Showing 162001 words to 165000 words out of 185789 words
tace."Ya zaki girgiza kai bayan akwai dalili." Kallonsa tayi da fadin." Yanzu nan Jarumi ya fita bayan ya gama rashin arziki na zaunar dashi na sheda masa hukuncin da muka yanke kai tsaye yace shi ba zai aureta ba shine abin yayi mata ciwo take kuka."
Kawu Ransa ya 'baci yace."To tunda haka ya za'ba shikkenan itama Jamilan ba zai aureta ba sai yaje ya nemi wata." yana gama maganarsa ya bar gurin cikin bacin rai.
Gwaggo tace."Hakan shine hukunci dama ai ba kowa ne yake zuga shi ba sai uwarsa da 'yan uwanta to itama Jamilan sai dai ta hakura yaje ya nemi auran a wani wajen.''
Ummatu tana share hawaye ta d'aga labulan dakin tace"Gwaggo wallahi ni bani na hana yaron nan auran 'yar uwarsa ba ku daina daukar alhakina.''
Gwaggo tace."To idan bake bace wacece Rabi aini babu abinda zance dake tunda dai bakya so ya yaron ki ya auri Sa'ida to itama Jamila sai ta ha'kura haka shi yafi alkairi."
Hawaye ta share da fad'in "Ni dai kiyi masa magana ya janye maganar yi min kishiya meye laifina a cikin al'amarin da har za'ayi min kishiya."
Gwaggo murmushi tayi tace."Ai ba zan hana abinda Allah ya halasta ba Rabi ke kin kasa tursasa d'anki ni kuma sai kizo ki sani na tauyewa d'ana rayuwa idan mata uku zai aura ba zan hana shi ya more rayuwarsa ba."
Ummatu hankalinta yayi masifar tashi tana kuka ta koma sashenta, zama tayi tana tunanin mafita babu shakka dole ta zauna da yaron akan al'amarin dan tana ji tana gani ba zata bari ayi mata kishiya ba.
Sai can dare ya dawo gidan yana kokarin bude dakinsa ta fito daga daki ya kalleta da mamaki a tare dashi yace."Umma baki bacci ba.'?
Tace."Eh na zauna zaman jiran shigowarka.''
Yace."To Allah yasa lafiya." Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace."Khalid babanka duk ya sheda min abinda yake faruwa ashe sun yanke maka hukuncin auran Sa'ida ban sani ba."
Yace."Eh nima dazu Gwaggo ke sheda min sai dai na nuna mata cewa bana ra'ayin hakan."
Tace."Ka aureta na baka Umarnin hakan." Wani sanyi yaji ya sauka a zuciyarsa dama abinda yake so yaji kenan daga gurinta.
Ya nuna kamar baya murna da al'amarin yace."Umma kina ganin babu matsala ba naso keda ita ku dinga samun matsala tunda jininku bai had'u ba."
Tace."Babu matsala mutukar zaka nuna mata cewa ni mai muhimmanci ce to zamu zauna lafiya."
Yace."Umma ba zan iya had'a ki da kowa ba saboda ke mahaifiyata ce babu wata 'ya mace da zan aura ta wulakanta min ke sabida haka ki kwantar da hankalin insha Allah ba zan bari ki wulakanta ba."
Murmushin jin dadi tayi tace."To nagode yaron kirki bari na kawo maka abinci." Yace."To nagode Ummana." kicin ta nufa shi kuma yana murmushin jin dadi ya bud'e dakinsa ya shiga cike da nishadi ya cire kayan jikinsa domin ya watsa ruwa.
Washe gari da safe kafin ma mahaifinsa ya tare shi da maganar shi ya rigashi bayan sun gaisa yake sheda masa da cewa ya amince zai had'asu su biyun ya aura.
Yace." Hakan shine yafi maka alkairi da zaman lafiya saboda haka sai ka fara shirye-shirye domin ba zamu ja dogon lokaci ba.''
Yace."Insha Allahu komai za'ayi komai cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." Kawu barin sa yayi a tsugune a gurin ya shige daki......Mikewa yayi ya nufi kofar Gwaggo domin su gaisa.
