Showing 123001 words to 126000 words out of 185789 words

Chapter 42 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24220

ina fata ba wata matsala bace."


Daurewa nayi nace."Babu komai bacci nayi shiyasa idon ya sanja." Yace."Okey to ya kike ya zaman kadaici." Mirmushi kawai nayi ban tanka masa ba.

Ya kalli agogon hannunsa da fadin."Ni zanje babban gida mu gaisa dasu." Nace."To ka gashe min dasu." Mikewa yayi yana fadin."Insha Allahu zasuji sa'kon ki.

Bayansa nabi da kallo har ya bude dakin ya fita.....Jingina baya na nayi jikin gadon na shiga tunanin rayuwa.



Sai kusan tara da rabi ya shigo gidan, gani na a zaune a falo ya bashi mamaki yace."Baki bacci ba."? A nutse na mike da fadin."Eh na tsaya ka dawo ne." Murmushi yayi na kar'bi wayoyinsa ina masa barka da zuwa.

Amsawa yayi ya rike hannuna muka nufi dakinsa.

Da kaina na hada masa ruwan wanka yana ta sa min albarka na fito masa da jallabiya da gajeran wando na ajiye kusa dani.....Daure da towel ya fito sai yayi saurin dauke kansa a maimakon ni naji kunyar ganinsa a haka sai ya kasance shi yake jin kunyata, dan sai naga kamar a tsarge yake tsayawa yayi bakin kofar toilet din da fadin."Bani kayan nan." Da sauri na mike da kayan a hannuna na kai masa, kawai sai naga ya koma toilet din ya banko kofar. sakato nayi da baki ina mamaki!
Ina nan tsaye ya fito ya wuce ni ba tare da ya tanka ba, a sabule nabi bayansa falon sai na sameshi zaune a kasan kafet yana duba loptop. zama nayi a hankali nace."Ba zaka ci abinci ba."?

Hankalinsa nakan Loptp din yace."Bari na rage aiki tukkun." shuru nai kawai na zuba masa ido ina mamakin al'amarinsa.

Kusan rabin awa yana aiki a loptop din kafin ya rufe a nutse ya kalle ni da fad'in "Tashi muje dainng din ki bani abincin." Mikewa nayi ya biyo bayana.

Tsaf na shirya masa abincin na tura masa gabansa zama nayi ina kallonsa yana cin abincin yana amsa waya

Nace."Yaya Aminu kayi abu d'aya mana ka ajiye wayar kaci abinci sai hakan yafi.''


Ba tare da ya kalle ni ba ya cigaba da wayarsa.....Ji nayi raina ya 'baci sai kawai na miqe na bar masa gurin.


Koda ya kammala cin abincinsa zuwa yayi ya dauki loptop dinsa bece min uffan ba ya bude dakinsa ya shige! ni dai mamaki ne ya kusa kasheni a gurin da kyar na iya kai kaina daki na kwanta.

