta tsaya suka gaisa da Gwaggo ita kuwa Ummatu ko kallonmu ba tayi ba ta bude gurinta ta shiga Lantana tabi bayanta.
Gwaggo da bakinta baya shuru tace."Sa'ida mai Ummatu zata siyar ta kawo dillaliya gidan nan."?
Nace."Gwaggo dan Allah ki daina shiga abinda babu ruwan ki kiyi shuru da bakin ki shi yafi miki alkairi."
Shuru tayi bata sake cewa komai ba sai dai sa'i da lokaci takan daga kai ta kalli kofar Ummatun nasan jira take su fito.
"To shikkenan Lantana sai ki aiko yaro da akori kura ya daukar miki na siyar miki akan dubu ashirin da biyar din." Ummatu ce ke wannan maganar a lokacin da suke fitowa daga gurin nata.
Lantana tace."To shikkenan yanzu yanzu ina komawa gida zan turo a dauka tare da kudin naki." Ummatu tace."To ina saurare."
Lantana ta kalli Gwaggo da fad'in "Gwaggo Allah ya bamu alkairi ni na tafi." Gwaggo tace."To ki gai da gida." Lantana na fita Ummatu da sauri ta juya zata bar gurin.
"Rabi." Gwaggo ta dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Fuska a murtuke ta juyo tana amsawa Gwaggo tace."Me zaki siyar ne."? Da sauri na kalleta ina jin masifar takaicin abinda take ina ruwanta Ummatu ko kanta da kanta zata siyar ido ne nata.
"Gwaggo ba abinda ya shafeki bane'' Ummatu ta mayar mata da amsa daidai da tambayarta. Gwaggo taji ciwo sosai tace." Duk abinda zaki siyar kije kiyi ta siyarwa ni dai nasan ba za'a zagi Ibrahim ba ace ya gaza a gidansa wannan ai cin mutunci ne rana gatse-gatse kije ki dauko dillaliya ta shigo mana gida me aka gaza dayi miki a gidan."?
Itama cikin rashin tausasa harshe tace." Ai dama ni bance Ibrahim ya gaza a gidansa ba tunda daidai gwargwado yana kawo abinci amma kuma suttura sai shekara shekara sannan ni na dauko Lantana ne domin tazo ta siyi katifar gadona saboda inada bukatar kudi."
Tana gama maganarta ta kad'a kanta ta shige gurinta.
Gwaggo ta bude bakinta cike da mamaki tana kallona.
Nace"Ai dama baki in yasan abinda zai fada bai san abinda za'a mayar masa ba tun farko sai da nace kiyi shuru kika k'i ai gashinan kin janyowa kanki cin mutunci.'"
Tace."Sa'ida ni ba wannan ne ya dame ni ba saboda cin mutuncin Rabi kuma wane iri ne ban sani ba ko ba kiji abinda tace ba wai zata siyar da katifar gadonta to a 'ina Ibrahim zai dinga kwanciya."?
Nace."Gwaggo babu ruwanki katifa dai ta Ummatu ce baki isa ki hana ta siyarwa ba saboda haka kiyi shuru da bakinki shi yafi miki alkairi Kawu kuma insha Allahu ba zai rasa gurin kwanciya ba ni nayi alkawarin siya masa katifa yasa a dakinsa shikkenan magana ta mutu."
Girgiza kanta tayi da fad'in "Lallai Rabi tayi nisa ko da yake ai nasan idan ta kar'bi kudin katifar gurin malamai zata kai asararriya kawai."
Shuru nayi ban tanka mata ba saboda bana so maganar tayi tsayi da dai naji taki tayi shuru sai na mike na shige daki na kwanta ina jira ta gama mana alalan nasha magani bacci mai nauyi ne ya dauke ni.
Gwaggo kuwa har akazo ka dauki katifar ba ta daina surutai ba tamkar ma wacce ake ingizawa Lantana da Ummatu sun sha habaici amma sai akayi sa'a cikinsu babu wacce ta tanka mata Lantana ta tafi da katifa ita kuma Ummatu ta shige gurinta da kudinta a hannu
****
*BAYAN SATI DAYA*
Khalid ya dan samu nutsuwa a gidansu Salmanu sai dai baya sakewa sosai a unguwar gudun kada yaga idon sani kullum yana dakin Salmanu a kwance yana shawarwari da zuciyarsa.
