Showing 159001 words to 162000 words out of 185789 words

Chapter 54 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24181

yana wani irin huci! tsaki naja raina a bace na zauna ina gyara wayata dake tarwatse a gurun.


Tace."Sa'ida don Allah ku sanyawa zuciyarku ruwan sanyi kece babba ki daina biye masa kuna shashanci na fiso idan kunyi aure ku zauna lafiya ku samu zuria masu albarka."


Cikin rawar murya nace."Gwaggo ya kike so nayi ne yaron nan fa ya raina ni kullum nunawa yake kamar shi yake gaba dani sam baya mutunta ni gashi ko wace irin magana idan ya tashi ya fad'a min babu abinda ya dameshi.


Tace."Hakuri zakiyi dashi Namiji ne koda babu alakar aure a tsakaninku dole ya dinga nuna miki iko da gadara duk da kin girmeshi to ballanatana kuma yanzu da zaki zauna a k'ar'kashinsa dole kiyi masa ladabi da biyayya."


Girgiza kaina kawai nayi ina tunanin yanda zama na zai kasance da yaron mutukar zai dinga nuna mun gadara da iko to babu shakka zamu kasance cikin fad'a da rashin zaman lafiya.



*BAYAN SATI UKU*
Al'amura suna cigaba da tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Ginin gidan da Khalid yake yayi nisa saura abinda ba'a rasa ba......Har yanzu babu cikakkiyar jituwa a tsakaninsa da Sa'ida ba dai sa fad'a sai dai da kyar suke kula junansu watarana ma haka zasu kwana su yini ba suyi magana da juna ba duk da cewar suna ganin junansu.

Jamila kuwa damuwa mai tsanani ta shiga a lokacin data samun labarin abinda yake faruwa taci kukanta ta k'oshi ta hakura Baito da Ummatu kuwa ai basu hakura ba sai yawon malamai suke wai lallai sai al'amarin auran ya ruguje sun kasa gane cewa komai nufin Allah ne.


Khalid lokacin da ya tashi had'a kayan aure komai iri d'aya ya siya sam bai bambamta tsakanin Sa'ida da Jamila ba abinda yayi wa budurwa shi yayi wa bazawara al'amarin da ya janyo cece kuce a can 'bangaran Ummatu kowa na fad'in albarkacin bakinsa Jamila kuwa yini tayi tana kuka ta dauka ai tunda ita budurwa ce zai bambamta da bazawara sai taga akasin haka.....K'awayen ta suka zugata akan tayi masa butsu ta nuna bata yarda ba.......Aikuwa ranta ne ya 'baci ta gwammace bata kira wayarsa ba dan masifa ya balbaleta da ita yace haka yayi niyya idan bata son kayan taje ta bayar shi babu wata mace data isa da sanja masa tsari. kashe wayarsa yayi ya bar ta cikin bacin rai.

Ummatu ma ranta ya baci mutuka amma saboda samun kwanciyar hankalinta a gidan yasa bata nuna bakin cikinta ba yanzu lalla'ba mijin nata take kada yayi mata kishiya shiyasa take masa ladabi da biyayya duk Umarnin sa bata tsallakewa.


Khalid a can Goran dutse bayan reka ya gina katafaran gida na gani na fad'a masoyansa suka cika da murna da farin ciki suna masa fatan alkairi.

Sati guda ana saukar al'kur'ani a gidan kafin a kulleshi aka cigaba da gudanar da shagalin biki.....Gidan Gwaggo cika yayi da mutanan kauyen Dambatta duk sun zo domin nuna farin cikinsu.....Bangaran Ummatu ma hidima take sosai ita da danginta.


Sa'ida tare suke gabatar da komai da Aminiyarta Hauwwa duk wani gyaran jiki tayi abinta sai dai kallo d'aya za kayi mata ka fahimci cewa kamar bata maraba da auran abubuwa da yawa sun tsaya mata a ranta tana tunanin irin zaman da za tayi da yaron kullum yana mata rashin mutunci da nuna cewa ita ba komai bace a gurinshi amma sam Jamila bata firgitata sabida ta san bata isa ta nuna mata komai ba.


