Showing 15001 words to 18000 words out of 185789 words

Chapter 6 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24191

duk yanda naso da nayi aure idan lokacin baiyi ba dole na hakura kuma kina maganar cewa na girma nayi shekaru babu aure ai bani kad'ai bace akwai dubban matan da suke zaune babu aure da yawa daga cikinsu ma sunfi ni girma da shekaru saboda haka ki daina wahalar da kanki akan al'amarina duk ranar da Allah ya kawo lokacin aurena babu mahalukin daya isa ya hana."


Tace."Eh duk da haka Sa'ida bakiji bahaushe yana cewa idan kana da kyau ka 'kara da wanka ba ni na yarda da maganar mai maganin nan domin aljani yana da suddabaru iri-iri saboda haka dan Allah kada ki watsa min 'kasa a ido."


Murmushi nayi nace."Gwaggo kenan dan Allah ki bar maganar nan kinga lokacin sallah yayi kije kiyi alwala ki sallah ki roki Allah ya za'ba min abinda yafi alkairi."


Tace."Sallah ko kince nayi ko baki ce nayi ba dole nayi kuma Ubangiji shima ya fad'a cewa bawa ya tashi ya nema shi kuma sai ya taimakeshi." Nace"Gwaggo ba'a irin wannan al'amari Ubangiji yayi magana ba, Allah yace." Ko ro'keni ni kuma zan amsa muku amma bece wani bawan sa yaje gurin malamin duba ba."


A tunzure! tace"Wai Sa'ida waye yace miki gurin malamin duba mukaje."? Nace."Gwaggo dan Allah maganar nan ta mutu haka magani dai idan dan ni kike siyo to kinyi asarar kudin ki dan bazan sha ba."

Ina gama maganata na fita daga dakin na barta tana bina da kallo.

Bayan mun idar da sallar sai ta mike ta fita daga dakin minti biyar ta dawo hannunta dauke da karamin kaskon wuta da garwashi a ciki.......kallo na bita dashi ganin ta d'aga 'karkashin gadonta tana lalube ledar data shigo da ita ta dauko ta saki zanin gadon ta rufe........ta shiga zazzage magungunan dake cikin ledar.....Wani tsumma ta kwance naga ta d'ebo maganin dake ciki ta zuba a wutar a take dakin ya turni'ke da haya'ki! tari ya sar'ke ni! haya'kin maganin ya dinga shiga bakina da hancina! a gigice na mi'ke na fita daga d'akin ina tari da rirri'ke kirji, ko gama dawowa hayyacina banyi ba itama ta fito daga dakin ido jazur! sai tari take hawaye na zuba daga idonta......





*Masoya a taimaka da sharing????*




*IDAN KINA BUKATAR KI BIYA KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP #600 NORMAL#300 .....ACCOUNT..... 0542382124....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO?????*




*9*
Haka Baba Iro ya fito ya same mu a tsaye muna tari ga haya'ki na fitowa daga cikin dakin. "Gwaggo lafiya me yake faruwa ne."? Miyau ta had'iya ido jawur tace." Haya'ki na kunna sai tari ya sar'ke muka fito muna shan iska." Yace."Gwaggo wane irin haya'ki ne wannan mai cutarwa.''?

Da sauri tace."Na mayu ne kwana biyu kasala tana damuna shine Uwale ta kawo min dama kuma ai sa'i da lokaci ina kunnawa ."

Shuru yayi yana kallonta nima na zuba mata ido ina mamakin 'karyar data shirga. Dakin ya shiga da sauri tabi bayansa tana kallonsa tace."Ibarahim me kake nema."? Yace."Garin haya'kin zan duba nagani." Tace."Aa ba sai ka wahalar da kanka ba ai ragowa ne na barbad'a a wuta shine fa ya turnu'ke gidan da haya'ki."

Yace."Gwaggo dan Allah ki daina yarda da camfi irin na mutane wane maye ne zai kamaki acikin unguwar nan."? Tace."Aa Ibrahim ai shi maye bashi da kama watakila ma ina hurd'a dasu ban sani ba, to dan nayi haya'ki ai ba laifi bane."