Salmanu ya shigo dakin da fad'in "Khalid ka tashi ga shawara nazo mana da ita."
Zaune ya miqe yana kallonsa da fadin" Nima kwanciyar nan da nayi shawarwari nake da zuciyata.
Salmanu yace."Legos zamu tattara mu tafi akwai wata 'kungiyar 'yan ball ta 'yan kano mai taken kano Pillas inaso muje mu fara gudanar da harkokinmu na ball a can Khalid ka iya buga 'kwallo jikina na bani kana da abinci a harkar.
'Karamin tsaki yaja yace."Wallahi na dauka zaka ce akawai company da yake bukatar irinmu a legos din wace irin ball kuma Salmanu mu fuskanci abinda yake gabanmu ina ganin tunda aikin ya'ki samuwa anan me zai hana mu tafi da takardun mu can mu gwada mu gani."
Salmanu yace."Eh dama haka za'ayi Khalid ai ba zamu dogara da abu guda ba idan aikin ya'ki samuwa ba sai mu mayar da hankalinmu gurin harkar k'wallo ba ko ya kaga ni."
Khalid yace."Salmanu nifa a halin yanzu aikin da zai ri'ke ni nake nema bana so nayi ta zama da girmana wani na dawainiya dani 'Kwallo tana kawo kudi amma sai mutum yana da hanya a harkar sannan duniya zata san dashi har ya samu wani abu."
Salmanu yace."Khalid ka kasa gane maganata dama ai ba wai zamu zauna a guri daya bane idan munje zamu dinga buge-buge nufi na duk inda ta fad'i daidai ne."
Ajiyar zuciya ya sauke yace."To shikkenan Salmanu amma dai akwai guziri mai yawa a gurinka ko dan ni ba wasu kudi masu yawa gare ni ba.
Salmanu yace."Babu damuwa insha Allahu zan tambayi kanin mahaifina zai taimaka min sannan Mamana ma zata bani goyon baya kuma zata taimaka mana.
Yace."To shikkenan Allah yasa muje a sa'a." Salmanu ya amsa da ameeen tare da fadin"Khalid ya kamata ka kunna wayarka ka kira gidanku ka shedawa mahaifinka yasa maka albarka ka kuma nemi gafararsa.
Yace."Salmanu wallahi tuntuni nake wannan tunanin amma na rasa ta ina zan fara ina jin kunyar abinda na aikata.
Salmanu yace."Daurewa kawai za kayi ita qaddara ai ba'a guje mata zuwa yanzu dai nasan zuciyoyinsu sunyi sanyi sai ka tausasa harshe gurin neman afuwarsu mussaman ita wacce ka 'batawa."
Shuru yayi yana me sunkuyar da kansa, Salmanu yace.''Bari na shiga gida na dauko mana abinci." Bayan fitar Salmanu daga dakin Khalid ya janyo jakarsa ya bude a nutse ya dauko wayarsa ya kunna kai tsaye number auntyn nasa ya lalubo ya shiga gurin kira.
Lokacin muna hanyar dawowa gida ni da 'kawata Hauwwa kiran ya shigo waya ta gabadaya hankalina ya dauke gurin hirar da muke shi yasa ban duba mai kiran ba na daga tare da sa wayar a kunne na.
A sanyaye naji maganarsa...."Auntyna barka da rana." Gabana ya yanke ya fad'i wayar ta kusa su'bcewa daga hannuna.....shuru nayi masa yace."Ina fatan kin warware ko."? nayi shuru ban tanka masa ba yayi d'an murmushi da fad'in "Kiyi hakuri sharrin shed'an ne ki gafarce ni dan Allah."
Ajiyar zuciya na sauke na kashe wayar na ajiye gabadaya yanayi na ya sanja.
Hauwwa na driving ta kalleni da fad'in "Kawata ina fata dai lafiya." da sauri nace"Lafiya mai kika gani."?
