Showing 153001 words to 156000 words out of 185789 words

Chapter 52 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24178

yana taka busassun kararen ice.

Jamila dake gefensa a zaune tace." Ya Khalid baka ta'ba zuwa bane naji kana tambayar kwatancen gidan."?


Ba tare da ya kalleta ba yace."Tun ina yaro k'arami rabo na da garin kinga kuwa dole kaina ya juye.''


Tace."Eh gaskiya ne kuma amma garin ya burgeni wallahi idan mukayi aure zamu dinga zuwa akai akai muna shan iska." Murmushi kawai yayi ya cigaba da juya sitiyarin motar.

Da kyar suka samu gidan yara yaran k'auyen suka cika bakin motar suna shafawa.

Gwaggo da kanta ta fito domin tar'bar sa sai dai ganinsa tare da Jamila yasa fara'ar fuskarta tayi rauni kadaran kadahan ta amsa gaisuwarta ta jagorance su shiga cikin gidan.

Tsakar gidan akayi musu shimfid'a jama'a maza da mata suka shiga turereniyar zuwa gaisuwa........Ya fito da kudi ya dinda basu yana Jin dadin yanda suke masa addua da fatan alkairi.


Duk abinda ke faruwa ina daki a kwance ina jinsu inaso na fito domin nayi tozali dashi ina jin takaicin na had'a idona da yarinyar.


Baba Larai ta kalli Jamila da fadin" Wato shine kika biyo shi saboda kada na riqeshi na hanashi tafiya ko to komai dai abinki nice Uwargidansa domin itama Gwaggon baya na take bi saboda haka duk ado da kwalliyar ki baki kama kafafuna ba."

Jamila ta dinga Dariya tana 'boye fuskarta ina jinsa yana tare mata da fadin." Ni me zanyi daku duk kun tsufa mussaman ke Baba Ladidi jikin ki duk jijiya da kai duk furfura babu abinda zaki burgeni dashi." Baba Ladidi ta riqe baki tana fadin."Wato wulakanci zakayi min kenan to ai da tsohuwar zuma ake magani kuma dame matar taka tafi ni itama ai bata da wani kumarin kirki dubeta kamar ka busheta tafad'i."

Gwaggo ta ta'be baki da fad'in "Aikuwa haka yaji ya gani sai yaje yayi ta fama watakila kuma a gaba za tayi qiba." Jamila shuru tayi jikinta duk yayi sanyi gabadaya taji wani irin tsanar Gwaggo a cikin ranta.


Sai da zamu tafi tukkuna na fito daga d'akin Uffan bance musu ba na kama hanyar fita Baba Ladidi tace.''Ke kuma ta bizaro babu sallama kinyi gaba na lura da akwai abinda ke damunki domin tun jiya kike nukufurci."


Kallonta nayi da fadin."Baba Ladidi sau dubu kike so nayi miki sallama ne.'' Tace."Ai wannan salamar daban take da sauran wacce mukayi." Nace."To shikkenan mu zamu tafi sai an kwana biyu." Tace."To Allah ya sadamu da alkairi muna jiran tsammani Allah ya kawo miki miji nagari muzo musha biki."
A zucci na amsa da ameeen nayi saurin ficewa daga gidan....



*Kika karanta min littafi baki biya ba ina bin ki bashi........Vip gruop#600 normal gruop#400.....account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*96*
Jikin motar suka same ni a jingine kauda kaina nayi har suka karaso gurin 'yan uwa da abokanan arziki sun kewaye motar sai bankwana suke mana Gwaggo sai hawaye take sharewa Baba Ladidi na taya ta nace."Dan Allah sallamar ta isa haka Gwaggo shigo mota mu tafi idan kuma baki gaji da zama a garin ba sai ki koma ki zauna mu dai tafiya zamuyi." Baba Ladidi tace."Rufe min baki ja'ira kawai dama ai ke na lura kamar dole akayi miki kika zauna damu komai abinki garin Dambatta shine tushen ki."

Yanda take masifa tana tada jijiyar wuya abin ya bani dariya gaban motar na bude na zauna da fadin."To ni dai na shiga mota Allah ya kaddara saduwarmu." Jamila tayi kicin-kicin da fuska ganin na zauna mata a mazauni ni kuwa ina sane nayi hakan domin da ita dashi dik neman rigima nake dasu.