Yace."Hakane gaskiya to dan Allah gwaggo kisan irin haya'kin da zaki dinga yi duba dai wannan kinsa gashi gabad'aya ya sar'ke muku numfashi."


Da sauri tace."Ai yau ne kawai hakan ta faru amma lafiya lau nake haya'kina to tunda ma dai maganin ya 'kare ai shikkenan."

Fita yayi daga d'akin ya kalleni cikin taushin murya yace."Sa'ida ki cigaba da hakuri da halin gwaggo ina nan inayi miki addua akan Allah ya kawo miki miji kiyi auranki."

Hawaye naji na kokarin kufce min nace."To Kawu nagode sosai." Yanda na lura dashi shima yana damuwa da halin mahaifiyar tasa dan dai bashi da yanda zaiyi da ita ne.''


Dakin na shiga na sameta tana gyara shimfid'a k'aurin maganin da haya'kinsa ya dinga sanyawa kaina yana juyawa bana tsammanin zan iya kwanciya a dakin domin kuwa zuciyata in banda tashi babu abinda take.

Tabarma da bargo na dauka na fita daga dakin....shimfid'awa nayi a wani dan loko a tsakar gidan na koma dakin na dauki fillo da wayata, kallo ta bini dashi har na fita daga dakin.


Gwara na kwanta a tsakar gidan yafi min alkairi." Waya ta na bude ina dubawa naga text d'in Alhaji Nura wai yana nan fa yana jiran amsa daga gare ni, murmushi kawai nayi ba tare dana bashi amsa ba na shiga WhatsApp ina dubawa.........Gwaggo da buta hannunta ta fito daga dakin ta nufi bandaki tayi uzirinta ta fito, sai da tazo kusa dani naji tana fad'in " 'Dakina ne babu wanda ya isa ya hanani yin abinda naga dama mutum yayi ta kwana a tsakar gida sauro ma ya ishe shi."

Uffan bance mata ba na cigaba da duba wayata, ta ajiye butar a bakin kofar dakin tace."Ai tabbacin mutum na tare da iskokai kenan gashinan ai saboda hayak'in yana da k'arfi sun koro ki daga d'akin ai duk abinda zakayi ba zan fasa turara haya'kin nan ba."

Ta gama surutan ta ban tanka mata ba cikin zuciyata ina ta shawarar matakin da ya kamata na dauka Khalid yana barazana ga rayuwata gwaggo tana kuntukawa zuciyata barina gidan shine yafi alkairi....."Sa'ida idan kin koma gidan mahaifiyarki anya kuwa ba zaki takura mata ba."? zuciyata ce take tunasar dani.....Ummana bayan rasuwar mahaifina wanda ta aura babban mutum ne mai iyali itace matarsa ta uku kuma bata dad'e a gidan ba ya cikashe ta hud'un babban gida ne mai d'akuna kowace na rayuwa ita da 'ya'yanta a dakinta sai dai duk ranar girkinta taje dakin maigidan......Alhaji Shamsu babban mutum ne kuma d'an kasuwa yana da shaguna masu yawa a kanti kwari suna harkar atamfofi tun bayan auransa da Ummana yaso na koma hannunsa Gwaggo tayi ta tsula musu rashin mutunci daga shi har Ummana tace babu wanda ya isa yayi iko dani tana raye jininta ba zaiyi agolanci a wani gidan ba.

Ganin irin rigimar da takeyi ne yasa duk suka hakura hidima sosai mijin Ummana ya dinga yi min duk sabgar karatuna shine ya dauki nauyi kuma duk ranar da naje gidan ziyara yakan bani kudi masu yawa na tabbata a yanzu idan nace zan koma gidan da zama zaiyi farin ciki sosai kuma zai kar'be ni da hannu biyu, tabbas akwai yiwuwar na koma gaban mahaifiyata da zama dan al'amarin gwaggo da Khalid yana nema ya shallake tunani na.

