Showing 39001 words to 42000 words out of 185789 words
haka ki daina wannan maganar Khalid ya zalince ni kuma insha Allah sai ubangiji ya saka min."
Hannu tasa ta goge fuskarta a sanyaye tace." yanzu yana ina Khalid din."? Shuru nai mata na fara kokarin sauka daga gadon...ta rirri'ke kafad'una tana taimaka min na mi'ke tsaye daurin zanina ta gyara min kamar 'yar kaciya haka muka fita tsakar gida.....Ta zaunar dani a kujera 'yar tsuguno kamar wata maijego mai haihuwar fari da sauri ta koma dakin ta dauko fulas cike da ruwan zafi tana share hawaye ta surka ruwan a buta ta kai min bandaki da fad'in "Shiga kiyi tsarki kafin na d'ora miki wani ruwan ki gasa jikin ki Allah zai saka miki abinda akayi miki.
Daurewa nayi na mike tazo wai zata taimaka min nace." Ki barshi gwaggo.'' gefe ta matsa ni kuma na dafa bango na shiga bandakin ina rintse idona......koda na tsuguna domin wanke najasar dake jikina kuka ne ya 'kwace min yi nake ina tsarkake jikina tare da yin tasbihi a cikin zuciyata.
Daga bakin kofar bandakin ta tsaya tana miko min zanin atamfa da fad'in "Kar'bi ki daura wannan sai na shigo miki da ruwan zafi ki shiga ki gasa jikinki a ciki."
Tausayi ta bani ganin yanda duk ta damu da ni banta'ba tsammanin zata yarda da lamarin ba.
Tana can uwar dakin na fito daga bandakin ganin maidaidaicin baho da ruwa a ciki yasa kawai na tattare zani na na shiga ciki....sai bayan dana shiga cikin ruwan kuma na shiga tunanin wanda zai shigo...
Gwaggo tana share hawaye ta cire farin zanin gadonta daya 'baci ta dinga kiran sunan Allah a cikin zuciyarta tana addua akan Allah ya kauda idanun 'yan gaza gani a cikin al'amarin.......zanin gadon ta fito dashi ta ajiye bakin kofar shiga gurin Ummatu.
Na bita da kallo ina mamakin abinda take nufi da yin hakan.....Tace."Sa'ida dole na ajiye sheda iyayen yaron nan su dawo su ga abinda d'ansu ya aikata ba zan shaqi takaici ni kad'ai ba."
Girgixa kaina nayi nace."Gwaggo ki dauke zanin gadon nan dan Allah bana so kowa yasan maganar nan." Da sauri tace."Sa'ida ko kowa bai sani ba to ya zama lallai Rabi da Ibrahim su sani daga haka sai a rufe magana a gida Khalid kuwa ya nemi gurin kwanciya dan ba zai 'kara shigowa gidan nan ba.''
Shuru nayi tare da yin 'kasa da kaina ta juya ta shige dakin tana surutai had'e dayin tur da abinda Khalid din ya aikata.....naji dadin ruwan zafin sosai hakan yasa na karfafa jikina na zubar da ruwan bahon kana na janyo ruwa a rijiya na daura alwala na nufin dakin..
Tsaf ta gyara d'akin ta ta kunna turaran tsinke sai kamshi yake.....dadduma na shimfid'a nasa hijabi cikin karfin hali da yanayi na jin jiri da hajijiya na tayar da sallah.....Itama alwalar ta fita ta d'auro ta dawo dakin.
Koda na idar da sallar kwanciya nayi kan daddumar na rufe idona....har yanzu gabana radad'in zafi yake min inaji kamar an tsaga da reza!! jin hawaye na nema ya kufce min yasa da sauri na shiga nanata kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'una.
A take kuwa na samu sassauci a cikin zuciyata na dinga jin imani da tsoron Allah na ratsa ni zuciyata ta shiga fad'a min cewa wannan al'amari daya faru dake ki daukeshi a matsayin qaddarar da kike tafiya da ita haki'ka duk wani abu da zai same ki a duniya mai dad'i ko mara dad'i a rubuce yake a lauhil mahafuz Allah shine yake zartar da iko akan kowane bawan sa Ki roki Allah ya tsayar miki nan kuma kisa a zuciyarki cewa baki sa'bi Allah da gangan ba sai dai karfi da aka gwada miki....Tsakanin ki da Alhaji Nura kuma fatan alkairi ne."