Ana ya gobe daurin Aure Yaya Aminu yayi sallama da ita Kin fita tayi Gwaggo tace."Kije babu kyau wulakanci ai yanzu kuma duk wani mai naci a kanki dole ya hakura tunda gobe idan Allah ya nufa zaki zama matar wani saboda haka kije kiji abinda yake tafe dashi."


Hauwwa tace."Nima dai haka na gani ai babu wata matsala." Nace .'' To shikkenan tashi ki raka ni muje." Tace." To shikkenan.


Yana jingine jikin motarsa kansa a kasa a nutse muka 'karasa kusa dashi.......Cike da damuwa ya dago kanshi na sunkuyar da kaina ina jin dan tausayinsa a cikin raina.

"Yaya Aminu ina wuni ina fatan kuna lafiya ya kasuwa." Cikin alhini da damuwa ya amsa da fadin."Amarya ya shirye-shirye."? nace."Alhamdulillhi." Hauwwa ta gaishe ya amsa yana dan 'kallonta.

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace."Sa'ida a lokacin da komai na rayuwata yayi min sauki a lokacin ne kikayi nisa da rayuwata ina cikin wani hali na tsananin damuwa naso ace nayi doguwar rayuwa dake sai gashi Allah ya raba tsakaninmu na samu labarin daurin auranki gobe hankalina ya tashi mutuka daga baya nayi hakuri ba barwa Allah wannan dalilin yasa nace bari nazo nayi miki fatan alkairi Allah yasa haka shi yafi alkairi a rayuwarmu...





*Kika karanta baki biya ba ina binki bashi......Vip gruop#600...normal gruop#400....Account... 0542382124.....Binta umar gtbank.....idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.*
*07084652362*
*BINTA UMAR ABBALE**97*
Sai da nayi ya'ki da zuciyata sannan na kwace kaina daga hannunsa kallonsa nayi idanuwansa sunyi jawur! sai wani irin kallo yake min yana cizan lips d'inshi harararsa nayi tare da jan tsaki kaina na dauke tare da gyara mayafi na da ya sauka kasan kafad'ata.

Ina ji yana saki wani irin nishi kafin ya kira sunana can kasan ma'koshinsa.

Kallonsa nayi fuskata a 'bace. Yace.'' Ina jin feelings ya za'ayi."? Cikin fad'uwar gaba nace."Ba zaka kunna mota mu tafi ba ko.''? Kafin yayi magana motar Alhaji Nura tazo ta wuce fuuuuu! gabad'ayanmu muka bi motar da kallo.

Kanshi ya shafa yana wani killer smile yasa key a motar ya tasheta muka bar gurin.

Takaici da b'acin ran abinda yayi ya sanya na dinga tsaki Allah-Allah nake mu isa gida na huce bacin rai na.

Ya kalle ni da fadin."Auntyna amma kin dan samu sassauci ko.''?

A wulakance na kalleshi ya kanne idonsa guda yana kallona da munafikin murmushi a fuskarsa.

Kauda kaina nayi daga kanshi ya dora hannunsa akan nawa da sauri na fizge hannu rai a 'bace nace."Khalid wallahi idan baka daina ta'ba min jiki ba zaka sha mamakin abinda zanyi maka."


Ba tare da ya damu ba yace."Me zaki min.''? shuru nai ya cigaba da cewa.'' Naga kamar kina so ne shiyasa nake so na rage min zafi okey tunda bakya bukata shikkenan."


Tsabar b'acin rai bai bari nace masa komai ba kawai na kauda kaina ina kallon hanya a haka muka isa gida babu wanda ya sake kula d'an uwansa.


Zaune a tsakar gida na same ta ita da Uwale suna raba tsaraba ganin shigowata yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah cikin mutuwar jiki na shiga daki na kwanta kan sabon gadonta rufe idona nayi ina tunanin abinda ya faru a tsakanina dashi.


Koda ya shigo gidan Gwaggo kin kallonsa tayi ta cigaba da abinda take yi Uwale ce kawai tayi masa magana, cikin jin haushi yace."Gwaggo sai ki daina zagi na gata nan na kawo miki babu abinda ya sameta."