"Sa'ida ya kike kwance a tsakar gida ke kad'ai."? Muryar Baba Iro naji a kaina. Da sauri na mike zaune da fad'in" Wallahi zafi ne ya isheni na fito amma idan gari ya saki zan koma daki." Yace."To shikkenan amma ina fatan sauro baya damun ki."? Nace."Eh da sauki tunda na kunna magani." yace."To babu damuwa."

Labulan d'akin Gwaggon ya daga yana dubata. Sunanta ya kira yaji shiru nace."Ai da alama tayi bacci." yace."Eh hakane to sai da safe." Nace."To Kawu Allah ya tashe mu lafiya."

Yana barin gurin na koma na kwanta waya ta na kashe na rufe jikina tare da addua a bakina.



Yana can gurin kallon ball sai kusan sha biyu shaura ya shigo gidan......shuru ko'ina yayi duhu da sauri ya fito da wayarsa ya kunna torchlight idonsa ne ya sauka kanta tana kudindine a cikin bargo garin ya saki ana iska sosai dalilin da yasa kenan cikin bacci taja bargon ta rufe jikinta har kanta.

Tsayawa yayi a kanta yana kallonta tare da haske ta da hasken wayarsa, a hankali ya tsuguna kusa da ita yasa hannu ya bude mata fuska idonsa ne ya sauka kan wayarta da take kusa da ita ya dauka da sauri ya mi'ke daga gurin.

Dakinsa dake cikin gurinsu ya bude ya shiga ya zauna bakin katifarsa a nutse ya kunna wayar ya shiga yi mata binkice, babu wasu tarkacen numbobin maza a ciki yaji dadin hakan Number Alhaji Nura ce kawai itama yana ganinta ya gogeta yana tsaki! yana kokarin kashe wayar text ya shigo.


Da sauri ya shiga yana dubawa, text ne daga Alhaji Nura ga abunda yake cewa.

_Gimbiyar mata kinyi shuru baki bani amsa ba kuma nasan kinga messengers d'ina Sa'ida ko kuma na cire tsammani ne.?_

Ya dinga wani irin huci! kibiyar kishi na sukar sa a ma'kogwaro a duniya nan bashi da babban wanda ya tsana kamar mutumin nan.


Hannu na rawa ya fara bashi amsa kamar haka.

_Alhaji kayi hakuri fa ban san amsar da zan baka ba shiyasa kaji nayi maka shuru to amma yanzu tunda ka tsananta inso na tabbatar maka da cewa ina da miji zamuyi auran zumunci da 'Dan uwana Khalid saboda haka dan Allah ka daina bibiyar rayuwata haka._

Tura masa text din yayi ya kashe wayar, fulas din abincin sa ya janyo ya bude a nutse ya fara ci bayan ya kammala ya dauki pure water guda yasha ya mike ya fita da wayar a hannunsa


Har yanzu tana kwance a tsakar gidan.....a jiye mata wayar yayi a kusa da ita ya juya da niyyar barin gurin shawara ya sanja ya dawo a da baya.

A hankali ya tsuguna gabanta 'kasa-'kasa ya shiga kiran sunanta.....mafarkinsa take gashi wai suna kwance a gado d'aya sun lullu'ba da bargo suna wasu abubuwa masu dad'in gaske, kawai ta dinga jin sautin muryarsa a kanta yana kiran sunanta.


A firgice ta mike zaune tana zazzare ido a kansa "Khalid me kakeyi anan gurin."? bakinta na fara tayi maganar tana dudduba jikinta addua take Allah yasa mafarkinta ba gaskiya bane.


A tausashe yace." Babu abinda nake ban jima da shigowa ba na ganki a kwance ke kad'ai aunty Sa'ida akwai sauro ki tashi ki koma a d'aki."


Shuru tayi masa ta mike da sauri ta fara kwashe kayan shimfid'ar sai ya shiga taimaka mata suka kwashe kayan shimfid'ar a tare, duk shige da ficen da suke Gwaggo nacan tana shirgar baccinta.


Fitowa tayi da niyyar kama ruwa, kawai sai ta ganshi a tsaye a jikin bango(Garu) gabanta ya fad'i! tai saurin dauke kanta hannunta ri'ke da buta ta nufi bandakin.


