Showing 114001 words to 117000 words out of 185789 words

Chapter 39 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24201

A raunane na amsa da "Ameeen ya Allah Kawu." Ya kalli Gwaggo da fadin." Baki ce komai ba Gwaggo.'' Tana cigaba da abinda yake gabanta tace."To me zance Ibrahim ai tunda kun riga kun gama yanke hukunci bani da tacewa.

Yace."Gwaggo kiyi hakuri kiyi wa al'amarin kyakykyawar addua." Tace."Ai tun jiya da ta fada min maganar nayi addua Babu komai ka tafi kasuwarka Allah ya bada sa'a."

Yanda ta fadi maganar zaka gane akwai wani abu a cikin ranta da yake damunta. A sanyaye yace."To shikkenan Gwaggo sai na dawo." Tace."Allah ya tsare ya bada sa'a." Ya amsa da ameeen yana kokarin fita.

Dago kanta tayi ta kalleni da fadin."Yanzu Sa'ida abinda kukayi shine daidai anya ba zaku rage son kai ba."?

Nace."Gwaggo me kuma mukayi."? Tace."Fisabilillahi Sa'ida yaron nan Khalid yana kulafucin ki amma ke sam bakya ta tasa wai shin dan Allah wace irin kiyayya kike masa haka me yasa ba zaki aureshi ba.

Cike da wani irin yanayi nace."Gwaggo wai don Allah me yasa kike dawo da hannun agogo baya na dauka tuntuni maganar Khalid ta wuce tunda zaiyi aurensa to me yasa zaki dinga tayar da abinda ya wuce.

Gefan zaninta tasa ta goge hawayen fuskarta tace."Wallahi tausayinsa nake ji Sa'ida ya kwallafa ransa a kanki sai wahalar dashi kuke hakika da ana sanja zuciya da sai na sanja masa zuciyarsa ya daina wahalar da kansa a kanki Jiya nan sai da ya bugo min waya yana cikin damuwa banda maganarki babu abinda yake mai zai sanya ba zakiyi mana kara ba? me zai sanya ba zaki tausayawa dan uwanki ba? Sa'ida duk fa namijin da Ibrahim yake so ki aura ba kamar d'an cikinsa ba zaifi so ki auri Khalid amma sabida baya so yayi miki dole yake rarrashinki da bin abinda kike so ke kuwa mai zai sanya ba zaki kyautata masa ba.


Cikin kuka nace."Wai shin Gwaggo ya kike so nayi ne? wallahi da mace tana auran maxa biyu a lokaci guda to da na auri Khalid da Yaya Aminu amma yanzu lokaci ya kure dole Khalid ya sake hakuri a karo na biyu tunda na ruga na amince da maganar auran Yaya Aminu duk sai mu barwa Allah abinda ya hukunta."



*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*




*66&67*
Gefan zaninta tasa ta share hawaye da fadin."Ai shikkenan Sa'ida tunda haka zaki ce dole nayi hakuri da hukuncin da kika yankewa kanki amma ni sam bana sha'awar ki da wannan mai ba'kar fuskar." Kallonta nayi ina mamakin maganarta Gwaggo idan bata son abu komai kyawun sa ta dinga kushe shi kenan amma in banda haka meye laifin Yaya Aminu kyakykyawa ne sosai Khalid din babu abinda zai nuna masa sai haske fata.

Nace."Gwaggo maganar nan ta wuce don Allah ki daina kuka da damuwa ki cigaba da addua ni da Khalid din Allah ya za'ba mana abunda yafi alkairi Gwaggo duk sonki da na auri Khalid idan Allah bai nufa ba dole ki hakuri kin san komai nufi ne na ubangiji mussaman sha'ani na aure ba'a katsalandan a ciki kawai ki roki Allah alkairi sai kiga ya tabbatar miki.