Haka rayuwar mu ta cigaba da tafiya tsayin wata guda da dawowarsa babu wata mu'amula ta aure data ta'ba shiga tsakanina dashi Kullum a dakinsa yake kwana a garkame! gabadaya ma ya daina yarda na ra'bi inda yake dan duk kokarin da nake masa idan ya dawo daga kasuwa sai ya dakatar dani yace naje na huta shima Allah ya bashi lafiya zai iya had'a ruwan wankansa.
Ganin wulakancin yayi yawa yasa na daina shiga dakinsa sai dai idan ya fito mu gaisa ya kama hanya ya fita.......Gashi kamar mara tunani kullum sai ya tura min kudi accont d'ina al'amarin dai sai kace hauka! kuka naci na koshi na yanke shawarar tun kararsa da magana domin dai ni na gaji ba auran kudi nayi ba halastaccan aure nayi irin wanda Allah yake so......Sai da ya fito falon sannan nima na fito daga dakina na sameshi a zaune yana abinda ya saba lissafi da amsa kiran waya cikin zuciyata nace."Ban ta'ba ganin sahoramin namiji irinka ba. Wayar hannunsa ya kashe ya kalle ni da fadin."Kina da wata bukata ne."? a nutse nace."Eh ina da ita." Ya zuba min ido da fadin."Ina sauraranki." Murya na rawa nace."Yaya Aminu wai me kake nufi ne."? Cikin wani irin kallo yace."Bangane ba."? Na d'aure fuska tamau! nace."Shin dutse ka ajiye a gidan ka kome? ko kana da lalura ne."? Tsira min ido yayi yana kallona na sake cin kunu da fadin."Tsayi wata d'aya da sati biyu nake cikin gidan nan naci na koshi naci nama nasha madara nasha nono na kwanta a Ac me kake tsammanin zai faru." ? Dariya yasa yana kallona, sai kawai hawaye suka 'kwace min. Nace."Wato saboda kai baka da damuwa ka maisheni mahaukaciya kana min dariya ko to wallahi na gaji ni zan samu mahaifiyarka na fad'a mata halin da ake ciki." Da sauran dariyar a fuskarsa yace." Ai ba sabon abu bane a gurinta idan kin fada mata tuna mata kikayi domin tafi kowa sanin matsalata." Hannu nasa na share hawaye da fadin."To me yasa kasan kana da matsala ka amince da aurena."? Jim yayi kafin yace."Kawai bana so na bijirewa umarnin mahaifina ne." Cikin takaici nace."To kawai daga yau ka kira kanka da mace tunda ka fita daga sawun maza wato har wani fad'a kake kana da lalura to zaman me kake a haka da ba zaka nemi magani ba."? Rai a d'an 'bace yace."Ke Sa'ida kada ki fad'a min maganar banza mana." Nace."Ai gaskiya ce." Hannu ya daga min da fad'in "To tunda dai kin damu yau zan jarraba na gani." Naji wani kuttun bakin ciki ya tokare min a ma'koshi nace."Wallahi tallahi kudin ka na banza ne tunda har ka sake ka mayar da kanka haka meye amfanin neman kud'in naka kana fama da lalura irin wannan." Shuru yayi min, na dinga masa surutai ina farfad'ar masa maganar da duk tazo bakina.....A fusace! yace."Ki tashi ki bani guri idan ba haka ba wallahi ranki zai 'baci! Mi'kewa nayi na bar gurin raina a mugun 'bace.!




*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE**SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min_*


_Na lura dai idan ban cigaba da littafin nan ba za'a samu masu zuwa inda nake?? nayi magana ya kai sau nawa wasu sun kasa fahimta wasu ma gani suke 'karya nake to na samu gilashi tunda naci kud'i ai dole a hanani nutsuwa Allah ya bamu rai da lafiya nagode sosai da k'auna da kuma kyawawan adduoinku zamu cigaba da littafi da yardar mai duka??_

*79&80*
Ajiyar zuciya na sauke cikin tararrabi nace."Gwaggo kije can k'auye ki samo wa Yaya Aminu magani shine manufar zuwana gurinki." Kauda kanta tayi tace."Sa'ida meye nawa a cikin wannan sha'ani haka kawai zan dauki kafa na tafi k'auye samo wa mijinki maganin ka'rfin maza ai dama hausawa suna cewa duk wanda ya sayi rariya yasan zata zubda ruwa ai GA IRINTA NAN garin son zuciyarki da kwad'ayin ki kin guji d'an uwanki yaro mai jini a jika kin auri mara lafiya saboda haka idan kin damu kuma kina so ki cigaba da zama da mijinki sai ki wanke k'afarki ki tafi k'auyen da kanki ki nemo masa maganin karfi ni kam babu inda zani." Ta kare maganar tana kokarin mikewa, kallo kawai na bita dashi zuciyata na wani irin tafarfasa kafin na ankara hawaye masu mugun zafi sun kufce min, maganganunta na dinga ji kasa- kasa a tsakar gidan "Haka kawai za'a sani zuwa k'auye akan wane dalili? ba zanje ba to kaji."!! Murya na rawa nace." Wato Gwaggo ke baki da sirri ko kin fita kina surutai a tsakar gida kina so ki fallasa sirrina ko."?

"Oh o! ni ba nufi na kenan ba Sa'ida maganar dai nake jajantawa." Cikin kuka nace."Ni dai maganar ta isa haka tunda dai ba zaki taimaka min ba sai kija bakin ki kiyi shuru."

