Showing 111001 words to 114000 words out of 185789 words
sai ki duba kiga ko wanene idan Khalid ne kada ki daga ki shareshi kamar yanda nake masa idan ya kira ni."
Murmushi kawai nayi ba tare da nace mata komai ba na nufi dakin da wayar a hannuna ina dubawa
Ganin number Ummana yasa da sauri na zauna gefan gado na shiga gurin kira da alama wayar tana hannunta domin sau daya tayi ringing ta daga, yanda naji muryarta a sanyaye yasa nima jikina ya mutu a nutse na gaisheta ta amsa tare da fadin."Ya mukaji da wannan abu."
Nace."Alhamdulillahi Umma." Tace."Kiyi hakuri kinji ko kowane mutum akwai irin kaddararsa kisa a ranki cewa dukkanin abinda ya faru da rayuwarki kaddara ce insha Allahu wataran sai labari."
Hawayen da suka zubo min na share murya na rawa nace."Insha Allahu Umma ki taya ni da addua akan Allah ya za'ba min abinda yafi alkairi."
Tace."Sa'ida addua kullum akanta muke Ubangiji Allah ya amsa mana adduo'inmu na alkairi." cikin sanyin murya na amsa da ameeen Ummana." Tace."Ki gaishe min da Gwaggo da kyau." nace."To zataji insha Allahu.'' Sallama mukayi da juna......Gwaggo ta shigo dakin tana fadin."Dawa kike waya ne."? Nace."Umma Habiba ce tace ma a gaisheki.''
Kallona tayi da fadin."Ita kuma a ina ta samu labarin abinda yake faruwa."? Nace."Watakila ko Kawu ya sanar da mijinta ne.''
Tace."Eh hakan zata iya yuwu wa Allah dai ya kyauta.'' cikin mutuwar jiki na amsa da "ameeen ya Allah.
*BAYAN SATI DAYA*
Na d'an samu nutsuwa hankalina ya dawo jikina sai nayi tunanin kiran Hauwwa a waya domun na sheda mata abinda yake faruwa..........Sosai Hauwwa tayi mamakin al'amarin daga bisa ni tace." Yanzu dai kinga ne abinda ke da akwai ko? a yanzu dai kin fahimci cewa auran Babban mutum bashi bane tunda gashinan wata shida har anyi an gama ya rattaba miki saki uku wallahi da Khalid kika aura ba zaki fuskanci wannan matsalar ba babban tashin hankalin ma mutumin nan yayi miki sanadin aikin ki."
Nace."Ni wallahi a yanzu shine babban abinda yake damuna wata shida bai zama lallai idan na koma aiki su kar'be ni ba......Hauwwa tace ko zasu kar'be ki sai an kai ruwa rana amma babu matsala ni zanyi miki kokari kin san Shugaban makarantar yana zawarcina zanje har ofis d'insa na lalla'ba shi." Nace."Yawwa aminiyata nagode kwarai dan Allah kiyi min kokari." Tace."Kada ki damu mybe ma gobe idan mun tashi na shigo domin mu tattauna." Nace."To shikkenan sai kin shigo Hauwwa nagode Allah ya bar zumunci." ta amsa da ameeen ya Allah ki gaishe min da Gwaggo." nace."Za taji insha Allahu."
Wayar na kashe ina jin sassauci a cikin zuciyata.....Gwaggo dake kad'i ta kalleni da fad'in." Naji kina magana komawa gurin aiki Sa'ida ke yanzu sai ki koma cikin maza bayan zargin da ake miki."?
Nace."Gwaggo kina so kenan na zauna a gida babu aikin fari bare na baki ko."? tace."Oh!o ni nafi so ki samu miji kiyi aure Sa'ida.'' Nace."Gwaggo kada kiyi min maganar aure a yanzu domin dai bashi ne a gabana ba'' Tace."To ai shikkenan idan lokacin auran yazo sai ki hana Allah ikonsa." shuru nayi mata domun nasan neman magana take.....Ummatu ta daga labulan dakin da waya a hannunta tana fadin."Gwaggo ga d'an d'akinki ya kira waya wai yana so ku gaisa.'"
