Showing 84001 words to 87000 words out of 185789 words

Chapter 29 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24226

shiga.


Maganarsa naji a saman a kaina, a furgice na mike zaune ina kallonsa tunda na ganshi a burkice nasan ya samu labarin abinda yake da akwai.

Yana huci! yace." Sa'ida an yanka ta tashi yau Allah ya tona asirinki Dr Maryam ta bud'a min dukkanin sirrukan ki saboda haka tunda ke kin kasance ma ha'inciya macuciya kije na sake ki saki uku! sai kiji ki auri yaron da yake bibiyarki har gidan auranki wanda dama shi nake zargin ya lalataki kafin aure na dake."!
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! kawai nake nanatawa a cikin raina yayin da nake jin wani irin mugun ciwon kai da mugun jiri d'akin sai juyawa yake dani a takaice dai ban san sanda ya gama cin mutuncinsa ya fita daga dakin ba.


*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
708 465 3262: *SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*




*58&59*
Na jima ina nanata kalmar innalillahi wa'ina ilahiri raji'un a fili da zucci kafin naji wani k'arfin gwiwa gami da danga a tare dani......mikewa nayi jiki a mace na bude wardrobe na had'a kayana cikin akwati tsaf sai da na kwashe kayan sanyawata da duk abinda nasan ina bukata nasa a akwatin kana na rufe ta da kyar ina tunanin wanda zai dau'kar min.

Hijabi na nasa na d'aga akwatin tare da janyo hannunta da yake mai tayoyi ce sai kawai naja ta na bude dakin na fito kaina a kasa dan ko kadan bana kaunar na hada idona dasu....maganarsa naji a kunnena yana fad'in "Tsaya ki tafi da sakamonki cutar da kikayi min kuma na barki da Allah."

Tsayawa nayi ba tare dana juya ba zuciyata in banda tafarfasa babu abinda take

Daf dani ya tsaya hannunsa rike da takardar sakin nawa...."Kar'bi ki fice min daga gida bana bukatar sake ganinki shiyasa nayi miki saki uku domin hukuncin daya cancanta dake kenan "

Hawayen dake kokarin kwace min na danne hannuna na rawa na kar'bi takardar da fad'in "Nagode ina rokon Allah yasa haka shi yafi alkairi.''

"Shine ma alkairi kije ki auri daidai dake amma ni ban kasance mazinaciya ba nasan Allah ba zai jarrabe ni da auran mazin.....Hannu na daga masa da fadin" Kaga ka daina kira na da wannan sunan tunda dai ka datse igiyoyin auranka shikkenan.

Aunty Murja dake zaune akan kujera tace."Ai gaskiya Abban Yusura kayi kuskure banji dadin sakin wulakancin da kayi mata ba haba ina laifi kayi daya ko biyu.A harzuke yace."Murja saki uku ne ya dace da wannan macuciyar saboda haka ki daina nadama dan na sake ta.

Juyowa yayi kaina yana magana ban tsaya sauraransa ba da sauri na bude kofar falon na fita ina jan akwatin kaya na.

Duk da babu wata tazara mai tsayi sai da na nemi adaidaita sahu ya sauke ni har kofar gida, dari biyu na bashi naja akwatin kayana na shiga gidan gabana har yanzu bai daina faduwa ba.

Yau Gwaggo towon alkama take sha'awa dan haka sau ta tuka abin ta da miyar bushashshiyar ku'bewa ta idar da sallar isha'i ta janyo kwanukan abincin domun taci nayi sallama a gidan.

Labule ta d'aga da fadin."Kamar muryar Sa'ida nake ji da daddaran nan." Nace."Itace Gwaggo.

Tana kallona tace."To maraba lale shigo daga ciki nima danshi (ra'ba) ne ya hana ni zaman tsakar gidan kin san kwana biyu an tafka ruwan sama.

Ina kokarin shiga dakin nace."Eh Kwarai hakane kwana biyu ana ruwa sosai."

"Amma dai lafiya dai domin na gan ki da akwati Allah dai yasa ba yaji kikayi ba.

