Showing 3001 words to 6000 words out of 185789 words
maganar a barta haka."
Murmushi kawai nayi na mike tsaye ina ninke dadduma, ta mika min pose din nata da fad'in "Kar'bi ki adana min kada ya shigo ya sake daukar min kudi." karba nayi na bude gurin da nake ajiye tufafina nasa key na kulle..........Da yake idan mun dauki albashi duk abinda nake bukata naci da sha dana d'aurawa ina siyan abina na ajiye duk ranar da akayi abinda bana ra'ayi sai nayi girkina naci na koshi, fita nayi tsakar gida na dauko doya a kicin na zauna tsakar gidan ina feraye wa.
Fitowa tayi daga dakin da buta a hannunta Gwaggo duk rintsi bata bari yara suyi mata wasa da butar alwalarta kullum butar ta cike take da ruwa Macace mai tsafta da kula da ibadah dama dan adam tara yake bai cika goma ba, ganin ina feraye doya yasa ta washe baki da fad'in "A lallai kice yau dadi zamu ci a gidan." Murmushi nai ina kallonta gwaggo akwai kwadayi amma bata yarda ta fitar da kudinta ta siyi abinda take so ba.
Nace"Eh lallai doya da kwai zan soya nayi miyar alayyahu saboda haka ke zaki bayar da kudin 'kwai dan banda kudi." shuru tayi tana kallona dariya ta kusa ta su'bce min.
Tace." Inji dai guda biyu zai isa." Nace"Haba gwaggo a wannan uwar doyar za'a sa 'kwai biyu guda biyar zaki siya." tace"Haba Sa'ida 'kwai biyar nawa kenan."? kai tsaye nace"Dari uku da hamsin." shuru tayi tana nazari kafin ta girgiza kanta tace"Bari dai nai sallah muyi maganar haba Jama'a yanda rayuwa nan tayi wahala kice 'kwai biyar ina laifi biyu ko uku."
Bin ta nayi da kallo ina k'unshe dariya gwaggo kenan mai kwad'ayin tsiya.......Hayaniyarsu naji yo daga waje kafin nayi wani yun'kuri sun shigo gidan su uku, babu walwala na daga kaina ina kallonsu su biyu suna sanye da kayan 'kwallo (ball) mayar da kaina kasa nayi na cigaba da abinda nake naji yace."Salim ku jira ni nasa kayana na fito." Suka ce okey kayi sauri dan Allah." cikin zuciyata nace "Aikin kenan." " Aunty Sa'ida barka da Yamma." a nutse nace" Barka Salim ya kuke." ya d'an sosa kansa yana mirmushi yace "Lafiya aunty muna fatan kina lafiya." " Lafiya Kalau nake." shuru gurin yay na minti biyu na dago kaina kawai sai naga sun zuba min ido! cikin 'bacin rai nace"Salim kaima ka fara zama mara kunya ko."? da sauri yace."Aunty mai ya faru."? girgiza kaina nayi nace"Kuje waje gashinan fitowa daga yau kada ku sake shigowa gidan nan tunda duk kun zama baligai."
Wannan magana da tayi a kunnasa ya karaso gurin yana mata kallon daya saba "Akan me zaki hanasu shigowa gida abokaina ne na 'kuruciya kin sansu kin san iyayensu kuma iyakacinsu nan bakin 'kofa ko wani yayi miki abinda bai kamata ba."
Nace"Khalid na hanasu shigowa gidan nan saboda bai kamata ba su tsaya a waje ka fito ka samesu." Girgiza kansa yayi yace." Keda Gwaggo babu nauyin auran kowa a kanku meye dan abokaina sun shigo kike fita kina yawo a titi gardawa na kallonki a ofis d'inku na malaman makaranta akwai baligan da suka ci uwar abokaina a kuyanci kike mu'amula dasu baki damu ba sai dan kawai abokaina sun shigo gida kice su daina shigowa ba zai yiwu ba."
"Khalid ni kakewa rashin kunya."? ba tare daya kulani ba yace." Salim ku muje dan Allah.'' gaba yayi suka rufa masa baya, girgiza kaina nayi aikuwa zan samu Baba Iro da maganar dole ya tsawatar musu akan su daina shigowa mutane gida kai tsaye.............
*Masoya a taimaka ayi min sharing??????*
*IDAN KINA BUKATAR KI BIYA KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE NORMAL GRUOP#300 VIP GRUOP#600 ACCOUNT.....0542382124....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE**GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO?????*
*3*
Motsin fitowarta daga band'aki yasa nai saurin kallon gurin, asuwakin ta dake kan taga (window) ta dauka tana gyarawa tace"Surutun me nake ji ne ina bandaki naji kamar muryar Khalid kuna sa'insa." shuru nayi mata saboda nasan ko na fada mata dalili bai zama lallai ta bani gaskiya ba, zama tayi kan kujera 'yar tsuguno tana kokarin sanya asuwakin a bakinta tace."Sa'ida in dai akace wannan namiji ne to komai 'kan'kantarsa jagora ne idan kina hantarar Khalid wani sa'in haushi kike bani dan duk 'kan'kantarsa da kika raina watarana shine zai jagorance ki." Kallonta nayi ina mamakin maganarta "A'ina Khalid din zai jagorance ni gwaggo dan Allah idan zaki fad'i magana ki dinga tsayawa kina tunani kafin ki fad'a yaro 'kan'kani kina maganar zai jagorance ni Khalid mai ya sani a rayuwa."?
