Showing 150001 words to 153000 words out of 185789 words
kika girka min zanci." Tace."To ina maka fatan alkairi yaro na Allah ya baka nasara a rayuwarka." Ya amsa da ameeen ya Allah." Yana fita tayi murmushi tare da girgiza kai tace."Cikin ruwan sanyi zan k'wace yaro na daga hannun ma'kiya na dakinta ta shiga ta dauki wayarta tana so tayiwa Jamila albishir da cewa auranta da Khalid ya kusa zuwa.
Kasa fita yayi sai da ya leqa dakin Gwaggon kamshin turaransa ya cika mana hanci satar kallonsa na dinga yi ta 'kasan idona yayi kyau har ya gaji yana sanye da k'ananun kaya kanshi sanye da f-cap sajensa ya kwanta a fuskarsa ba'ki sosai sai kyalli yake.........Ganinsu suna cin d'umame na towo da jug din kunu da kosai a gabansu yasa ya cire Booth din dake kafarsa ya shiga dakin ya zauna kusa dani lokaci k'ankani na rikice feelings mai zafi ya taso min gabad'aya k'amshin dake tashi a jikinsa ya gigita ni."
"Gwaggo zan sha kunun nima." a shagwabe ya fadi maganar." Uffan ba tace masa ba ta cigaba da kur'bar kunun ta tana had'awa da kosai.......Hannu ya miqa yana kokarin kar'bar kofin hannunta tayi saurin janyewa tana harararsa. murmushi yayi ya dauki kosai d'aya yasa a bakinsa ya juyo yana kallona. saurin kauda kaina nayi daga kansa......Matsowa yayi kusa dani sosai yasa hannu cikin d'umamen towon dake gabana ya gutsira yasa a bakinsa. kallonsa nayi ya d'aga min gira da fad'in ."Ko kada nasa miki albarka." Hannuna na tsame daga cikin kwanon towon nace."Na koshi ai ka cinye ragowar." girgiza kansa yayi da fadin."Ni nafi karfin naci ragowar wani ko kin manta da hakan.''? Jim! nayi ina kallonsa da nazarin maganarsa ya 'kura min ido da fad'in."Ina fatan kin gane inda maganata ta dosa ." ? Murmushin takaici kawai nayi na kauda kaina ina mamakin tsagerancin sa.
Gwaggo tace."Yau dai za muyi balaguro zamuje mu huta mu barwa masu gida gidansu su sakata su wahala."
Yace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."? share shi tayi ta cigaba da abinda take. Kallona yayi da fad'in." Ina zakuje."? Ba tare dana kalleshi ba nace." Nima ban sani ba." shuru yayi na minti biyu kafin yace."Gwaggo kiyi hakuri kada kuje ko'ina nayi alkawarin raba muku gida keda Ummatu kowa kofar sa daban."
Tace."Ai baka burge ni ba na d'auka zaka gina mata k'aton gida ta shiga ta zauna tunda naji tana alfahari da kai cewa kayi kudi zaka share mata hawaye."
Dariya yasa yana kallonta yace."Gwaggo ina kudin suke ni talaka ne kuma almajiri mai nema wai mai yasa mutane suke zuzuta magana ne."
Tace."Aa kada ka butulcewa Allah mana Khalid kana da kudi tunda kullum cikin kyautarsu kake." Yace."Tom Allah ya 'kara bud'a min hanyar samu." a zuciyarta ta amsa da "Ameeen."
Yace."Gwaggo yanzu ba zaki bani kunun nasha ba." Girgiza kanta tayi da fadin."Kaje uwarka ta baka." Ya rike bakinsa yana mamakin maganarta. Ni kam mi'kewa nayi na fita tsakar gida domin wanke hannuna. abun mamaki ina dawowa na tarar dashi da kofi cike da kunu yana sha. cikin zuciyata nace " dama duk cika baki ne ba zata iya kauda kanta a kansa ba.