A sanyaye na zauna gefan tabarmarta nace." Ya sake ni Gwaggo."

Wani irin shocking taji a jikinta da sauri tace."Sa'ida me kike fad'a"?

hawaye na zuba nace."Gwaggo ina nufin Alhaji Nura ya sake ni kinga ma shedar nan." Takardar hannuna na mika mata.

A sanyaye tace."Yo ni ina nayi karantawa Sa'ida me ya faru mutumin nan yayi miki wulakanci kuma saki nawa yayi miki."

"Saki uku ne."? Na fada muryata na rawa, Gwaggo innalillahi wa'ina ilaihi raji'un kawai take nanata wa cikin furgici tace."Sa'ida anya mutumin nan kuwa yana da hankali saki uku a lokaci guda ke kuwa wane irin laifi kikayi masa."?


Cikin kokarin danne damuwata nace." Asiri ne ya tono Alhaji Nura ya gane 'boyayyan sirrin dake lullu'be shine ya yanke min wannan hukuncin."


"Sa'ida ta ina zai gane ke ba budurwa bace bayan da farko kinyi masa bayani kuma ya amince.

hawaye na share nace." Nifa Gwaggo bana zargin kowa da mutuwar aurena sai Khalid." Da sauri tace."Tofa! bakya zargin kowa sai Khalid to me yayi miki yaron da tuntuni ya tafi gurin sana'arsa.

Hannu nasa na share fuskata nace."Gwaggo Khalid yaje gidana kuma har cikin 'kuryar dakina sai da ya shiga kuma Alhaji ya shigo ya sameshi.

Gwaggo rike baki tayi da fad'in "Ashe dai duk jan kunnan da nayi wa yaron nan be ji ba sai da yaje to me yaje yayi miki."?

Nace."Gwaggo ya kike tambayata me yaje yayi min gashinan abu a zahiri Khalid yaje gidana dan ya lalata min aure to bukatarsa ta biya sai ya zuba ruwa a kasa yasha.


Gwaggo ta dinga girgiza kai tana fadin."Kai amma wannan al'amari beyi dadi ba Khalid kuma bai kyauta duk da khalid ya kasance dan uwanki amma ai bai cancanta yana baligi irin wannan ba ya shiga gidan matan aure ba tare da neman izina ba dik abinda Alhaji Nura yayi masa na hukunci daidai ne tunda shi ya taka sharia.

Nace."Gwaggo to me yasa kin san gaskiya kike takewa me yasa bakya ganin Laifin Khalid kuma me yasa kike fifitashi akaina."

Cikin nutsuwa tace."Sa'ida kada ki fassarani da wata manufa mara kyau ni dake da Khalid dik daya kuke a gurina babu wanda yafi wani hakika kuma naji bakin ciki da takaicin abinda yayi saboda haka an jima idan ya kira ni a wayar daya siya min zan nuna masa 'bacin raina."

Shuru nayi ina sha'kar bakin ciki! ta girgiza kanta tana jimanta al'amarin tace."Wai saki uku a gaskiya wannan mutumin bashi da hankali ko kad'an wallahi naji ciwon abinda yayi."

Nace."Gwaggo kiyi min addua kawai Allah yasa haka shi yafi alkairi Allah ya za'ba min miji nagari."

A sanyaye ta amsa da ameeen ya rabbi. dakin ya sake daukar shuru na 'yan mintina kafin nace."Gwaggo kin tuna asibitin da kika rakani a washe garin ranar da Khalid yayi min fyad'e."?

Kallonta tayi a sanyaye tace."Sa'ida bana so naji kina wannan maganar wallahi babu dadin ji.'' Cike da takaici nace."Gwaggo har duniya ta nad'e ba zan daina maganar nan ba kuma ba zan fasa neman sakayya gurin Ubangiji ba."

Babu walwala a tare da ita tace."To naji ya isa haka magana dai tuntuni ta wuce tayar da ita bashi da amfani yanzu sai ki fuskanci abinda yake gabanki.

Nace."Magana ai tuntuni na barwa Allah yanzu ma dalili tayi shiyasa na fada miki abinda yake zuciyata.

