Showing 183001 words to 185789 words out of 185789 words

Chapter 62 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24237

karya kake kana satar kwana kana kawo min saboda rashin tsoron Allah.'' " Kada ki sake k'aryata ni." yafadi maganar a kufule. Nace." To idan kana da gaskiya ka bari a kira ta a tambaye ta mana." Tsugunawa yayi a gabana a sanyaye yace." Ko kin kirata ba zata saurareki ba saboda tana cikin fushi." Nace."Khalid wallahi kaji tsoron Allah kana azabtar da iyalinka kana kuma dorawa kanka nauyin zunubi." Ya jima yana kallona kafin yace."Wace irin azaba nake muku? kuna so na kwanta a kasa ku takani kenan.''? Girgiza kaina kawai nayi Yace."To mu bar wannan maganar muyi wacce zata taimaka mana." Nace "Kasan Allah yau kome za kayi ba zaka samu abinda kake so ba bani ma da lafiya ta kaina nake." A marairaice yace."Don Allah ki bari nayi ko Allah zai sanya ki samu ciki wallahi haihuwa nake so." Kallonsa nayi ya wani langwab'e kai sai lumshe idanuwansa yake. " Kayi hakuri ka bari sai girki yazo hannu tukkuna." Wani irin kallo yake min fuskarsa ta rikid'e da bacin rai yace."Saboda kinga ina sonki kike wulakanta ni." ? Kokarin bar masa gurin nake ya rike min hannu "Ba zan kara tunkarar ki da wata bukata ba." cikin zuciyata nace." Dama haka nake so." Hannuna ya saki yaje ya kwanta kan bed komawa nayi kan Kujarar na kwanta ina sauke ajiyar zuciya sosai naji dadin yanda yayi zuciya dama haka nake so ya kyaleni na huta.......Washe gari da safe babu yabo babu fallasa muka gaisa cikin rashin kuzari ya zauna yayi breakfast, yana shiga wanka kira wayarsa dake samar mirror, Ina dubawa naga sunan Ummatu. ajiye wayar nayi yana fitowa na fad'a masa, daukar wayar yayi ya zauna kusa dani..............."Rai a b'ace naji maganarta "Khalid ni zaka tozarta ko? me Jamila tayi maka kace ta fice maka daga gida."? Yace." Ummatu ki kwantar da hankali yanzu zan shigo na sheda miki dukkanin abinda yake faruwa." Tana kuka tace."Aa ai zuwanka bashi da amfani tunda ban isa na baka umarni ka dauka ba kana so ka tozarta ni ko to shikkenan kaje duniya ce." Kafin yace wani abu ta kashe wayarta. Shuru yayi da wayar a hannunsa nace."Me tayi maka da zaka kore ta a gidanka." ? Hannu ya daga min da fadin." Ba abinda ya shafe ki bane." Nace."Ya shafe ni tunda ya shafe ka." Tsaki yaja ya mike ya nufi wardrobe kayansa ya dauko yasa yana d'acin rai Nace."Don Allah duk abinda tayi maka kayi hakuri ka dawo da ita dakinta ina amfanin hakan idan laifi tayi maka bata wannan sigar zaka hukuntata ba tunda kaga 'yar uwarka ce.'' Uffan bece min ba ya kwashi wayoyinsa da key na mota ya bude kofa ya fita ya barni da mamaki...........Baito har kofar Gwaggo ta shiga ta dinga zazzaga masifa Gwaggo tace."Baito ni dik abinda yake faruwa bani da labari amma kuyi hakuri dukkaninmu mu jira zuwansa domin muji laifin da tayi masa. Baito tace."Bayan daukar kwanan da yake yana kaiwa Jikarki duk hakan be isheshi ba sai da ya koreta to wallahi daku da malamin dake muku aiki sai munyi maganinku." Gwaggo tace."Baito kece kika yarda da shirka da surkulle ni Allah kadai na gazgata saboda haka dik abinda zakuyi kuje kuyi." Baito na numfarfashi ta fita daga gurin...Ita kuwa Gwaggo hawaye