Uffan ba tace masa ba cikin b'acin rai ya juya zai fita tace."Kasa a kwashe wannan kayan da ka siya akan hanya domin na raba kashi biyu na aikawa da uwarka nata ta dawo min dashi ban san abinda take nufi ba."


Shuru yayi yana kallon kayan shi kam ya rasa me yake da mun Ummatu kishi take da Gwaggo ko meye dalili oho.

Yana fita kofar Ummatun ya shiga nan ya same su suna ta hayaniya sai zagin Gwaggo suke da zuriar ta.


Tsabar 'bacin rai ya hana shi shiga dakin ya tsaya a bakin kofa yana tambayarta kai tsaye tace.'' Bata bukata yanda ya raba musu gida to ya raba musu cefane saboda haka idan yana bukatar albarka a rayuwarsa to itama yaje yayi mata siyayya ita kadai ba tare da wani ba.


Dakinsa ya bude ya kwanta abin duniya ya taru yayi masa yawa masifar Gwaggo da Ummatu sai masifaffiyar sha'awar da take damunsa birgima kawai yake kan gadon yana rungume filo ji yake tamkar yaje ya turmushe ta ya biyawa kansa bukata babu wacce yake muradi sai ita lips d'inshi yake ciza yana turje-turje a gadon a haka Jamila ta shiga dakin ta sameshi.


Ganin yana juye-juye yasa da sauri taje ta zauna kusa dashi tana tambayarsa.

Jajayen idanuwansa ya tsira mata yana kallonta sama da 'kasa.

"Yaya Khalid me yake damun ka."? Hannunta ya janyo ta fad'a jikinsa rikon tsauri yayi mata ya dinga mutsika ta nonowanta yake luguda ita kuma sai kokarin kwace wa take tana so tayi kuka a sarqe yace." Ki barni na samu sassauci."


"Yaya Khalid ka bari don Allah." tafad'a tana kwace jikinta Ture ta yayi ta kusa faduwa. wuyan rigarta ta gyara sai zare ido take.

Da hannu ya nuna mata kofa da fadin."Tashi ki fita tunda baki da amfani." Jiki a mace take kallonsa ya sake buga mata tsawa da fadin." Ba dake nake ba." Simi-simi ta mike tsaye hanyar fita ta nufa ya bita da wani wulakantaccen kallo kwata - kwata yarinyar ba tayi masa ba bata da 'kira da zubi irin na mata saboda zai rage zafi da ita take masa hauka shiyasa yaji gabadaya abin ya fice daga ranshi.

Saukowa yayi daga gadon ya dauki jallabiyarsa yasa gabanshi ya dan fito ta saman rigar bai gama kwanciya ba.

Daga bakin kofa ya tsaya yana magana da mahaifiyar tashi....Tace."A'a bani da lemon tsami sai dai idan siyo maka za'ayi."


Ba tare da yayi magana ba ya kama hanya ya fita kofar Gwaggo ya shiga, lokacin ina tsugune bakin famfo ina daura alwalar la'asar tsayawa yayi yana kallonta hankalinsa yayi masifar tashi ganinta da daurin kirji jikinta ko'ina a cike babu rama, ya dinga wani irin nishi jikinsa sai kyarma yake.


Ina mikewa na ganshi tsoro ya bani matu'ka kallon sama da kasa nayi masa na ganshi duk a firgice! Dauke kaina nayi na wuce na barshi a gurin.


Jin sawun tafiyarsa a baya na yasa da sauri na shige dakin yaron tsoro yake bani.

Zuwa yayi ya kwanta rashe-rashe kan gadon Gwaggo ta bishi da kallon mamaki carbin hannunta ta cigaba da ja tana nazarin sa.



So nake na shirya jikina amma saboda tsabar kallon k'urrulan da yake min yasa gabad'aya duk na rasa yanda zanyi.

Kayan na d'auka na fita dasu wani karamin daki na shiga na shirya jikina na fito.

Har yanzu yana kwance a gadon sai juye-juye yake dadduma na shinfida na tayar da sallah ba tare na kalli inda yake ba.


"Kai kuma lafiya kazo kayi min kayi rashe-rashe akan gado."? shuru yayi mata idonsa a rufe sai shafa marar sa yake.