Jin irin shawarwarin da zuciya take bani yasa naji wani irin kwari a jikina na mike zaune a ina kallonta da carbi a hannunta tayi zugum! tana kallon guri guda nace''Ba zaki koma gidan bikin bane."?
Girgixa min kai tayi tace."Ya za'ayi na kuma fita na barki ya dawo ya 'karasa ki yaro mara imani yasa miki k'arfi ya fatataka miki budurci na tsorata da jinin da nagani Sa'ida."
Kaina na sunkuyar k'asa ina tunanin artabun da muka sha ni dashi.... ko da wane ido zai kalli mutane? ko da yake ai mara kunya ne zai iya fittikewa akan 'karya domin ya kare kansa.
Haka muka kasance a zaune cikin jajantawa juna dan har sai da naso na fita dauriya domin sa'i da lokaci ina hankalce da ita tana sa hannu ta goge hawaye a fuskarta.
Sai yamma Ummatu ta shigo gidan.....bakin kofar dakin ta tsaya da fad'in "Gwaggo lafiya baki koma gidan bikin ba? jama'a sai cigiyarki suke."
Girgixa kanta tayi tace."Rabi tashin hankalin dana tarar a gidan nan ne ya hana ni komawa gidan bikin ina fata kinje kinga dakin amarya."?
Ummatu tace."Aikuwa ni na wakilce ki dan dani aka kai Suwaiba dakinta ba kiga gidanta ba yayi kyau kuma sosai Jummai tayi kokari dan tayi mata kayan daki masu kyau."
"Ba shakka." abinda tace kenan tayi shuru da bakinta...Ummatu tasha jinin jikinta ganin yanayin rashin walwalar dake tare damu sai kawai ta bar gurin tana ta'be bakinta.
Tazo shiga gurinta taga zanin gado a kud'indine kuma kamar an goge jini dashi....cike da mamaki ta dauka tana dubawa wannan zanin gadon ai na Gwaggo ne. sai kawai ta nufi dakin Gwaggon da zanin gadon a hannunta
"Gwaggo wannan ba zanin gwadon da kika siya kwanaki bane."? tafada tana nuna mata.
" Shine Rabi ki warwareshi sosai ki duba kiga meye a jiki."
Ummatu tace."Haba Gwaggo ai ba sai na warware ba gashinan ina ganin jini kaca kaca a jikinsa."
Murya na rawa tace."Jinin budurcin Sa'ida ne Khalid ya dawo gidan bayan fitar mu ya haike mata a cewarsa tunda shi bai samu nasarar auranta ba to sai da taje gidan mijinta a fanko."
Ummatu ta shiga watsa mana wani irin mugun kallo kafin tace............!
*Littafin na kudi ne.....Kada ki siya ki fita dashi....'yar uwa kada ki ganshi a gruops kiyi sharing.... Idan kika karanta min littafi baki biya ba ina bin ki bashi! 'Yar uwa idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake.....Vip gruop#600....normal group #300.....account... 0542382124....Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*22&23*
"Gwaggo wannan wace irin magana ce kikeyi? Ina khalid yake a gidan da har zai aikata wannan mummunan akin! Gwaggo shuru-shuru fa ba tsoro bane gudun magana ne ya za'ayi yarinya tayi fasiqancin ta sannan a laqabawa wanda baya nan Khalid tun karfe bakwai na safe ya fita daga gidan nan ballanatana ayi masa mummunan sharri irin wannan."
Gwaggo ta nuna kirjinta da fad'in "Rabi ni kike wa rashin kunya har kina fad'in shuru shuru ba tsoro bane to me kike nufi? kin san dai ba zan qi Khalid naso Sa'ida ba tunda duk daya suke a gurina abinda kuma yasa na yarda da al'amarin shine jiya da daddare na jima tare dashi ina tausar zuciyarsa akan auran Sa'ida da Alhaji Nura na dinga kawo masa misalai ina fahimtar dashi cewa shi aure rabo ne Allah ya kaddara cewar Sa'ida ba matar auransa bace dan haka sai ya hakura ya nemi wata.....Idan kikaji irin munanan kalaman da ya dinga yi sai kin riqe baki wannan dalilin yasa na yarda da abinda ya aikata."