Koda ta fito yana nan tsaye a inda yake......Sai tasha jinin jikinta cikin sauri tayi nufin shiga dakin ya tare mata hanya...... shuru tai tana kallonsa yasa kirjinsa ya danne nata sai ta jingina jikin bango(garu) bata so tayi magana jama'ar gidan su tashi in banda Kawu Iro babu wanda zai yarda da ita Ummatu da Gwaggo zasu ce sharri tayi masa.

Yasa hannunsa ya zagaye 'kugunta dashi sosai ya matseta a kirjinsa yana sakin wani irin nishi kafin yayi magana da wani irin voice "Auntyna dan Allah ki taimaka ki bani bakinki nasha kinji ko."

Shuru nayi masa ya dinga wasu irin sambatu yana ya mutse min jikina......"Khalid kafi karfina sharrin ka ya girmi tunani zan had'aka da Allah yayi min maganinka." cikin rawar murya nayi maganar.

Jikinsa na kyarma ya tallafo fuskata a hankali yace."Auntyna kada ki had'ani da Allah idan na lalace kema kin lalace aunty Sa'ida bani da laifi kaunarki ta riga ta gama kassara ni mutukar zan gan ki nakan rasa nutsuwata dan Allah da darajar Annabi Muhammad (SAW) ki amince da soyayyata."


Girgiza kaina kawai nakeyi hawaye bakin ciki da takaici na kwararo min.....Harshensa yasa ya shiga lashe hawayen yana tsotsar kumatuna kokarinsa ya kamo bakina na fuzge fuskata da sauri nasa 'karfi na tureshi yayi taga-taga zai fad'i! da sauri ya fizgo hannuna a lokacin da nake kokarin shiga dakin kawai na jini a kwance a kirjinsa........Bakinsa yasa a daidai kunnena yana sakin wani irin nishi kafin yasa hak'ori ya d'an ciji fatar kunnena da fad'in "Kina so rayuwata ta salanwace ko aunty Sa'ida mutukar baki amshi soyayyata ba zan iya rungumar transformer ta tashi dani na bar duniya."

Ji nayi kamar na shaqe masa wuya saboda takaici na sake yunkurin tureshi ya ri'ke ni gam! gam! yana shanshana jikina tsigar jikina ta dinga tashi............."Kada dai wannan yarinyar bata shigo ba." Muryar Gwaggo ce ta doki kunnuwanmu da sauri muka kalli bakin kofar d'akin hasken torchlight d'inta dalll! da alama fitowa tsakar gidan take kokarin yi da sauri ya sake ni yayi gaggawar shiga gurinsu, ni kuma jikina na rawa na d'auki butar dake ajiye a bakin kofa....ta fito daga dakin tana surutai gani na yasa ta dauke kanta ta nuna kamar bata damu ba nima bance mata komai ba na mika mata butar ta ta kar'ba da sauri na shige dakin ita kuma ta nufi bandaki...




*Masoya a takaima da sharing????*



*IDAN KINA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE....VIP GROUP #600 NORMAL GROUP.... #300.....ACCOUNT... 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE**GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO?????*



_*Free pege ya kusa 'karewa kuyi maza ku hanzarto domin ku biya kudin karatu?????? Masu tambayata na turo musu littafin su biya kudinsu sai a sasu a gruop?? Sannan dan Allah masu plashing su bari! idan kin san ba siyan book d'in nan zakiyi kada ki dauki number ta kiyi min magana dan Allah mu muntuna junanmu???? Masoya masu kaunar cigabana ina sauraranku fa???? Free Pege ya kusa 'karewa ku hanzarto!!!!*_



*10*
Na jima kafin bacci ya dauke ni. Da safe kuma na tashi da wata irin kasala da damuwa dan ina idar da sallar asubahi ko hijabin jikina ban cire ba na kwanta kan daddumar. idona kawai na rufe ba don nayi bacci ba sai dan tunanin yanayin rayuwa hakika abunda ya faru tsakanina da Khalid ya tsaya min a raina na rasa yanda zanyi na tunkari gwaggo da maganar gashi ina jin kunyar Baba Iro na ce masa d'ansa yana min me? al'amarin da akwai nauyi da kuma kunya idan ya yarda to na tabbata Gwaggo da mahaifiyarsa Ummatu ba zasu yarda ba zasu ce nai masa sharri ne, amma haki'kanin gaskiya lamarin da akwai ban tsoro da firgici a ciki ina tsoron ranar da zai samu galaba akaina to kuwa tun kafin zuwan ranar gwara na nemawa kaina mafita.

