Showing 120001 words to 123000 words out of 185789 words

Chapter 41 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24189

dadi Yaya Khalid duk kuruciyarsa da wayewarsa ya rasa wacce zai mak'alewa sai sauran maza A makaranta fa kullum cikin bin ofis din malamai take suna aikata masha'a." Baito tayi karaf tace."Eh ai gashinan shima tana lalata shi yaro bashi da lafiya ta rungumeshi a kirjinta nayi magana kakar tasu ta daure musu gindi sabida rashin mutunci to wallahi Rabi tun wuri ki tashi tsaye akan d'anki dan mutukar kika zauna kina zuba ido akan duk abinda yake faruwa to zaki d'ora hannu aka sabida tsabar bakin cikin da takaici."

Ummatu tace."Baito kiyi shuru kawai da bakin ki ai da Khalid din da ita mai daure masa gindi duk zanyi maganinsu akwai lokacin da zai zo na nuna mata cewa ni nake da hakki akan d'ana sabida nice uwarsa ni na haifeshi nayi wahala dashi babu wacce ta isa tayi min iko akan ikona wallahi akan hakan sai dai duk abinda zai faru ya faru." Baito tace."Kamata yayi ma ki cigaba da neman taimako gurin malamai dan dole sai ana sa miki hannu a cikin Al'amuranki idan kina so kiga daidai." Ummatu ta shiga bin dakinta da kallo tana neman abunda zata d'aga ta siyar......."Baito yawon malam sai kana da kudi kina dai kallo yanzu bani da katifa a dandayar kasa nake kwanciya sai dai idan samiru na zan siyar."
Baito tace."To meye a ciki don kin siyar da Katifa da Samiru ai dama kafin bukata ta biya dole sai ansha wuya sabida haka wannan karon kawai idan munje gidan malam zamu sa ayi musu farraqu ma'ana a rabashi da kakar tasa haihatahaihatan!." Jamila tace."Eh Baito abinda zakuyi kenan sannan don Allah nima idan kunje kusa malam yasa masa soyayyata a cikin zuciyarsa.
Baito tace."Kada ki damu Jamila zan nema miki taimako kuma ki kwantar da hankalinki Khalid kamar ya aure ki ya gama."
Jamila mirmushin jin dadi tayi da fadin."Nagode sosai Baito.......Motsin shigowar Gwaggo gurin yasa sukayi shuru da bakinsu Gwaggo tace."Rabi kina ina ne? ki bude min dakin Khalid zan daukar masa kayan sawa yayi wanka." Ummatu da sauri ta fito daga dakin tana fadin."Gwaggo shi ba zai shigo yasa kayan da kansa ba sai kinzo kin daukar masa ni bani da mukkulin dakinsa.

Gwaggo tace." To da yaya aka samu ma yayi wankan kin san jikinsa babu kwari shiyasa na karbi mukkulin dakin nasa gashi a hannuna kizo ki bude min dakin.


Ummutu ba don ranta yaso ba ta kar'bi Mukkulin ta bude mata dakin, a maimakon tayi tafiyarta sai taja tunga ta tsaya tana kallon Gwaggo na bude wardrobe d'in kayansa tana fad'in 'Yar karamar riga yace a dauko masa kin san garin akwai zafi."

Ummatu shuru tayi sai hararar ta take, Gwaggo ta dauko masa shirt da 3qutar tana fadin."Naga yafi amfani da irin wannan a lokacin zafi." Nan ma Ummatu uffan ba tace ba.


Gwaggo ta bita da kallo tana nazarinta lokaci guda ta fusata tace." Rabi da kika ja tunga kika tsaya kina kallona ko gadi na kike yi dan kada nayi masa sata."

Ummatu da sauri tace."Aa Gwaggo ni ba haka nake nufi ba.

Gwaggo tace."Haka ne mana Rabi menene na tsayawa a kaina kina kallona gashi ina miki magana kinyi banza dani."


