Showing 45001 words to 48000 words out of 185789 words
abinci ba domin ka kori yunwar dake damun ka ita kanta yunwar wata matsala ce mai zaman kanta saboda haka kaci abinci kawai ka kwanta kaja istgifari akan abinda kayi."
Yace."Salmanu Istgifari tun ina kan aikata al'amarin nake yi sai dai kace na d'ora wani akan wanda nake amma ni ma babu shakka nasan nayi kuskure mai muni kuma wallahi sai yanzu nadama da dana sani suka dame ni Salmanu abinda hakuri bai baka ba rashin sa ba zai baka ba, na bi son zuciyata na janyowa iyayena zagi shine babban abinda yake damuna."
Salmanu yace."Idan maganar ta tsaya a cikin gidanku ai asiri ya rufu amma kuma gaskiya banji dadin yanda kake nuna rashin damuwarka akan Aunty Sa'idar ba yanda na lura kamar kafi fargabar halin bakin cikin da iyayenka zasu shiga."
Yace."Hakane Salmanu ina tausayawa iyayena sosai akan aunty Sa'ida domin ni ina ganin duk abinda ya faru a tsakaninmu itama tana da laifi mai zai sanya ta dinga zagi na tana nuna ban isa ba Salmanu idan kaga irin cin mutuncin da take min sai kayi mamaki wannan dalilin yasa na yanke mata irin wannan hukuncin dan data bini a sannu a hankali duk haka ba zata faru ba."
Salmanu yace."Gaskiya ne maganar nima ko kad'an bana son raini su kuma mata daga zarar sun d'an girmaka ko yaya ne sai su rainaka itama abinda tayi maka bata kyauta ba Ai *GA IRINTA NAN!* abu yazo ya faru gabad'aya kai da ita kun fad'a cikin masifa kuncin rayuwa."
Ajiyar zuciya ya sauke ba tare da ya sake cewa komai ba ya dauki pure water daya yasa a bakinsa sosai yaji dadin ruwan saboda yanda ya sanyaya masa kirji Salmanu ya bude fulas din abinci da kansa ya zuba masa wanda zai isheshi yasa masa cokali a ciki ya tura masa gabansa.......
*Littafin na kudi ne.....Kada ki siya ki fita dashi, Idan kika ganshi kada kiyi sharing a gruops.......'Yar uwa idan kika karanta min littafi baki biya ba to ina binki bashi.....idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake.....Vip gruop#600....normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umat gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta whsap da wannan number.*
07084653262
08089965176
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*26&27*
Cikin ikon Allah gami da tasirin addu'oin dana durfafa bacci mai nauyi ya dauke ni tunda na kwanta kuma ban farka ba sai asubah...... da salati a bakina na bude idona lokacin itama Gwaggo ta tashi zaune tana laluben torchlight d'inta. "Sa'ida tashi asubah tayi ina tunanin ma an idar da sallah dan ga gari nan ya fara haske." Waya ta na laluba na kunna inna duba lokaci shida da kwata ba a jima da idar da sallah ba.
cikin rashin 'kwarin jiki na mike buta na dauka zan fita tace."Kada kisa ruwan sanyi a gabanki Sa'ida akwai na zafi a fulas ki surka."
Ba tare da nace mata komai ba na surka ruwan na fita dashi a hannuna kai tsaye band'akin nayi nufin shiga Ummatu ta fito daga ciki da buta a hannunta.
Sai nayi saurin kaucewa na bata hanya, ta tsaya tana watsa min kallon banza kafin tace."An dai ji kunya an kuma aikata abin kunya Insha Allahu sai asirinki ya tonu a gari kowa sai ya gane mugun halinki.''
Uffan bance mata ba na shige bandakin ina jin wani irin tsanarsu ita da d'an nata.
Koda na tsuguna domin fitsari sai da na kusa kuka dan gurin rikice min yayi da zafi kamar wanda akasa reza aka tsatstsaga.