Tana goge bakinta da asuwakin tace"Oho! ni dai na fad'a miki gaskiya ki daina raina Khalid da 'kan'kantar shekarunsa komai girmanki ba gagararsa zakiyi ba." Cike da bacin rai nake kallonta, ta d'auraye asuwakin ta ajiyeshi a gefe cikin nutsuwa ta fara d'aura alwala.
Kaina na girgiza ina jin tamkar zuciyata ta tsage saboda 'bacin rai gwaggo ta iya kuntukawa mutum abin haushi tayi kamar ba tayi ba, tabbas da wata ko wani ne yayi min wannan banzar magana wallahi sai nayi masa rashin mutumci amma da yake itace babu yanda na iya da ita dole nayi hakuri dan idan nace zanyi magana zata iya yanko wata maganar da zata tarwatsa min zuciya amma idan ba haka ba me zanyi da Khalid bayan manyan mazan dake sona a waje.
Sai da na daidaici cewa ta idar da sallahr na shiga dakin, tana zaune kan dadduma cikin hijabi da carbi a hannunta tana ja, ka'ida ne dama idan ta idar da sallar la'asar sai tayi zaman lazimi nace" Zan dauki kudin 'kwan a Pose d'inki."
Kanta kawai ta d'aga min na bude sif din na dauko pose din nata na zuge! gudar dari biyar na dauka na mayar da sif din na rufe...... fita nayi domin na samu yaron aike cikin ikon Allah na hango almajirin gidan Alhaji Nura ni'ki-ni'ki da kayan miya a hannunsa, da sauri nace"Sule dan Allah siyo min 'kwai kantin Dauda." da sauri yace."To aunty Sa'ida." kudin ya kar'ba ya tafi na juya da sauri na koma cikin gidan, Ummatu na samu ta fito daga gurinta tana d'auraye kwanuka. sannu nayi mata ta amsa ciki-ciki. wucewa nayi ciki ina girgiza kaina na rasa abinda na tsarewa Matar kwata-kwata bata kaunata duk abinda takeyi min a gidan na ganin ido ne.
Har yanzu Lazimin take sai kawai na shiga kwashe kayan wanke-wanken dake dakin na kaisu bakin rijiya na ajiye,
Wani irin kallo naga tana bina dashi kafin ta shiga bin kayan wanke-wanken da kallo tace"Sa'ida dan wulakanta abinci shine kika fito da abinci kika zuba masa ruwa idan bakwaci ai sai ku bawa almajirai shima wanda yake kawowa yana shan wahala kafin ya samo ya kawo amma na lura daka ke har Gwaggon bakwa tausaya masa."
Jikina a sanyaye nace"Wallahi na manta ban duba ba na zuba ruwa akai kin san ni bana cin d'anwake shiyasa to ban san abinda ya hana Gwaggo cin nata ba."
Da sauri tace"To yaya kuwa za'ayi taci bayan taga kina feraye doya ai ba zataci ba ni banta'ba ganin kwad'ayayyiyar mata irin wannan ba."
Kallonta nayi ina mamakin maganarta tsaki taja ta cigaba da aikinta, Gwaggo ta bankad'a labulen d'akinta ta fito tana fad'in" Surutan me nakeji ne nifa bana san husuma a gida." Ummatu aikinta ta cigaba dayi bata tanka mata ba nace."Gwaggo babu wata husuma da zata faru ki koma d'aki.
Tace."Ummatu naji kamar kina maganar d'anwake ko."? Tace."Eh hakane Gwaggo Sa'ida ta fito dashi naga ko d'aya baku ci ba shine nake mamakin hakan ai da kun san ba zakuci ba sai kuyi min magana na rage garin."
Tace."Au!! Sai na fada miki ? Rabi tuntuni fa kin san ni D'anwake bai dame ni ba me zai sanya ki dimanci yi mana shi a gida." Da sauri tace."To gwaggo shi aka bani akace na sarrafa shi Maigidan daya kawo shi zakiyi wa wannan maganar." Gwaggo bakinta ta ri'ke tana jijjiga kanta
Ganin al'amarin na nema ya girmama yasa na shiga basu hakuri....Ummatu kwanukan ta ta dauka ta shige gurinta, Gwaggo ta zungura mata bakinta tanai mata yen-yen! da hannu. Dariya ce ta kusa ta su'bce min ta ri'ke hannuna 'kasa-'kasa tace"Rabu da ita Sa'ida 'bakin ciki takeyi ganin kin yanka doya zaki soya tunda ta fito da hassadarta a fili ko d'and'ane kada ki bata mu cinye kayanmu." Tsabar dariyar dake cina ta hanani bude baki nai mata magana da sauri na tsuguna domin wanke kwanukan. ta cigaba da magana 'kasa-'kasa! nace "Dan girman Allah gwaggo ki tafi ki zauna a daki kada taji wata magana ranta ya 'baci matar nan iya 'kokari tanayi dake duk wata rashin kunya da takeyi miki kece kike janyowa kanki."