Gwaggo da kyar 'yan uwa suka barta ta shiga motar Shi kuma ya tsaya yana sallamarsu sosai yayi musu rabon kudi tamkar wanda bai san ciwonsa ba.

Kokarin bude motar yake ya ganta a tsaye tasha kunu yace."Jamila shiga mota mu tafi mana."

A marairace tace."Yaya Khalid ai ta zauna min a mazaunina."

Cikin motar ya duba ya ga yanda na wani 'kame a zaune kaina na dauke ina sake cin magani......Wani irin kwarjini tayi masa ya kalleta da fadin."Ki bata guri ta zauna mana."

Ko kallonsa banyi ba, Gwaggo tace."Jarumi wai tsayuwar me kukeyi ne kai da ita."?

Yace."Gwaggo gata nan tayi mata fin karfi ta zauna mata a gurinta."

Gwaggo tace."Aa ban gane ba wane irin fin karfi kuma."?

Yace."Gwaggo kamata yayi ace Matata itace a kusa dani to ita kuma aunty Sa'ida saboda neman fad'a ta zauna mata a guri."

Gwaggo rai a bace tace."Au motar daga gidansu tazo da ita kenan? ashe har an daura auran naku babu labari to ai shikkenan ke Sa'ida fito mata daga gurin zama sai muje mu samu motar haya inace dai duk mota mota ce kuma zamuje gida kalau."

Kokarin fitowa take daga motar yayi sauri mayar da ita da fadin." Yi hakuri ki zauna." Gwaggo taja tsaki da fadin." Yo idan ba tsiya ba ya za'ayi tace lallai sai ta zauna a kusa da kai inace da ita da Sa'idar duk daya suke.''


Girgiza kansa yayi yace."Aa ba daya suke ba wannan auntyna ce ita kuma wannan wife d'ina."

Tace."Kai kasan wani Wife ka shiga mota mu tafi kawai." Juyawa yayi ya kalleta duk jikinta yayi sanyi yace."Yi hakuri ki shiga ki zauna kusa da kishiyarki Gwaggo muje gida."

Rai a bace tasa hannu zata bude motar yayi saurin bude mata yana rarrashinta hakan yasa taji sassauci a cikin zuciyarta.

Sai da ya tabbatar ta zauna sosai sannan ya rufe motar ya bud'e mazauninsa ya zauna da bisimillah a bakinsa...........A hankali na sauke ajiyar zuciya a cikin raina dama babban burina na kuntatawa yarinyar naji dadi sosai da ranta ya 'baci.


Shuru motar babu mai magana sai dai shi jefe-jefi yana amsa waya tinda ya zauna nake satar kallonsa gabad'aya yaron ya gama tafiya da imani na yau yayi ado cikin manya kaya riga tazarce ta shadda kanshi da hula irin ta kanawa yayi wani kwarjini da kamala babu wanda zai ce bashi da iyali saboda yanda Allah yayi masa suttura ta kowane bangare.


Kasuwar 'yan kaba yayi parking gilashin motar ya sauke yayi magana da daya daga cikin masu siyar da kayan miya yace."Yana son kayan miya masu kyau." Motar ya bude ya fita sukayi magana ya bashi kudin yana tsaye yasa masa komai buhu a bayan motar motar ya kunna muka bar gurun.

Gwaggo tace."Kai kuma me za kayi da uban kayan miya haka."? Yace."Gwaggo ke na siya wa kina min miyar ki mai dadi."


Murmushi tayi tace."Aikuwa nagode za kuwa kasha miya." Yace."Tom nagode Gwaggo yanzu idan mun isa gida zan tura kasuwar Janguza a siyo kaji da zabi ko."

Tace."Aa sai dai ka bari a kwana biyu tukkuna domin mutanan Dambatta sun bamu kaji masu yawa motar tsarabar mu nasan ta isa gida tunda tun safe direban ya tashi."


Yace."Tom mungode kwarai." shuru motar babu wanda ya sake magana ringing din waya ta ya katse shurun.......Alhaji Nura ne saboda mugun haushin yaron yasa na daga wayar murya ta na gyara yanda za tayi dadi na fara magana a hankali-hankali wanda duk 'kwa'kwar mutum ba yanda za'ayi ya ji.