Tace."To me kika ji na k'ara cewa? ai magana kuma ta wuce wannan yaro Khalid kuma Allah ya sanya masa dangana."
Ameeen na amsa ina kokarin mi'kewa tsaye


*Bayan sati biyu*
A tsakanin kwanakin Yaya Aminu yazo guri na mun gaisa sosai kuma yanda yake nuna kulawarsa a kaina yasa na gane cewa lallai ba dole akayi masa ba domin 'karara yake nuna min so da kauna ga uwar hidimar da yake min sai kace hauka ya kawo min sabuwar waya mai kyau da tsada kudi kuwa duk bayan kwana uku ko hudu zan ga alert dubu ashirin dubu talatin har dubu hamsin turo min yake idan nayi masa magana sai yace shine yayi niyya idan inada bukatar ya 'kara min wasu sai nayi magana, al'amarin ya dinga bani mamaki mutuka gidan Hauwwa naje domin mu tattauna maganar dan gaskiya ni kudin da yake bani suna bani tsoro ni ba auran kudi nake so nayi dashi ba nafi bukatar idan na aureshi ya rike ni tsakani da Allah mu zauna lafiya.....Koda Hauwwa ta gama jin bayani na sai tayi dariya tana fadin."Sa'ida kenan ke yanzu saboda rashin wayo da dubara har magana kike masa ya daina baki kudi? to idan ya daina baki wa kike dashi wanda zai baki? komai fa da kika gani yana da lokacinsa saboda haka ki kwantar da hankali Idan kullum zai dinga sa miki million a accont dinki kada kice masa don me kiyi godiya kawai idan baki kar'ba ba wasu can a waje su za su kar'be Yana da kudi to me zaiyi dasu tunda dai shi bashi da nauyin kowa a kansa ke d'in dama ke zai bawa sai mahaifiyarsa da sauran 'yan uwansa saboda haka ki nutsu ki samu abinda kika samu kafin lokaci ya kure miki."

Shuru nayi ina ta nazarin maganarta tace."Ni wallahi nayi miki murnar auransa domin ta ko'ina yayi bashi da makusa saboda haka kawai ki kwantar da hankalin ki ayi al'amarin nan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali."

Ajiyar zuciya na sauke nace."Shikkenan Hauwwa Allah yasa hakan shi yafi alkairi." ta amsa da ameeen tana kokarin mikewa tace."Bari na kawo mana abinci." ido kawai na bita dashi ina mamakin son kud'inta Na lura bata da tsinkaye da tunani mutukar akan kudi ne.


Can gidan Alhaji Shamsun kuwa kowa yana cikin farin ciki manya da yaransu amma banda mahaifiyarsa Hajia Mariya tun sanda maigidan ya sheda mata hukuncin da ya yanke take cikin k'unci sam bata so d'anta ya fara da bazawara a ganinta kamar hakan koma baya ne domin kuwa babu abinda d'anta ya rasa na jin dadin rayuwa to ta yaya za'a ce lallai sai ya auri bazawara sai kawai ta yanke shawarar tun karar maigidan da maganar Alhaji Shamsu tunda yaga take taken ta ya bude mata wuta sosai ya nuna mata kuskuranta yace kuma mutukar yana numfashi to sai anyi auran don haka kawai tayi addua domin shine abinda ya cancanta." Sanin halin mijin nata yasa bata sake tankawa ba duk irin hidimar da akeyi a gidan idone nata su kuma kishiyoyin nata sai suke ganin kamar kawaici da kunya take irin na d'an fari Tsakaninta da Umma Habiba babu wata matsala dan ko a fuska bata nuna mata cewa bata son auran ba, ta bar komai a cikin zuciyarta tana dai kallonsu sai farin ciki da murna sukeyi........Manya akwati mai sheda cike da manya kaya masu tsada aka kai wa Sa'ida a matsayin kayan lefe Gwaggo da Ummatu da sauran jamaa suka dinga mamaki ko auranta da Alhaji Nura bata samu wannan alkairi ba Gwaggo dai gajiya tayi da duba kayan sabida tsabar yawan su ta bar gurin sai surutai takeyi Ummatu kam sai da ta lissafa iya adadin kayan lefan Atamfa Talatin les Talatin shadda talatin komai dai gashinan kamar hauka don tsakar gidan cika yayi da kayan makota nata shigowa suna gani sai can dare kafa ta dauke a gidan......Koda Kawu Iro ya dawo Gaggo turkeshi tayi da fadin."Ibrahim wai shin meye sana'ar wannan yaron ne."? Yace."Gwaggo wa kike nufi."? Tace."Aminu mana."? Murmushi yayi yace." Siyar da tufafi ko wane iri shine sana'arsa a 'kalla yana da rumfuna sama da biyar a kantin kwari kuma akwai wani babban company da suka bude a chana suke sarrafa audiga ai bai fiye zama a gari ba.