'Kasa-'kasa tace."Eh ba zan taimaka ba kije da kanki ki nemawa mijinki magani ehe." Khalid ne ya shigo gidan a lokacin da take maganar, Yace."Surutan me kike ke kadai ina aunty Sa'idan."?

"Tana daki surutai kuwa dole nayi domin kamawa tayi." Ganin yanda ta fadi maganar da bacin rai yasa yace."Me ya faru gwaggo dan Allah ki dinga samawa kanki lafiya."

Tana wanke kayan miya tace."Khalid al'amarin ne ai da bakin ciki wallahi shiyasa na kasa hakuri."

Yace."To koma dai menene sai ki barwa Allah kiyi addua akan Al'amarin."

"Oh!o ni babu wata addua da zanyi ai ita ta janyowa kanta." Shuru yayi yana kallonta ta bude baki zata cigaba da magana na fito daga dakin ido jajur nace." Gwaggo idan kika fada masa sirri na zanyi miki Allah ya isa."

Gabadaya ita dashi suka juyo suna kallona. baki ta ri'ke tace."Sa'ida ni zaki wa Allah ya isa."?

Kafin nayi magana ya magantu cikin bacin rai yace."Wai aunty Sa'ida me yake faruwa ne da har kike wannan maganar Ni bare ne da har kike gudun naji sirrin ki."

Share shi nayi na nufi hanyar fita raina a masifar 'bace! hanya ya tare yana watsa min wani irin kallo yace."Ba zaki tsaya ki huta ba zaki tafi gashinan Gwaggo na kokarin dora miki girki.

Murya na rawa nace."Khalid bani hanya na wuce na tafi." Girgiza min kai yayi yace."Ba zaki tafi ba sai naji Abinda yake damunki."

"Khalid ko kaji babu abinda zaka iya yi min." Karaf Gwaggo tace."Aikuwa shi yake da abinyi." Kallonta nayi raina a 'bace nace."Me kike nufi."? kanta ta sunkuyar ta cigaba da abinda take.

Tsaki naja k'asa-kasa na juya da niyar fita, da sauri ya tare ni da gangar jikinsa saurin janyewa nayi tsigar jikina na tashi wani irin kallo nai masa "Bani hanya na wuce." Kansa ya girgiza min babu walwala a tare dashi ya rike hannu na.

Gabadaya jikina ya mutu ya jani muka zauna kan tabarma.....shuru na minti biyar Yace."Gwaggo fada min matsalar auntyna ko ina da magani.

Tace."Bari naje na kai markade na dawo tukkuna." Mikewa yayi ya kar'bi kayan miyan da fadin."Bari na samu yaro a waje na bashi ya kai miki."


Tace."To yawwa hakan yayi." da sauri ya fita ita kuma ta dauki tukunyar nama tana wankewa......"Gwaggo kada ki fadawa yaron nan abinda ya shafe ni kinga bai kamata ba.

Shuru tayi min ta cigaba da aikace aikacen ta.....Murya na rawa nace "Gwaggo kina jina ko."

"Sa'ida shin baki ji abinda ya fada ba? yace watakila yana da taimakon da zaiyi miki babu laifi idan yaji matsalarki."


"Ni dai na fada miki kada ki fada mas......shigowarsa gidan ta katse maganata ya zauna kusa dani da fadin." Gwaggo ina sauraranki.

Kallonsa tayi tace."Khalid Sa'ida tazo akan na taimaka mata naje k'auye na samowa mijinta maganin 'karfin maza wai bashi da lafiya."

Sunkuyar da kaina kasa nayi kaina sai sarawa yake nayi da nasanin zuwana gurin Gwaggo da wannan maganar..........Cikin wata kasalalliyar murya yace."Aunty ne hakane maganar Gwaggo."?

Kasa dago kai nayi na kalleshi ballantana na bashi amsa kunyar duniya ta ishe ni.

Murmushi yayi wanda ya tsaya iya le'bansa yace."Auntyna ya haka ta faru kuma ashe kallon kitse ki kai wa rogo shin ya sunan wannan auran naki tunda babu biyan bukata ta aure."?