Waya ta na d'auka ina dubawa nan naga text din Yaya Aminu yana bani hakuri akan abinda ya faru wai zai zo da daddare yayi min bayani akan irin cigaban da ya samu domin yaje gurin wani mai magani dake wani k'yauye ya samo magani kuma yayi dace maganin ya kar'be shi." Murmushin takaici nayi cikin zuciyata nace."Allah ya kyauta bana tsammanin zan tsaya na saurari mutumin nan sabida har yanzu ban mance irin wahalar da nasha a hannunsa ba..
*Kika karanta min littafi baki biya ba ina bin ki bashi......Vip gruop#600 normal group #400....account... 0542382124....Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*95*
Idar da sallah ta kenan kira ya shigo waya ta, a nutse na mika hannu na dauki wayar dake gefe na Yaya Aminu ne ya kira ajiye wayar nayi domin ko na dauka ban san abinda zan ce dashi ba gabadaya yanzu bana bukatar wata alaka ta sake had'a ni dashi. wani kiran ne ya sake shigowa Gwaggo ta kalle ni da fadin." Sa'ida kina ji ana kiran wayarki ko.''? Kallonta nayi da fadin."Yaya Aminu ne." Jim tayi na minti biyu kafin tace."To ki daga mana ai gaisuwa baya nufin wani abu." Wayar na dauka tare da sata a kunnena a nutse nace."Salamu alaikum." Ajiyar zuciyarsa naji kafin ya amsa da "Wa'alaikissalam ranki ya dade barka da dare."
Cike da mamakin yanda yake kwantar min da kai na amsa da fadin."Barka dai Yaya Aminu ya gida da harkoki.'' ?
Cikin jin dadi ya amsa da "Alhamdulillahi komai lafiya amma ina bukatar ganin ki yanzu domin ina tsaye a kofar gidanku ."
Nace."Sai dai kayi hakuri wallahi domin yanzu ina da uziri." Shuru yayi da alama maganata ba tayi masa dadi ba, Yace."Sa'ida alkairi ne ya kawo ni gurin ki don Allah ki fito ki bani aron lokacin ki."
Shuru nayi ina jinsa yana ta magiya da karyar da kai. nace."Shikkenan ganinan zuwa." godiya yayi min kafin ya kashe wayar.
Kallonta nayi tana jan carbi nace."Gwaggo zan dan leqa gurinsa domin naji abinda yake tafe dashi."
Tace."To shikkenan Allah yasa alkairi ne." Cikin zuciyata na amsa da ameeen hijabi na nasa na nufi kofar gidan.
Yana tsaye jikin motarsa idonsa kuri a kofar gidan a nutse na karasa inda yake babu sukuni a tare dani na gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska yana bina da wani irin kallo.
Nace."Yaya Aminu kai nake saurare." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Sa'ida Allah ya bani lafiya yanzu garau nake daidai da kowane jarumin namiji wannan shine albishir din da nazo miki dashi."
Kallonsa nayi babu walwala a fuskata nace."Allah sarki amma na taya ka murna Yaya Aminu Allah ya kiyaye gaba."
Ya amsa da ameeen nagode matata." murmushin mamaki nayi wai matata........."Sa'ida kina jina ko." kallonsa nayi da fadin."Ina jinka ." Yace."Inaso kiyi hakuri ki dawo d'akin ki tunda dai ba kiyi iddah ba."
Murmushi nayi nace."Yaya Aminu a yanzu dai babu wannan maganar a tsakaninmu bana bukatar sake zaman aure dakai a halin yanzu kayi hakuri idan maganata ta 'bata maka rai."
Gabad'aya yanayin sa ne ya sauya ya koma wani irin cikin rarrashi yace."Sa'ida don Allah kada muyi haka dake ki dubi lamarin nan da idon rahama wallahi yanzu zan iya dauke miki dukkanin bukatunki."
Ina kokarin bashi amsa wata mota tayi parking a gabanmu ni dashi duk muka bi motar da kallo wannan dai ba motar Khalid bace.
Alhaji Nura ne ya fito daga motar cikin manya kaya kansa sanye da hula damanga hannunsa rike da key na mota ya karaso inda muke tsaye.
Kauda kaina nayi gabana na wani irin faduwa. hannu ya mikawa Yaya Aminu sukayi musabaha. Yaya Aminu yayi bala'in shan kunnu domin dai jikinsa na bashi wani abu."
