Showing 9001 words to 12000 words out of 185789 words
ta salwance." hawayen takaicin da nake kokarin dannewa sune suka kufce cikin rawar murya nace."Khalid sake ni."
"Um!um! Aunty naji dadin rungumeki ki bari na samu nutsuwa ina cikin tsananin damuwa."
Yafad'a yana goga gefan fuskarsa a tawa.
Shuru nai jikina gabad'aya ya mutu ko yaya nayi motsi da niyyar kwace jikina zai sake matseni sai wani irin nishi yake!
"Khalid ni kake wa wannan iskancin ko? ni kake matsewa a soro saboda baka da mutunci Khalid."! murya a sha'ke nake magana.
" Aunty Sa'ida har abada babu tozarci a tsakani na dake abinda kikayi min d'azu ya 'bata min rai ko abinci na kasa ci Aunty me yasa zaki za'bi wancan Alhajin ki barni me nai miki ko ni ba namiji bane."
Cikin sanyin murya yake maganar yana yawo da hannunsa a jikina.
"Khalid ka daina mafarkin abinda ba zai faru ba kasan Allah duk maitarka akaina sai ka hakura dan ni nafi karfin'ka kaje ka nemi daidai da kai."
Fuskata ya d'ago yana kallona, naga idonsa yayi jajawur a take tsigar jikina ta tashi! fuskata na fizge! da sauri na daga hannu da niyyar kwad'a masa mari! yayi saurin ri'kewa.
Girgixa kansa yake Cikin 'kunar zuciya yace."Ni nafi karfin ki mare ni auntyna! na amince ni maye! ne amma akanki aunty Sa'ida ba zan fita a rayuwarki ba sai na tabbatar da cewa kin zama mallakata mu zuba ni dake."!
Tsaki naja na tureshi da fadin"Shashasha mara hankali kawai." gabana ya tare cikin 'bacin ran da banta'ba ganinsa dashi ba yace."Kada ki 'kara kirana da shashasha zan baki mamaki."
"Me zakayi min."? nafada ina watsa masa harara......Murza yatsun hannunsa yayi yace." Sai ranar da kika 'kara kirana da kalmar sannan ne zakiga abinda zanyi."
"Mtwwws! tsaki naja na ra'ba ta gefansa na shiga gidan.....Ajiyar zuciya ya sauke bayan shigewarta gidan ya shiga shafa kirjinsa yana lumshe ido har yanzu yana jin tudun nonowanta a kirjinsa, cikin mutuwar jiki ya fita daga gidan.
" To shikkenan Uwale zan duba maganarki wallahi dama nima sai da nayi wannan tunanin ace yarinya kwata-kwata bata so ayi mata maganar aure bayan tana da mane ma dole ne a nemi taimako." Uwale na kokarin magana na shiga dakin, sai ta washe baki da fadin"Babban mace hakima kin dawo kenan sannu lallai kin dauko rana."
Sama-sama na gaisheta na cire hijab din jikina na fita daga dakin na tsani alaqar Gwaggo da Uwale ko kad'an......Bayan fitarta Uwale tace."To shikkenan Gwaggo sai kinzo ina sauraranki." Gwaggo mi'kewa tayi domin yi mata rakiya tana fad'in "Insha Allahu gobe zanzo sai muje Allah dai ya rufa asiri." kallo na bisu dashi ina tunanin inda zasuje....Gwaggo ta dawo gidan tana kallona a fakaice kafin ta shiga dakin, mikewa nai nabi bayanta domin na kafa mata hujjata akan irin iskancin da Khalid keyi min...
*Masoya a taimaka da sharing a gruops??????*
*IDAN KINA SO KI BIYA KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP GRUOP...600 NORMAL 300 ACCONT...0542382124.....BINTA UMAR GTBAK IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE**GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO?????*
*_Ya Allah kayi mana katangar 'karfe tsakaninmu da ma'kiya! Ya Allah ma'kiyi wanda na sani da wanda ban sani ba Allah ka katange ni dashi???? Ubangiji Allah ka tsare gabanmu da bayanmu Allah dukkanin mai nufin mu da sharri ko wane iri ne Allah ka mayar masa kansa, Allah a gida da waje ka kare mu damu da zuriarmu Ameen ya hayyu ya 'kayyumu????_*
*6*
"A'a Sa'ida bana san sharri! A ina kuka had'u da Khalid d'in da har zakiyi masa wannan gundumeman sharrin yaron da tun d'azu ya fita dan babu yanda banyi dashi ba ma ya zauna yaci abinci yace baya ci sannan kawai kizo kice yana k'okarin lalata dake a soro."