Tace."Ke Rabi raba ni da wannan yaron ki fada masa ni bana bukatar magana dashi a yanzu." Tace."Gwaggo me yayi zafi."? Tace."Rabi duk irin kulawa da rarrashin da nakewa yaron nan besa yaji maganata ba to ni kam me zaice dani ai na daina wahalar da kaina a kansa."
Ummatu jikinta a mace ta bar gurin...Gwaggo taja tsaki da fad'in "Kawai kin d'auko wata kod'add'iyar yarinya kin nana masa ya aura yarinya sai kace zabiya tana yawo sai kace takand'a babu kumari babu 'kira da cika irin na mata.'"
Dariya nasa ina kallonta nace."Gwaggo kefa naji kina kod'a yarinyar kina cewa sun dace da juna gata kyakkyawa mai kuruciya."
Tace."Ai ni banta'ba 'karewa yarinyar kallo ba sai ranar da ta zo gaishe ni lokacin yana nan be tafi ba ranar nayi azimin litinin yaje ya dauko ta wai tazo tayi min sannu da shan ruwa tsabar haushi ko kayan data kawo min ban duba ba na bawa al'amajirai."
Nace."Yanzu dai kina nufin bakya kaunar al'amarin kenan."? Tace."Yo Sa'ida me Jarumi zai samu a jikin yarinyar nan jiki a bushe ko'ina babu kumari sai qashi shi kuwa kato dashi tubarkallah ai yana da kyau ya samu 'koshashshiyar mace yanda zai more kuruciyarsa.
Dariya nayi sosai ina kallonta nace."Gwaggo wai dan Allah me yasa bakya kunyar fadar magana ne? Tace."Sa'ida wace kunya kuma ai gaskiya na fad'a.'' Nace."To Allah dai kyauta Gwaggo ni dai shawarar da zan baki ki kauda kanki daga al'amarin nan idan kika ce zaki zuga Khalid ya bijirewa umarnin mahaifiyarsa zaki jefe shi a masifa sannan Ummatu da 'yan uwanta zasu dinga jin haushinki."
Tace."To dama Sa'ida ni ina ruwana yaje ya aureta nasan duk daran dad'ewa sai ya sake aure tinda ni nasan halin fitinarsa wannan siririyar yarinyar ba iyawa za tayi dashi ba."
Ina dariya nace."Gwaggo ai ba'a nan take ba sai kiga mace mara qiba amma sai ki sameta da juriya da kuzari ita kuwa mai qibar sai ki sameta da raki da rashin juriya.''
"Ummm! tace ta cigaba da abinda takeyi a jiyar zuciya na sauke a hankali nace." Gwaggo ni dashi Allah ya za'ba mana abinda yafi alkairi ki tsananta dayi mana addua.'' Tace."Insha Allahu Addua ba zamu bari ba har sai ranar da numfashi ya fita daga gangar jikinmu."
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*64&65*
Ina fita bakin titi adaidaita sahun Salim taci burki a gabana, dauke kaina nayi ina sake tamke fuskata ya leko da kansa da fadin."Aunty Sa'ida ina zuwa haka."? Ba tare dana kalleshi ba nace."Hotoro na nufa." Murmushi yayi cike da kulawa yace."Aikuwa zaki jima baki samu babur ba domin a daidai wannan lokacin munfi dau'kar 'yan kasuwar kwari da bakin asibiti amma tunda Allah ya had'amu kawai ki shigo na kai ki.
Jin abinda yace yasa na shiga babur din ba tare da nayi masa musu ba, jan babur din yayi da sauri muka bar gurin......Sai da mukayi nisa sosai kira ya shigo wayarsa jin ya ambaci sunan Khalid a maganarsa yasa gabana faduwa, shuru ina sauraran maganar tasu yace."Okey to ni yanzu ina kan hanya amma idan na samu nutsuwa zan kira ka mu tattauna wata magana." Daga can bangaran Khalid yace."Okey to shikkenan nima ai na kusa shigowa garin domin nayi muku sallama zamu tafi amarica wasa." Salim cike da jin dadi da farin ciki yace kai amma nayi murna da farin ciki abokina Allah ya kara daukaka yasa ka zama zakaran gwajin dafi Allah yasa ka ciyo mana kofi.
