Showing 42001 words to 45000 words out of 185789 words
ko ki barwa Allah zai saka miki sannan inaso ki dauki wannan al'amari a matsayin qaddara wacce ta riga fata insha Allahu Allah zai dubi maraicinki Khalid kuma da ya aikata miki wannan abu ni da kaina zan kaishi a hukuntashi .
"Ajiyar zuciya na sauke ina goge hawayen fuskata nace." Kawu insha Allahu zan sanyawa raina dangana akan wannan al'amari sannan maganar kai khalid hukuma ka janye nasan tunda zalinci ya aikata sai Allah ya hukuntashi a duniya ko a lahira."
Girgiza kansa yayi yace."Sa'ida idan nayi haka naci amanar zumuncin Allah kuma duniya zata zage ni dole ne na dauki mataki akan dukkanin wanda ya ta'ba martabarki."
Kafin nace wani abu yayi gaggawar fita daga gidan...jiki a mace na bishi da kallo ina girgiza kaina.
Ummatu yun'kurawa tayi zata mi'ke Gwaggo ta dakatar da ita da fad'in "Rabi kin gama koke-koken ne."? Ummatu ta zuba mata ido tana kallonta, Tace." To wallahi kada naji da wai! maganar nan ta fita waje al'amarin nan ya zama sirri a tsakaninmu idan kika fad'awa dangin ki maganar nan wallahi kinji na rantse sai kin fi kowa 'bacin rai."
Ummatu girgiza kanta tayi ba tare da tace mata komai ba ta kad'a kanta ta fita daga dakin ranta a mugun 'bace.
Inda nake bata kalla ba ballanatana ta tanka min ta bude kofar gurin ta ta shige tare da bugo kofar da karfin gaske!
A hankali na mi'ke na nufi dakin jiri da hajijiya na neman su kayar dani a gurin.
'Bangaran Khalid kuwa yana fita kai tsaye can Na'ibawa 'yan lemo ya nufa gidansu abokinsa Salmanu wanda suka gama karatu a tare tun kafin ya isa gidansu abokin nasa ya kirashi a waya ya sanar masa zuwan nasa sai kawai ya kashe wayarsa yasa a jakar kayansa yasan dole daka gida a nemi inda yake shiyasa ya kashe wayar gabad'aya.
Kawu Iro yana fitowa daga gidan kai tsaye Gidansu Salim ya nufa babban abokin yaron nasa yana kokarin aika yaro gidan Salim din ya fito ganinsa yasa da sauri ya risina yana gaisheshi.
Kawu ya amsa tare da Tambayarsa ina abokinsa yake.
Salim yace."Wallahi baba nima yanzu na dawo gidan na tarar da key na adaidaita sahu wai d'azu Ya aiko yaro dashi a ajiye min da nazo mahaifiyata take min bayani shine fa yanzu na fito da sauri zan siyi kati nasa a waya na kirashi naji dalilin da yasa ya kawo min key din
Kawu yace."Ai tuntuni nima nake kiran wayar tasa taqi shiga amma dai jeka siyo katin ka gwada kiransa ko Allah zai sa wayar ta shiga."
Salim da saurin gaske ya nufi gurin sayar da katin gabadaya hankalinsa a tashe yake da abinda abokinsa ya aikata a daidaita sahu wuya take a gari shi ya samu an bashi sojan gona yana samun kwabo da dari amma saboda bashi da hankali ya dawo da key din.
Kawu Iro kuwa bayan wucewar Salim daga gurin sai ya samu gefan dakalin dake 'kofar gidan ya zauna yana jiran dawowarsa.
*Littafin na kudi ne.....kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing.....Idan kika karanta min littafi baki biya ba na biki bashi.....'yar uwa idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake....Vip group #600...normal group #300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*24&25*
Jiki a sanyaye ya 'karaso kofar gidan nasu Kawu Iro na ganin yanayin fuskarsa ya gane akwai matsala Babu walwala a tare dashi yace."Ka kira wayar ne."?