kawai take sharewa tana jin bakin ciki da takaicin abinda yaron yayi.........Kwata-kwata Ummatu kin sauraran uzirinsa tayi ta rufe shi da fad'a Baito tana taya ta Jamila tazo ta fada musu karya da Gaskiya sun yarda da maganarta sosai al'amarin yayi masa ciwo ya kuma kudiri aniyar sakin yarinyar tunda ta zame masa annoba....Koda ya shiga gurin Gwaggo ma rufe shi tayi da fada tace."Wannan ai shashanci ne saboda kawai kun samu sa'bani da yarinya sai ka koreta wannan ba hukunci bane." Yace."Gwaggo yarinyar nan fa rashin kunya take min sam bata ganin girmana Sa'ida da take da shekaru sama da nawa tana bani girma tana mutuntani amma Jamila ban isa ta durk'usa min ba kullum cikin tsiwa da izgilanci har da zagi ni ba sakaran namiji bane wallahi matakin da zan dauka a kanta dukkaninku ba zai muku dadi ba." Gwaggo jikinta yayi sanyi tace."Kai amma yarinyar nan bata da mutunci ashe haka kake fama." Yace."Eh hakuri kawai nake da ita a gurin Sa'ida kawai nake samun sasaauci " Tace." To ni na zare hannuna a maganar duk hukuncin da zaka yanke kaje ka yanke hausawa suna cewa(Mai daki shi yasan inda yake masa yoyo.")
Sati guda da faruwar al'amarin Jamila taji shuru babu wani labari tana zaune a gida bata san makomarta ba kullum idan sukayi waya da Ummatu babu wata cikakkiyar magana sai kawai ta shirya ita da kanwarta sukaje har gida suka ci mutuncin Ummatu tas. Al'amarin yayi masifar bata tsoro cikin damuwa ta kira wayar Baito ta sheda mata irin cin mutuncin da jamila tazo tayi mata budar bakin Baito sai tace." Ai hakan da sukayi shine daidai tunda ke kin zama shashasha kin kasa tan'kawara d'anki sai abinda yake so zaiyi saboda haka ni banga laifin Jamila ba Ke da d'anki kun riga kun 'bata mana Zumunci dan haka kada ki sake kira na a waya mutukar ba abin arziki zaki fada min ba." Ummatu a ranar yini tayi cikin tsananin damuwa da tashin hankali, ashe da sauran rina a kaba dan a daran ranar Kawu ya sheda mata da maganar daurin auransa ranar Jumaa mai zuwa, ihu! ta dinga kurmawa kamar zautacciya ta nufi kofar Gwaggo tana kuka na fitar hankali....A lalace Gwaggo ta kalleta tace." Yanzu ke Rabi wannan ba abun kunya bane a gurin ki saboda kawai za'ayi miki kishiya kike kuka sai kace wata k'aramar yarinya." Tace."Gwaggo me nayi miki kika tsaneni yanzu ace Mijina zai kara aure amma a munafurce ni ba za'a fada min ba." Tace."Ashe nice munafuka tunda ni nasa shi yayi auran." Tace." To Gwaggo me yasa zaki sashi yayi aure bayan kema baki ta'ba zama da kishiya ba sai shi." Tace." Allah ne bai nufi mijina da ya kawo min abokiyar zama ba saboda haka idan zakiyi misali ki daina had'ashi dani Ibrahim zaiyi aure babu mahalukin daya isa ya hana abinda Allah ya hukunta." Ummatu tasa bakin hijabinta ta share hawaye ta bar kofar dakin cikin tsananin damuwa da tashin hankali.................Tun daga ranar daya nemi ni naki bashi hadin kai bai sake ba tsakanina dashi ido ne idan magana ta kama muyi ya shige ya tafi harkokinsa...........Ana ya gobe daurin Auran Kawu Hauwwa tazo take sheda min cewa sun tsayar da ranar daurin auransu ita da Yaya Aminu sosai nayi farin ciki da jin hakan, da zata tafi ta dinga tsokana ta da uwar biyu nace." Wai ke waye yace miki ciki