Showing 102001 words to 105000 words out of 185789 words
sameshi zaune a kasan kafet yana duba loptop. zama nayi a hankali nace."Ba zaka ci abinci ba."?
Hankalinsa nakan Loptp din yace."Bari na rage aiki tukkun." shuru nai kawai na zuba masa ido ina mamakin al'amarinsa.
Kusan rabin awa yana aiki a loptop din kafin ya rufe a nutse ya kalle ni da fad'in "Tashi muje dainng din ki bani abincin." Mikewa nayi ya biyo bayana.
Tsaf na shirya masa abincin na tura masa gabansa zama nayi ina kallonsa yana cin abincin yana amsa waya
Nace."Yaya Aminu kayi abu d'aya mana ka ajiye wayar kaci abinci sai hakan yafi.''
Ba tare da ya kalle ni ba ya cigaba da wayarsa.....Ji nayi raina ya 'baci sai kawai na miqe na bar masa gurin.
Koda ya kammala cin abincinsa zuwa yayi ya dauki loptop dinsa bece min uffan ba ya bude dakinsa ya shige! ni dai mamaki ne ya kusa kasheni a gurin da kyar na iya kai kaina daki na kwanta.
Haka rayuwar mu ta cigaba da tafiya tsayin wata guda da dawowarsa babu wata mu'amula ta aure data ta'ba shiga tsakanina dashi Kullum a dakinsa yake kwana a garkame! gabadaya ma ya daina yarda na ra'bi inda yake dan duk kokarin da nake masa idan ya dawo daga kasuwa sai ya dakatar dani yace naje na huta shima Allah ya bashi lafiya zai iya had'a ruwan wankansa.
Ganin wulakancin yayi yawa yasa na daina shiga dakinsa sai dai idan ya fito mu gaisa ya kama hanya ya fita.......Gashi kamar mara tunani kullum sai ya tura min kudi accont d'ina al'amarin dai sai kace hauka! kuka naci na koshi na yanke shawarar tun kararsa da magana domin dai ni na gaji ba auran kudi nayi ba halastaccan aure nayi irin wanda Allah yake so......Sai da ya fito falon sannan nima na fito daga dakina na sameshi a zaune yana abinda ya saba lissafi da amsa kiran waya cikin zuciyata nace."Ban ta'ba ganin sahoramin namiji irinka ba. Wayar hannunsa ya kashe ya kalle ni da fadin."Kina da wata bukata ne."? a nutse nace."Eh ina da ita." Ya zuba min ido da fadin."Ina sauraranki." Murya na rawa nace."Yaya Aminu wai me kake nufi ne."? Cikin wani irin kallo yace."Bangane ba."? Na d'aure fuska tamau! nace."Shin dutse ka ajiye a gidan ka kome? ko kana da lalura ne."? Tsira min ido yayi yana kallona na sake cin kunu da fadin."Tsayi wata d'aya da sati biyu nake cikin gidan nan naci na koshi naci nama nasha madara nasha nono na kwanta a Ac me kake tsammanin zai faru." ? Dariya yasa yana kallona, sai kawai hawaye suka 'kwace min. Nace."Wato saboda kai baka da damuwa ka maisheni mahaukaciya kana min dariya ko to wallahi na gaji ni zan samu mahaifiyarka na fad'a mata halin da ake ciki." Da sauran dariyar a fuskarsa yace." Ai ba sabon abu bane a gurinta idan kin fada mata tuna mata kikayi domin tafi kowa sanin matsalata." Hannu nasa na share hawaye da fadin."To me yasa kasan kana da matsala ka amince da aurena."? Jim yayi kafin yace."Kawai bana so na bijirewa umarnin mahaifina ne." Cikin takaici nace."To kawai daga yau ka kira kanka da mace tunda ka fita daga sawun maza wato har wani fad'a kake kana da lalura to zaman me kake a haka da ba zaka nemi magani ba."? Rai a d'an 'bace yace."Ke Sa'ida kada ki fad'a min maganar banza mana." Nace."Ai gaskiya ce." Hannu ya daga min da fad'in "To tunda dai kin damu yau zan jarraba na gani." Naji wani kuttun bakin ciki ya tokare min a ma'koshi nace."Wallahi tallahi kudin ka na banza ne tunda har ka sake ka mayar da kanka haka meye amfanin neman kud'in naka kana fama da lalura irin wannan." Shuru yayi min, na dinga masa surutai ina farfad'ar masa maganar da duk tazo bakina.....A fusace! yace."Ki tashi ki bani guri idan ba haka ba wallahi ranki zai 'baci! Mi'kewa nayi na bar gurin raina a mugun 'bace.!