"Eh wallahi nayi tafiya ne zuwa kauye amma yanzu gamu a kan hanya okey kada ka damu Alhaji kasan komai nufin Allah ne." Shuru nayi ina sauraran kalaman da yake min mirmushi nayi ina sake yin k'asa da murya nace." Haba dai yaushe zan wahalar da kai kazo d'auka na ka huta kawai tunda yanzu gani tare da direba."


Wani irin cin birki motar tayi! Gwaggo da take gyangyadi ta bude ido da sauri tana salati.

Kallonsa nayi sai huci! yake yana zufa(gumi) "Fitar min a mota."! abinda ya fada kenan idonsa yayi jajawur!! Gwaggo tace." Lafiya me yake faruwa ne."?


Bai saurareta ba ya bude min mota kokarin tura ni waje yake sai kyarmar jiki yake.


"Khalid wai meye haka bana son wulakanci fa.''

''Kin san Allah sai kin fitar min a mota tunda dai ni ba direban ki bane."

Shuru nai ina kallonsa nace."Idan na fita a mota a nan gurin wace motar ce zata d'auke ni.'' ?

"Ke kika sani malama ki fita tun kafin nayi miki rashin mutunci wallahi."

Dariya nayi ina kallonsa kawai naji ya angiza ni waje nayi saurin dafe motar raina yayi masifar 'baci!


Gwaggo kuka tasa da fadin."To tunda ka kore ta a motar ka nima ka bude min mota na fita mara mutunci kawai."

Ko kallonta beyi ba ya figi motar da karfi suka bar gurin......Sakin baki nayi ina kallon hanyar da suka wuce ikon Allah kenan mirmushin takaici nayi na girgixa kaina. waya ta na dauka number Alhaji Nura na laluba kiransa nayi akan yazo ya dauke ni na bashi kwatancen gurin.

Ranar da ake 'kwallara wa itace ta dame ni na samu inuwa na zauna ina mamakin rashin mutumin yaron nasan kishi ne ya rufe masa ido har yasa ya yi min wannan rashin mutuncin.



"Mara mutunci kawai wato har kayi arziki da zaka dinga wulakanta 'yan uwanka to shikkenan zamu isa gidan Wallahi sai na samu Ubanka duk na sheda masa abinda kake yi ni mai zanyi da Rabi da Uwarta ai sun cutar dani tunda suka had'a ka aure da wannan afiruwar yarinyar da ido sai kace na tsaka nasan itace ta zuga ka ka kori 'yar uwarka a motar ka.


Jamila ta fashe da kuka da fadin." Wallahi Gwaggo babu ruwa na ni ban san abinda ya had'a su ba kawai naji suna mayar da magana a tsakaninsu.


A fusace! tace." Rufe min baki munafuka kawai ai duk sharrin ku sai dai ya koma kanku masu mugun hali kawai." Jamila kuka kawai take tana shar'be majina.......Yana jinsu yayi musu shuru abinda ya dameshi shi ya dameshi wai kamar shi zata kira shi da direba abin yayi masa zafi mutuka. wani irin tsanarta yake ji a zuciyarsa ita da bazawarin nata.


Koda suka isa gidan Gwaggo taga yanda ya sauya bai burgeta ba zaginsa kawai take tana cin mutuncinsa sosai tayi masa tatas sannan tace ita bai burgeta ba tunda arzikinsa ya zama na izgilanci.

Tana shiga gidan taga kayan tsarabar su jibgi guda a kicin ajiyar zuciya ta sauke ta shiga dakinta ta zauna tana bin ko'ina da kallo sam hakan be burgeta ba hankalinta na kan Sa'ida hawaye suka shararo mata tace."Allah kayi min maganin Rabi da Uwarta Baito.


Ya jima a motar a zaune kafin ya fito ya shiga gidan.......Dakin Gwaggon ya nufa ya sameta tana kuka duk ta rasa yanda za tayi.


Da hannu ta nuna masa kofa da fad'in."Ka fita bana son ganin ka aini duk mutumin da zai tozarta Sa'ida to babu ni babu shi har abadah kuma wannan gyaran gidan da kayi sam baka burge ni ba gwara zamana a Danbatta akan na zauna a karkashin inuwarka."