Yana wani Muzurai ya kalleni da fadin."Gimbiya inaso nayi magana dake." Kallonsa nayi fuska a cukune nace."Alhaji wace irin magana ce wannan ina tare da mijina kake so kayi magana dani"
Hularsa ya tura k'eya yana murza fatar goshinsa yace."Mijinki wane iri bayan ya sake ki kada kiyi tsammanin bana bibiyar Lamuranki."
Kaina na sunkuyar kasa ina mamakin al'amarin......Muryar Yaya Aminu naji a fusace! yace."Alhaji wa kake da suna.? Kada ka kuskura ka shiga gonar da bata ka ba domin a halin yanzu Sa'ida matata ce saboda haka duk sanda ka sake zuwa inda take da niyyar zawarcin ta to zamu tsaya gaban hukuma dani kai.''
Alhaji Nura ya kalleshi sheqeqe! yace."Aminu kayi shuru ka daina wata fuffuka ka bari mazaje suyi magana anan gurin kai ka san kanka nima nasan kaina saboda haka dama tsautsayi da kaddara ne yasa har na saketa ka aura yanzu kuma na dawo zan mayar da ita dakinta dan haka kai zan jawa kunne ba kai zaka ja min kunne ba."
Hannu na daga musu murya na rawa nace."Ni dai yanzu dik cikin ku babu wani wanda zan komawa auransa dan haka fad'a da cece kuce bai kamace ku ba kuyi hakuri kowa Allah ya bashi daidai dashi."
Gabad'ayansu suka zuba min ido suna kallona nace."Ni zan shiga gida sai an jima." Yaya Aminu sarkin zuciya a fusace! ya bude mota ya shiga da gudu ya bar gurin.....
Shi kuma da sauri ya tare ni "Haba Sa'ida don Allah kada ki tafi ki tsaya mu fahimci juna mana wallahi nayi nadama na gane kece matar rufin asiri na."
Kallonsa nayi a sanyaye nace."Ni dai yanzu bani da wata magana da kai Alhaji nasan dai kasan babu kyau neman aure a cikin iddah saboda haka ko na 'kare iddah bana tsammanin zan komawa auranka."
Da sauri yace."Idan saboda Murja kike wannan maganar tuntuni na saketa saboda na gane cewa ita din ba matar rufin asiri bace kece matar arziki Sa'ida shiyasa lokacin dana samun labarin mutuwar auranki raina yayi fari tas saboda nasan Allah ne ya amsa addua ta akan ki."
Murmushi nayi nace."Amma naji dadi sosai daka gane gaskiya akan abinda nake fad'a maka dama irin wannan ranar nake so tazo sai dai ina so na tabbatar maka da cewa ni ba zan komawa auranka ba kayi hakuri kaje ka sasanta da matarka."
A marairace yace."Babu maganar sasanci a tsakani na da Murja domin shaidaniya ce ina nadamar auranta."
Ta'be baki nayi nace."To Allah ya kyauta zan shiga gida a gaishe da yara." Da sauri ya sake tare min hanya cikin faduwar gabana nake kallonsa.
Yana kokarin magana motar Khalid ta shigo layin.....A hankali motar take tafiya saboda yanda matasa da yara suka kewaye ta hayaniya gabadaya ta cika gurin da kyar suka bashi guri yayi parking ai yana fitowa suka rufu a kansa hannu kawai yake d'aga musu Salmanu da Salim suka bud'a masa hanya ya wuce duk da haka sai da aka samu wa'inda suka bi bayansu.
Kallo guda yayi mana ya kauda kansa sai da suka karasa bakin kofar gidan ya tsaya suka d'anyi magana da abokansa kafin ya shige su kuma suka bar kofar gidan.
Ajiyar zuciya na sauke gabad'aya jikina yayi sanyi da al'amarin yaron.........Muryarsa naji yana fadin."Sa'ida wannan yaron nan ne ko."? A sanyaye nace."Eh.'' Yace." Duk da ban kasance ma'abocin kallon k'wallon 'kafa ba na samu labarin dau'ka'kar da Allah yayi masa kuma ashe shine ya zama Gwarzon shekara ko."?