Salim ya girgiza kansa da fadin"Wallahi kuwa Na kira ya kai sau bakwai tana katsewa gabadaya hankalina ya tashi da abinda Khalid yayi baba kasan sai da muka sha wuya sosai kafin mu samu adaidaita sahun nan amma kuma Khalid ya dawo da mukkulin babu wani dalili mai k'arfi.''
Kawu Iro ya miqe da fad'in "Salim ka kwantar da hankalinka Khalid dai a yanxu ba za'a kirasa yaro ba yana da hankali yasan abinda yake adaidaita sahu kuma daya dawo maka da ita kansa yayiwa mugunta sai kayi gaggawar mayarwa da mai ita a samu wanda yake bukata a bashi."
Salim yace."Kawu kayi hakuri dan Allah zan jira Khalid din ya dawo daga dik inda ya tafi sai naji dalilin da yasa ya aikata hakan.
Kawu Iro ya girgiza kansa cikin takaici yace."Salim zaka wahalar da kanka domin abokinka yayi nisa saboda yasan rashin kyautawar da yayi sabida haka nake shawartarka da kayi gaggawar mayarwa da mai babur din nan key d'insa."
Salim a sanyaye yace."To shikkenan Kawu insha Allahu gobe zanje na kai masa key din." Kawu ya miqa masa hannu sukayi sallama da juna ya wuce ya barshi a gurin a tsaye yana mamakin maganarsa to wane irin abun kunya abokin nasa ya aikata da har zaiyi nisa da gida." da yaga bashi da mai bashi amsa sai ya juya jiki a mace ya shiga cikin gidan nasu.
A ranar Ummatu qin d'ora tunkunya tayi har wajen tara na dare babu labari Gwaggo ta hau surutai akan lamarin Ina daga kwance nace."Gwaggo dan darajar Allah da Annabi kada ki sake tada wata tarzomar ki rabu da ita tunda ba tayi girkin ba ki dauki taliya ki dafa tunda kina da ragowar miya ni dai bana tsammanin zanci wani abu."
Tace."Haba Sa'ida ai wannan iskanci ne da wulakanci Ibrahim na iya bakin kokarinsa a gidan nan amma matar nan take kokarin tona masa asiri a unguwa yanzu bayan bakin cikin da muke ciki tana so mu kwanta da yunwa kenan."
Nace."Gwaggo ki kyaleta kada ki biye mata kinga rashin kunya take miki ni kuma zuciyata bata dad'i watarana idan ta 'kure ni dole na mayar mata da martani shiyasa bana so kina biye mata kuna fad'a ma'kota na jinku."
Tsaki tayi ta girgiza ta fara kokarin mi'kewa......Fita tayi ta dauko 'yar tukunya ta dawo dakin da fad'in "Ai sai ki kunna min gas din ko." Motsawa nayi na mike zaune ina ya mutsa fuskata, cikin kulawa tace."Yana da kyau dai ki sake shiga cikin ruwan d'umi idan kuma baki daina jin zafi ba gobe sai muje asibiti a dubaki dan na lura yaron nan ya gwada miki mugunta.''
Nace."Gwaggo babu wani asibiti da zanje idan kin sauke kisa min ruwan zafin ya isa." Tace."To ai shikkenan Allah ya kyauta." ciki zuciyata na amsa da ameen tare da kar'bar ashanar hannunta na kunna mata 'karamin gas din ta dora tukunyar akai.
Tana sa taliyar a cikin kunyar Kawu ya daga labulan dakin. tace."Ibrahim ka dawo kaga har yanzu ja'irin yaron nan bai shigo gidan ba."
Yace."Gwaggo bana tsammanin fa Khalid na kusa dan tun dazu ake kiran wayarsa a kashe abokinsa Salim ya tabbatar min da cewa ya mayar masa da mukkulin adaidaita sahun da ya samo masa shin gwaggo duk me ya janyo haka? Khalid yasan bashi da gaskiya shiyasa ya gudu."