Juyawa yayi ya fita daga gidan....yana kokarin shiga motar shi mahaifiyarsa ta kirashi babu yanda ya iya haka yaje ya sameta itama ta rufe shi da fad'a dan Jamila tana kuka wurjajan ta shiga gidan.

Tace."Wato kana fifita Sa'ida akan matar da zaka aura ko? kada fa ka manta Jamila 'yar dan uwana ce kuma matsayi biyu take dashi a gurinka mai zai sanya a hada baki da kai aci mutuncin ta.

Rashin abin cewa yasa kawai ya bata hakuri Amma ranshi ya baci da abinda Jamilan tayi masa dole yaja mata kunne mutukar tana bukatar zaman lafiya dashi.



Yana fitowa ya shiga motar da sauri hanyar Dambatta ya nufa gabad'aya nadama ta baibayeshi sai tunanin halin da take ciki yake.


Alhaji Nura na isa da motarshi shima ya isa gurin Kusan a tare suka fito daga motar.......Kallon kallon aka shiga yi Khalid zuciyarsa ta sake yin duhu yana ji tamkar yaje ya sha'ke masa wuya ya huta da ganin fuskarsa .

Da sauri ya karasa inda take tsugune....."Ki tashi ki shiga mota mu tafi'' Mik'ewa nayi na ratse shi zan bar gurin.

Hannuna ya ri'ke da sauri na juyo rai a 'bace nace."Sakar min hannu ko kuma ranka ya 'baci yanzu."

"Me zaki min na 'bacin rai ki burge shi."? Ido jawur nake kallonsa yana wani irin huci! yace." Babu wani abu na 'bacin rai da zakiyi min ki burgeshi tunda nasan dake dashi na riga na gama yi muku illah a rayuwarku so duk wani abu da zakiyi min ba zan damu ba."



Hannuna na fizge da sauri nayi nufin barin gurin. sai yayi gaggawar kamo 'kuguna ya had'a bayana da 'kirjinsa ri'ke ni yayi sosai a jikinsa.

Alhaji Nura ya rintse idonsa yana jin wani irin d'aci a ma'kogwaronsa. wani irin kishin yaron ne ya taso masa.



Kokarin kwace jikina nake yana sake matse ni hankalina ya tashi gashi motoci na wuce wa a kan titi.


"Khalid bana son iskanci ka sake ni ko bakaji ba."

Sake rike ni yayi ya tsirawa abokin gamayyarsa ido.........Alhaji Nura jiki a sanyaye ya karaso gurin da fad'in." Kai Yaro ba sai kayi haka ba sannan zaka nunawa duniya cewa kai din mara tarbiya ne."

Sosai yaji ciwon maganarsa sai ya share cikin sigar 'kunsa bakin ciki yace."Ashe kai sai yanzu ka san bani da kunya ai na dauka ta fad'a maka cewa ita d'in saura nace sai da naci na rage ka samu so kaga k'arshen rashin kunya kenan."


Alhaji Nura ya goge gumi da hankicin rai a 'bace yace." Ta fad'a min yanda al'amura suka faru ai dama shaid'ani ne kuma don kayi mata fyad'e a farko hakan ba zai hanani auranta ba tunda ina mata sahihiyar k'auna."


Tsaki yaja yace."Kaga malam kaja motar ka kayi gaba wallahi ba zata shiga motarka ba na fada maka magana guda.


Alhaji Nura yace."Kai kada fa kayi min rashin kunya anan gurin ka sake ta idan ba hakaba yanzu na had'a ka da hukuma."


A fusace! yace."Idan uwar hukuma zaka had'ani da ita a shirye nake da kai dasu Mtsww." Ya 'kare maganar yana jan tsaki.

Kallona yayi idonsa sunyi jawur! yace."Sa'ida kina kallon yaron nan yana kokarin zagina ko." sunkuyar da kaina nayi gabadaya na rasa yanda zanyi Yaron ya galabaitar dani gurin rikon tsaurin da yayi min ga wani irin tausayin Alhaji Nura da ya rufe ni.