ne dani." Hararata tayi da fadin." Kada ki rainawa kanki hankali mana gashinan duk kin sanja kammani kinyi haske da ki'ba goshinki sai kyalli yake." Murmushi nayi nace "Wallahi Hauwwa kunya nake ji wai yau nice dauke da cikin yaron nan Har bana so na fita jama'a su gane gashi gobe Kawu zai daura aure ina jin nauyin zuwa gidan sabida surutun mutane." Tana dariya tace."To menene abin kunya Yaro da babban duk aiki d'aya suke dan Khalid yayi miki ciki ba' abun kunya bane abun alfahari ne." Nace."Hakane." Sallama mukayi da juna na koma cikin gidan da tunanin halin da Gwaggo zata shiga idan ta fahimci cikin da nake dashi..........Washe Da sassafe muka shirya ni dashi muka nufi gidan.Gwaggo taci kwalliya da atampa super tayi lalle a kafafu da hannaye idonta rambad'e da kwalli dauri kuwa har gaban goshi Uwale na kusa da ita suna hira.....Khalid daga bakin kofa ya tsaya suka gaisa ya nufi massalacin da za'a daura auran........Tun kafin na zauna Uwale take rangwada bud'a tana kallona Gwaggo kuwa sai murmushi take tana gyara min gurin zama na zauna da kyar tace."Sannu ashe haka kikayi nauyi babu labari." Cike da mamaki nake kallonta tace."Ga ciki nan har ya huda zani kai alhamdulillhi Allah nagode maka." Nace."Gwaggo waye yace miki ciki ne dani.'' Tace."Idona ne ya gane min munafuka dake da mijin naki." 'Yar dariya nayi nace."Shima Khalid din be sani ba." Tace."Karya kike kina kareshi ne.'' Nace."To shikkenan idan ya shigo sai ki tambayeshi.'' Tace."Ai ba sai kin fada ba yanzu cikin watanshi nawa."? Shuru nayi ina tunanin watannin cikin.Uwale tace."Ai kin san cikin fari ba kowane yake iya gane sanda ya sameshi ba amma dai daka gani yayi kwari." Tace."Aikuwa dai cikin fari tunda ya huda zani ya fito to da alama daf yake da zuwa duniya." Uwale tace."To Allah dai ya raba lafiya." Cikin zuciyata na amsa da ameen ameen....Nace."Gwaggo a ina amaryar Kawu zata tare."? Tace."Can unguwar gadon kaya ne Khalid ya siya mata gida mai kyau shine uwarsa take bakin ciki yanzu maganar da nake miki ma tayi yaji tana gidansu sannan har gida Jamila tazo ta zageta taci mata mutunci tas." Nace."Kai amma banji dadin wannan labarin ba wallahi.'' Uwale tace."Ai duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba to tasa ma ko d'umi ba za tayi ba.".................Khalid tun bayan kammaluwar daurin auran ya tafi harkokinsa bai dawo ba sai yamma likis sai da yaci abinci ya samu damar gabatar da sallar magariba.........Gwaggo ta kalleshi bayan dawowarsa daga massalaci tace."Sannu munafiki to abinda kuke 'boyewa yau Allah ya nuna min." Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta. Ta kalleni da fadin." Kince shima bai sani ba ko."? Nace."Eh mana Khalid ko kasan ina dauke da juna biyu."? Kamar wani shashasha ya girgiza kansa." Mafici ta kwada masa da fadin " Ni zaku mayar shashasha ko."? Hankalinsa ya shiga yana kallona babu wasa a tare dashi yace."Yaushe kika samu cikin bani da labari."? murmushi nayi da fadin." Tsayin wata biyar kenan." Ya dinga kallona yana so ya gazgata magana. Nace."Kada kayi kokwanto domin kai ka kasance mara kula shiyasa baka fahimta ba amma lokatan da nake gudunka da kamshin turaranka yaci ace ka gane abinda yake da akwai."