Ina 'kokarin magana Ummatu ta bankad'a labule ta shigo dakin da fad'in"Wace magana naji kunayi kuna kuma kiran sunan Khalid." Gwaggo tace."Ke! Rabi abinda ba'a sa da kai ba dad'in kallo gareshi a'ina kikaji mun kira sunan Khalid da har zaki bankad'a labule kishigo a fusace."
Murmushi tayi tace."Gwaggo kenan duk fa maganar da kuke a kunne na ke Sa'ida ki shiga hankalinki dani wallahi wato Khalid din zakiyi wa sharri sabida baki da kirki to tun wuri kije ki nemi d'an iskan da yake lalubeki a soro amma ba Khalid ba."
Ido na zuba mata har ta 'kare maganarta ban tanka mata ba, Gwaggo tace."To tunda dai kin fad'i abinda ya kawo ki tafi kuma wallahi kada naji maganar nan a bakin kowa mutukar maganar nan ta fita dukkaninku sai ranku ya 'baci."!
Ummatu ta'be bakinta tayi ba tare da tace uffan ba ta kad'a kanta ta fita daga d'akin.
Duk yanda naso na daure kasawa nayi hawaye na zuba nace."Gwaggo wato nice 'yar iska lalatacciya ko? dukkaninku baku yarda Khalid zai iya aikata abinda na fad'a ba kun goya masa baya ya cigaba da bibiyata ko okey to shikkenan Gwaggo yanzu na gane matsayina a gurinki dan gashinan a zahiri kin nuna min cewa kinfi kaunar Khalid a kaina alhalin duk kece kika haifi iyayenmu to babu komai Gwaggo kinji na rantse da Allah duk ranar da Khalid yayi kuskuran sake ri'ke min hannu sai na d'auki tsatstsauran mataki a kansa.''Cikin zafin zuciya nake maganar.
Tace."To me zakiyi masa idan ya ri'ke miki hannu naga dai shine zai aureki to meye abin tayar da hankali kuma." Da sauri nace."Dake dashi zan kai ku gurin alkali sai kiyi masa bayanin da kikayi min yanzu."
Ha'barta ta ri'ke tana girgiza kanta tace."Lallai Sa'ida ni zaki kai gurin alkali."? "Kwarai kuwa mutukar baki daina daurewa Khalid gindi ba wallahi sai na dauki wannan matakin." shuru tayi tana kallona, nasan mamakina take, dan na 'kara tsoratata nace" Yanzu ma bari na kira wani abokin aikina wanda d'an uwansa yake aiki a kotun musulunci ta kasuwa na fad'a masa dukkanin abinda yake faruwa." Da sauri ta rike hannuna tana kokarin kar'be wayar tace."Sa'ida ashe baki da hankali kina so ki tona mana asirin gida."
Nace." Wane irin zan tona asiri ai gaskiya ce idan munje gaban alkali sai kuyi bayani dake dashi wanda kike daurewa gindin."
Hannunta na rawa tace"Yi hakuri dan Allah abar kaza cikin gashinta domin hakan yafi mutunci zan samu Khalid din naja masa kunne ya daina ta'baki tunda dai ba'a d'aura aure ba."
Nace."Shin yanzu kin yarda da maganata akan Khalid din ko kuwa baki yarda ba."? Da sauri tace."Haba na yarda mana dama sabida kada maganar tayi tsayi ne yasa kikaji nace ban yarda ba amma nasan Khalid zai aikata kuma zanja masa kunne kiyi hakuri kinji ko."
Ajiyar zuciya na sauke nace"To wannan karon dai na hakura idan ya 'kara kwatantawa to zaiga abinda zai biyo baya." Tace."Bama zai 'kara ba insha Allahu.''
Mi'kewa nayi na fita daga dakin ina jin tana fad'in"Kizo ka abincin naki ai tuntuni na shigo miki dashi daki." Nace."Wanka zanyi tukkuna." Da sauri tace."To shikkenan sai kin fito." Bakin rijiya na nufa na cika bokiti da ruwa na dauka na kai bandakin, dakin na koma domin cire kayan jikina.