Ruwan zafin na fara watsa a gurin ina rintse idona anya kuwa ba zan amince da shawarar Gwaggo ba muje asibiti a duba gurin nan kada yaron nan fa ya jefa ni a matsala.
Idona na rufe ina watsa ruwan a gurin ina tunano irin girman Joystick d'insa babu shakka Allah yay masa hallita sosai tabbas wani abu mai muni yana iya faruwa dani tunda gashinan gurin ya kume! sai zafin azaba yake min
Sai da na 'karar da zuwan d'umin tas na mike a hankali tare da mayar da wando na na fito lokacin Ummatu ta jima da barin gurin
Daki nayi nufin zuwa na dauko brush ta fito dashi a hannunta. hannu nasa na kar'ba tace."Ai naga baki dauka ba shine nace ko mantawa kikayi." A hankali nace mata ina sane ban manta ba.
Hanyar bandaki ta nufa kafin ta shiga sai da ta jima a tsaye a bakin kofar bandakin tana addua sannan ta shiga.
To koda na idar da sallah zamewa nayi na kwanta kan daddumar na shiga tunanin irin rayuwar da zan fuskatanta anan gaba nasan dai dole sai na fuskanci kalubale mai muni tunda nayi rashin babban abu mai muhimmanci a tare dani.
Tana shigowa dakin kira ya shigo waya ta da sauri tace."Yauwa duba ki gani ko shine." hannu na mika na dauki wayar ina kallonta nace."Wa kike nufi.''? Tace."Khalid mana." Kawai na tsaya ina mata kallon mamaki kafin nace." Gwaggo Khalid ya kira ni a waya yace dani me."?
A sanyaye tace."Ai ba zai rasa abin fad'a ba dan jiya kwana nayi ina mafarkinsa wai yana cikin mawuyacin hali kuma a mafarkin da nayi dashi ya bani hakuri yana hawaye yace duk abinda ya faru tsautsayi da qaddara ne shiyasa nayi tunanin ko zai kira ki a waya ya baki hakuri."
Kai na girgiza nace."Kinga Gwaggo kiyi sallar ki kina 'batawa kanki lokaci waya ba Khalid ne ya kira ba Alhajina ne."
Sai tayi min shuru ta hau gyara zaman hijabinta a wuya.
Alhaji Nura wayar ya sake kira bayan katsewarta na d'aga cikin nutsuwa nace."Ranka ya dade barka da asubah ina fata ka tashi lafiya."?
Ajiyar zuciya ya sauke yace."Sa'ida kina ina ne ina kiran waya kusan sau uku tana katsewa."
Nace." Bana kusa da wayar ne shiyasa kayi hakuri." Yace."Okey babu damuwa ya gida yasu Gwaggo ina fatan kowa lafiya."?
Nace."Alhamdulillahi ina lafiya Gwaggo ma haka." Yace."To masha Allah nace ya shirye-shirye ina fatan duk wani abu da kike bukata kin rubuta insha Allahu ranar juma'a nake so a kawo lefe idan yaso idan sati ya zagayo a daura auran."
Naji gabana ya wani irin fad'uwa ! shuru nayi duk na rikice bakina yayi nauyi sai magana yake na kasa bashi amsa ina can ina tunanin yanda zata kaya.
"Gimbiya kina jina ina magana kinyi shuru nace wane shiri da tanadi kika yi min a matsayina na ango."
A sanyaye nace."Alhajina kenan kada ka damu nayi maka tanadin alkairai masu yawa ni dai buri na ka ri'ke ni tsakani da Allah da amana kuma kayi adalci a tsakani na da matarka."
Yace."In dai wannan ne kada ki damu Sa'ida ni tsayayye ne a gidana matata kuma baki da matsala da ita tana da saukin kai da fahimta inaso idan kinje ku had'e kanku kuma ki bata girmanta."
Nace."Insha Allahu zan kiyaye nima sai kace mata ta dauki ni a matsayin 'yar uwa ba kishiya ba." Yayi dariya da fad'in "Ai tuntuni da haka ta dauke ki kullum idan zanzo gurinki tana bada sakon gaisuwarta yanzu haka ma tana kusa dani a kwance.'"