Inda nake ya dawo ya fara kokarin daga rigata. na rike hannunsa da fadin." Me za kayi."? Kai tsaye yace." Gani zanyi." Gwaggo tace" Bude masa ya gani ya tabbatar.'' Kin bude masa nayi ya janyo ni jikinsa ko kunyar Gwaggo ya daga rigar cikina suka tsirawa ido ita dashi Gwaggo ta share hawayen farin ciki a fili tace.''Allah kasa ina da rabon ganin abinda ke cikin nan." Shi kam hannu yasa ya dauke 'yar 'kwallar dake kokarin fitowa daga idonsa yasa hannu kan cikin yana shafawa a hankali a hankali yace."Gwaggo kinga yaro na a cikin Aunty ko."? Gwaggo tace."Eh na gani Jarumi ikon Allah ai yafi gaban wasa ashe da kai zata fara haihuwa duk aure-auren da tayi kaddara ce rabon yana tare da kai." Yace."Gwaggo babu abinda zance da Ubangijina da yayi min wannan kyautar.'' Tace."Kwarai kuwa baka da bakin magana amma abinda za kayi ka kara kusanci dashi shine salatin ANNABI MUHAMMAD (SAW) Yace."Allah ya karawa Annabi daraja da wasila filjannati." Gabad'aya muka amsa da "Ameeen ya Allah.'' Zaune na mike ina gyara rigata yana min wani irin kallo ya janyo ni jikinsa rungumeni yayi tsam-tsam a jikinsa yace." Gwaggo ina rokon Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya a zamantakewar auranmu sannan ina rokon Allah ya azurta mu da zuria masu albarka." Tana murmushi ta amsa da "ameeen ya Allah Jarumi Amma meye makomar Jamila ne."? Ajiyar zuciya ya sauke yace " Gwaggo nasha fad'a muku cewa babu wata mace da zan bari ta wulakanta min iyayena tun ranar dana samu labarin irin cin mutuncin da yarinyar tayi wa Ummatu na datse igiyar aura na da ita taje tayi aure ni na gama zama da ita har abadah." Gwaggo tace."Subahanallahi amma gaskiya banji dadin wannan al'amarin ba Jarumi me yasa ka yanke irin wannan hukuncin kana so duniya ta zage mu ko."? Yace "Gwaggo rabuwa ta da Jamila ita tafi alkairi saboda haka kiyi addua akan Allah yasa hakan shi yafi alkairi." Tace."To shikkenan Allah ya kyauta amma yana da kyau kaje kayi bikon mahaifiyarka a gidansu." Yace."Babu inda zanje mijinta shine zaije yayi bikon ta idan yana bukatar zama da ita saboda haka kada ki sake sanya ni cikin al'amarin tunda lokacin da sukayi auransu ban sani ba." Yanda ya fadi maganar ya nuna mata cewa ransa a 'bace yake. Tace."Kayi hakuri ba laifin Ibrahim bane tunda shi dai bece mata ta tafi gida ba itace ta tafi." Yace."To idan yana ra'ayin cigaba da zama da ita sai yaje yayi bikon ta." Tace."Sosai kuwa ai dole ma yaje ya daukota ta dawo dakinta ta zauna kishiya kuma ba akanta aka fara ba.".............Kwanciya nayi bacci na nema ya dauke ni yace na tashi mu tafi gida Gwaggo tace." Ka barta ta kwana mana." Girgiza kansa yayi yace." Gwaggo mai rabani da matata sai mutuwa ba zan barta ba" Tace."To ai shikkenan ba sai ka fada min bakar magana ba." Ni dai dariya kawai nake musu tana fada yana fad'a haka muka fito har soro ta rako