Bayan sallahr isha'i kasancewar ana zafi a gari gashi babu wuta sai mukayi shimfid'a a tsakar gida muna hira, Ya shigo gidan cikin rashin 'kwarin jiki ya zauna kusa da ita da fad'in "Wash Allah Gwaggo na gaji wallahi nayi mutukar galabaita."
Zaune ta mi'ke tana gyara daurin dankwalinta tace."Yaron kirki ina kaje ne kuma me kayi ka gaji kana yawo cikin ka babu komai ina fata dai ka samu wani abu kaci."?
Ajiyar zuciya ya sauke 'kasa-'kasa ya d'an kalli mutuniyar tasa kafin yace." Wallahi Gwaggo har yanzu banci abinci ba Yau Salim ne ya jani yawo cikin adaidaita sahunsa." Tace."Allah sarki to ina fata ka samo d'an kwabo da d'ari.'' Goshinsa ya murza yace." Na samu me kike bukata."?
Baki ta washe tace."Ina bukatar Gashashshiyar kazar Malo mai nama." Dariya yasa yana kallonta yace."Gwaggo kina san dad'i a rayuwarki duba dan Allah kin iya fad'ar Malo mai nama." itama dariya tasa harda tafa hannu tace."To yaron kirki waye baya san dad'i ai mutukar ban takura maka ba to ka siyo min kazar malo mai nama." Khalid ya dinga dariya yana kallonta.
Takaicin abinda suke ya isheni sai kawai na dauki wayata ina dubawa, naji yace."Gwaggo ko kudin kenan yau sai kinci kazar Malo." Yun'kurawa yayi ya mi'ke tsaye yana kokarin sa takalmansa yace."Auntyna ke me kike so."? Banza nai masa, Tace."Sa'ida kina ji ya nayi miki magana ko babu dai kyau gaba."
Ba tare dana kallesu ba nace."Bana bukatar komai." Tayi sauri tace."Kaji wai bata bukata." Yace."Okey to babu damuwa ai " hanyar fita ya nufa tace"To ina jira dan Allah kada ka fita abokai su ri'ke ka har nayi bacci." Yace."Yanzu zan dawo nima yunwa nakeji ai." tace."To kafin ka dawo bari na fito maka da abincinka." Ba tare da yace wani abuba ya fita daga gidan
Mi'kewa tayi ta shiga daki ta dauko masa fulas din abincinsa kana ta dauko kofin silba ta ciko masa da ruwan randarta tazo ta ajiye a kusa da ita.
Kallonta nayi rai a 'bace nace"Gwaggo keda zaki sanja masa fuska saboda laifin da yayi shine harda dauko masa abinci ko da yake ai nasan kin manta tunda kinga ya samo kudin siya miki kaza idonki ya rufe to har yanzu ina nan akan bakana."
"Aa Sa'ida ban manta ba ina sane inaso yaci abinci ya huta sai nai masa maganar." "Umm! nace naja bakina nai shuru! jin maganarsa shida abokansa a soro yasa na mi'ke na shiga daki, yana shigowa kai tsaye 'kofar Ummatu ya nufa da fad'in " Gwaggo ina zuwa."
Da sauri tace."Aa zo ka bani leda ta kafin ka shiga bana so ta za'be abinda ka shigo dashi.''! Dariya nasa ina mamakin 'karfin halin Gwaggo mata ta haifi d'anta amma ta fita iko dashi.....Dawowa yayi da baya ya mi'ka mata leda guda tace."To yawwa yanzu naji magana ka fito ga abincin naka." Yana 'yar dariya yace."To Gwaggo." Gurin mahaifiyar tasa ya nufa domin itama ya bata tata ledar.
kwance a d'an tsakar gidanta ya sameta da Mafici a hannu tana firfita shigowarsa yasa ta mike zauna tana kallon ladar hannunsa.....Zama yayi gefan tabarmar da take zaune yace."Ummatu me zai sanya ki takura kanki bakya fita babban tsakar gida kisha iska sosai."
Girgixa kanta tayi tace."Khalid 'kyaleni anan yafi min kwanciyar hankali akan na fita Gwaggo ta fad'a min ba'kar magana."