Kawu ya kalleta da fadin." Kin Umarci Yaron nan da ya amince da bukatarmu ko."? shuru tayi tana kallonsa yace."To ki sani hakan da kikayi ba zai hana ni na 'kara aure ba domin tuntuni mun riga mun gama daidaitawa da matar da zan aura dan haka sai ki shiga nutsuwarki." Ummatu baki a sake take kallonsa har ya gama abinda yake ya fita daga dakin......Jiki a masifar sanyaye ta nemi guri ta kwanta tana sak'awa da kwancewa tunda take bata ta'ba tsammanin Mijinta zai iya yi mata kishiya ba, hawaye masu zafin gaske suka dinga sauka a fuskatarta.
Khalid yana can dakin Gwaggo yana neman magana lokacin daya shiga dakin tana bandaki wayarta ya hango kan gado yaje ya dauka yana mata binkice duk number da ba tayi masa ba sai da ya goge sai tsaki yake ja yana girgiza kai.......Cikin wannan yanayin ta shiga dakin ta sameshi.
Hannu ta mike ba tare da tayi masa magana ba. ya harari hannun tsaki yaja ya cigaba da abinda yake da wayar.
Da karfi ta fizge wayar daga hannunsa ta fad'i gurin dake tayi wawar faduwa a take komai yayi pieces a gurin.
Gwaggo tace."Subahanallahi wai me yake damun ku ne sai kuyi ta fad'a sai kace tsofaffin karnuka a haka zakuyi auran."
Ba tare da yace komai ba ya mike zai fita daga dakin da sauri na wafci wayarsa dake aljihun gaban rigarsa ban tsaya jiran komai ba na buga ta da bango." Gabad'aya ta watse a gurin.
Ido jawur yake kallona "Kin san kudin wayar nan kuwa zaki buga min ita da bango(garu)
Hannu na daga masa da fadin." Kaga ban bukaci sanin kudin wayarka ba kawai ka daina shiga sabga ta meye zaka daukar min waya kana duba min."
Rai a 'bace yace.''Dole nayi bunkice a wayarki saboda nasan baki da gaskiya ina so ki daina hurd'a da kowane namiji mutukar kina bukatar ki zauna lafiya."
"Ko an daura min aure da kai baka isa ka hana ni mu'amula da wanda ya cancanta ba namiji ko mace so saboda haka wannan abin bashi ne mafita ba."
Girgiza kansa ya kalleta da fadin .''Gwaggo kina jina da ita ko." ? Tace." Khalid kaine mai laifi ina ruwanka da wayarta ai sai ka bari a daura auran in yaso sai ka fara kafa mata doka da ordar."
Yace."Okey kema abinda zaki ce kenan? auran nan fa tilas akayi min.'' Tace." Kaga ba cewa nayi ka 'bata min rai ba kazo kayi tafiyarka inda zakaje aure tilas akayi maka kuma idan ka kwantar da hankalin ka zai zame maka alkairi."
Tsugunawa yayi ya kwashi sim card dinshi ya fice daga dakin yana wani irin huci! tsaki naja raina a bace na zauna ina gyara wayata dake tarwatse a gurun.
Tace."Sa'ida don Allah ku sanyawa zuciyarku ruwan sanyi kece babba ki daina biye masa kuna shashanci na fiso idan kunyi aure ku zauna lafiya ku samu zuria masu albarka."
Cikin rawar murya nace."Gwaggo ya kike so nayi ne yaron nan fa ya raina ni kullum nunawa yake kamar shi yake gaba dani sam baya mutunta ni gashi ko wace irin magana idan ya tashi ya fad'a min babu abinda ya dameshi.
Tace."Hakuri zakiyi dashi Namiji ne koda babu alakar aure a tsakaninku dole ya dinga nuna miki iko da gadara duk da kin girmeshi to ballanatana kuma yanzu da zaki zauna a k'ar'kashinsa dole kiyi masa ladabi da biyayya."
Girgiza kaina kawai nayi ina tunanin yanda zama na zai kasance da yaron mutukar zai dinga nuna mun gadara da iko to babu shakka zamu kasance cikin fad'a da rashin zaman lafiya.