Tace."Ka rabu da ja'iri Ibrahim ai duk guje-gujen da zaiyi dole ya dawo gida ya same mu hukunci kuma kada ka fasa yi masa domin ya aikata abinda da ya zama dole a hukunta shi."
Kawu ya kalli inda nake kwance cikin kulawa yace."Sa'ida ya jikin naki ina fata dai babu wata matsala."? Kafin nai magana tace"Tun d'azu take ya mutsa fuska tana tafiya da 'kyar shine nace gobe muje asibiti a dubata ko yayi mata rauni tace ba za'aje ba xata cigaba da shiga ruwan zafi."
Shuru yayi yana me sunkuyar da kansa 'kasa hakika wannan al'amari ya tsaya masa a zuciya....a sanyaye yace."Sa'ida kiyi hakuri aje asibitin a dubaki kada kuma wata matsalar ta afku."
Murya na rawa nace."Kawu ba sai anje asibiti ba insha Allahu babu matsala." Girgiza kansa yayi yace."To shikkenan ai dama haka ake so.....Kokarin fita yake sai ya kuma yatsa yana kallon tukunyar dake kan gas yace."Gwaggo me kuma kike dafawa da dare haka."?
Da sauri na rigata magana da fad'in "Taliya ce nace ta dafa min ina sha'awa." Yace."To na fahimta." sai da safe yayi mana ya fita daga dakin.
Ummatu na 'kuryar dakinta tana sa'kawa da kwancewa ya shiga yana kiranta tana jinsa tayi saurin kwanciya tare da rufe jikinta, rufe idonta tayi kamar mai bacci yazo ya tsaya a kanta yana fad'in "Rabi tashi ki dauko min abinci na dawo da yunwa."
Ta bude ido cikin yanayi na masu bacci tace."Ai sai dai kayi hakuri dan wannan fargabar ita ta hana ni na shiga kicin nayi wani abin arziki nima a haka zan kwana da yunwa."
Rai a 'bace yace."Saboda ke zaki iya kwanciya da yunwa sai ki azabtar da rayuka tun safe da zan fita na baki kudin cefane bayan tsabar abinci da nake dashi a gidana amma saboda wani dalilin ki na banza da wofi kin ki yin girki a gida kina so nida mahaifiyata mu kwana da yunwa kenan."
Zaune ta miqe tana kuka tace."Ibrahim dan Allah ka saurara min haka naji da wannan masifar da take damuna wallahi ina hakuri a gidan nan mahaifiyarka a d'azu babu irin cin mutuncin da ba tayi min ba akan kawai na kare d'ana daga zargin da ake masa ni wallahi har yanzu ban yarda Khalid ne ya aikata abunda kuke zarginsa dashi ba.
Rai a 'bace yace."To idan bashi ne ya aikata ba mai ya hana shi dawowa gida? kuma mai yasa ya kashe wayarsa Rabi wai me yasa kike da son zuciya ne yarinyar nan Sa'ida itama haihuwarta akayi mai yasa kike fifita d'anki a kanta kema uwa ce ya kamata ki dinga adalci a cikin al'amuran ki a zahiri yaro ya aikata abu kuma ya nuna kansa amma sabodo son zuciyarki kice baki yarda ba k'azafi akayi masa."
Komawa tayi ta kwanta tare da juya masa baya alamun duk maganganun da yake basu gamsar da ita ba, Kawu Iro cikin 'bacin rai ya fita daga dakin kai tsaye hanyar fita daga gidan ya nufa ba zai zauna da yunwa akan yaron da bai ji tausayinsa ba.
Gwaggo ta fito daga bandaki da buta a hannunta tace."Ibrahim ina kuma zakaje ai na dauka ka shigo gida sai da safe."
Jim yayi kafin yace."Gwaggo zan fita na nemi abinda zanci ashe wai Rabi bata baku abinci ba."? Tace."Eh ka rabu da ita da halinta kada kaje ko'ina zo muje daki kaci abinci ko baka ga ina dafa taliya ba."