Tana 'kokarin magana ya sake kira kamar kada na dauka sai kawai na yanke shawarar dagawa sabida kada ta zargi wani abu.
Zazzafar ajiyar zuciyarsa naji a cikin kunnena kafin yace."Ya maganar wacan 'katon mutumin mai k'aton tumbi." Yana nufin Alhaji Nura. Nace."Khalid kada ka sake kiran waya ta kaji ko ba kaji ba."?
Jin sanyayyar muryarta yasa shi sake sauke ajiyar zuciya ya lumshe idonsa yana sake gyara kwanciya 'kasa-'kasa yace."Aunty Sa'ida idan kin janye maganar Alhaji Nura zan dawo gida idan kuma baki janye ba to ina mai tabbatar miki da cewa sai dai kuyi hakuri dani domin zanyi nisa kuma ba zan dawo ba.''
Nace."Khalid ka tafi 'karshen duniya kaji ko ba abinda ya dame ni bane aurena da Alhaji Nura yana nan yanda ka sani ranar Juma'a mai zuwa daurin aure."
Ya fesar da wani zazzafan huci! ya mi'ke zaune gumi! na yanko masa yace."Okey ina fata dai kin sheda masa cewa saura na zai samu domin duk na kwashe roman sai da ya samu sud'i."
Da sauri na kashe wayar gabana na dukan uku-uku addua nake a zuciyata akan Allah yasa Hauwwa ba taji komai ba.
Kiran wayar ya sakeyi na dauka da sauri na kasheta gabadaya, Hauwwa tayi dariya da fad'in "Khalid kenan kice dai har yanzu bai hakura ba."
Cikin basarwa nace" Hauwwa rabu da shashasha dan Allah idan ya gaji zai hakura."
Tayi dariya da fad'in "Ni kam ina sha'awar yanda yake nuna miki so hakan yana burgeni wallahi."
Nace."Hauwwa ke kin fiye budurwar zuciya wallahi ina abun yake a gurin Khalid me ya iya a soyayya sam baya burge ni wallahi."
Ta kalleni tana so ta gazgata maganata nace."Kwarai kuwa Hauwwa soyayya sai babban mutum wanda yasan abinda yake amma irin wannan soyayya tasu Khalid ai shirme ce."
Tace."Ni kam a gani na Sa'ida soyayya duk soyayya ce babu babba babu yaro a cikin ta na tabbatar da cewa babu abinda Alhaji Nura zai nunawa Khalid d'an zamani ne sai dai ma ya nuna masa wani abun."*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*35&36*
Cikin tsananin tashin hankali Salmanu ya nufi inda Khalid ke kwance ya tarairayoshi jikinsa yana kiran sunansa, Jama'ar dake gurin suka rufo kansu gurin ya hargitse da kace nace kowa yana fadar albarkacin bakinsa akan abinda ya faru Salmanu shi dai babban damuwarsa abokinsa ya farfado! direban motar ne ya karaso gurin hannunsa rike da jarkar ruwa ya bude da saurin gaske ya shiga tuttulawa khalid ruwan a jikinsa, yana gamawa dashi da sauri ya karasa inda mijin matar nan yake a kwance shima ya daga jakar ruwan ya kwara masa a jikinsa cikin ikon Allah gabad'ayansu suka farfad'o cikin jigata Khalid ya dinga kiran sunan Allah yana jin yanda kansa ke wani irin sarawa! hannu yasa saman goshinsa ya shafo jini Salmanu yace."Sannu Khalid ai ka auna arziki." kallonsa kawai yayi ya juya yana kallon jama'a dake gurin suna surutai da hayaniyar kowa sai gyara jakar kayansa yake Yace."Salmanu ina matar nan take bana so su cutar da ita."
Salmanu yace ."Sai dai hakuri ai sun tafi da ita."
Kansa ya dafe yana kiran sunan Allah! Ihu! mai karfi sukaji da sauri ya dago kansa mijin matar nan ne yake kurma ihu mutane na rirrikeshi wai sai ya tafi neman matarsa jamaa sun hana shi ga 'yarsa sai sandara ihu take itama.
Khalid cikin karfin hali ya mike Salmanu yace."Ina zakaje Khalid kai ma fa kana bukatar taimako.