Jarumta da dauriya na aro na dago kaina tare da 'bata fuska nace. "Kaga Khalid wannan magana bata shafeka ba ba naso na sake jin kayi wata magana akai."


Hannu ya tusa a tarin sumar kanshi yana wani irin murmushi kasa kasa yace."Magana ta shafe ni tunda har ta shafe ki ko kin manta abinda yayi Khalid shi yayi Sa'ida."?

Shuru nayi masa tare da dauke kaina.

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Kin san me."? shuru nai masa yace." Kina jina ko."? ba tare da na kalleshi ba nace."Kunne ne ke ji."

"Okey inaso kiyi min bayanin yanayin mijin naki akwai wani mai maganin hausa a Lego's da zan had'a ku dashi.


Da sauri na dago kaina ina kallonsa.....da murmushi a fuskarsa ya daga min gira domin so ya tabbatar min da maganarsa........ Kaina na sunkuyar kasa Nace." Ina ganin ba sai kaji wani abu ba kawai ka bani number mai maganin."


Girgiza kansa yayi idonsa kuri a kaina yace."Bashi da waya mai maganin abinda yasa kuma kikaga nayi magana wani abokinmu da yake fama da rashin lafiya irin ta mijinki ya samu lafiya dalilin zuwa gurin mai maganin.

Shuru nayi ina nazari yace."Ko dai baki yarda dani ba aunty Sa'ida ni yanzu babu wani abu da yayi saura a tsakaninmu sai zumunci ina tausaya miki rayuwar aure babu biyan bukata."


Zuciyata ce naji ta karye nace."Khalid ya zanyi kaddara ce a haka." cikin sigar bugun ciki yace."Kina nufin wancan alhajin ma haka yake bai da lafiya.

Kamar wata shashasha na d'aga masa kaina a raunane nace."To gwanda shi akan Yaya Aminun amma duk tafiyarsu daya.

Khalid ya danne 'bacin ransa yace"Okey shi Alhaji Nuran kina gamsuwa dashi kenan."? Ba tare dana kalleshi ba nace."Babu laifi."

Shuru yayi yana yaqi da zuciyarsa......."Yanzu kin yarda dani zaki min baya nin matsalar mijinki ko kuwa."?


"Khalid idan zaka taimaka mana zan fada maka." yayi mata wani irin kallo da fadin." Zan taimaka muku saboda haka ke nake sauraro meye matsalarsa."?



"Bashi da lafiya gabadaya tunda mukayi aure bai ta'ba biya min bukatata ba." shuru yayi na minti biyu da 'kyar yace."Kina nufin gabanshi baya tashi kome? ko kuma sha'awa ne baya yi."?

Shuru nayi kunya ta hanani magana....Yace."Aunty Sa'ida ke nake saurare." Da kyar nace."Khalid Yaya Aminu abun yayi masa yawa baya sha'awa sannan kuma gabanshi 'karami ne irin na yara baya mi'kewa."

Sunkuyar da kansa yayi yana 'boye dariyar dake kokarin kufce masa amma inaa sai da ta su'bce ta futo fili ya dinga yi yana kallona ni kuwa kamar shashasha na dinga kallonsa gabana na wani irin faduwa.

Gwaggo ta fito daga kicin hannunta ri'ke da ludayi tace"Jarumi wannan wace irin dariya ce haka."?

Da kyar ya gimtse dariyar yace."Gwaggo je ki cigaba da aikin ki." kicin din ta koma tana fadin."To Allah ya kyauta dai.


"Juyowa yayi yana kallona da murmushi a fuskarsa, rai a 'bace nace." Ashe baka da mutunci ko ? ka mayar dani sakarai na fada maka sirri na kana dariya."


Fuskarsa ya gyara yace."Auntyna naso na gimtse dariyar amma sai da fita okey mu bar wannan maganar muyi mai amfani ko."

Tsaki naja tare da kauda kaina gefe.....Yace."Ki kwantar da hankalin ki insha Allah idan na isa Lego's zan samu me maganin mu tattauna dashi mybe ma idan zan sake zuwa nazo muku da magani Allah yasa a dace amin."