Shuru tayi ba tai magana ba, nace."Wannan likitar data duba ni ashe kawar aunty Murja ce."

Kallona tayi da mamaki a tare da ita, na cigaba da cewa "Itace duk ta warware masa komai shi kuma ya fusata ya yanke min wannan hukuncin kafin na fito daga gidan ba kiji irin zagi da cin mutuncin da Yayi min ba."

Hawaye ta goge tace."Ki rabu dashi daga shi har ita likitan Allah zai saka miki kuma duk wanda ya tona asirin wani shima sai Allah ya tona nasa yanzu ni tsorana Allah da Annabi kada maganar ta fita jama'ar gari su dinga yi mana wani irin kallo." Tana kuka take maganar.

Gabadaya naji zuciyata ta karye zafafan hawaye suka fara zubo min nace."Gwaggo insha Allahu hakan ba zata kasance ba idan kuwa maganar ta fita to zan tattara kayana na gudu gurin mahaifiyata."

Kuka takeyi sosai tana kallona had'e da girgiza kanta, Kaina na sunkuyar kasa ina shakar hanci tare da jin tsananin tausayinta a cikin raina.


"Gwaggo ba'kuwa kikayi ne na fito domin d'ibar ruwa naji magana a dakin ki.'' Maganar Ummatu ce ta dawo damu nutsuwarmu tana tsaye a bakin kofar dakin hannunta ri'ke da labule.


Ido muka had'a tace."Au ashe Sa'ida ce." Nace."Eh Ummatu Ina wuni ya gida."?


Ta amsa a sake tana tambayata maigidana....Gwaggo tace."Rabi wane maigida kike tambaya bayan ya sake ta.

Da sauri tace."Gwaggo ban gane maganarki ba." Tace."Ina nufin Alhaji Nura ya saki Sa"ida saki uku."

Da sauru tace."Subahannallahi Sa'ida garin ya haka ta faru me kikayi masa."?


Gwaggo a d'an hasale tace."Rabi har kin manta ashe."? Kallonta tayi jikinta duk yayi sanyi Gwaggo ta cigaba da cewa"Ko wane namiji dai yana kulafucin wannan abu (budurci) to da Alhaji Nura ya tabbatar da cewa Sa'ida bata dashi shine ya yanke shawarar sakin ta."


Ummatu shuru tayi jikinta duk yayi la'asar Tace."To amma me yasa tun farko beyi magana ba sai da tayi wattani a gidansa Gwaggo anya wannan ce matsalar."

Girgiza kanta tayi tace."Rabi wannan ce matsalar ko kinqi ki kin so sai matsala ta biyu ashe Khalid duk jan kunnansa da nayi akan kada yaje gidan mutumin nan sai da yaje saboda tsabar wuce gona da irin nasa har 'kuryar daki ya shiga.

Ummatu gabanta na fad'uwa tace."Gwaggo a yaushe Khalid din yaje gidan bayan yau satin sa uku da tafiya.

Tace."A ranar da zai tafi yaje da safe kuma Alhaji Nuran ya ritsa shi a dakin baccin sa Rabi wace irin masifa yaron nan yake so ya janyo mana


Ummatu taji 'kwalla ta cika idonta Itakam ta rasa wace irin masifa ce wannan wane irin kwadayi da kulafuci yaron keyi akan wacce bata dace dashi ba, aranar da Gwaggo take masa fada akan kada ya kuskura yace zaije gidan tana jinsu har ta shiga dakin tasa baki tayi masa gargadi sosai ashe jinsu kawai yake da kunne ya mayar dasu shashashai sai da yaje ya dauko musu magana.



Kai ta kad'a ta bar gurin ba tare da tace komai ba, Gwaggo tace."Duk kauce-kaucen da za kiyi dole sunan Khalid ya fito a cikin mutuwar auran Sa'ida."


Koda kawu ya dawo ya sameni a gidan bai kawo komai ba a cikin ransa muka gaisa a nutse ya shiga gurin sa domin cin abinci da hutawa.