Ummatu ganin Gwaggo na nema ta mayar da al'amarin babba yasa da sauri ta bar gurin ba tare da ta sake magana ba, Gwaggo taja tsaki da fadin."Ke dai naga sanda zakiyi hankali." fitowa tayi daga dakin ta kulle ta fita daga gurin.


Yana zaune jinge ne da bango (garu) daga shi sai gajeran wando tunda ya fito daga wanka ya zauna a haka ko mai bai shafa ba kawai ya tsira min rikitattun idanunsa, ni kam jikina ne yayi sanyi da kyar na iya masa magana akan yasa kayan da ya cire kafin Gwaggon ta kawo masa wanda yake so.

Girgiza min kansa yayi alamun ba zai sanya ba ya cigaba da hautsina ni da salon kallonsa.


Jiki a mace na mike domin fita daga dakin ina ganin zama na a dakin zai iya haifar da d'an da bashi da ido domin kuwa wani irin masifaffen feelings ne ke taso min......Hannuna ya rike na juyo ina kallonsa tare da kokarin kawar da abinda ke taso min.....A marairaice yace."Ina zakije kuma? bayan kin san kallonki kad'ai yana sanyawa naji sanyi a cikin zuciyata.

Ba tare da nayi nazarin maganar ba nace."Khalid ni kuma zaman ka ne a haka bana so sabida ina jin wani iri a tare dani." ido ya tsira min da munafikin murmushi a fuskarsa yace."Kina son suffata kenan dama ai na san ni kadai ne namijin da zai iya dake.

Da sauri nace."Aa ba haka nake nufi ba Khalid ina nufin zaman ka babu riga zai janyo mana matsala kada Gwaggo tayi ba'ki zasu zargi wani abu.

Murmushi kawai yay ya janyo ni na zauna a cinyarsa cike da mamaki nake kallonsa gabana na wani irin bugawa, hannuwansa yasa ya zagaye 'kuguna ya dora fuskarsa a kirjina a kasalance yace." Ina mutukar shiga cikin shauki idan na dora fuskata a kirjinki."


Cikin tashin tsigar jiki na dauke fuskarsa daga kirjina na fara kokarin mikewa daga jikinsa ya wani ru'kun'kume ni yana sakin wani irin nishi!! ture fuskarsa nayi raina a d'an 'bace nace."Khalid kada kaga na sakar maka fuska ka dinga kokarin shige gona da iri sake ni don Allah."


Shuru yayi be tanka min ba ya cigaba da cusa fuskarsa a kirjina! jikina ne ya soma rawa nasa karfi ina tureshi kamar mayen 'karfe yana mannewa a jikina......'Kwalla ta cika idona ni kam na rasa wace irin masifa ce wannan? hakura nayi na kyaleshi sai goga fuskarsa yake a sassan wuya na yana sake rungumeni a jikinsa.......Koda Gwaggo ta shigo taga abinda yake faruwa salati tasa da fadin." Wane irin rashin mutunci ne wannan Sa'ida saura kwana uku daurin auranki kuke wannan shashanci.''


Hawaye suka kwace min dama nasan ba zata ga laifinsa ba dole ni zata d'orawa laifi nace."Gwaggo wallahi ba laifina bane nasa ne kina ganin yanda ya matse ni a jikinsa ko."

Gwaggo tsawa! ta buga masa murya na rawa tace."Kai Khalid idan kai romio ne gurin soyayya dole ka hakura da yarinyar nan wannan wace irin masifa ce? wato kuna so ku janyo min abin kunya ko? kuna jin yanda Baito take yar min da habaici tana kokarin d'aid'aita min zuria."

Hawaye na goge nace."Gwaggo wane abun kunya kuma? ai abin kunya tuntuni an riga anyi sa." Tace."Sa'ida wannan lamari da ya faru idan ban dani dake da khalid din waye ya sani? sai Rabi ita kuma mijinta ya gargad'e akan maganar nasan babu wanda zata fadawa."

Murmushin takaici nayi ba tare da nace komai ba na yunkura domin sauka daga jikinsa, saki na yayi na mike tsaye, ya zuba min idanunsa da sukayi jajawur!