A fusace! tace."Gwaggo idan duk jikina kunne ne ba zan yarda da wannan k'anzon kuregen ba, a ina Sa'ida taga wani budurci da har jininsa zai 'bata zanin gado kawai dama dai ta dawo gidan ne da niyyar ta d'ora masa sharri saboda ta tsaneshi."!
Cikin takaici da 'bacin rai nace."Ummatu idan nayi wa Khalid k'azafin zina meye ribata a duniya."
"Ke! saurara kada ki kuskura ki sake kiran yaro na da wannan sunan Khalid ba mazinaci bane."! a fusace tayi maganar tana kumfar baki.
Gwaggo ta zabaro! itama a fusace! tace." To menene shi idan ba mazinacin ba Rabi nace ki fad'a min menene shi Khalid ya cancanta a kirasa da wannan suna tunda har ya iya haikewa 'yar uwarsa."
Ummatu ta fashe da kuka da fad'in "Jama'a wannan wace irin masifa ce Gwaggo ashe akwai ranar da zaki goyi da bayan 'karya akan gaskiya kin fi kowa sanin halin Khalid ba zai aikata wannan mummunan aikin ba."
Gwaggo ta girgiza kanta cikin takaici da bakin ciki tace." 'Dan yau ne fa Rabi ba'a shedar mutum sanin abinda yake zuciya sai Allah amma ko shakka ba nayi Khalid shine yayi wa 'yar uwarsa fyad'e a tunaninsa idan hakan ta faru sai a janye maganar auran Alhaji Nura ayi dashi."
Ummatu zaman dirshan! tayi a gurin tana kuka tare da fad'in "Ni kam ba zan yarda da wannan k'azafin ba duk inda za muje a haka nake kuma ina da 'yan uwan da zasu tsaya min a gaban al'kali amma inaji ina gani ba zan yarda ayiwa yaro na qazafi ba."
Gwaggo tace."Ummatu ashe wu'ka zaki d'abawa kanki wane mahaukacin ne ya fad'a miki ana fita da irin wannan sirrin."?
Shuru tayi tana lalube a wayarta Gwaggo tace."To Wallahi tallahi kada ki kuskura naji maganar nan a wani guri Rabi idan kika sake kika fad'awa dangin ki abinda yake faruwa to zakiyi nadama mai tsananin gaske."
Hawaye ta share hannu na rawa tasa wayar a kunnenta tana fara ringing ta katse ta sake kiran wayar ta sake katsewa a sanyaye tace."Duk inda yake nasan yana kan hanyar dawowa gida gwara yazo ayi komai a gabansa ."
Gwaggo tace."Ko yazo ko bai zo ba shine munafiki kuma dole ya fuskanci hukunci domin shi da shigowa gidan nan har abadah."
Saurin kallonta tayi rai a tsananin 'bace tace."To idan bai shigo ba ina kike so yaje ya kwana."? kai tsaye tace."Ya tafi can dangin ki dama su suke d'aure masa gindi."
Ummatu ranta ya 'baci! kawai sai ta shiga farfad'ar bak'aken maganganu wanda Gwaggon ta kasa hakuri itama ta shiga mayar mata da martani suka dinga cacar baki Ummatu ta dage sai rashin kunya takewa Gwaggo........''To dama me nake samu a gidan idan ba wahala ba lafiya lau aka dauko ni daga gidan ubana da kuzari na da qiba ta amma tsabar wahala da yunwa tasa duk na lalace sai me idan kin sa shi ya sake ni."
Ummatu ce ke wannan maganar tana sakin wani irin nishi na bacin rai! Gwaggo tace."Rabi ba zan sa Ibrahim ya sake ki ba amma zan sashi yayi miki kishiya tunda ke baki da mutunci wato dama zuwa kike gidanku kina kwance mana zani ko duk tsiyarki Ibrahim yayi miki abinda uwarki da ubanki ba suyi miki ba."