Gwaggo bayan ta tabbatar da cewa yaci abinci ya huta sai ta fito tsakar gida tana 'kwala masa kira, da sauri ya bude kofar gurun nasu ya fito yana fadin"Gwaggo lafiya dai ko? Ina S'ida ina fatan ta tafi gidanta.


Tace."Sa'ida tana nan ai kuma ta dawo kenan sabida saki ukun da mijin nata ya rattaba mata."

Kawu wani irin gumi! ne ya jika masa riga baki na rawa yace."Gwaggo me yasa mutumin nan zaiyi mana haka? me yarinyar nan tayi masa da har zaiyi mata irin wannan hukuncin

Kai tsaye tace "Munafurtar sa akayi Ibrahim me yasa tun farko baka sameshi ka fada masa abinda ya faru ba.

Yace." Gwaggo ya za'ayi na tonawa yarinyar nan asiri? wane namiji ne kike gani zai ji wannan al'amari ya yarda da auran."

Tace."To ai *"GA IRINTA NAN!* An yanka ta tashi domin dai likitar data duba ta a washe garin ranan da al'amarin ya faru To itace ta tabbatar masa da gaskiyar lamarin bayan haka kuma ashe Khalid a ranar da zai tafi sai da yaje gidan saboda kuma wace gona da iri irin nasa har uwar daki ya b ita a takaice ma dai sai da maigidan ya shiga ya same shi Ibrahim ka fad'a min shin Khalid me yake nufi da aikata hakan."?





*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*




*62&63*
B'angaran Aunty Murja kuwa duniya sabuwa suka bude shafin iskanci iri-iri ita da mutanan ta Hajiya Aziza tuni ta dawo da zuwa gidan domin daga zarar maigidan ya fita 'Kawartata zata kira ta a waya tazo su yini suna shaid'ancinsu shiyasa kwata-kwata bata damu da lallai sai yayi sex da ita ba sabida tana samun biyan bukata a gurin abokanan shaidancinta a nasa bangaran kuma kullum cikin shi mata albarka yake yana fad'in babu wata 'ya mace da ta cancanta yayi rayuwar aure da ita sai ita domin ta kowane bangare tana kula dashi kuma tana masa biyayya duk abunda ya nuna baya so tana kokarin kiyayewa kullum kokarinta ta kwantar masa da hankali saboda haka ta kwantar da hankalinta ba zai sake yi mata kishiya ba tunda ya fahimci cewa yanzu mata suna suka tara.....Aunty Murja sosai taji dadin kalamansa sai ta cigaba da yi masa kwance-kwance a zahiri kenan a bad'ini kuwa Allah ne kad'ai yasan irin ta'asar da take tafkawa.


"Assalamu alaikum mutanan gidan nan kuwa suna nan."? Uwale ce ke rangwada sallama a cikin gidan...Gwaggo ta fito daga bandaki da buta a hannunta tace." Wa'ailaikissalam Uwale kece da tsakar rana haka."?

Uwale tace."Wallahi kuwa daga *Janguza* nake naje nayi siyayya kin san yau ranar kasuwa ce." Gwaggo tace."Ayya Uwale kin san zakije Janguza mai yasa baki shigo kin kar'bi sautu na ba nima daddawata ta'kare tuntuni nake so a siyo min."

Uwale tace."Ai naga bake kike girgin gidan ba shiyasa banyi tunanin shigowa na fada miki ba."

Gwaggo tace."Aa watarana ni nake girkina shiyasa za kiga bana rabo da kayan miya busassu."

Uwale tace."To ai babu matsala bari nayi sallah na huta sai na raba kayan dana siyo kashi biyu ki dau daya na dauki daya."

Gwaggo tace."Ayi haka kuma Uwale." Murmushi tayi ta ajiye buhun hannunta da fad'in "Aikuwa anyi an gama Gwaggo ai babu abinda zaki nema a gurina na hana ki."

Gwaggo tace."To nagode Uwale Allah ya kara zumunci." ta amsa da ''ameeen." Gwaggo ta mika mata butar hannunta ta kar'ba da sauri ta shiga bandakin.