Yace."Na gani Gwaggo.'' tace."To muje daki kaci ka koshi ka shareta da bak'in halin ta.'' Girgiza kansa yayi yabi bayanta d'akin suna maimaita maganar.
Salmanu shuru yayi kawai ya tsirawa abokin nasa ido yana kallonsa. Khalid yace."Salmanu ka tsananta lallai sai na fad'a maka damuwata na fad'a maka kuma ka tsira min ido kana kallona."
Salmanu yace."Khalid dole na kalleka saboda abinda ka aikata yanzu dan Allah ina soyayya take a nan? ashe dama duk irin haukan da kake a kanta sha'awarta kakeyi yanzu kai baka ji kunyar haike mata ba? bayan kullum kana ikiririn so da 'kaunarta me zai sa ba zaka so abinda take so ba."
Gumi ya goge a sanyaye yace."Salmanu hankalina ya gushe tunani na yayi nisa a lokacin dana aikata wannan al'amarin nasan ban kyauta ba amma ina ganin hakan da nayi shine daidai domin ina tsammanin dole su janye maganar auran da zasuyi mata su nemi inda nake."
Salmanu yace."Khalid wannan ba dubara bace komai na rayuwa ana bin sa ne a sannu a hankali ba'a gwaggawa Khalid duk abinda kaga mutum bai samu ba a duniya ba to ba rabonsa bane kai mai yasa baka hakura da qaddara ba kabi son zuciyarka ka aikata abinda zai jefe zuk'atan iyayenka a damuwa kai ma duk da kabi son zuciyarka a yanzu nasan babu wanda ya kai ka nadama gami da damuwa yanzu kasan a wane irin hali na damuwa da bacin rai iyayenka ke ciki a gaskiya ni kam banji dadin wannan abu daya faru ba wallahi kuma ban ta'ba tsammanin zaka iya cutar da aunty Sa'ida ba sabida irin son da kake mata."
Girgiza kansa kawai yake kafin ya dago kai ido jawur yace."Salmanu sanin abinda yake cikin zuciyata sai Allah domin shi kad'ai yasan irin son da nake wa Aunty Sa'ida wannan al'amari daya faru tsakanina da ita tsautsayi da qaddara ne a lokacin a fusace! nake da irin abubuwan da take min bayan haka kuma kasan shi so babu abinda ba yasa mutum ya aikata amma bana ta'ba tsammanin zan iya daina sonta har duniya ta nad'e."
Salmanu yace."To ai shikkenan yanzu wace shawara ka yanke na ganka da jakar kaya."
Yace."So nake na bar garin kano gabadaya idan 'kura ta lafa sai na dawo." Salmanu yayi shuru yana nazarin maganar kafin yace."Eh wannan tunanin yayi kyau kayi nesa da gida kafin zuciyoyinsu suyi sanyi amma ina baka shawara kancewa ka nemi iyayenka a waya ka basu hakuri itama Aunty Sa'idar ka kirata ka bata hakuri ka nuna mata nadamarka."
Ya sharce gumin goshinsa yace."Insha Allahu haka za'ayi abokina nagode 'kwarai da shawararka.......Salmanu yace."Haba ai babu komai Khalid an riga an zama daya ina jinka tamkar d'an uwana na jini shiyasa gabadaya da naji al'amarin nan hankalina ya tashi."
Khalid girgiza kansa kawai yayi shima jikinsa duk yayi sanyi da abin kunyar daya tafka tun a mota yake tunanin mawuyacin halin daya bar auntyn nasa a ciki sai kuma fargabar tashin hankalin da iyayensa zasu shiga idan sukaji abinda ya aikata.
Salmanu mi'kewa yayi ya kama hanyar fita da fad'in "Bari na shiga gida na kawo maka abinci." Khalid ya sauke ajiyar zuciya da fad'in "Nagode abokina."
Bayan fitar Salmanu da minti uku sai ya bude jakar kayansa ya dauko wayarsa a nutse ya kunna ya nemi number Salim. domin yana so suyi magana a tsakaninsu."