Khalid yace."Ameeen abokina nagode sosai sai na jika." Salim yace."Babu damuwa zan kira ka idan na samu nutsuwa." Sallama sukayi da juna kowane ya kashe wayarsa.....Jikina ne yayi na d'an fahimci wasu maganganun nasu. ta mirror ya kalleni da murmushi a fuskarsa yace."Aunty Sa'ida kinji Khalid zai zo sallama ko? kullum yana sake samun nasara akan harkokinsa dan Allah ku taya shi da addua.
"Humm! kawai na iya cewa na kautar da kaina ina kallon hanya, to shima Salim din ganin babu fuska sai yaja bakinsa ya rufe ya cigaba da abinda yake gabansa.
Lokacin dana shiga dakin su biyu na samesu a zaune ga dukkanin alamu muhimmiyar magana suke tattaunawa, a nutse naje na zauna kasan kafet tare da risinar da kaina kasa nace." Alhaji barka da safiya." cike da nuna kulawa ya amsa da barka dai Sa'ida kin 'karaso."? Nace."Eh wallahi." Kallonsa nayi kansa a sunkuye yana kallon kasan kafet nace."Yaya Aminu ina kwana."? babu yabo babu fallasa ya amsa min.
Dakin yayi shuru na 'yan mintina. Alhaji yayi gyaran murya tare da kallona, jikina yayi sanyi na sunkuyar da kaina kasa ina addua akan Allah yasa alkairi ne.
"Sa'ida naji uzirin ki a bakin Kawun ki Ibrahim inda yake fada min cewa kina so ki koma gurin aiki hakane ko."? a sanyaye nace." Eh hakane Alhaji dan tuntuni komai ya kammala gurin aikin nawa sun kar'bi uzirina sunce babu damuwa zan iya komawa bakin aiki."
Yace."To shikkenan Sa'ida amma ban tari hanzarin ki ba ina neman wata alfarma a gurin ki ina fata zan samu."
Kallonsa nayi ina mamakin maganarsa a duniya akwai abinda mutumin nan zai nema a gurina na kasa yi masa.
Nace."Alhaji ko wace irin alfarama kake nema a gurina zanyi maka mutukar inada iko da ita.
Yace."To Alhamdulillahi Sa'ida nagode sosai da kika karrama ni sabida haka dan Allah inaso ki amince na had'aku aure da Yayanki Aminu domun hakika naji ciwo da takaicin abinda Alhaji Nura yayi miki da k'ananun shekarunki ya sake ki."
Na dinga jin wani irin shocking a jikina gumi duk ya tsatstsafo min banta'ba tsammanin haka daga gurinsa ba shuru nayi bakina ya mutu murus na rasa ma abinda zance."
Yace."Sa'ida kinyi shuru ko baki amince ba."? a sanyaye na dago kaina na kalleshi kafin na mayar dashi kasa nace."Alhaji na amince mutukar shi Yaya Aminun ya amince zai aure ni da zawarcina.
Murmushi yayi yace."Alhamdulillahi naji dadi sosai kuma kada ki damu da Aminu yanzu kafin ki shigo muka gama magana dashi ya tabbatar min da cewa ya kar'bi auranki kamar yanda na umarce shi."
Nace."To shikkenan Alhaji Allah yasa hakan shi yafi alkairi." ya amsa da ameeen ya Allah ya d'ora da fad'in "maganar aiki ki bar ta tunda anayi ne domin biyan wasu bukata na yau da gobe na tabbata idan Allah ya kaddara auraki da Aminu baki da matsala tunda Alhamdulillahi Allah ya rufa masa asiri."
Gumin saman goshina nagoge nace."To shikkenan Alhaji duk yanda kace hakan za'ayi Allah yasa haka shi yafi alkairi." ya amsa da ameeen ya Allah." Umarnin tafiya ya bani na mike a sanyaye na fita daga dakin.
Zaune na sameta a bedroom dinta tana ninke kayan sawarta, zama nayi gefan gado kuka ya kwace min.....a nutse ta juyo tana kallona kuka nake sosai! tace."Sa'ida ki rufa min asiri na fita kunyar mutumin nan dan Allah kada ki watsa min kasa a ido."