Dakin ta shiga tana tashi na da fadin."Lokacin sallar la'asar yayi, mikewa zaune nayi ina murza idona na daga kai na kalli agogon dake kafe a bangon dakin. Hudu da minti ashirin da sauri na mike na fita tsakar gidan domun daura alwala.

Ha'da ido mukayi da ita a lokacin data fito daga bandakin. fuskata na gyara sabida nasan halin matar da sa ido da bindiddigin tsiya....Uwale tsugunawa tayi tana daura alwala tana satar kallon Sa'ida da mamakin zuwanta gidan.

Butar ta miko min da fadin."Alwala zaki d'aura ne."? Kar'ba nayi tare da daga mata kai na shige bandaki na barta a gurin.

Uwale dakin Gwaggo ta nufa tana zancan zucci, a maimakon data shiga dakin ta tayar da sallar sai ta tsaya ta tallafe ha'barta da fad'in "Gwaggo lafiya kuwa? Zuwana gidan nan uku ina ganin Sa'ida da farko na dauka zuwa tayi ziyara yau kuma sai na cire wannan tunanin ganinta ta fito da alamun bacci a idonta ga kayan jikinta irin na zaman gida shin wai meke faruwa ne."?


Gwaggo ta kalleta da fadin." Uwale yi sallar tukkuna sai muyi maganar." Uwale ba dan ranta yaso ba ta tayar da sallar tana wasi-wahsi tsabar son gulma ko minti biyar ba tayi ba har ta idar da sallar ta juyo tana fuskantar Gwaggon da fadin."Ke nake sauraro."

Gwaggo tace."Uwale ai tsayin watanni biyu da suka Wuce mijin nata ya saketa har saki uku."!

Uwale ta zabga salati tana sake tallafe ha'ba tace."Akan wane dalili me tayi masa da zai ci mata mutunci irin haka."?


Gwaggo tace."Babu wani dalili Uwale giyar kudi ce kawai take d'ibarsa shiyasa yayi mana wannan wulakancin."

Uwale tace." Kai amma wannan mutumin anyi d'an iska mara mutumci yana yawo da kuttun ciki kamar an kifa kwarya ya samu santaleliyar yarinya son kowa 'kin wanda ya rasa amma yayi mata wannan wulakancin shin yanzu wane mataki kuka dauka a kansa."?


Gwaggo tace."Uwale kenan wane mataki kuwa zamu dauka mun barshi da Allah." Uwale tace."Aikuwa idan ni yayi wa wanna iskancin ba zan yarda ba sai nabi malamai na dagula masa lamuransa."

Gwaggo tace."Uwale rabu dashi kawai da sannu Allah zai nuna masa kuskuransa.......Gyada kanta tayi tace." Ni kuwa Gwaggo da zaki yarda da na raka ki gurin wani malami dake cikin unguwar 'yar kwad'i yayi miki aiki akan D'an iskan nan haka kawai ya mayar da yarinya karamar bazawara.

Gwaggo na kokarin yin magana na shigo dakin fuska a murtuke nace."Uwale ashe baki daina biye-biyen malamai ba." Kallona tayi tana hangame baki. Nace."Kin kai matakin shekara sittin a duniya wane jin dadi kike nema a duniya? me kike bukata kuma? Uwale rayuwarki ta dauko gangara a matakin shekarun da kike kai kamata yayi ace kullum kina istigifari domin neman gafarar Allah amma saboda tsabar son duniya kina sake miqe 'kafarki duk inda wani malami ko d'an tsubbu yake kin san gurin kiyi ta yawo da silifas kina asarar kud'in ki shin me kike so ki zama? Wallahi mutukar kika mutu baki tuba ba sai kin shiga wuta domin kin sa'bawa Allah da umarninsa." Gabadaya daga ita har Gwaggon jikinsu yayi sanyi....Na kallesu da fad'in "Ni idan domin ni zakuje gurin wani malami to bana bukata nafi bukatar ku daga hannunku sama ku rokar min Allah ya za'ba min abinda yafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login