Tace."Koda naji duba kaga irin uban lefen don Allah mutane sai gulma suke shigowa mu ba kudi muke so ba albarkar aure muke bukata.

Murmushi yayi yace."Gwaggo kenan ai mutane dama ba zaki rabasu da wannan gulmace gulmacen ba to duk dai wanda ya shigo da sunan ganin kayan lefe sai ku nuna masa shine abinda ya dace."

Tace."To Allah ya kyauta dai ya rufa asiri." ya amsa da ameeen ya rabbi tace."Yanzu sati nawa suka d'iba domin daurin aure."? Yace." Kwana bakwai ne rana ita yau kenan." Tace."To Allah ya nuna mana. " ya amsa da ameeen yana kokarin barin gurin tace." D'azu da safe kuwa Khalid yace yana kan hanya zaizo gobe ko jibi wai zasu tafi america suyi wasa."

Yace."Gwaggo Nifa bana son yaron nan da wannan harkar kafurci ne tsagwaronsa." Tace."Ibrahim nima bana so to ya zamuyi idan ya kasance anan abincinsa yake.


Yace."Dole idan yazo na zauna dashi domin bana tsammanin zan barshi ya koma Lego's din nan bare ya tafi wata uwa duniya america Buga ball da turawa ya haramta." Tace."Ai ko bada da turawa ba ma buga ball a ko'ina ne bai halasta ba kamar an tozarta ahalin gidan Annabi ne." Yace."Gwaggo ai ba kama bane Gaskiya ne duk wanda ya buga ball kamar yana buga kawunan Shirafa'u Jikokin Annabi Muhammad (SAW) wannan dalilin yasa idan ya dawo zan zauna dashi akan al'amarin.

Tace."To shikkenan Allah Ubangiji Ya za'ba abinda yafi alkairi." Ya amsa da ameeen tare da barin gurin


To koda Hauwwa tazo ganin kayan lefen itama sai da tayi mamaki mussaman data ga set din gold har biyu da 'kirar saudi dana dubai ta dinga mamakin al'amarin tana girgiza kanta ta kalleni da fadin."Ke dai Sa'ida 'kashin ki na manyan mutane ne duba dan Allah lefe sai kace na 'yar gatan budurwa."

Murmushi nayi kawai nace."Hauwwa kenan Ni wallahi yanzu duk ba wannan ne a gabana ba burina kawai naga na zauna kalau a dakin aurena dan bana so da kuruciya ta kawai a dinga lissafin min aure ina addua akan Allah yasa anyi kenan.

Tace."Ki daina wani wasiwasi da zancan zucci insha Allahu baki da matsala da Aminu tinda yana sonki zai kula dake kamar yanda kike bukata." Wannan kalaman nata suka sanya ni naji sanyi a cikin zuciyata sai kawai muka shiga tattauna yanda al'amuran biki zai kasance.



Ya kama saura kwana uku daurin aure Khalid ya dira a garin ni lokacin ma bana gidan ina gidan Hauwwa tare da masu gyaran jiki.

Kawai naji kira ya shigo waya ta dana duba sai naga number Gwaggo ce amma kuma ina daga wayar naji muryar Ummatu tana fad'in "Sa'ida sai ki zuba ruwa a kasa kisha ga Khalid a kwance yana aman jini.

Gabana ya dinga buguwa nace."Ummatu ban gane maganarki ba. Tana kuka tace."Ai dama ba zaki gane ba tunda bukatar ki ta biya ni dai idan ki kayi sanadiyar mutuwar yaro na Allah ya isa." Kafin nace wani abu ta kashe wayar.