Shuru nai masa ban tanka masa ba ya karaci surutan sa ya mike cike da wani irin nishadi ya kama hanya ya fita daga gidan domin sallama da abokanansa.


Gwaggo aikace aikacen ta kawai takeyi taki cewa dani komai haushin hakan yasa na mike ina gyara mayafi na sai Uwale ta rangwada sallama a gidan, ganina ya sanya ta washe baki da fadin."Aa amarya ce a gidan." Gwaggo ta fito daga kicin da fadin."Aikuwa dai Uwale kece da hantsi."

Tana kokarin zama kan tabarma tace."Wallahi kuwa ai 'kauyen daburau zan tafi yanzu kwana biyu basir ne ya tayarwa Ayuba shine zanje na samo masa magani acan.

Gwaggo tace."Aikuwa gwanda da kika shigo domin dama koda baki shigo ba nayi niyyar zuwa gidanki da wata magana."

"Gwaggo ni zan tafi."? Kallona tayi da fadin." Aa ki koma ki zauna mana tunda neman taimako kika zo ga Uwale zataje kauyen daburau sai ki bata sautu."


Ji nayi kamar na kwada mata mari saboda takaici da bakin cikin abinda take takalmana nake kokarin sanyawa sai kawai ta fashe da kuka da fadin."Wannan yarinya kina nema ki sanya zuciyata ta buga ko wato ba zaki ji maganata ba zaki tafi wacan uban abincin waye zai ci."


Uwale ta sassauta fuska da fadin."Haba Sa'ida kada ki tafi mana ki zauna mu tattauna magana naji matsalarki."

Ajiyar zuciya na sauke na cire takalmi na na zauna tare da fadin."Ni ba zakiji komai daga bakina ba ita data fara fada miki maganar ta karasa fada miki."


Uwale ta kalleta da fadin."Gwaggo me yake faruwa ne."? Da saurin gaske ta shiga fada mata abunda yake faruwa


Uwale tayi murmushi tare da fadin."Yo ai Sa'ida wannan matsalar ba sabuwa bace mu da muke yawo gidajen masu magani mu muke ganin abubuwa wannan matsalar itace ke damun wasu mazan kuma idan anyi katari da magani mai kyau sai kiga an dace saboda haka ki kwantar da hankalinki yanzu ki bada sadaka sai nayi sauri na tashi na tafi insha Allahu kafin la'asar na dawo.

Shuru nayi ina nazarin maganarta.....Gwaggo ta fusata! da fadin."Ke duk wanda zai taimaka miki sai kin zarge shi ki saki zuciyarki ki bada sadakar magani tunda dai ke kikaji kika gani sai ki daura d'amarar neman magani."


"Uwale dan Allah kada naji maganar nan a wani guri." hankalina a kanta nayi maganar .

Gabad'ayansu suka rike baki Uwale cikin jin haushi tace"Sa'ida munafuka kika mayar dani kome."?


Da sauri nace"Aa ni ba haka nake nufi ba halinki na sani idan labari yayi miki dadi sai ki manta ki fadi abinda bai kamata kowa yaji ba."


Cikin takaici Gwaggo tace."Uwale tashi kiyi tafiyarki ina dalilin wannan abu yarinya ta dinga kokarin cin fuskarki a banza a wofi."

Da sauri nace."Gwaggo kinga don Allah ki tsame kanki daga cikin maganar nan tunda dai ke kinqi taimakawa ai sai kija bakin ki kiyi shuru ki kyale wanda zasuyi.

Tsaki taja ta bar gurin.

Handbag d'ina na bude na dauko kudi dubu dubu guda biyar na bata da fadin "Uwale ga sadaka Allah ubangiji yasa a dace." Hannu tasa ta 'karba da fadin."ameeen ameeen." Na mika mata dubu daya da fadin."Ga wannan sai ki kara kudin mota." tasa hannu ta kar'ba da fadin."To nagode a na tashi na tafi kada naje na samu layi a gurin.''

Nace."To shikkenan Allah yasa a dace."Takalmanta tasa tana amsawa ta leqa kicin a gurguje tayi sallama da Gwaggo ta fita daga gidan.


Mikewa nayi jiki a sanyaye naje na kwanta gadon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login