"Khalid ka sakar min jiki dan iska mara mutunci kawai." A zafafe ya juyo dani muka kalli juna gani nayi fuskarsa ta rikid'e...."Ni ne dan iska."? K'asan makoshi yayi maganar......Kirjinsa na kaiwa duka...ya had'e ni da kirjinsa sosai ya matseni gabansa na fad'uwa nawa ma haka. Ina kokarin kwace wa yayi gaggawar tallafo fuskata bakina ya kama da nasa ya ri'ke da kyau wani irin sha yake wa bakina jikina da nasa sai karkarwa yake.


Alhaji Nura rintse idonsa yayi jikin motarsa ya dukufa hawayen takaici da bakin ciki naso ya kufce masa.


Kafafuna ne sukayi sanyi na dinga kokarin faduwa a gurin kawai ya tallafe ni daukar yara yayi min ya nufi motarsa zaunar dani yayi ban san inda kaina yake ba sai lokacin daya kunna motar tukkuna na dawo nutsuwata can na hango Alhaji Nura jingine a motarsa kamar ya d'ora hannu aka yayi ta kurma ihu!


Wasu zafafan hawaye ne suka kwace min na kalleshi yana driving hankalinsa kwance............Hannu na kai da niyyar kwad'a masa mari yayi gaggawar ri'kewa motar tayi tangal-tangal ta sauka daga kan titin da hannu d'aya ya tsayar da ita ya juyo yana kallona da fadin." Mari na zakiyi."? hawaye na share nace."Shaid'anin banza da wofi kawai ."

Sakar min hannu yayi yana murmushi yace."Kema ai shaid'aniyar ce.'' Ya kunna motar yana kokarin tafiya na rike sitiyarin da fad'in "Sauke ni ko kuma na haddasa mana accident."


Shuru yayi yana kallona ina huci nace."Gwara min Alhaji Nura akan ka mara mutunci wai kai kayi arziki da kudi da mota shine zaka tozarta ni ko."


Dariya yasa ya mayar dani shashasha! "Ni har yanzu banyi arzikin da zanyi izgalanci da wulakanci ba laifi kika aikata min na hukunta ki daidai da abinda kikayi mi."

Sitiyarin motar na hau murd'awa motar ta dinga gargada tana cijewa, hankali a tashe yace." Dan Allah kiyi hakuri kada ki kashe mu lokacin mu beyi ba tukkuna ina bukatar nayi doguwar rayuwa kafin na mutu."


Cigaba nayi da murd'a sitiyarin motar na wani irin abu cikin tashin hankali ya cire key din ri'ke ni yayi ya matse tsam a jikinsa sai kyarma yake yana had'a gumi! hakuri yake bani akan abinda yayi min.

Jikina ne ya mutu nayi lakwam a jikinsa gabad'aya ya kashe min jiki da yanda yake min magana kasa-kasa yana marmatsa min sassan jiki.



*Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi*
*Vip group #600.....Normal gruop#400......Account... 0542382124.....Binta umar gtbank... idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE**97*
Sai da nayi ya'ki da zuciyata sannan na kwace kaina daga hannunsa kallonsa nayi idanuwansa sunyi jawur! sai wani irin kallo yake min yana cizan lips d'inshi harararsa nayi tare da jan tsaki kaina na dauke tare da gyara mayafi na da ya sauka kasan kafad'ata.

Ina ji yana saki wani irin nishi kafin ya kira sunana can kasan ma'koshinsa.

Kallonsa nayi fuskata a 'bace. Yace.'' Ina jin feelings ya za'ayi."? Cikin fad'uwar gaba nace."Ba zaka kunna mota mu tafi ba ko.''? Kafin yayi magana motar Alhaji Nura tazo ta wuce fuuuuu! gabad'ayanmu muka bi motar da kallo.

Kanshi ya shafa yana wani killer smile yasa key a motar ya tasheta muka bar gurin.

Takaici da b'acin ran abinda yayi ya sanya na dinga tsaki Allah-Allah nake mu isa gida na huce bacin rai na.

Ya kalle ni da fadin."Auntyna amma kin dan samu sassauci ko.''?

A wulakance na kalleshi ya kanne idonsa guda yana kallona da munafikin murmushi a fuskarsa.

Kauda kaina nayi daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login