" Khalid kana jina ko."? Jajayen idanunsa ya bude yana kallonta. Gwaggo ba yarinya bace ta gane abinda ke damunsa.

"Gwaggo bani da lafiya.'' Can kasan ma'koshi yayi maganar.

Ba tare da nuna kulawa ba tace." Me yake damunka."? Shuru yayi mata. Tace."Tom tunda ba zaka fada ba ka tashi ka fita ka bani guri.


A sanyaye yace."Gwaggo aure nake so marata ciwo take." shuru tayi tana kallonsa.

Ya mike zaune yana kallonta tace."To ai kana da matar a hannu ba sai kawai a daura auran ba."


Shuru yayi ya kasa magana sai cizan lips d'inshi yake......Mikewa tayi ta fita daga dakin....juyowa yayi yana kallona na watsa masa harara kasa-kasa nace."Fitinanne kawai." ashe yaji abinda nace sai kawai na ganshi a gabana.


Da sauri naja baya da fadin."Meye haka." ? "Wane suna naji kina kira na dashi."? tsaki naja tare da kokarin barin gurin.


Hannuna ya janyo nayi zaman d'abaro a jikinsa da sauri ya cusa hannuwansa cikin hijabin jikina Brest d'ina ya kama da duk hannuwansa yana wasa dashi.


A tsorace na fizge jikina gabana na wani irin fad'uwa nace." Wato Kai baka da mutunci ko." Mikewa tsaye yayi nayi saurin kaucewa danne ni yayi ya had'e da bango (garu) gabana ya dinga duka! "Ki taimaka min auntyna." a shaqe yayi maganar.


Ihu! ne kawai ban kurma ba idanuwa na duk sunyo waje....."Khalid matsa daga jikina kada Gwaggo ta shigo ta same mu a haka."



Kai ya girgiza da fadin."Ki bani bakin ki nasha shi nake muradi.

Hawayen bakin ciki suka kufce min ni kam Allah ya had'ani da jaraba.


Motsin shigowar Gwaggo mukaji da sauri ya matsa daga jikina ta shigo dakin ganin mu daf da juna cikin alamun rashin gaskiya yasa tayi kasaqe tana bin mu da wani irin kallo.......Yun'kurin barin gurin yayi kawai ya fad'i kasan kafet.....tsakanin ni da ita ban san wanda ya riga wani zuwa inda yake ba.


"Khalid menene? me yake damun ka."? Gwaggo ce ke masa wannan tambayar ni kuwa hannunsa kawai na rike sai zare ido nake a kanshi.


Zaune ya miqe da fadin.'' Cikina ne ke ciwo sai rashin kwarin jiki Gwaggo bacin ranki ne ya janyo min shiga damuwa."


Hannunta na rawa ta dauki d'an karamin kofin data shigo dashi dakin tasa masa a bakinsa da fadin."Ga magani na had'a maka kasha zakaji sassauci."


Hannunsa ya d'ora akan nata ya shanye ruwan lemon tsamin tas sai wani irin gumi yake jikinsa na wani irin rawa.


Ya kai kimanin rabin awa a dakin kafin ya samu sassauci yace wanka zaiyi Gwaggo da kanta ta had'a masa ruwan wanka ya shiga yayi ya daura alwala ya nufi massalaci.


Gwaggo kuwa ta kudurci wani abu a zuciyarta tana ganin shine maslaha ga rayuwar jikokin nata.
*****
Bayan sati hudu Khalid yayi tafiya zuwa kasar chadi inda k'ungiyar *Manchester* na kasar suka gayyace shi wasa a babban filin wasan su dake kasar....Tafiyarsa kasar Chadi tasa hankalina ya kwanta na sake a gidan ina sabgogina wanda ada bana iya sakewa ina yi saboda yanda yake takurawa rayuwata.


Ranar wata Alhamis muna zaune nida Gwaggo muna hira tace."Sa'ida ni kuwa me zai hana ki rabu da zawarawan nan dake bibiyar ki."

Nace."Me yasa kika ce haka Gwaggo.''? a nutse tace."Kwanakin baya da muna magana da Babanku Ibrahim akan lamarin auranki sai yake cewa da zaki amince da auran Khalid da yaji dadi yana ganin kamar idan kin auri yaron matsalar ki tazo karshe to nima hankali na yafi kwanciya da ki auri dan uwanki domin kwata-kwata bana sha'awar ki koma gidan Aminu ko Alhaji Nura domin gidan jiya zaki koma.