Ummatu ta fashe da kuka da fad'in "Ni dai Allah ka jarrabe ni da jarabar Suruka tinda na auri d'anta banji dadi ba."
Nace."Gwaggo Ummatu kuyi hakuri dan darajar Allah kada makota su fara shigowa gidan asiri ya tono ni akai wa laifi kuma na barwa Allah."
Gwaggo tace."Dama shi ne alkali shi kuma wanda ya aikata zai girbi abinda ya shuka a nan gaba."
Ummatu da sauri tace."Insha Allahu zina ba dai a zuria ta b.......Shuru tayi ganin Kawu ya shigo gidan.
Ganin fuskarta jage-jage da hawaye yace."Me yake faruwa ne."? Ummatu ta tsuguna gurin tare dasa kuka.
Sai ya daga labulan dakin Gwaggo yana tambayarta...Tace."Shigo ciki ka samu nutsuwa na sheda maka abinda ya faru a gidan."
Jikinsa a sanyaye ya cire takalminsa ya shiga dakin ya zauna har lokacin Ummatu kuka take tana girgiza kanta ya ma za'ayi ta yarda da wannan qazafin.
Hankalinsa akan Sa'ida yace."Me ya samu fuskarki ta kumbura haka ga idanunki sunyi jawur kamar wacce taci kuka ta koshi."
Zuciya tace ta karye naji hawaye na nema ya kufce min cikin rawar murya nace"Babu komai Kawu."
Sai ya kalli Gwaggo yana neman 'karin bayani. tace."Rabi mi'ko min zanin gadon nan idan kin gama d'ibar albarkar."
Ummatu a sanyaye ta dauki zanin gadon ta shiga dashi dakin ta miqa mata ta juya zata fita tace."Aa ai babu inda zakije zauna nan tunda ga Ibrahim din ya dawo ayi magana a gabansa."
Ummatu gabanta ya buga tana jin tsoro kada ya sake aunata gidansu. jiki a sanyaye ta nemi bakin kofa ta zauna.
Gwaggo ta shiga warware zanin gadon... da sauri nasa hannu na 'karbe ina girgiza mata kai hawaye na zuba a saman fuskata.
Murya na rawa tace."Sa'ida ki bari a nuna masa sheda." nace."Gwaggo dan Allah dan Annabi maganar nan ta isa haka a barta ni na barwa Allah." da kyar na'karasa maganar saboda kuka mai karfin daya kufce min na miqe da saurin gaske na fita daga dakin guri na samu na tsuguna na dinga kuka ina kiran kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'una."
Baba Ibrahim jiki a mace yace."Gwaggo dukkanin abinda yake faruwa a gidan nan nake so ki fad'a min dan girman Allah kada ki 'boye min komai."
Ta girgiza kai tare da fad'in "Ibrahim ai ranar wanka ba'a 'boyan cibi wannan lamari ya zama dole ka sanshi domin kana da hakkim sanin abinda d'anka Khalid ya aikata akan marainiyar Allah."
Hawaye ta share tace."Ibrahim Khalid tinda ya samu labarin auran Sa'ida da Alhaji Nura ya tayar da hankalinsa ya dinga jifan al'amarin da mugwayen kalmomi tare da yin ikirari mai muni kancewar mutukar ba'a janye maganar auran Alhaji Nura ba to ba zai yarda ba sai ya dauki mataki! jin haka yasa na zaunar dashi na dinga rarrashinsa akan yayi hakuri ya barwa Allah komai na rayuwa rabo ne ashe yaron nan bai dauki nasiha ta ba ya shirya mugun abu.....'Dazu nida Rabi muka tafi gidan bikin 'yar gidan Jummai muka bar Sa'ida a gidan ita kadai tana bacci to wannan damar khalid ya samu ya haike mata a takaice dai Khalid shi yayiwa Sa'ida fyad'e abinda nake so na fada maka kenan."