Cikin rawar murya nace."Umma anya al'amarin nan zai yiwu kuwa Yaya Aminu saurayi ne ya za'ayi ace za'a had'ashi dani bazawara sai nake ganin kamar tilas akayi masa baya sona.
Girgiza kanta tayi tace."Sa'ida idan ma tilas akayi masa ai shine ya janyowa kansa me yasa tuntuni baiyi aure ba me ya rasa na rayuwa yana da kudi gida da mota to me yake jira kuma ki daina kiransa saurayi sai dai ki kirashi tuzuru domin ya tashi daga sunan saurayi ya koma matashi kuma baki wuce sa'ar auransa ba ni dai babban burina ki bani had'in kai akan wannan al'amari domin kin san Alhaji ya wuce komai a gurinmu."
Shuru nayi ina girgiza kaina gabadaya kaina ya kulle na rasa wane irin tunani zanyi idan Allah ya kaddara aurena da yaya Aminu wace irin rayuwa za muyi ni dai ba zan iya d'orar da halinsa ba tunda ba zaune nake dashi ba abinda dai zan iya tunawa shine yana da saukin kai da iya mu'amula sai dai halayen mutum basa fitowa sai zama yayi zama ina tsoron abinda zai faru a rayuwar auranmu domin a yanzu gabadaya auran ya fice min daga rai mussaman idan na tuna irin zaman da nayi a gidan Alhaji Nura gabadaya sai naji auran ya fice min daga raina.
Salim sai da ya koma gida cin abincin rana ya samu damar kiran wayar abokin nasa....Khalid yace."Wai wace irin magana zaka fada min ne."?
Salim yace."Khalid wai auran aunty Sa'ida ya mutu ne."? Cike da mamaki yace."Me yasa ka fad'i haka."? Yace."Sau tari ina ganinta a unguwa idan zata wani guri a takaice dai yau ma ni na dauketa a babur dina na kaita hotoro kuma mayafinta a kafad'a gaskiya jikina na bani babu aure a tare da ita.
Khalid ya saki sanyayyar ajiyar zuciya yana murmushi yace."Lallai kace na dawo gida da kwarin gwiwata." Salim yace ."Wai kai don Allah har yanzu baka hakura da ita ba."?
Yace."Salim idan kaga na hakura da aunty Sa'ida to kace bukatata ta biya na aureta amma na rantse maka muddun ina numfashi sai na hanata sunkuni.
Salim yace."Khalid ka ji tsoron Allah ka nemi za'bin Allah kada kace zaka tsananta akan dukkanin hukuncin da Allah ya zartar."
Ajiyar zuciya ya sauke yace."Salim Allah ne ya d'ora min kaunarta kuma kullum idan zan dungura goshina a 'kasa sai na rokeshi da ya za'ba min abinda yafi alkairi tunda naga har yanzu zuciyata ta kasa hakuri da ita na tabbata a gaba ina tare da nasara zan cigaba da bibibyar rayuwarta har sai sanda Allah ya cika min burina ."
Salim ya dinga girgiza kansa yana mamakin al'amarin a sanyaye yace."To ai shikkenan tunda kace haka Allah ya za'ba mata dukkanin abinda yafi alkairi." ya amsa da ameeeen ya Allah.
Suna yin sallama da Salim din ya shiga kiran wayarta lokacin tana tare da mahaifiyarta tana sake kwantar mata da hankali....koda taga kiran nasa daukar wayar tayi ta kashe tana jan tsaki.
Cikin jin ciwon abinda tayi masa ya nemi number Wayar gwaggo ya shiga gurin kira, ta dauki wayar tana dubawa ta gane sunansa da yayi mata serving da *Jarumi* yau dai tayi ra'ayin d'aga wayar domin dama can daurewa take tayi kewarsa.
Tana dagawa ya sauke ajiyar zuciya da fadin."Har naji sanyi a cikin raina.'' Tace."Khalid ka kyauta akan abinda kayi." Da sauri yace."Gwaggo me nayi kuma babu gaisuwa sai ki fara 'korafi.''? a fusace! tace."Ka kashewa Sa'ida aure sai ka zuba ruwa a kasa kasha."