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE**SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*56&57*
"Khalid me yasa zaka shigo min daki bayan cewa nayi ka tsaya a falo na fito me yasa kake so ka janyo min matsala a gidan aurena." ? Ba tare da yace uffan ba ya mayar da kofar ya rufe ya durfafo inda nake tsaye, gabana ya tsananta faduwa cikin rawar baki nace."Ka juya ka fita falo gani nan kaga maigidan yana nan bai fita ba kada ya shigo ya gan ka wata matsalar ta afku." Cikin zuciyarsa yace."Dama ai ni so nake matsalar ta afku. daf dani ya tsaya hucin numfashinsa na sauka a fuskata, kauda kaina nayi tare da matsawa daga kusa dashi. cikin wani irin voice yace." A yanzu Babu wani abu da yake tsakani na dake sai alkairi ni banzo gidanki da niyyar na kashe miki aure ba." Na kalleshi da fadin."Amma dai kasan babu dadi mutumin nan ya shigo ya ganka har gadon baccinsa." Murmushi yayi yana shafa sajensa yace."To menene? ai da sauki ma idan ba wani abu ya shigo ya tarar muna aikatawa ba." Nace."Kasan yanzu yana da ikon d'aukar mataki akanka ko tunda ka shigo masa gida ba tare da izininsa ba." 'Yar dariya yayi idonsa a kaina yace."A'ina zai gan ni da zai dauki mataki a kaina an jima kadan na bar garin." Tsaki! naja cikin jin takaicin abinda yake na ratse shi domin fita na bar masa dakin....Kawai naji ya riko hannuna. cikin wani irin shocking na juyo da saurin gaske na fuzge hannuna da fad'in "Kada ka sake idan kuma ka'ki sai ka fuskanci 'bacin rai."
Daf dani ya matso yana kokarin magana. Ya shigo dakin. naji gabana yayi wani irin rugugi! da mugun sauri na janye jikina gwiwata a bala'in sanyaye na nemi bakin gado na zauna ina zare ido!
Cikin basarwa yace."Alhaji barka da wannan lokaci." Alhaji Nura bai amsa masa ba ya karaso cikin d'akin fuskarsa tamkar hadarin dake daf da zubar da ruwan sama.
"Kai me ya kawo ka gidana? waye kuma ya baka damar shigowa har dakin bacci na."? A nutse yace."Afuwa Alhaji nima nasan ban kyauta ba kuma a yanzu ma maganar da mukeyi kenan da ita tana nuna min rashin dacewar abunda na aikata kayi hakuri dama nazo nayi mata sallama ne zan koma gurun sana'ata Lego's. "
Yace."Kada ka kuskura ka kara shigo min cikin gida domin ni ban yarda da kai ba babu ruwana da 'yan uwantakar dake tsakaninku."
Cikin mamaki yake kallonsa kafin yace."Kana nufin zaka iya raba hanta da jini kenan."? Alhaji Nura yaji tamkar ya soka masa wuka a ma'koshi yace."Kai ashe baka da kunya ? ka taka sharia ka shigo gidana babu izini na amma kake kalubalanta ta."
Killer smile yayi yace."Aa Alhaji naji kana wata magana ne mara ma'ana shiyasa nayi wannan maganar shigowa gidanka kuma babu izini ai na nemi afuwarka.