Idona a rufe na soma jin 'kaurin maganin jiya a hancina. da sauri na bude idona na mike zaune ina kallonta tana tsaye a kaina da 'karamin kasko a hannunta tana turare ni haya'ki.

Da saurin gaske na miqe dan har sai dana bugeta waje na fita na tsaya a tsakar gida ina mayar da numfashi wani irin jiri da ciwon kai ne yake taso min.

Fitowa tayi da haya'kin tana fad'in "Sai dai idan waje zaki fita amma duk inda zaki shiga a gidan nan sai na turara miki haya'kin nan dan ba zanyi asarar kudina a banza ba."


Ido jawur na kalleta tana sake kusanto inda nake da haya'kin nace."Gwaggo Kina so 'bakin cikin ku ya kasheni ko."? Shuru tayi min ta cigaba da turo kaskon haya'kin inda nake.


Takalma na nasa da sauri na kama hanyar fita daga gidan kamar wata zararriya. tace."Au! futar zakiyi kuwa."? ko kallonta banyi ba nasa kai na fita daga gidan.


Karo muka buga a lokacin da yake kokarin shigowa hannunsa rike da wata k'aramar bakar leda.

Yanda yaga jikinta na rawa yasa yayi saurin rike hannunta a nutse yace."Aunty Sa'ida ina zaki da sassafe haka? yau asabar babu makaranta."

Zuciyata ta karye na daure ban bari hawayen sun zuba ba nace."Khalid Sake ni." Girgiza kansa yayi a tausashe yace."Ba zan sake ki ba aunty dan na lura bakya hayyacinki."

Ido na tsira masa shima ya tsira min nasa, a haka Baba Iro ya shigo ya same mu....Gyaran muryar da yayi itace tasa muka ankara da shigowarsa yace."Lafiya na ganku a tsaye a soro."?

Hannuna dake cikin nasa ya sake ri'kewa yace."Baba da alama babu lafiya dan nima nazo shigowa mukayi karo da ita zata fita a gigice.''


A nutse ya kalleni da fadin"Sa'ida me yake faruwa ne.''? Hawayen da nake kokarin dannewa suka kucfe nace ."Kawu maganar dai guda d'aya ce."

Yace."Gwaggo ce ko.''? kaina na d'aga nace"Eh tun jiya ta hanani zaman lafiya a dakinta tace aljanu ne dani kawai yanzu ina kwance na ganta a kaina tana bunka min haya'ki."

Baba Iro ya shiga girgiza kansa yana mamakin halin rigima irin na mahaifiyarsa. yace."Sa'ida kiyi hakuri kinji ko mu shiga gidan za'a sasanta."

Nace."Kawu nifa idan ba haya'kin nan ta daina bunkawa ba ba zan shiga dakinta ba."

Khalid yace."Muje duk inda haya'kin yake zan daukeshi na yar dashi."
Jin abinda yace yasa na yarda muka shiga gidan a tare.

Suna tsaye ita da Ummatu suna magana......"Wallahi ajanu ne da ita gashinan daga jiya zuwa yau duk ta kasa nutsuwa sakamakon turaran da nake mata kinga yanzu tayi waje a gigice." Ummatu tace."To ai kuwa tunda dai an gano bakin zaren sai a cigaba da nema mata magani.....shigowarmu yasa duk suka kallemu.

Khalid kai tsaye dakin ya nufa yana neman maganin Gwaggo kamar ta sani ta dauka ta bawa Ummatu ta 'boye mata....Kawu Iro yace "Gwaggo wannan wace irin rayuwa ce dan Allah ya kike nema ki furgita yarinya kina cewa tana da aljanu a ina suke? Gwaggo na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login