Salim na kallo a wayarsa yaga kiran abokin nasa da sauri ya daga hannunsa sai kyarma yake yace."Khalid kana ina ne tun dazu ake ta kiran wayar ka bata shiga mahaifinka ma yazo yana nemanka hankalinsa a tashe.
Khalid yace." Salim nayi nisa da gida saboda wani dalili shiyasa ma kafin na tafi na kai mukkulin babur gidanku nace a ajiye maka inaso ka mayarwa da mai shi abunsa ya bawa mai bukata sannan don Allah gobe da safe kaje can gida kafin mahaifina ya fita kasuwa kace masa nace dan Allah dukkaninsu su gafarce ni."
Salim jikinsa yayi sanyi yace."Khalid wai me yake faruwa ne? yanda naga hankalin mahaifinka a tashe ya dameni gashi kuma kai yanzu kana wasu zantukan da suka sanyayyar min da jiki."
Murmushi yayi irin na takaici da nadama yace."Salim kai abokina ne tun na 'kuruciya kasan halina sannan kasan abinda zanyi da wanda ba zanyi ba qaddara da tsautsayi sun afka min na haikewa Aunty Sa'ida bayan na samu labarin maganar auranta da Alhaji Nura."
Salim yace."Khalid magana kake yi a cukurkud'e! ka fito fili kayi min bayanin da zan fahimta ka haikewa aunty Sa'ida to me hakan yake nufi."
A sanyaye yace."Ina nufin nayi mata fyad'e a d'azu da rana." "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Khalid garin ya akayi haka ta faru? A garin ya ka aikata wannan mummunan aikin akan masoyiyarka."
Yaji hawaye na nema su kufce masa daurewa yayi ya aro dauriya yace."Tsautsayi da qaddara ne sai kuma son zuciyata nima nasan ban kyauta ba dan Allah ka riqe min sirri na bana so kowa yaji wannan magana salim."
Salim ya dinga jijjiga kansa gumi! na yanko masa yace."Wallahi Khalid ko a mafarki ban ta'ba tsammanin zaka aikatawa aunty Sa'ida haka ba me tayi maka mai zafi ashe dama duk 'karya kake ba sonta kake ba."
A tunzure! yace."Wai ya zaku dinga fad'a min wannan banzar maganar ne? Salim me ya janyo hakan idan ba so ba? ka fad'a min maganar da zata sanyaya raina ba irin wannan ba! har abada ba'a sanjawa towo suna wannan abu da ya faru tsakanina da ita ya sake saka min so da kaunarta a cikin zuciyata."
Salim yace."Kayi hakuri Khalid naga kamar ranka ya 'baci amma dai kasan kowaye yaji wannan al'amari dole ya razana dole kuma ya shiga tantama akan son da kake mata amma babu komai qaddara ta riga fata kamar yanda ka fada cewa tsautsayi da qaddara ne ya janyo maka to ina rokon Allah ya kare faruwar wani abu anan gaba."
Can 'kasan ma'koshi ya amsa da ameeen ya Allah nagode abokina sai na sake kiran wayarka." Salim yana kokarin yayi magana Khalid din ya kashe wayarsa yabi wayar da kallon mamaki kafin yayi yunkurin sake kiran sa domin yana so tambayeshi inda yake a halin yanzu yana fara kira a kace masa wayar a kashe take, dan suna gama magana Khalid din ya kashe wayarsa ya mayar da ita cikin jakar kayansa.
Salmanu ne ya shigo dakin hannunsa da fulas ba abinci da maidaidaicin plate da cokula ya ajiye a gabansa tare da bude karamin firjin dake dakin ya dauko masa ruwa da lemo masu sanyi kallonsa yayi da fad'in "Khalid kaci abinci ka samu nutsuwar zuciya kuskure ne dai ka riga ka tafka sai sa ka kiyayi gaba."
Yace."Salmanu bana tsammanin zan iya cin wani abu a halin yanzu cikina a cunkushe nake jin sa bana sha'awar komai."
Salmanu yace."Ai dama ba dan dad'i zaka ci