Shuru nayi na minti biyu kafin nace."Gwaggo yanda yaron nan yake nunawa kamar yafi k'arfi na bana so azo ayi abu rayuka suna 'baci kin san dai Ummatu bata k'aunata ko."


Tace."Sa'ida Rabi bata isa ta hana abinda Allah ya hukunta ba ki kwantar da hankalin ki kuma khalid karya yake yace yafi karfin ki shin ko baki ga yarinyar da zai aura bane? kin fita komai na mata saboda haka ni yanxu amincewarki kawai nake bukata."

Ajiyar zuciya na sauke nace."Shikkenan Gwaggo Allah ya za'ba abinda yafi alkairi." Cike da jin dadi ta amsa da ameeen insha Allahu dake dashi zakuyi farin cikin wannan al'amarin.
Cikin zuciyata na amsa da "Allah yasa haka."


To bayan ya dawo gida da kwana biyu Gwaggo ta kirashi domin ta sheda masa halin da ake ciki..........Shuru yayi bayan ya gama sauraranta tace."Jarumi kayi shuru ko ba zaka aureta ba."?


Babu wata alamar farin ciki a tare dashi yace."Gwaggo don Allah ku bar maganar nan ni bana da ra'ayin auran bazawara a halin yanzu."


Gwaggo taji kamar ya soka mata wuka a makoshi murya na rawa tace."Abinda za kace kenan.''? shuru yayi yana duba wayarsa.

Wulakantaccen kallo nayi masa nace."Khalid ba fa kaine autan maza a duniya ba kada ka dauka rasa mijin aure nayi A'a duk wannan abinda ake ina bin umarnin iyayena ne bani da wata damuwa idan baka aureni ba sai me? akwai dubban mazan da suka fika komai a duniya."


Ba tare da ya kalle ni ba yace."An san da haka me yasa aka zo ana min magiya da 'yar murya kije ki auri maza dubu bai dami Khalidu ba."

Hawayen bakin ciki suka ciko idona nace." Kana cewa ba zaka auri bazawara ba tun farko wane shegen ne ya lalata min rayuwa ."?

Kallona yayi yana huci! yace."Ni kike zagi."? a harzuke! nace."Eh na zage ka ko zaka rama ne."?

Gwaggo ganin al'amarin yayi zafi sai ta shiga tsakani rai a bace tace."Ka tashi ka tafi tunda ba zaka bi umarnina ba babu komai."


Mi'kewa yayi ba tare da wata damuwa ba ya fice daga dakin......Takaici da bakin ciki suka taru sukayi min yawa. kwanciya nayi kasan kafet hawaye masu zafi suka dinga zuba a saman fuskata.




*Kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Vip gruop#600....Normal gruop#400.....Account.... 0542382124....Binta umar gtbank.....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*98*
"Ki daina kuka kina damun kanki komai abinsa sai ya had'aku ku biyu ya aura mutukar yana kaunar zaman lafiyarsa."

Zaune na mike ina kallonta da sauran hawayen a idona nace."Gwaggo don Allah ku rabu da yaron nan tunda baya so babu dole a cikin al'amarin nan insha Allahu Allah zai kawo min miji daidai da rayuwata na aura."


Girgiza kanta tayi tace."Sa'ida insha Allahu baki da miji sai Khalid na gaji da wannan al'amarin shima tsiya ce kawai amma yana sonki yana so ya 'bata mana rai ne saboda haka kada ki damu Khalid ko yana so ko baya so sai ya had'aku ku biyu ya aura."

Ina kokarin magana Kawu ya shigo dakin ya shirya cikin manya kaya da alama fita za'ayi hankalinsa a kaina suka gaisa da Gwaggo


A sanyaye na gaishe na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun hannuna.....Cikin rashin jin dadi yace."Sa'ida ina fatan lafiya naga idonki yayi jawur wani abu ya faru ne."?

Hawaye ne suka zubo min nasa hannu na goge ina girgiza kaina.

Gwaggo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login