Jiki a mace na kalli Hauwwa dake kallona nace."Wai Khalid ne ya dawo yake aman jini." da sauri tace."Aman jini kuma."? Murya na rawa nace."Eh." Tace."Sa'ida me ya janyo masa to."? cike da mamaki nake kallonta Nace."Haba Hauwwa ya kike tambayata kamar baki san komai ba."?

Tace."Ashe dai har yau be hakura ba."? nace"Gashinan kuwa mybe daya samu labarin daurin aurena al'amarin ya afku.''

Tace."Kai gaskiya wannan yaron yana nacin sonki haba ai ya dace ace ya hakura kuma tinda dai yanzu kinyi masa nisa gabad'aya ma ke jininki bana 'kananun yara bane sai ya hakura kawai."

A sanyaye nace." Zai hakura ai yaron mugun naci ne dashi bayan abinda yake bukata ya samu a gurina to menene na kulafuci." Kallona tayi tana neman 'karin baya ni a maganata, na share maganar ina kokarin mikewa tsaye.....Yarinyar dake sa min salatif a kafata tace." Aunty ya zaki tashi kuma ki zauna a cigaba da saka salatif din kada yasha iska."

Ina kokarin sa hijabi na nace."Mansura bana tsammanin zan zauna zaman 'kunshi a yanzu zanje na duba halin da d'an uwana yake ciki."

A sanyaye tace."To aunty Allah ya bashi lafiya."Hauwwa ta kalleni da fad'in." Amma zaki dawo ko."? Nace."Watakila zan dawo idan hali yayi." Tace."To shikkenan Allah ya sauwake."

Babu cikakkiyar nutsuwa a tare dani na amsa da ameeen nagode jakata na dauka da sauri na kama hanyar fita.



Yanda naga sun masa rumfa yasa gabana ya tsananta faduwa murya na rawa na kira sunansa yana kwance a kan katifa idonsa a rintse.......Jin muryar ta yasa da sauri ya bude idonsa, saurin sunkuyar da kaina nayi haka kawai naji ina jin nauyi da kunyarsa.... motsa bakinsa yake yana so yayi magana sai ya fasa ya mayar da idonsa ya rufe kawai sai ganin hawaye mukayi yana sauka a kuncinsa...

zuciyata ta karya ina rawar Murya na kalli Gwaggo da tayi firgai-furgai hawaye duk ya bushe a fuskarta nace."Gwaggo mu tafi asibiti dashi a duba shi sosai ina aman jinin da yayi."? ina maganar ina bin tsakar gidan da kallo.


Tace."Sai kawai mu zauna zaman jiran ki ai tuntuni mukaje asibiti suka duba shi suka kuma bashi magani aman jini kuma an wanke domun ke baki isa ayi miki 'karya ba.


Nace."Gwaggo me ya kawo wannan maganar ai nima ba 'karyatawa nayi ba." Dauke kanta tayi ta cigaba dayi masa firfita da maficin hannunta, tsakin Ummatu naji akaina kafin na juyo ta bar gurin tana surutai.

Girgiza kaina nayi nasa hannu na goge hawayen da suka zubo min.....Tace."Sa'ida ai kuka yanzu kika fara tunda baki da tausayi sai Allah ya sakawa wanda kika zalinta.

Shuru nai mata na mayar da hankalina kansa har yanzu idonsa a rufe yake murya na rawa na kira sunansa.

Shuru yayi bai amsa min ba, na sake kiran sunansa tare da kama hannunsa......da mugun sauri ya fizge hannunsa ya bude idonsa yana kallona cikin Sha'kakkiyar murya yace."Bana bukatar ganin ki Aunty Sa'ida I hit you i hit it !! na tsane ki! bana sonki! sai kinga sakamakon abinda kikayi min kije ki auri duk wanda zaki aura ni kuma zan mutu da sonki a cikin raina." Yana maganar yana tari da riqe kirji! Gwaggo duk ta gigice tana rirrikeshi cikin dauriya na hau katifar sosai ina kokarin rikeshi kamar walkiya ya juyo a zafafe ya hankad'e ni na fad'i a kasan gurin! da hannu yake nuna ni yana so yayi magana amma kuttun bakin ciki ya hanashi kawai sai jini muka gani ya ambulo daga bakinsa.