Mikewa tsaye nayi rai a 'bace! nace."Khalid kama hanya ka fita bana bukatar ganinka a gidan aurena."
Wani irin kallo yayi mata zuciyarsa na wani irin zafi ya lura duk da ya kar'be budurcinta mutumin na sonta yana kuma kishinta bai ta'ba tsammanin cewar za tayi watanni a gidansa ba tare da ya sake ta ba.
Murmushi yayi ya kalleta ya kalli mijin nata yace."Kuyi hakuri da aikin 'kuruciya kada kuma ku fassara abinda nayi da wata manufa mara kyau saboda haka ni na barku lafiya."
Hanyar futa ya kama gabad'ayan mu muka bishi da kallo har ya bude kofar dakin ya fita......Kaina ya juyo yana wani irin numfarfashi da huci! yace."Ashe dama baki da mutunci da kamun kai Sa'ida."?
Shuru nayi masa domin nasan nike da laifi. ya cigaba da cewa''Sabida rashin kamun kai da rashin sanin darajar aure ki gayyato tsohon saurayin ki dakin auranki shin me hakan yake nufi.''?
Cikin 'kokarin kare kaina nace."Wallahi bani na gayyatoshi ba shigowa yayi." a fusace! yace."Rufe min baki munafuka idan baki bashi fuska ba ta yaya zai shigo min gida har dakin bacci na''
Kaina na sunkuyar 'kasa ina addua a cikin zuciyata.....Cikin sigar cin mutunci da wulakanci ya cigaba da zazzaga min bala'i yana fad'ar duk maganar da tazo bakinsa.
Cikin kuka nace."Ni dai dan Allah kayi hakuri an san ba'a kyauta maka ba amma ka daina zargi na da yaron nan wallahi babu abinda mukayi wanda ya sa'bawa sharia.
"Babu abinda kukayi na shigo na sameku daf da juna kamar zaku rungume junanku." shuru nayi ban tanka masa ba, ya cigaba da cewa''To wallahi wannan shine na farko kuma shine na karshe duk ranar da yaron nan ya sake shigo min gida a bakin auranki."
Da sauri na daga kaina ina kallonsa da mamakin maganarsa.....Yace.'' Kwarai kuwa ki kalleni da kyau ni ba yaro karami bane da zaku dinga wasa da tunani na na lura har yanzu da akwai soyayyar yaron nan a zuciyarki sabida haka wallahi kuka ci amanata sai na baku mamaki.
Hannu nasa na goge hawayen fuskata nace."Amma dai kasan ba zaka hana ni zumunci dashi ba ko."?
"Babu ruwana da wani zumuncin ku idan kun had'u can kuje kuyi amma ban lamunce a shigo min gida ba." Yana gama maganarsa ya bude dakin a fusace ya fita.
Kwanciya nayi naci kukana na koshi a gaskiya Alhaji Nura bashi da sauki mugun masifaffen mutum ne mara fahimta.........Gabadaya dauke min wuta yayi a gidan ya daina shiga sabgata ko nice da girki bama mu'amular arziki fuska a murtuke yake 'kare kwanakin sa ya bar min dakina babu kyakykyawar mu'amula. sosai na shiga damuwa mai tsanani domin a cikin 'yan watannin da muke shiri dashi na saba sosai dashi da soyayyarsa tunda duk ranar girkina sai munyi auratayya duk da baya bani had'in kai sosai amma ina gamsuwa dashi......Gabadaya sai na shiga cikin wani irin yanayi na tashin hankali da fargaba gefe guda kuma ga masifaffiyar sha'awar dake nema ta zautar dani.
Yau dai girki na ne kuma nayi alkawarin neman sa a kan hakki na domin ba zan zauna kullum marata na ciwo ba. Koda ya shigo dakin kai tsaye toilet ya nufa yayi uzirinsa ya fito ba tare da ya kalli inda nake zaune ba ya haye gadon yaja bargo ya rufe jikinsa.