Nace."Naji dadi sosai da irin kulawar da take min dan Allah kace ina gaisheta." Yace." Bari kawai na bata wayar ku gaisa." kafin nace komai naji muryarta ta doki kunnena.
Muryarta naji cikin 'yar fara'a tace" 'Kanwata kin tashi lafiya."?
Cike da kulawa na amsa da "Lafiya kalau Wallahi ya kwanan yara."? ta sake 'Yar dariya da fadin." Yaran ki sun kwana lafiya suna can suna shirin skull." Nace."To masha Allahu Allah ya basu ilimi mai amfani."
Ta amsa da "ameen 'kanwata ki gaishe min da Gwaggo da kyau." Nace."Insha Allahu za taji." sallama mukayi naji muryarsa yana fad'in "Gimbiya sai an jima ko."?
Cikin jin nauyi nace." Eh Alhaji yanzu zanyi shirin makarana ne." Yace."Okey to babu damuwa bari na barki ki shirya idan anjima na sake kira."
Nace."To shikkenan sai an jima." da sauri na kashe wayar domin ba naso magana ta cigaba da tsayi a tsakanin mu kodan saboda matarsa dake kusa dashi.
Gyaran muryar ta naji kafin tace."Amma matar nan tana da kirki da alama kuma zaku zauna lafiya da juna dama ai tuntuni nake samun labarin kirkinta a bakin Uwale tace ai ta fito daga babban gida ne.''
Nace."Nima nayi mamakin yanda take mu'amula dani da alama tana da sau'kin kai ba kuma ta dauki al'amarin da zafi ba."
Gwaggo tace."To Allah ya kauda 'yan gaza gani akan al'amarin." Nace." Ameeen ya Allah."
Shuru d'akin yayi na minti biyu ta kalle ni da fadin."Naji kina maganar zuwa makaranta haba Sa'ida yanzu sai ki shiga cikin jama'a kina tale 'kafafu har yanzu fa tafiyarki bata dawo daidai ba."
Shuru nayi ina tunanin maganar ta tabbas nima nasan tafiya ta ta sanja domin ina jin jiki gurin taka kafafuna nace."Gwaggo inaji dai shawararki zan duba.
Kallona tayi, nace."Idan mun karya zaki raka ni asibiti a duba gurin nan a gani ni kadai nasan azabar da nake ji."
Tace."Haba dama ni jikina yayi sanyi da yanayin yanda kike tafiya kafafu a bud'e Allah dai yasa yaron nan bai 'kara miki kofa ba."
Gabana ne ya fad'i! na sunkuyar da kaina ina addua Allah yasa kada maganar Gwaggo ta zama gaskiya idan Khalid yayi sanadiyar bud'ewar gabana ai ya cuce ni.
Hankalina ya tashi nace."Gwaggo tashi ki shirya mu tafi asibitin nan." Tana kokarin magana Kawu Iro ya daga labulan dakin da alama daga massalaci yake...a nutse suka gaisa da mahaifiyarsa na gasheshi ya amsa cike da kulawa yana tambayar jikina.....A sanyaye nace."Da sauki Kawu."
Yayi jim! kafin yace."Gwaggo yanzu yanzu Salim abokin Khalid ke sheda min cewa jiya ya kirashi a waya sunyi magana da juna."
Gwaggo da sauri tace."Yauwwa to Alhamdulillahi me yace dashi dan wallahi jiya kwana nayi ina munanan mafarkai akansa.
Kawu Iro ya girgiza kansa da fadin"Gwaggo dole kiyi munanan mafarkai akan Khalid domin kuwa ya aikata abu yazo ya dameshi a maimakon yazo ya nemi gafara sai kawai ya yanke shawarar barin gari yanzu haka dai ba'a san inda yake ba.
Murya na rawa tace."Kai jama'a! wannan wace irin masifa ce."? da sauri yace."Gwaggo daina kiran masifa shi da ya janyo ta to akansa zata 'kare."