Ihu! na kurma! a kid'eme na sake hawa katifar na kamo shi gefan hijabi na nasa ina goge masa ina kuka wurjajan na kalleshi da fadin."Khalid ashe da gaske ne? me yayi zafi Khalid kada ka kashe kanka don Allah kayi ta wakkali ka cigaba da neman za'bin Allah.''

Zafafan hawaye ne suke sauka a kumatunsa hannu na na rawa na dinga goge masa ina kuka da fadin."Kayi hakuri dan Allah ka barwa Allah lamarin nan Khalid ka daina aman jini kada kasa mu cikin masifa.

Gwaggo da tausayin su ya isheta sai ta mike jiki a sa'bule ta shiga dakinta tana share hawaye da adduar d'auki daga Allah.


Rarrashin sa na cigaba dayi ina shafa kanshi da bayansa gabad'aya ya lafke a jikina sai ajiyar zuciya yake saukewa nauyin sa be dame ni ba ni dai buri na yayi min magana yaja bakinsa yayi shuru idonsa a rufe sai sake sakin jikinsa yake a jikina.


A hankali na kira sunansa. Ya bude idon yana kallona nace."Kayi hakuri ko."? tsira min rikitattun idanun nasa yayi nayi tsai ina karanta abinda yake cikinsu.......Babu wata alama data nuna ya dauki nasiha ta.....Hannuna na turmutsa cikin tarin suman kanshi a sanyaye nace."Khalid komai na rayuwa yana tafiya ne da ikon Allah duk yanda mutum yake son abu idan Allah baya sonsa da abun dole ya hakura shiyasa kaji ina cewa kayi hakuri ka nemi za'bin Allah Ni bana 'kin ka Khalid idan Allah ya kaddara aurena dakai duk rashin sona dole na hakura don Allah ka kwantar da hankalinka.

'Kuguna ya zagaye da hannuwansa, kallonsa nayi gabana na faduwa.........."Zaki auri wani ya 'karasa kwashe min Ni'ima ko."? yafada cikin sar'kewar murya. gabana na wani irin bugawa nake kallonsa....lumshe idonsa yayi ya sake yin release a jikina.......Bana bukatar wani banza ya ra'bi jikin ki aunty Sa'ida ke kuma gashi kina ta basu goyon baya akan hakan yanzu me kika hango a tare da wannan mutumin da zaki aura ko kudinsa kike so."?

Ajiyar zuciya na sauke ina kokarin cire shi daga jikina nace."Khalid me yasa kullum kai baka daukar nasiha ka daina barin shed'an yana tasiri a tare da kai aure nufin Allah ne.

Kansa ya d'ago yana kallona na kauda kaina da sauri! hannu yasa ya juyo da fuskata yana kallona yace."Idan na tafi amarica na tafi kenan ba zan dawo ba tunda kince na fita daga rayuwarki na fita har abadah zan barki kiyi zaman aure.

Hawaye suka kwace min nace."Kada ka yanke wannan hukuncin Khalid America ba gurin zama bane kada ka biyewa sharrin zuciya ka jefe mu a cikin masifa."

Murmushi mai ciwo yayi yace."Zama na a Najeria babban Jidali ne bana tsammanin zan iya barin ki ki zauna kalau a gidan auranki idan nayi nesa sai kinfi samun kwanciyar hankali." Sosai nake hawaye ina girgiza masa kai.....Hannu yasa yana goge min hawayen muka kurawa juna ido.....Haka kawai nake jin mugun tausayinsa na ratsa ni Khalid yana masifar sona babu shakka da maganar aurena da Aminu ba tayi nisa ba zan iya hakura na aureshi ko ya samu nutsuwa sai dai kash lokaci kadan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login