Murya na rawa nace."Ina da magana da kai." shuru yayi min be tanka ba. Nace."Ni gaskiya na gaji da irin wannan zaman da mukeyi ina cikin matsatsi da takura ya kamata kayi hakuri da abinda ya faru ka daina fushi mu cigaba da mu'amula kamar yanda muka saba.''
Nan ma uffan bece ba. na matsa jikinsa ina kokarin shiga bargon ya mike a fusace! yace."Kada ki kuskura ki hana ni bacci Sa'ida idan kuma kin 'kiji to ranki ne zai 'baci."A sanyaye nace."Bangane ba Alhaji dan na matso kusa da kai sai na hana ka bacci."
Yace."Eh bana bukatar wata fitina a yanzu ni bacci zanyi na huta gajiya.'' Kai tsaye nace."Ni kuma gashi ina bukatarka ya za'ayi kenan."?
Tsaki yaja ya juya min baya. na dauki hannu na dora a bayanshi a harzuke ya ture ni dan har sai da na kusa faduwa a kasan gadon.....Na bishi da kallon mamaki! rufe jikinsa yayi ya gyara kwanciyarsa kawai sai naji wasu zafafan hawaye masu ciwo sun kwace min.
Sauka nayi daga gadon na kwanta kasan kafet tare da takure jikina wata irin gawurtacciya sha'awa ce take taso min na dinga mutsu-mutsu ina takure jikina hawayen bakin ciki da dana sani suna ta ambaliya a fuskata.
Yanda naga rana haka naga dare da asuba ina jin motsinsa ya tashi ya shiga toilet yayi wanka ya fito yayi shirye-shiryensa ba tare daya ko kalli inda nake kwance ba ya kama hanya ya fita daga dakin.
A daddafe na mike na shiga toilet nayi wanka na dauro alwala na fito riga da zani na atamfa nasa a jikina ko mai ban shafa ba nasa hijabi na tayar da sallah......Koda na idar da sallar kasa fita falo nayi sai nayi kwance a kan daddumar ina matse hawaye marata har yanzu ciwo take mun.
Muryar Yusura naji a kaina tana fad'in "Aunty Sa'ida kizo muyi breakfast inji babanmu."
Bude idona nayi ina kallonta dishi-dishi a idona nace."Kije gani nan." Yarinyar ta bude kofa ta fita ba.
Sun dan zauna zaman jiran fitowarta da suka ga bata fito ba sai kawai ya umarcesu da suyi breakfast d'insu..............Ba tare da damuwar komai ba ya shige ya tafi kasuwa bai ko duba halin da take ciki ba.
Sai kusan sha d'aya da rabi na samu sassaucin abinda yake damuna na mike da mataccan jiki na fita falon......Shuru yaran duk sun tafi makaranta ita kuma tana sama kamar tsuntsuwa, gurin cin abincin na nufa naja kujera na zauna a nutse na had'e tea domin shi kadai nake jin zan iya sawa a cikina ba tare dana sa madara ba na dauki cup din ina kur'ba tare da had'awa da soyayyan dankali da kwai.
Koda na gama karyawa banyi tunanin shiga kicin ba kai tsaye daki na koma na kwanta kan bed wayata na dauka na nemi number Hauwwa ita kadai nake jin zan iya fadawa matsalata.
"Kinga Sa'ida ki rabu da mutumin nan tun kafin ya jefa rayuwarki a matsala wannan ce shawarar da zan baki." Hauwwa ce ke wannan maganar bayan ta gama sauraran duk jawabin da nayi mata.
Shuru nayi ina nazarin maganarta Tace."Ni wallahi a rayuwata na tsani maza marasa adalci irinsu Alhaji Nura Sa'ida wallahi bana shakka wannan halayyar tasa itace ta janyo matarsa take lesbian saboda baya tsayawa ya biya mata bukatarta kawai kansa ya sani bukatarsa na biya shikkenan bai damu da halin da zaku shiga ba.