Kawu Iro yayi 'kasa da kansa wani irin gumi! mai d'umi ya dinga tsatstsafo masa! hular saman kansa ya cire baki a bushe? yace."Gwaggo Khalid irin tozarcin da xaiyi mana kenan ? me mukayi masa a rayuwa? me kuma Sa'ida tayi masa da zai keta mata rigar mutumci wane irin kallo Alhaji Nura zaiyi mana a matsayin mu na iyayen yarinyar nan Gwaggo da sadakin wani Khalid ya aikata wannan 'barnar? idan Alhaji Nura ya kusanci yarinyar yaji ba daidai ba wani irin kallo zaiyi mata? me zai biyo baya a zamantakewar auranta."
Gwaggo ta goge hawaye a sanyaye tace."Shine dama babban tashin hankali da damuwar ai kawai Ibrahim ka ajiye maganar Alhaji Nura a gefe a mayar masa sa kud'insa Sa'ida babu namijin da zata aura a cikin wannan halin ta samu nutsuwa Khalid din dai shi zamu hakura ta aura asirinmu ya rufu.''
Kawu ya girgiza kansa cikin mugun takaici da nadamar haihuwar yaron yace."Gwaggo Sa'ida bata dace da macucin yaron nan ba saboda haka ki daina wannan maganar tsayin wattani biyar mun kar'bi sadaki a hannun mutumin nan ya za'ayi ace za mayar masa hakuri kawai za muyi a daura auran mu cigaba da addua kafin muga abinda Allah zaiyi."
Tace."To ai shikkenan Ibrahim yanzu wane mataki ka dauka akan Khalid din......Girgiza kansa yayi da fad'in "Kotu zan kai shi Alkali ya yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata wallahi ba zan bari mutucin marainiyar Allah ya tafi a banza ba.
Ummatu ta fashe da kuka da fad'in " Haba kai kuwa wace irin magana ce wannan? kana nufin d'an cikin ka zaka kai kotu akan abinda baka da tabbas a kansa."
Ya kalleta yace."Rabi ke zaki qalubalanci maganar mahaifiyata a gabana me kike nufi? kina so ki fada min cewa Gwaggo sharri tayi wa d'anki kome."
Girgiza kanta tayi tace."Aa ni ba haka nake nufi ba naji kana maganar kai shi kotu nace kafin ka yanke wannan hukunci ka tsaurara binkice akan al'amarin."
Cikin fusata! yace."Ba zan tsautsara binkicen ba! ni d'an halak ne kuma nasan *ZAMANI* Khalid babu abinda ba zai aikata ba tunda yasa son zuciya a ransa. mahaifiyata ba zata 'kir'kiri sharri ta d'ora masa ba."
Tace."Ai ba haka nake nufi ba ita Sa'idar me yasa bakwa ganin laifinta Khalid fa yaro ne akanta to har yaushe ma zai iya sarrafata ballanatana yayi mata fyad'e."
Takaici ya cika zuciyar Kawu Iro yace."Rabi idan baki daina magana anan gurin ba ranki zai mummunan 'baci! wane irin rashin tarbiya ne wannan a gabana kike kokarin 'karya ta mahaifiyata."
Gwaggo tayi murmushi wanda bai kai ciki ba tace."Ibrahim rabu da ita haka ita 'karya ai fure take bata 'ya'ya ita wai tana so ta kare d'anta akan abinda ya aikata idan kin kareshi a duniya a lahira fa."?
Ummatu tayi shuru tana shaqar hanci....Kawu Iro ya dauki wayarsa yana lalube number Khalid din ya nemo ya shiga kira.....Is swich Up. wayar a kashe take.
Ya dinga kira ana fada masa a kashe take...Gwaggo tace."Ai dole ya kashe waya tunda yasa abun da ya aikata ai da tuni ya shigo gidan."
Kawu Iro ya mike da sauri ya fita daga dakin.....tsayuwarsa naji a kaina na dago da sauri ina kallonsa....'bacin rai da damuwar da nagani a fuskarsa yasa wasu hawayen sake yankowa hakika Khalid ya jefa zuciyoyin mu cikin masifar tashin hankali
A sanyaye yace."Ki daina kuka kinji