Yace."Salmanu mutumin can ya bani tausayi zanje na rarrashe ne."
Kafin Salmanun yayi magana ya bar gurin Salmanu yabi bayansa zuwa inda mutumin ke zaune jamaa sun kewaye shi suna bashi hakuri.
Khalid ya dafa kafad'arsa ya dinga rarrashin sa kancewa yayi hakuri ya barwa Allah insha Allahu Allah ba zai basu nasara akan matarsa ba.....Yana kuka yace."Matata ciki ne da ita d'an wata uku gashi bata da cikakkiyar lafiya mahaifiyarta na Lego's ta matsa min da cewa tana so taje ta gaisheta hakika dana san wannan tsautsayin zamu hadu dashi to da ban amince da tafiyar nan ba.
Khalid yace."Kayi hakuri abokina dukkanin abinda kaga ya faru da kai da matarka rubutacce:ne daga Allah kayi mata addua kawai akan Allah ya ku'btar da ita.
Kansa ya sunkuyar kasa hawaye masu zafin gaske suna zubo masa hakika yana son matarsa so mai tsanani yana jin tsoron 'yan fashin nan su haike mata su kasheta da wahala.
A firgice ta tashi zaune tana rarraba idanuwanta a dakin kafin ta fara lalube kan shimfid'arta salati takeyi a zuciyarta tana kiran sunan Allah.
Fitilar ta ta kunna dakin yayi haske jiki a sanyaye ta mike ta dauki buta ta fita bandaki ta shiga ta kama ruwa ta fito garin yayi tsit Allah yana saukar da ikonsa.
Alwala ta d'aura ta shiga dakin ta gyara dadduma ta tayar da sallah.
Nafila tayi raka'a biyu tayi sallama sai ta daga hannunta sama hawaye ya 'kwace mata tana kuka take fad'in "Ya Ubangiji Allah ka karkato da hankalin yaron nan gida Allah ka yafe masa kada ka d'ora masa mummunar kaddara Allah Khalidu mai laifi ne a gurinka Allah ka sassauta masa Allah kada ka jarrabe mu da abinda ba zamu iya ba." Kuka ne yaci k'arfinta hannuwanta a sama ta kasa saukewa.
A tsorace na mike zaune ina kallonta gabana na faduwa nace"Gwaggo lafiya meye kike kuka me ya faru."?
Adduar ta shafa a fuskarta murya a dushe tace."Sa'ida dan Allah da Annabi ki yafe wa Khalid abinda yayi miki kaddara ce ki yafewa dan uwanki ko ya samu sassauci.
A sanyaye nace."Gwaggo me ya faru dashi.?
Tana rawar murya tace."Mummunan mafarki nayi dashi Sa'ida amma kafin na farka daga baccin na manta ni dai nasan na ganshi cikin mawuyacin hali jina jina da jini.
Gabana ya fad'i! nace."Gwaggo mafarki ba gaskiya bane ki daina gazgazata shi." Girgiza kanta tayi tace."Sa'ida ni bazan kira kaina waliyyiya ba ba kuma zan kira kaina 'yar baiwa ba amma Allah yakan nuna min abu a mafarkina mai dadi ko mara dadi kuma mafarkin yakan zama gaskiya ko mutuwa za'ayi Allah yakan nuna min a mafarkina shiyasa hankalina ya tashi da yin wannan mummunan mafarkin.
Shuru nayi har yanzu kuma ban daina jin faduwar gaba. ta cigaba da cewa "Dan Allah kice kin yafe masa ko ya samu sassauci." A sanyaye nace"Gwaggo tuntuni na yafe masa ki kwantar da hankalin ki."
Tace."To nagode sosai Allah yayi miki albarka na amsa da ameeen ya rabbi.
Kasa komawa bacci mukayi har asubah tayi mukayi sallah muna idarwa tace lallai wai sai na kira mata shi a waya, to nima nawa 'bangaran jikina yayi sanyi da al'amarin ban yi mata musu ba na kunna wayata na fara laluben number sa.
Na kira sau kusan biyar bata shiga, nace"Gwaggo kin dai ji da kunnanki wayar taki shiga ko."