Yace."Ummatu idan da sabo yaci ace ki saba da halin Gwaggo wata irin macace mai wani irin hali bayan haka kuma akwai rikicin tsufa a tare da ita." Girgiza kanta tayi tace."Khalid dama ai kai baka ganin laifin Gwaggo duk abinda tayi daidai ne a gurinka."
Girgiza kansa yayi yace."Ba haka bane wallahi Ummatu yanzu a matsayin na shekarun Gwaggo dole ayi mata uziri shiyasa kikaga duk abinda tayi nake biye mata saboda samun nutsuwarta ba wai bana san laifinta bane."
Tsaki taja tace."Duk da da akwai tsufa to da akwai iskanci wannan tsohuwar guda ce Khalid ni kad'ai nasan irin takaicin da take kuntuka min a gidan nan."
Yace."To kiyi hakuri dan Allah komai mai wuce wa ne gashi kema na siyo miki nama." Kar'ba tayi tana duba ledar tace."Sai da ka kai musu suka za'ba tukkuna ni aka kawo min saura ko."
Girgiza kansa yayi yace."Aa Ummatu duk d'aya ne wallahi dake da Gwaggon." Tace."Ai kamata yayi ka daina daidaita ni da ita tunda ni na haifeka idan kana neman albarka sai kayi min biyayya."
Yace."Ummatu dan Allah ki daina irin wannan maganar wallahi dake da Gwaggo duk daya kuke a gurina ke kika haifeni dole kina da martaba ta mussaman a gurina Gwaggo kuma itace ta raine ni har na girma Gwaggo bata san 'bacin raina komai ta samu nawa ne abinci wannan Gwaggo bata ci sai tare dani sai dana na tafi makaranta tukkuna muka raba kwano da ita Gwaggo takan iya hana cikinta abu ta ajiye min Ummatu kada ki manta Gwaggo itace tayi rabin dawainiyar Karatuna idan tayi sana'arta haka zata tattara kudin ta bani nayi hidimar makaranta dasu duk lokacin da nazo hutu sai ta bani kudi wata bukatar zata taso Gwaggo tayi Baba yayi a haka fa akayi ta tafiya har Allah ya kawo ni wannan lokacin da nake daf da kammala makaranta kinga kuwa dole na kyautata mata domin ta taka muhimiyyar rawa a rayuwata."
"Khalid wato ka sani a gaba kanayi min gori ko? to ko banyi maka hidima ba ai ba zaka iya biyana irin dawainiyar cikin ka da haihuwar ka ba, saboda haka kada ka sake sani a gabana kana kawo min wata banzar magana."
Shuru yayi yana jinta sai fad'a take masa yace."To Ummatu kiyi hakuri dan Allah insha Allahu ba zan kara ba." Shuru tayi masa ta mike ta nufi kicin plate ta dauko tazo ta zauna tana kokarin sa naman a ciki.....mikewa yayi ya fita daga gurin, nan ya samu Gwaggo a kashingid'e har taci ta gyatse tana gyangyad'i! zamansa a kusa da ita yasa da sauri ta tashi zaune tana fad."Khalid ka fito."
"Umm." kawai yace ya zauna ya dafe kansa, cikin kulawa tace."Menene yake damunka."? Shuru yayi yana girgiza kansa, 'kasa-'kasa tace."Kada ka damu da barazanar Sa'ida akan abinda kayi mata d'azu nan ta titsiye ni tanayi min jaraba wai sai ta kaimu kotu ni dakai."
Cike da mamaki! yace."Akan wane dalili zata kaimu kotu kuma me nayi mata da har take wannan furucin."? Da sauri tace."Yi magana a hankali Dan bana tsammanin tayi bacci."
Tsaki yaja 'kasa-'kasa yace."Me tazo tace anyi mata."? Gwaggo murya a 'kasa tace."Wai cewa tayi kana tare ta a soro kana lalubeta."
Yanda Gwaggo ta fadi maganar yasa dariya ta 'kwace masa yace."Ni sharri kawai tayi min abinda ma yau ban yini a gida ba." Gwaggo tace."To nima haka nagani ta shigo fuska a murtuke ta dinga jaraba dan har mahaifiyarka taso ta biye mata na shiga tsakaninsu, jin tana maganar kaimu gaban alkali yasa na bata hakuri nace zan ja maka kunne."