Gwaggo taja tsaki da fad'in "Kai kam Jarumi ban san inda zaka kai jaraba da fitina ba to ni bana son wannan d'abi'ar taka zan iya zare hannuna daga kanka mutukar kace haka zaka cigaba dayi.


A sar'ke yace.''Gwaggo ki gafarce ni." Uffan ba tace masa ba ta mika masa kayansa. ganin yana kokarin sa kayan a gabanmu yasa ni da ita muka fita daga dakin.


Fitowa yayi ba tare da ya kalli inda muke zaune ba ya nufi gurinsu.....Har yanzu suna zaune suna sa'ka mugun zare.

Ummatu ta kalleshi da fadin." Dama jira nake ka shigo domin nayi maganar karshe da kai Ga Baito ka Jamila su zasu zama sheda bayan Ubangijin mu.''


Ji yayi gabansa ya fad'i! A sanyaye ya nemi guri ya zauna yana kallonta sai kawai ta fashe da kuka tasa gefan zaninta tana share hawaye tana kallonsa tace."Yanzu Khalid abin kunyar da zaka janyowa zuriarmu kenan."?

Yace."Ummatu me kuma ya faru."? Tana kukan tace."Baka da lafiya kana Fama da kanka Baito ta shigo ta samaku kai da Sa'ida kun rungume junanku shin hakan me yake nufi.''?


Kansa ya sunkuyar kasa domun dai bashi da abin fad'a.....Ta cigaba da cewa."To wallahi wannan shine na farko kuma shine na 'karshe Khalid idan ka 'kara shiga sabgar Sa'ida Allah ya isa ban yafe maka ba." Da saurin gaske ya kalleta.....Baito tace." Ba wai zamu raba ka da 'yar uwarka bane Aa muna gudun mugun halinta shiyasa kaga bama so kana mu'amula da ita idan kana so kayi albarka a rayuwarka to kabi maganar mahaifiyarka."

Ya dinga jin kansa yana masa wani irin ciwo......Ya kalleta ido jawur yace."Ummatu Sa'ida 'yar uwata ce ta jini ta yaya zakiyi min tsakani da ita."


Tace."Gaisuwa kawai na amince maka kayi da ita ban yarda ka sake wata mu'amula da ita ba ka cire sonta daga ranka na rabaka da ita har abadah kazo ka rungumi Jamila itace za'bin da nayi maka."


Gumin goshinsa ya sharce! ya sunkuyar da kansa kasa yana jin wani irin nauyi a kirjinsa......Cikin tsawa! tace."Saboda kai sakarai ne har ka iya yarda sonta ya janyo maka aman jini to bari kaji idan ka kwanta ka mutu bata da damuwa kuma ba zata fasa auranta ba, saboda haka kayi wa kanka fada ka cire ta daga ranka.


Ya dago kansa yana kallonta a shaqe yace."Ummatu insha Allahu daga yau nayi miki alkawarin cire Sa'ida daga raina na hakura da ita har abadah mutukar zaki samu farin ciki a cikin zuciyarki.


Murmushin samun nasara tayi tace."To Allah Ubangiji yayi maka albarka Khalid." jiki a mace ya amsa da ameeen ya mike ya fita daga dakin.

Mukkuli yasa a dakinsa ya bude ya shiga ya kwanta rigingine yana tunanin rayuwa tabbas dole ya hakura ko yaki ko ya so saboda duk yanda yaso da al'amarin rayuwarsa ya kasance Allah bai so ba dole ya bi maganar mahaifiyarsa mutukar yana so yaga nasara a rayuwarsa amma shi kansa yasan cire auntyn nasa daga cikin rayuwarsa babban jidali ne.....