Gefan hijabinta tasa ta goge hawaye da fad'in "Wannan yaro Allah dai yasa baiyi nisa da gari ba Ubangiji Allah ya karkato hankalinsa ya dawo gida.
Kawu yace." Gwaggo Khalid gwara yayi nesa damu domin hakan shine nutsuwa da kwanciyar hankalinmu."
Tace."Haba Ibrahim ai hannunka ba zai ru'bewa ka yanke ka yar kayi hakuri ka yafe masa." Kallonta nayi ina mamakinta wato dai Gwaggo wahainiya ce mai sanjawa a duk sanda ta so jiya babu irin zagin da ba tayi wa Khalid ba amma yau gashi kuka take a kansa duk ta tashi hankalinta har ta manta abinda ya aikata.
Kawu Ibrahim na kokarin barin gurin Ummatu ta karaso hannunta ri'ke da tire na silba mai fadi kayan karin kummalo ne a kai.
Ta shigo dakin tare da ajiye tire din a gabanta a dakile ta gasheta Gwaggo ta shaqi hanci tana amsawa tace.''Rabi bukatar ki ta biya akan Khalid kinyi masa baki ibtila'i ya sauka a kansa *GA IRINTA NAN!* mai afkuwa ta afku ya tattara kayansa ya bar gari gabadaya."
Ummatu gabanta na faduwa tace."Gwaggo wace irin magana ce wannan? wane irin baki zan jefi d'an ciki na dashi dan Allah Gwaggo ki dinga tauna magana kafin ki fad'eta."
Gwaggo a fusace! Tace."Haba Rabi wallahi ko shakka ba nayi bakin ki ne ya kama yaron nan me yasa kika dinga zaginsa har kina masa Allah ya isa idan ya sake magana da Sa'ida ashe har ke kin isa ki raba shi da 'yar uwarsa."?
Ummatu shuru tayi tana nazari! dama tasan tsakaninta da d'anta Babu sirri komai za tayi masa sai yazo ya fad'awa kakarsa ashe zuwa yayi ya fad'a mata gargadin da tayi masa akan Sa'idar.
Gwaggo tace."Wattanin da suka gabata yaron nan yazo gurina ransa a 'bace yake sheda min abubuwan da kukayi masa keda mahaifiyarki wato kece harda cewa duk sanda ya sake wata magana da Sa'ida Allah ya isa to gashinan Allah ya isan da kikayi masa ta sauka a kansa Rabi kin cutar da d'anki da kaifin bakin ki."
Ummatu jikinta yayi la'asar cikin 'kokarin kare kanta tace."Aa Gwaggo ki daina wannan magana ni bance masa Allah ya isa ba nasan dai nayi masa fad'a a kancewa kada na sake gani ya shiga sabgar Sa'ida domin ba sa'arsa bace."
Gwaggo tace."Ke har kin isa ki raba zumuncin da Allah ya halasta? akan wane dalili zaki raba shi da 'yar uwarsa."? jin yanda take daga murya yasa tayi saurin mi'kewa domin fita daga dakin dan bata so mijinta yaji abinda yake faruwa.
Gwaggo cikin masifa tace."Shashashar uwa kawai wacce bata aiki da ilimin ta haka kawai saboda rashin tsinkaye da tunanin abinda zai faru a gaba kin cutar da danki."
Ummatu dai uffan ba tace mata ba ta shige gurinta jikinta a masifar sanyaye Khalid ya gudu ya bar gari to ina ya nufa? wasu zafafan hawaye suka shiga sauka a fuskarta ta zauna a d'an tsakar gidanta tana kuka mara sauti tare da nadamar abinda tayi.
*Hattara Iyaye masu kausasa kalma a kan 'ya'yansu ku kiyaye yi wa 'ya'yan ku Allah ya isa ko kuma jeka zaka gani wannan kalmar tana da had'ari sosai duk halin da d'anki ya shiga kece sanadi*
Gwaggo bayan fitar Ummatu Kukanta taci ta koshi ina kallonta da mamakin halayyarta da kyar ta iya shan kunu taci kosai uku ta janye tiran daga gabanta...Lokaci ni har na gama shiryawa na kalleta babu walwala a tare dani nace."Shin zaki raka ni asibitin ko kuma nayi tafiyata."