Yace."Gwaggo da kin sani ma baki wahalar da kanki gurin bata hakuri ba ni ba d'an iska bane da zatayi min irin wannan sharrin nima zan dauki mataki a kanta dan kafin ta kaini 'kara kotu ni zan kaita tunda tayi min sharri."! Sosai ya fitittuke yake kare kansa Al'amarin ya dinga bani mamaki! dan duk maganar da suke ina jinsu raina kuma ya 'baci sosai da naji Gwaggon na rarrashinsa har tana cewa ai dama tasan Sharrin nai masa ba zai aikata ba, naji tamkar na fita naci masa mutunci sai dai kawai na taushi zuciyata na hakura na kyaleshi ina tunanin irin matakin da zan dauka a duk ranar da ya sake kuskuran ta'ba jikina..
*Masoya a taimaka da sharing a gruops????*
*IDAN KINA BUKATAR KI BIYA KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP #600 NORMAL#300 ACCOUNT.... 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER.*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO???*
*Pegen na yau naki ne*
_*Gwanata FATIMA SUNUSI RABI'U Matashiyar marubuciya mai fasaha da amfani da basirar ta a inda ta dace Ina kaunarki Takwara kamar yanda kike 'kaunata????*_
*7*
Cikin nutsuwa na kalleta tana ta shiryawa nace."Wai Gwaggo ina zakije ne da sassafe haka."? Tana shafa mai a kafafunta tace."Wallahi ugunwa zamuje da Uwale amma ba zan dad'e ba zan dawo dan ina da aiki a gabana Salisu mai kanti yace nayi masa lagwani zai siya."
Nace."Gwaggo wannan wace irin unguwa ce da zakuje da safe karfe bakwai da rabi kifa duba lokaci ki gani ko karyawa bakiyi ba amma kina kokarin fita."
"Kinga Sa'ida kada ki takurawa rayuwata ina ruwanki da inda zani zaki dameni da surutai.'' Nace." Babu ruwana amma bari naje na fad'awa Baba Iro cewa Uwale zata jaki yawo."
Da sauri nayi yun'kurin fita ta ri'ke gefan rigata da fad'in "Dawo na fada miki inda zamuje." komawa nayi na zauna ina kallonta, tace."Jikar Uwale ce take aljanu shine zamuje mu kar'bo mata magani gurin wani malami."
Cike da mamaki nace."Gwaggo Uwale ta fara d'ora ki a turba mara kyau ko yanzu tsofai-tsofai daku ina ku ina zuwa gurin malami."
"Sa'ida kada ki fassara mu da wata manufa bakiji abinda na fad'a ba jikar Uwale Nafisa itace take aljanu shine zan rakata ta kar'bo mata magani."
Nace."Dole sai kin rakata ita bata san hanya ba."? A tausashe tace."Tasan hanya mana nima ai inso malam d'in ya taimaka min."
"Me yake damunki da zakije gurin malami ya taimaka miki ba zakiyi alwala ki roki Allah ba."
shuru tayi bata bani amsa ba, nace." Gwaggo ki kiyaye kada Uwale ta jaki gurin bokaye da girma da mutuncin ki me kike nema a duniya wanda ba zaki rok........."Sa'ida wai ni sa'arki ce ne da zaki zauna kina kokarin fad'a min maganar banza waye yace miki gorin bokaye zamuje."?
Ganin yanda ta fusata yasa na sassauta murya "Gwaggo kiyi hakuri idan kinji shaushin maganata halin Uwale na sani na rashin tsoron Allah da san duniya."
"To naji wuce kiyi tafiyarki nama fasa zuwa tunda zargin da kikeyi min kenan." Murmushi nayi na cigaba da shirye-shiryen tafiya makaranta.......Ummatu ce ta daga labulan dakin ta shigo da sallama a bakinta, dukkaninmu muka amsa mata ta ajiye jug din kunun dake hannunta tace."Gwaggo ina kwana."? Ciki ciki ta amsa tana dauke kanta kamar itace tai mata laifin.....Ummatu ta juya zata fita a nutse nace."Ummatu antashi lafiya." ? ta amsa ba tare data juyo ba....."Rabi yau