_Kuyi hakuri da yanayin labarin littafin nan ku cigaba da karantawa a yanda yake insha Allahu a gaba zaku gane inda na dosa NAGODE_


*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*




*72&73*
A ranar da Gwaggo tazo gidan sai da ta kusa bani kunya gabansu Layuza sai wasu irin maganganu takeyi akan gidan da kuma maigidan sai da nayi mata jan ido tukkuna tayi shuru da bakinta tana yin sallar azuhur tace ita tafiya za tayi abubuwan kwad'ayi na had'a mata masu yawa nasa direba ya dauketa ya kaita har gida, Gwaggo koda ta koma gidan kasa shuru tayi da bakinta da Kawu Iro ya shigo ta tare shi da maganar wai anya kuwa A harkar kasuwanci Yaya Aminu ya tsaya baya yakan kai wannan uwar dukiya daka gani bata Allah da Annabi bace." Kawu Iro zaunar da ita yayi ya dinga yi mata nasiha gami da kawo mata misalai Allah yakan arzita bawansa da dukiyar da bai san iya adadinta ba saboda haka ta kwantar da hankalinta duk wani binkice yayi ya kuma tabbatar da cewa mutumin a harkar kasuwanci ya tsaya." Gwaggo dai shuru tayi da bakinta tana jajanta al'amarin.

Gwaggo kullum za tayi girkin ta da nama taci ta koshi ta ajiyewa mutumin nata idan ya dawo tace masa yazo yaci abinci kai tsaye yake ce mata ba zai ci ba ya gwammace yaci garau-garau din da mahaifiyarsa tayi ko kuma yaci aljihunsa.....Gwaggo tayi tai masa naci shi kuwa yace."Ba zai ci ba dole take hakuri ta kira almajirai ta raba musu sadaka.


"Khalid kwata-kwata fa ni ban amince maka da wannan tafiyar ba, kai harkar ball din ma gabadaya bana sonka da ita ka hakura ka zauna a gida ka fara kasuwanci shine yafi alkairi a tattare da kai.

Cikin wani irin yanayi na damuwa yake kallon mahaifin nasa yace." Baba kayi hakuri ka lamunce min tafiyar nan akwai nasara a cikinta.

Kawu Iro yace."Ai dama duk hanyar shaid'anci zaka samu nasara a tare da ita hanyar Allah da Annabi kuwa kun dinga kawo suka a cikinta to ni dai na gama magana mutukar ni na haifeka ban lamunce maka tafiya wata america ba.

Kawu Iro na gama maganarsa ya bar gurin.....Ya jima a tsugune a gurin yana sa'kawa da kwancewa kafin ya mike kai tsaye gurin Gwaggo ya nufa domin kuwa yana ganin itace kadai zata iya tursasa mahaifinsa ya barshi ya tafi inda yake muradi.


Tana zaune da kwanon farfesun kaji a gabanta gefe ga lemo nan irin na kwali farfesun take sha hankali a kwance Gwaggo har wani qiba tayi saboda ka'bakin arzikin da Sa'ida take kawo mata duk bayan kwana uku ko hud'u......Dakin ya shiga ya zauna yana kallonsa....Sai ta tura masa kwanon farfesun da fadin."Gashinan ko kayi sha'awa."

Girgiza kansa yayi yace."Bana bukata." Kwanon farfesun ta janye ta cigaba dasha tana tauna tsokar data dahu luguf.

Yace."Gwaggo Alfarma nake nema a gurun ki." Tace."Ai dama tinda naga ka shigo dakina ka zauna nasan da walakin goro a miya.

Sajensa ya shafa yace."Eh wallahi Gwaggo ke kadai ce zaki umarci Kawu Yayi abinda kike so."

Tace."Eh kwarai kuwa ai mahaifinka yana da biyayya duk abinda nace inaso to shima yana so.

Yace." Yawwa Gwaggo dan Allah kice masa ya barni na koma gurin sana'ata."

Tace."To akan me dama zaice ba zaka koma ba."? Yace."Kin san kwanaki nayi miki magana kancewa zamuje america muyi wasa to tafiyar ce ta taso dan tun satin da ya wuce oganmu yake kiran waya ta na bashi hakuri kancewa insha Allahu ya tsammaci zuwa na a cikin satin nan to kuma yanzu da nake shedawa Kawun maganar yake cewa shi bai amince ba.


Tana sud'e hannunta tace."Khalid wace irin ball ce har sai anje america mai zai hana ka ka cigaba da buga abarka a cikin 'kasar ka nima wallahi sam bana sonka da wannan harkar.