Tace."Zan raka ki mana Sa'ida tashin hankalin tafiyar Khalid ne ya hana ni shiryawa baki ga ma ko karyawa na kasa yi ba."
Ba tare da na kalleta ba nace."Ke ki kaga zaki iya." shuru tayi min ta miqe ta fita minti uku ta dawo dakin ta dauki mai ta shafa a kafafunta hijabin ta tasa da fad'in "Ai asibiti ne ba wata kwalliya ake ba."
Ba tare da nace komai ba na miqe da jakata a hannuna bayana ta biyo da kwad'o (mukkuli) a hannunta.....kar'ba nayi na kulle kofar dakin. kana muka kama hanya muka tafi.
Pravite hospital mukaje na yanki kati kai tsaye ofis din da aka tura ni na nufa....lokacin akwai wata a ciki sai da ta fito tukkuna na shiga Gwaggo tana kokarin bina nace ta zauna na shiga na fito.
A nutse ta kalleni bayan ta gama sauraran jawabi na tace."Sa'ida dole zaki kwanta a gado na dubaki dama ai mafi akasari irin haka na kasancewa mussaman a daran farko akan samu matsala irin wannan matsalar."
Hawaye suka cika idona wai daran farko naji takaicin wannan magana tata, babu kuzari a tare dani na shiga d'an d'akin data nuna min na shiga na kwance zani na tare da cire pant d'ina.
bayan na kwanta a gadon tasa safa a hannuwanta ta shiga duba gurin hawaye masu zafin gaske suka shiga gudana a fuskata wai yau ni Khalid ya janyowa wannan tozarcin.
Kallona ayi tare da fad'in "Ki tashi baki da wata matsala abinda yasa gabanki ya tsatstsage lokacin da mijin naki yazo ka kar'bar hakkinsa kinyi gaddama hakan shi ya janyo miki matsala shiyasa kullum muke fada cewa duk budurwar da mijinta yazo kar'bar hakkinsa a daran farko to yana da kyau ta bashi hadin kai kada tayi wani yunkuri domin ceton kanta dan ko tayi ba zai bari ba daga karshe ma ta janyowa kanta wata matsala amma dai ke gabanki normal yake bai kar'u ba zafi da rad'ad'i kuma zaki daina ji insha Allah yanzu zan rubuta miki magunguna idan kun fita sai ki siya."
Cikin kokarin danne damuwar dake taso min nace."Nagode Dr." safar hannunta ta cire ta watsa a dustbin kafin ta fita daga dakin.
Kati na ta miko min mai dauke da magungunan data rubuta min...na kama hanya zan fita ta dakatar dani. juyawa nayi ina kallonta a tausashe tace."Sa'ida kada kice naiyi miki katsalandan kamata yayi ace tare da mijin naki ku kazo asibiti.
Kaina na sunkuyar ina nazarin maganar da zan fad'a mata....."Wallahi tafiya ce ta kama shi a washe garin ranar daurin auran mu shine dalili."
Kallona naga ta nayi kamar bata yarda da maganata ba, nace."Dr nagode da kulawarki." hannu ta d'aga min da sauri na fita daga ofis din ina mamakin bin
diddigi irin na mutane....
*Littafin na kudi ne....kada ki siya ki fita dashi idan kika ganshi kada kiyi sharing.....'yar idan kika karanta min littafi baki biya ba ina bin ki bashi....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake.......Vip gruop#600....normal gruop#300....account.. 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*30&31*
Cikin wani irin yanayi na damuwa Salmanu ya shiga dakin ya same shi.....Ya ajiye fulas din abincin a gabansa da fadin"Abokina yane na ganka a cikin wani irin yanayi dubi yanda kake zabga gumi sai kace wanda yayi tsere." Ajiyar zuciya ya sauke ido jawur yace."Salmanu dole ne ma