Murmushi yayi had'e da shafa sajensa yace." Gwaggo ni kada ku d'aura min laifi ta yaya zan kashe mata aure bayan bana gari dama can auran matacce ne.''
Tace."Kafin ka tafi ai ka shirya kitumurmurar da ta janyo mutuwar auran ashe bakaji maganar da nayi maka ba sai da ka wanke kafa kaje gidan kuma saboda tsabar rashin mutumci ka shiga har dakin baccinsu."
Yar dariya yayi yace."Gwaggo cewa tayi nayi mata wani abu dana shiga k'uryar dakinta."? Tace."Oh!o ai ko bakayi mata wani abuba tunda mijinta ya shigo ya ganka dole ya zargi wani abu a tsakaninku tunda dama can akwai soyayya.
Ajiyar zuciya ya sauke da fadin."To ai shikkenan magana ta kare Allah yasa haka shi yafi alkairi."
Tace."Dama ai haka zakace tunda haka kake so to kama daina rawar jiki domin babanka yayi rantsuwa akan ba zaka aureta ba.
'Dif! yayi yana jin wani d'aci a makogwaronsa yace."Gwaggo akan me? zaiyi rantsuwa? akan me zai hana abinda Allah ya halasta." Tace."Ai bani zaka tuhuma ba wayarsa zaka kira ka kai masa k'abali da ba'adi." Tana kare maganar ta kashe wayar tana fad'in "Ja'iri kawai mara zuciya tamkar yarinyar nan ce mace a duniya ya nace dole sai ya aureta
Khalid ka sa'ke yayi da waya a hannunsa gumi sai tsatstsafo masa yake babu shakka dole yaje gida a kurkusa domun yana jin tsoron ayi masa sakiyar da babu ruwa.
Yamma likis na koma gida Gwaggo ta dinga bina da kallo tana so tayi min magana amma tayi shuru da bakinta sai bayan muyi sallar magariba ne na kalleta da fadin."Gwaggo kin san abinda yake faruwa kuwa."?
Girgiza kanta tayi tace."Ina zan sani bayan naga kamar kina 'boye min ai shiyasa nayi shuru da bakina na zuba miki ido."
Ajiyar zuciya na sauke nace."Dama so nake ki samu nutsuwa tukkuna na sheda miki abinda yake faruwa.
Tace."To ina sauraranki Allah yasa alkairi ne." a nutse nace."Alhaji ne ya nemi alfarma akan na auri babban d'ansa Aminu."
Zuba min ido tayi tana kallona kafin tace."Sai kika ce masa me."? a sanyaye nace."Gwaggo na amince domin ba zan iya jayayya dashi ba mutumin bai cancanci haka daga gurina ba.
Tace."Ai dole ki fadi haka mana dama ai abinda yake nufi kenan shiyasa yace kije yana neman ki ashe maganar kenan zai kama ya aura miki yaronsa da yake fama da matsala."
Nace."Gwaggo wace irin matsala kuma don Allah kiyi wa al'amarin kyakykyawar fahinta."
Tace."Sa'ida ni kam bana miki sha'awar auran wannan mutumin sam baku dace ba." Nace."Gwaggo saboda me kike ganin bamu dace ba."
"Haka kawai banyi na'am da al'amarin ba amma tunda har kin amince masa to bani da tacewa sai dai kawai nayi miki fatan alkairi."
Shuru nayi kaina a kasa ina nazarin maganarta to ko dai Gwaggo ta hango wani nak'asu ne a tarrare da Yaya Aminun yasa take fad'ar wannan magana! Ni dai a zahiri ban ga makusa a tare dashi ba cikakken namiji ne wanda ya tara dukkanin abinda ake bukata sai dai hausawa suna cewa abinda babbah ya hango yaro ko ya hau tudu ba zai hangoshi ba.
Kwana nayi da tunani da zullumin al'amarin da safe da Kawu ya shigo nake fada masa yanda mukayi da Alhajin....Yace."Sa'ida ina da masaniyar komai domin kafin kije ku tattauna sai da ya kira ni har gida naje na sameshi ya sanar dani komai tabbas naji dadin al'amarin kuma na taya ki murna samun nagartaccen namiji kamar Aminu ina rokon Allah ya tabbatar muku da alkairi. "