*BAYAN SATI UKU*
Al'amura suna cigaba da tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Ginin gidan da Khalid yake yayi nisa saura abinda ba'a rasa ba......Har yanzu babu cikakkiyar jituwa a tsakaninsa da Sa'ida ba dai sa fad'a sai dai da kyar suke kula junansu watarana ma haka zasu kwana su yini ba suyi magana da juna ba duk da cewar suna ganin junansu.
Jamila kuwa damuwa mai tsanani ta shiga a lokacin data samun labarin abinda yake faruwa taci kukanta ta k'oshi ta hakura Baito da Ummatu kuwa ai basu hakura ba sai yawon malamai suke wai lallai sai al'amarin auran ya ruguje sun kasa gane cewa komai nufin Allah ne.
Khalid lokacin da ya tashi had'a kayan aure komai iri d'aya ya siya sam bai bambamta tsakanin Sa'ida da Jamila ba abinda yayi wa budurwa shi yayi wa bazawara al'amarin da ya janyo cece kuce a can 'bangaran Ummatu kowa na fad'in albarkacin bakinsa Jamila kuwa yini tayi tana kuka ta dauka ai tunda ita budurwa ce zai bambamta da bazawara sai taga akasin haka.....K'awayen ta suka zugata akan tayi masa butsu ta nuna bata yarda ba.......Aikuwa ranta ne ya 'baci ta gwammace bata kira wayarsa ba dan masifa ya balbaleta da ita yace haka yayi niyya idan bata son kayan taje ta bayar shi babu wata mace data isa da sanja masa tsari. kashe wayarsa yayi ya bar ta cikin bacin rai.
Ummatu ma ranta ya baci mutuka amma saboda samun kwanciyar hankalinta a gidan yasa bata nuna bakin cikinta ba yanzu lalla'ba mijin nata take kada yayi mata kishiya shiyasa take masa ladabi da biyayya duk Umarnin sa bata tsallakewa.
Khalid a can Goran dutse bayan reka ya gina katafaran gida na gani na fad'a masoyansa suka cika da murna da farin ciki suna masa fatan alkairi.
Sati guda ana saukar al'kur'ani a gidan kafin a kulleshi aka cigaba da gudanar da shagalin biki.....Gidan Gwaggo cika yayi da mutanan kauyen Dambatta duk sun zo domin nuna farin cikinsu.....Bangaran Ummatu ma hidima take sosai ita da danginta.
Sa'ida tare suke gabatar da komai da Aminiyarta Hauwwa duk wani gyaran jiki tayi abinta sai dai kallo d'aya za kayi mata ka fahimci cewa kamar bata maraba da auran abubuwa da yawa sun tsaya mata a ranta tana tunanin irin zaman da za tayi da yaron kullum yana mata rashin mutunci da nuna cewa ita ba komai bace a gurinshi amma sam Jamila bata firgitata sabida ta san bata isa ta nuna mata komai ba.
Ana ya gobe daurin Aure Yaya Aminu yayi sallama da ita Kin fita tayi Gwaggo tace."Kije babu kyau wulakanci ai yanzu kuma duk wani mai naci a kanki dole ya hakura tunda gobe idan Allah ya nufa zaki zama matar wani saboda haka kije kiji abinda yake tafe dashi."
Hauwwa tace."Nima dai haka na gani ai babu wata matsala." Nace .'' To shikkenan tashi ki raka ni muje." Tace." To shikkenan.
Yana jingine jikin motarsa kansa a kasa a nutse muka 'karasa kusa dashi.......Cike da damuwa ya dago kanshi na sunkuyar da kaina ina jin dan tausayinsa a cikin raina.
"Yaya Aminu ina wuni ina fatan kuna lafiya ya kasuwa." Cikin alhini da damuwa ya amsa da fadin."Amarya ya shirye-shirye."? nace."Alhamdulillhi." Hauwwa ta gaishe ya amsa yana dan 'kallonta.
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace."Sa'ida a lokacin da komai na rayuwata yayi min sauki a lokacin ne kikayi nisa da rayuwata ina cikin wani hali na tsananin damuwa naso ace nayi doguwar rayuwa dake sai gashi Allah ya raba tsakaninmu na samu labarin daurin auranki gobe hankalina ya tashi mutuka daga baya nayi hakuri ba barwa Allah wannan dalilin yasa nace bari nazo nayi miki fatan alkairi Allah yasa haka shi yafi alkairi a rayuwarmu...