Nace."Eh shine kam." Yace."Masha Allah gaskiya na taya shi murna amma yayi aure kuwa.''? Girgiza kaina nayi nace."Beyi ba har yanzu."
Yanayinsa ne ya sauya yace."Don Allah kada kice zaki aureshi domin ke yanzu kin wuce tsaran auransa."
Da mamaki a fuskata na kalleshi da fadin."Ashe dama mace tana wuce sa'ar auran Namiji."?
Shuru yayi yana kallona. Nace." Idan Allah ya kaddara aurena da yaron babu mahalukin da ya isa ya hana ayi saboda haka kai dai kawai kayi addua akan al'amarin." Ba tare da na tsaya na saurari maganarsa ba nayi saurin barin gurin.
Tunda na shiga soron gidan nake jin sautin muryarsa na tashi sama-sama da alama shi da Gwaggo ne domin itama naji muryarta........." Ni wallahi ban ta'ba ganin mara hankalin mace irinta ba me za tayi da wannan shashashan mutumin da har zata fita tana magana dashi." Wannan maganar kunnuwa suka ji "Mara hankali." sunan da ya kira ni dashi ya masifar 'bata min rai.
Muryarta naji tana fad'in "Ai kasan halinta ba'a bata shawara ta dauka ni ai cewa tayi dani Aminu ne ashe bashi bane Alhaji Nura to idan gidansa take so ta koma sai ta d'aura niyya."
Yana kokarin magana na kasara gurin. tsaki yaja da sauri ya bar gurin yana wani irin huci! Kallo na bishi dashi ina mamakin sa.
Magana take kokarin yi na daga mata hannu da fadin."Gwaggo don Allah bar maganar nan raina a 'bace yake a halin yanzu."
Da sauri tace."Ai dole kiyi bacin rai tunda ke ba zaki dinga fad'ar gaskiya ba.
Murya na rawa nace."Wai ke Gwaggo dan Allah duk abinda Khalid yayi daidai ne a gurin ki kina jifa yana kirana da shashasha mara hankali sa'ar sa ce ni kome."?
Shuru tayi min nace."To idan baki masa magana ba wallahi ransa zai 'baci dan ba zan kyaleshi ba.'' Tace." Ai gaskiya ya fad'a me kike kufalaci a gurin Alhaji Nura bayan kin san irin zaman da kikayi dashi a baya."
Nace." Ni dai kawai addua zaki min bana son k'ananun magana ki nema min alkairi a gurin Allah."
Tace."To Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi.'' amsawa nayi da ameeen Na shiga d'akin raina duk a 'bace Gwaggo duk cika bakinta akan Yaron na banza ne zaiyi mata laifi ta gama surutai da cin alwashi a kansa amma daga zarar yazo shikkenan sai ta manta. tayi tai masa rawar jiki tamkar wanda ya sammace ta.
Khalid da asubar fari ya fita motsa jiki can filin wasa na Sharad'a Har muka gama shirye-shiryen mu muka had'a tsaraba muka tafi k'auyen D'ambatta bai dawo gidan ba......Ummatu kuwa yini tayi cikin walwala da farin ciki danginta suka cika gidan suna d'orawa da saukewa.
Sosai ranshi ya 'baci da ya dawo ya tarar da basa nan wayarsa ya dauko ya lalubi number ta ya shiga gurin kira.
Ina kallon kiran nashi naqu d'aga wa domin yayi masifar bani haushi jiya da daddare ya kira ya kai sau hudu ban daga ba ya hakura da kiran. Kwanciya na gyara kan gadon bunun Baba Ladidi ina jiyo hirarsu a tsakar gidan Gwaggo ta samu 'yan uwa sai fara'a da farin ciki takeyi su kuma sun ke waye ta kowanne da kwanon abincinsa suna farin ciki da zuwanta garin nasu na gado.
"Sa'ida wai Gwaggo tace ki fito kici abinci." muryar Jikar Baba Ladadi naji a kunnena.
Ba tare dana tashi zaune ba nace."Kice gani nan zuwa.'' Yarinyar ta juya da sauri ta fita.
Zaune na mike ina gyara dankwalina ya sake kiran wayar......Dauka nayi a hasale nace."Wai menene."? Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ki had'ani da Gwaggo za muyi magana."