mu tana mana fatan alkairi...............Bacci nayi a motar sai da muka isa gidan ya tashe ni da kansa ya bude min mota na fito, ya rike hannuna muka nufi cikin gidan sai tarairayata yake har yaso ya bani tausayi. tare mukayi wanka na dinga Jin feelings na taso idona a lumshe nake kallonsa yana cud'a jikinsa nace."Kazo kayi min idan ka gama. Yace."Okey kada ki damu ." Yana gamawa ya daura towel yazo yana min duk sha'awar dake taso masa danneta yayi ya kauda kansa yayi mata wankan kamar yanda ta bukata, yayin da ita kuma nata b'angaran tayi masifar galabaita sai kallonsa take tana lumshe ido da lasar lips hannunta ya rike suka fito daga toilet din gefan bed ya zaunar da ita ya bude wardrobe kayan bacci ya dauko musu yasa nasa ya karaso gadon da nata, da kyar na iya kar'bar kayan nasa a jikina na kwanta ina kallonsa zaune a Sofa yana duba wayarsa a sarqe nace."Kazo ka kwanta mana." Yace."Yanzu zanzo kada ki damu." lumshe idona nayi ina jan ajiyar zuciya.....Jin shigowarsa cikin bargon yasa na sauke ajiyar zuciya dan motsawa nayi na Juyo ina kallonsa idonsa a rufe bakinsa yana motsi da alama adduar bacci yake.....Sunansa na kira ya bude ido yana kallona nace."Babynka yana bukatar ku gaisa." Murmushi yayi yace " Yanzu zamu gaisa" Dad'i ne ya ratsa ni, dan matsowa yayi ya daga rigar jikina sumbatar cikin ya dinga yana surutai Na dinga murmushi ina kallonsa ya gyara min rigar yana kallona fuskarsa na fitar da annuri yace."Mun gaisa yace yana gaishe dake." Dariya nasa nace."Aa ni ba irin wannan gaisuwar nake so kuyi ba." Tsira min ido yayi yace" Wace iri kike so."? Jikinsa na matsa nasa hannuna a kirjinsa da fadin.'' Irin wacce kuka kwana biyu bakuyi ba." Yace." To ai ke kika hana mu shiyasa na kyale ki." Da sauri nace." To yanzu ina bukatar ku gaisa" a kasalance yace."Kin amince kenan."? Nace." Eh na amince ku gaisa sosai da sosai." Murmushin jin dadi yayi yasa hannu ya janyota jikinsa ya rungume ta tsam-tsam! a kirjinsa suka dinga sauke wani irin numfashi........
*ALHAMDULILLAHI*
_Jama'a Nan na kawo 'karshen wannan Littafin mai suna GA IRINTA NAN! Ina rokon Allah ya yafe min kuskurena ladan dake ciki kuma Allah ya had'amu dashi Ina mika godiya ga 'Yan Vip group godiya ta mussaman a gare ku, dubban masoyana ina godiya ta mussaman nagode kwarai da adduarku Allah ya kara kauna ina alfahari daku?????? Sai mun sake saduwa daku a littafina mai zuwa. NAGODE_
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
*BABBAN YARO*
*MASHAHURI*
*LADADI KWADAGA*
*SADAUKI OMAR*
*NIDA YAYA SADAM*
*TSANTSAR BUTULCI*
*'YAR BANGAR SIYASA*
*DA WATA A KASA*
*MADADI*
*RUWAN DARE*
*KWARYA TABI KWARYA*
*GA IRINTA NAN*
*Ga mai bukatar d'aya da cikin books din sai ya nemi wannan numbers domin karin bayani 08089965176_07084653262* *BINTA UMAR ABBALE*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login