*Kika karanta baki biya ba ina binki bashi......Vip gruop#600...normal gruop#400....Account... 0542382124.....Binta umar gtbank.....idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.*
*07084652362*
*BINTA UMAR ABBALE**99*
Cikin nutsuwa nace."Nagode Yaya Aminu ina maka fatan alkairi a rayuwarka insha Allah Ubangiji zai mu sanya maka da mace tagari wacce ta fini komai da komai na rayuwa." Girgiza kansa yayi cikin wani irin yanayi yace."Bana tsammanin zan samu kwatankwacin mace kamar ki ni kaina nasan nayi babban rashi a rayuwata.
Murmushi nayi nace."Kada ka cire tsammani insha Allahu za'a dace." Murmushi yayi yana girgiza kanshi. hannu yasa a cikin aljihu key ya fito dashi ya miqa min da fadin." Ga wannan sannan za kiga sak'o na insha Allah."
Key din na kar'ba ina dubawa "Yaya Aminu wannan fa."? Yace." Mota ce na baki kyauta." shuru nayi ina kallonsa yace."Gata can acan tsallaken." da sauri na kalli gefan mota ce ta gani ta fad'a. Hauwwa na zubawa ido da fadin." Ki taya ni gani Hauwwa." Murmushi tayi tace."Kyautar manya kenan Alhaji Mungode kwarai Allah ya kara suttura." Da fara'a a fuskarsa ya amsa da ameeen ya Allah.
Kallonsa nayi cikin damuwa nace."Yaya Aminu anya kuwa wannan motar ba tafi karfina ba kuwa." ? Yana dariya yace."Kece kika fi karfin mota a gurina idan kuma zaki iya tuka jirgin sama sai na siya miki."
Hauwwa tasa dariya tana kallona. kaina na sunkuyar gabad'aya al'amarin ya daure min kai.
Yace."To ni zan tafi Allah ya sanya alkairi yasa gidan zaman ki ne."
Kaina na dago nace."Yaya Aminu nagode nagode sosai nima zanyi maka kyauta ina fatan zaka kar'ba hannu biyu."
Yace."Duk abinda ya fito daga gurinki ina bukatarsa.
Hauwwa na kalla tana tsaye tana murmushi nace."Wannan aminiyata ce bani da kamar ta ina fatan idan na baka amanarta zaka riqe da kyau."
Zuba mata ido yayi yana murmushi yace."Kai amma nagode da wannan kyautar Nayi miki alkawarin riqe amanar k'awarki.'' Murmushi nayi na kalleta da fadin."Hawwa ga amanar Yayana nan."
Kallona kawai take tana mamakin hukuncin dana yanke mata. murmushi nayi na kalleshi da fadin."Ya Aminu bani wayarka nasa maka number ta." da sauri ya bani nasa masa number.
Ya kalleta da fadin."To amanata sai na kira ko." murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta.....Yana kokarin shiga motarsa Khalid yayi parking din tashi.
Gabana ne ya fad'i! haka kawai nake jin tsoron masifar yaron.
Da sauri nace "Yaya Aminu ka gaishe da mutan gidan nagode sosai yace." Zasuji da kyau sai na shigo daurin aure gobe."
Nace."To Allah ya kaimu.'' Hauwwa ta matsa daga jikin motar yaja ganin Khalid din ya fito daga motarsa yasa ya sauke glass yana masa magana. Khalid sama-sama ya amsa yana d'aga masa hannu. da sauri nace."Hauwwa mu shiga gida.'' saboda ina jin tsoro kada ya wulakanta ni a gabanta.
Gabana ya tara na tsaya ina kallonsa. Sassauta fuskarsa yayi suka gaisa da Hauwwa ta shige cikin gidan ni kam tare ni yayi da gangar jikinsa ya matse ni a bango murde hannuna yayi ya kwace key din.
Yana wani irin huci yace."Wannan key din na menene."? Cikin faduwar gabana nace." Yaya Aminu ne ya kawo min mota a matsayin gift
Wani irin kallo yake min kafin yace."Ke kika nuna masa kina bukatar mota."?