"Okey." abinda nace kenan na kashe wayar gabadaya na ajiyeta. fita nayi tsakar gidan na samesu suna hira sai raha suke a tsakaninsu.
A takaice dai sai da waya ta tayi kwana hudu a kashe sannan na kunna ina sane nayi masa haka saboda na kuntukawa zuciyarsa.
Text messages d'insa ne suka shigo har uku ko wanne sai da na bud'e na karanta dukkaninsu ba'kar magana ce dan zagi na ne kawai beyi ba ya kira ni da shashasha ya kai sau nawa har da fadin Ban san inda yake min ciwo ba. tsabar bakin ciki da takaici ya sani zubar da hawaye.....nasa hannu na goge da fadin.'"Yaron nan ya gama raina min hankali Allah ka cire min jarabar sonsa a zuciyata.
Aikin gidan ake gadan-gadan domin k'wararrun ma'aikata ya d'auko suka ruguje gidan abinka da tsohon gini irin nada sosai aka samu fili ba tare da 'bata lokaci ba ma'aikata suka fitar da Foundation na zamani aka shiga aikin gidan babu kama hannun yaro........ cikin sati biyu anyi an gama sai abinda ba'a rasa ba gida yayi kyau mutuka ya haske layin Khalid ya kashe kudi sosai gurin aikin gidan Kofar Gwaggo daban Kofar Ummatu daban komai iri daya ya sa musu set na gado da kujeru da sauran abubuwan bukata Ummatu ta dawo amarya gwaggo ma haka. Ummatu ta dinga jin haushin hakan 'yan uwanta na zugata dan kakarsa Baito kishin Gwaggo take sosai ta turkeshi da masifa akan lallai itama sai ya gyara mata gidanta ya sanja mata kayan daki.'' Yace."Shikkenan ta bari idan an kwana biyu zaiyi mata. Hankalinta ne ya kwanta jin abinda yace.
Muna can bamu san abinda ke faruwa ba domin tuntuni ya daina kiran waya ta tunda ba dauka nake ba, kwanan mu ashirin da biyar muka fara shirye-shiryen tafiya.
Tsarabar da mutan kauyen suka had'a mana har taso tayi yawa nace."Baba Ladidi a wace mota zaku kaimu gida da wannan uban kayan." Tace."Ai ba za'a rasa a kori kura ba yanzu idan na fita zan shiga gidan Dije mijinta a kori kura yake ja sai ta fada masa cewa gobe zai dauki kaya ya kai birni.'' Gwaggo tace."To hakan yayi Allah ya kaimu goben." Ta amsa da ameeen ya Allah.
Da daddare ina shirye-shiryen kwanciya ya kira wayar cikin mamaki na dauka ina dubawa ina so naji muryarsa amma kuma ina gudun ya 'bata min rai da ba'kar maganarsa.
Daga wayar nayi a nutse nayi sallama. ya amsa a cunkushe da fad'in." Yaushe zaku dawo gida.''? "Gobe idan Allah ya kaimu." Yace."Okey to kada ku biyo motar haya zan zo na dauke ku domin nima inaso na gaisa da dangi na kuma nuna musu matar da zan aura.''
Nace."Okey to sai kazo din." da sauri na kashe wayar gabana na wani irin fad'uwa! Zai zo ya nuna musu matar da zai aura lallai Khalid wato yana so ya kuntukawa rayuwata tunda ya gane inda na dosa a kansa.
Da kyar bacci ya dauke ni na tashi sukuku don da kyar ma na karya nayi wanka na kimtsa jikina jama'ar garin sai shigowa sallama sukeyi.......Gwaggo kuwa sai share hawaye take sam bata so ta tafi ta bar 'yan uwanta.
Kiran wayarsa ya tabbatar min da cewa ya shigo garin....da kyar nace."Idan ka tambayi gidan Malam mai doki kazo gidan ai babu wuyar kwatance." Yana kokarin magana na datse wayar ina jan tsaki!
Ransa ya 'baci da abinda tayi masa ya ajiye wayar ya cigaba da tafiya da motar a hankali a hankali