Nace."Hauwwa nima na fara zargin haka wallahi dan gaskiya idan ya kasance Aunty Murja tana da karfin sha'awa kuma tana da rauni to zata iya jefa kanta cikin matsala amma ni bana fatan nayi wannan harkar Hauwwa zan duba shawarar ki dan gaskiya ina masifar 'kwaruwa a zamantakewa ta da mutumin nan."
Tace."To shikkenan Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi." na amsa da ameen ya Allah 'kawata nagode kwarai da gaske."
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya yau da dad'i goge babu ta 'bangaran maigidan babu dad'i bangaran Aunty Murjar ma haka domin kwata kwata yanxu ni da ita bama shiri tun ranar da ta fahimci cewa na gane abinda takeyi ta sanja taku a gidan bata shiga sabgata sai da ni sa'i da lokaci inayi mata magana idan tayi ra'ayi ta amsa idan ba tayi ba ta share ni...........
Ranar Wata laraba tayi bakuwa da yake a falo suka zauna ina jin hayaniyarsu a dakina a nutse na bude kofa na fito. ganin matar dake zaune a kusa da ita yasa gabana ya yanke ya fadi da sauri nayi niyyar komawa daki sai kuma na fasa domin nasan sun riga sun gan ni! A dake na k'arasa falon na nemu kujera na zauna da fadin."Aunty Murja bakuwa kikayi ne."? Yau da mutuminci ta amsa min da "Eh wallahi dama yanzu take cewa zata tafi kuma baku gaisa ba.
Nace." Allah sarki ina kallonta nace."Ina wuni ya gida ya yara."? Ta amsa tana min wani irin kallo kaina na sunkuyar kasa gabana na faduwa ina addua a zuciyata akan Allah yasa bata gane ni ba.
Tace."Ni kam kamar na san wannan fuskar taki." na kalleta tare da kokarin kauda fargabata nace."Allah ko."? Tace."Kwarai kuwa kamar kece watanni takwas da suka wuce kikaje asibiti keda wata tsohuwa domun a duba miki virginal d'inki."
Nace."Anya kuwa bani bace." 'Yar dariya tayi tace."Kece mana ko ba sunanki Sa'ida ba."? Nace."Sunana Sa'ida mana." Tace."Sannan kuma kice min bake bace." shuru nayi mata domin idan nace zanyi magana zan iya fashewa da kuka shikkenan asirina ya tonu.
Aunty Murja tace." Maryam naji kina maganar wata takwas da suka wuce kuma yanzu auransu da Abban Yusura wata biyar kenan.
Tace."Nima dai abinda ya bani mamaki kenan lokacin taje akan a dubata ko ta qaru a d'inke ta lokacin dana duba sai na fahimci cewar kamar tayi gardama ne a lokacin da za'a kar'bi budurcinta sai na rubuta mata magunguna. har nake tambayarta ina mijinta a lokacin take cewa dani yayi tafiya shine yace tazo asibiti a dubata duk ina da sheda a rubuce."
Aunty Murja ta dinga yi min wani irin kallo ni kuma sai wani irin gumi nake zabgawa tamkar wacce tayi gudun famfalaki.!
Mi'kewa nayi jikina a bala'in mace na bude dakina na shiga na fada a saman gado kuka na dinga rafsawa ina kiran sunan Allah.
Aunty Murja wayarta ta dauka da fad'in "Dama neman hanyar da zan hukunta yarinyar nan nake domin nima data rufa min asiri zan rufa mata dan haka yanzu zan kira Abban Yusura a waya yazo kiyi masa bayani da bakin ki."
Dr Maryam tace."Aa Murja kada kiyi haka dan Allah wallahi ni ban fadi wannan maganar da wata manufa ba ki rufa mata asiri ta zauna dakinta."
Murmushin takaici tayi tace."Maryam