Harara na watsa masa da fadin."Wace irin magana ce wannan haka kawai sai nace ya siya min mota shine yayi niyya."
Yace."Okey to kada kisa a ranki zaki shiga motar nan zan bashi key d'insa bana bukata kuma wallahi idan bai fita daga sabgarki ba zaku sha mamaki na dake dashi.''
Cikin galabaita nace."To naji matsa min hanya na shiga gida."
K'ara matseni yayi yana bin fuskata da kallo, idanuwana suka ciko da ruwa fitinar yaron nan har tsoro take bani."
"Me zan samu ne."? maganarsa ta dawo dani hayyacina kallonsa nayi idanuwansa sun k'ankance.
" Ba zaka bani hanya ba ko anya kuwa kana so auran nan yayi albarka kuwa."?
"Saboda me kika fadi haka."? ajiyar zuciya na sauke nace." Me yasa kake lalube ni a duk sanda ka samu dama wannan ba so bane sha'awa ce."
Fuskata ya tallafo yana kokarin had'a bakina da nasa fizgewa nayi da karfi na buge shi. zan bar gurin yayi gaggawa riko hannuna.
Wani irin numfashi yake saukewa ya matseni tsam-tsam a kirjinsa wasu irin maganganu yake fada min a kunne tsabar shiga rud'ani yasa sam ban fahimci komai ba sai da ya gama lugwigwita min jiki sannan ya sake ni....Hawaye na goge na tureshi da karfi na shiga gidan da saurin gaske.
*RANAR DAURIN AURE*
Cikin nufin Allah Khalid ya angwace da mata biyu wanda suka kasance 'yan uwansa na jini ranar daurin auran Gwaggo sai da tayi kuka saboda tsabar farin ciki babban burin ta ya cika ta had'a aure a tsakanin jikokinta guda biyu hakika tayi farin ciki da zuwan ranar.
'Bangaran Umma Habiba ma tayi nata taron daidai gwargwado sannan tayi zama na mussaman da amaryar tayi mata nasiha mai ratsa jiki ta kuma koya mata dabaru na zaman aure da kishiya daga karshe tayi mata fatan alkairi da samun zuria masu albarka.
'Bangaran Ummatu kuwa abin babu dadi da albarka dan babu wanda yake fadin alkairi sai sharri sun zaunar da Jamila sai hud'ubar banza suke mata ita kuma mara wayo ta zauna tana sauraransu sannan suka dirka mata maganin mata suna ganin kamar hakan dubara ce.
Ko wacce tana 'bangaran ta Sa'ida taji dadin hakan dama kwata-kwata bata bukatar abinda zai had'a ta da yarinyar kowa ya zauna a mazauninsa hakan yafi alkari.
Sai wajan d'aya na dare ya shigo gidan a mutukar gajiye abokansa ne suka riqeshi suna ta celebration na murnar auransa.
Kai tsaye part d'inta ya nufa gajiya ba zata hana shi abinda yayi niyya ba.
Lokacin da ya shigo dakin na jima dayin bacci motsinsa naji Lokacin da ya fito daga toilet zaune na mike ina kallonsa ya fito da towel ra taye a wuyanshi gaban mirror ya tsaya ya goge jikinshi turare ya fesa ya bude wardrobe jallabiya yasa ya juyo yana kallona.....dauke kaina nayi tare da mike kafafuna a gadon.
"Kije ki dauro alwala muyi nafila." Ba tare da nace masa komai ba na nufi toilet din. fita yayi daga dakin ya nufi gurin Jamila domin ya dubata
Bacci ya sameta tana yi ba tare da ya tasheta ya fita daga dakin tare da ja mata kofa.
Da hijabi a jikina ya same ni ganin ya tsaya akan dadduma yasa na mike na tsaya a bayansa, raka'a biyu muka gabatar ya daga hannuwa sama nima nayi irin yanda yayi muka jima a haka yana addua yana shafawa na shafa a fuskata mikewa nayi na koma gadon na zauna.
Kallona yayi babu walwala a tare dashi yace."Kinci abinci ko ."? Yanda yake 'bata rai nima haka ciki ciki nace .'' Eh naci." ba tare da yace wani abuba ya kashe fitilar dakin. Gadon ya k'araso ya cire jallabiyar jikinsa