Yace."Gwaggo kada kice haka mana zuwa na america matakin nasara ne domin kuwa zanje mu fafata da manya manyan 'yan ball wanda suka shahara sukayi suna duniya tasan dasu."


Hararasa tayi tace."Kai kuma shahara kake nema da makiya Allah da Annabi kenan."? Girgiza kansa yayi da sauri yace."Aa Gwaggo ai ba kafurai ne kawai ba harda musulmai a ciki kowa yana kokarin ya nuna bajintarsa ne."


Shuru tayi masa ya matsa kusa da ita gami da rike hannunta yana rarrashinta. Tace."Shikkenan ka kwantar da hankalin ka zan sameshi muyi magana Allah ya za'ba maka abinda yafi alkairi."


Cike da farin ciki ya amsa da ameeen Uwargidana." Harararsa tayi tace."Ina uwargidanka amma ka daina cin abincina ko da yake ai nasan uwarka ce take zuga ka." Cikin kulawa ya kalleta da fadin."Gwaggo babu ruwan Ummatu ni ne dai ba zanci wani abu da ya shafi aunty Sa'ida ba kin san haka tsarina yake ba tun yau ba.


Tace."In banda abinka kuma wane kishi za kayi bayan komai ya wuce kake cutar kanka." Yace."Kinga Gwaggo dan Allah a bar maganar duk nau'in abincin da nake so naci ina da kudin siya ba sai kin tursasa ni naci abincin ki ba.

Tace."To ai shikkenan tunda haka ka za'ba, mi'kewa yayi yana kallon agogon hannunsa yace."Ni zan fita gurin abokaina." Tace."To sai ka dawo." Fitowa yayi tare da sa takalmansa ya fita daga gidan.


Kullum ta Allah Yaya Aminu yakan kira waya ta sau biyu ko uku mu jima muna hira dashi al'amarin ya dinga bani mamaki ganin gabadaya baya nuna wani d'oki da zumud'in irin na angwaye idan ya kira waya ta hirar kasuwancinsa kawai yake min babu wata kalma mai dadi irin to so da nuna cewa ina bukatar ki abin ya dinga bani mamaki yana sani a cikin damuwa! a gaskiyar magana lamarin yana min ciwo sabida ni na kasance mace mai son soyayya inaso naga namiji na kula dani da nuna min so......Amma Yaya Aminu sam babu wannan a tare dashi shidai harkokinsa yasa a gaba.

Yau asabar Allah yayi nufin dawowarsa sosai nayi gayu cikin shaddan galila taji uban stone work nayi ado da gold wuya da hannu sai zuba kamshin tururuka nakeyi ni kaina dana tsaya gaban mirror sai da nayi mamakin uban kyawun da nayi......Amma abin mamaki wanda akayi kwalliyar dominsa bai wani kula sosai ba dan bayan na bashi abinci yaci dakinsa ya bude ya shiga ya kwanta, sai nayi tunanin binsa dakin koda na ta'ba kofar sai naji a kulle. jiki a sabule na bar gurin zama nayi kujerar falo abin duniya ya dame ni, ga Layuza da Karima sun tafi sai ya kasance ni kadai a gidan dana gaji da zaman falo mikewa nayi na shige dakina na kwanta kawai sai hawaye suka 'balle min wannan wane irin ango ne mara kula. sosai naci kuka na na koshi bacci ya dauke ni.

Sai daf da la'asar na tashi a gurguje nayi wanka na fito daure da alwala sai dana kimtsa jikina tukkuna na tsaya kan dadduma na tayar da sallah.

Ina sallama ya shigo dakin daga kai nayi ina kallonsa kamshin turaransa duk ya cika dakin a shirye yake da alama futa zaiyi.....zama yayi gefan gado har na shafa addua na juyo muka hada ido dashi, murmushi yayi min da fadin"Amarya." ya'ke kawai nayi naje na zauna kusa dashi tare da gaishe shi, ya amsa cikin kulawa ido ya tsira min kafin yace."Naga idanuwanki sunyi jawur

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login