A sanyaye tace."Watak'ila sun kashe shi." naji gabana ya yanke ya fad'i!
Kallonta nayi hawaye na kwarara a fuskarta tace."Sa'ida na d'an tuno mafarkin ganin sa nayi wasu mutane masu baka'ken kaya sun zagaye shi da bundigogi a hannunsu suna ta dukansa."
Nace"Gwaggo ki samu nutsuwa dan Allah in sha Allahu Khalid na raye cikin koshin lafiya."
"Kayya! Sa'ida bana tsammanin yaron nan nada rai.'' nace" Bari gari ya waye sai a sake kiran wayar tashi."
Tace."to shikkenan." tagumi! ta zabga har yanzu hawaye take cikin zuciyata nace ko wane irin so da kauna take masa.....Nace"Gwaggo yau ba zaki kunna redio ba."?
Kanta ta girgiza min na dauki redion na kunna mata na ajiye mata kusa da ita.
Dauka tayi tana kokarin kashewa tace."Sa'ida rabu dani nayi salati a zuciyata yau bana sha'awar jin redio nafi bukatar na samu nutsuwar zuciya nayi wa yaron nan addua.
Nace"Hakane Allah ya kare shi." ta amsa da ameeen ya rabbi.'' Mikewa nayi na fita tsakar gida domin d'ora ruwan wanka, sai naji motsin fitowarta na jiyo ina kallonta naga tana sa takalmanta da kudi a hannunta.
Nace"Ina kuma zakije da sassafe haka'' Tace."Zanje gidan Marka mai waina na siya domin nayi wa almajirai sadaka."
Shuru nai ina kallonta har ta fita daga gidan na girgiza kaina tare da cigaba da abinda nake.
Har nayi wanka na fito nasa kaya na Gwaggo bata dawo gidan ba, na zauna cikin damuwa na dauki mai ina shafawa a jikina Kawu Iro ya daga labulan dakin, da sauri na gaisheshi ya amsa cikin kulawa yana fad'in "Gwaggo tana bandaki ne."?
Nace." Aa ta d'an jima da fita wai taje gidan Marka siyo wainar gero."
Yana kokarin magana ta shigo gidan. Kawu Iro Kallo guda yayi wa mahaifiyar tasa jikinsa ya mutu ganin yanda ta zabge idunuwanta sunyi fululu.
Yace."Gwaggo lafiya me yake faruwa."? Hawaye suka 'kwace mata tace."Ibrahim babu lafiya domin kuwa Jiya a zaune na kwana tunda nayi mummunan mafarki da yaron nan Khalid na kasa rintsawa.
Yace."Gwaggo dan Allah ki cire damuwar Khalid daga cikin ranki kada ki janyo wa kanki ciwo mai tsanani.
Tace."Ibrahim idan kaga na cire Khalid a raina to mutuwa nayi amma ba zan ta'ba daina damuwa dashi ba.''
Tana gama maganarta ta wuce gurin Ummatu.
Ummatu na tsaka da dama kunu ta ganta ta shigo kicin din, gabanta ya fadi! tunda suke a gidan sai ta irga iya adadin shigowarta gurinta bai fi uku ko hudu ba Allah dai yasa ba wata masifar bace.
"Gwaggo ina kwana."? tafada babu cikakkiyar sakewa.
Gwaggo cikin kulawa ta amsa da fadin" Rabi gurin ki nazo.'' Ummatu ta saki ludayin da take dama kunu dashi tana kallonta .
Gwaggo ta 'kas'kantar da kanta da fad'in "Dan Allah Rabi'atu ki gafarci yaron nan kiyi hakuri ki masa addua Akan Allah ya sassauta masa domin jiya ni nasan mummunan halin dana ganshi a mafarkina.
Ummatu jikinta yayi sanyi tace." Gwaggo dama ai ni ban 'kullaci Khalid ba tunda dama ban yarda da zargin da kuke masa ba.
Tace."To hakane to amma dan Allah ki dage dayi masa addua saboda bakin uwa albarka gare shi ki daina zuwa kina asarar kudin ki a banza addua zaki masa