Tsaki! taja tace"Kinga na bar maganar yanzu ina canji na na 'kwai ina lazimi naga kin dauki dari biyar."
Ina kokarin bata amsa Sule ya shigo! sai ta hau washe bakinta tana kallon ledojin hannunsa dan ta dauka Alhaji Nura ne yayo aiken daya saba.......Yace."Aunty Sa'ida gashi." Kar'ba nayi nace."Nagode Sule." ya juya ya fita daga gidan bayan ya gaisheta...ta kalleni da fadin" Ganin ledoji a hannunsa Wallahi na dauka aike ne Alhaji yayo mana." shuru nai mata na cigaba da wanke-wanke na sai ta bar gurin tana surutai irin wanda ta saba.
Ina daf da kammala soya doyar ya shigo gidan jikinsa bud'u-bud'u! d'auke kaina nayi ciki-ciki na amsa sallamarsa, bece min komai ba ya nufi bakin rijiya ya cika bokiti da ruwa yana wanke jikinsa, kamar wacce akace d'ago kanki ki kalleshi naga jikinsa jagab! yana kokarin cire rigar jessi d'in jikinsa cikin gaggawa na kauda kaina daga kansa gabana ya dinga faduwa ganin yanda gajeran wandon jikinsa ya ji'ke jagab dik ya manne masa a jiki girmansa ya fito sosai...... zama yayi bakin rijiyar ya cigaba da wanke jikinsa sam babu wata damuwa a tare dashi.
Har ya gama abinda yake a gurin ban sake kallonsa ba ta gefan idona naga tashinsa daga gurin, ajiyar zuciya na sauke cikin zuciyata nace"Khalid Allah ya shiryar da kai hanya mai kyau.
Bayan na gama sai na d'ora ruwan wanka na d'auki fulas din doyar na nufi daki dashi ,karo muka buga da ita tace."Yawwa gwanda da da kikayi kika gama magariba tayi nima yanzu alwala zan d'aura."
Ajiyar zuciya kawai na sauke na bata hanya ta wuce na shiga dakin fulas din hannuna na ajiye na fito domin nima na daura alwalar.
Sai da nayi wanka tukkuna na samu sukunin zama naci soyayyar doyar. lokacin ita Gwaggo har taci ta koshi ta kishingida tana saurarar redio, zaune ta mike tana gyara daurin dankwalinta tace"Sa'ida badan hali Rabi ba kisa mata biyu a plate a miqa mata ta mayar da yawu."
Nace."Aiko baki fad'a ba dama sai an bata hakkinta." komawa tayi ta kwanta tana sake gyara ma daidaicin fulas din dake gabanta.
Nace"Wannan fulas din na gabanki meye a ciki."? Tace."Doya ce na ajiyewa Khalid saboda nasan yana san doya da kwai shima."
Karamin tsaki naja nace"A maimakon ki ajiyewa Kawu sai ki ajiyewa wani Khalid Baba Iro shi yafi cancanta ki ajiyewa doya ba wannan yaron ba."
Tana gyara redion ta tace."Khalid nayi niyyar ajiyewa doya saboda haka sai ki shafa min lafiya." Ta'be bakina nayi a nutse na fara cin doyar dake gabana ina had'awa da lemo.
Labulan d'akin ya d'aga yana magana, tayi saurin mi'kewa zaune da fad'in "Yawwa yaro nagari shigo kaci doya da kwai da zafin ta."
Baiyi niyyar shiga dakin ba amma ganin mutuniyarsa cikin 'karamar shart irin ta shan iska yasa ya shiga dakin ya zauna suna fuskantar juna....fulas din ta tura gabanshi da fadin" Gashinan da zafin ta dan bata jima da gama soyawa ba."
Girgiza kansa yayi yace."Bana bukata." da sauri na kalleshi ina mamaki! nasan halinsa da kwadayi dole shima zaiyi sha'awar doyar amma kai tsaye yace baya so."
Gwaggo jikinta ne yayi sanyi tace"Saboda me ba zaka ci ba." Babu walwala a tare dashi yace."Gwaggo daga ranar dana cigaba da cin abincin Aunty Sa'ida zata cigaba da raina ni daga yanzu mutukar abu nata ne a gidan nan to kada ki ajiye min idan ina bukata zan siyo da kudina."
Tace."Aa wannan ai doyar ce kawai tata amma 'kwai ni na siya da kudina dan Allah ka daure kaci." Girgixa kansa yayi yana duba wayarsa. Yace."Gwaggo bafa zanci ba wallahi koda zan kwana da yunwa kuwa."
Ba tare dana kalleshi ba nace"Kanka ka cuta yaro." Uffan bece min ba ya cigaba da dube-dube a wayarsa.
Nace"Gwaggo ai sai ki ajiyewa Kawu dama shi yafi cancanta da ki kyautatawa ganin irin dawainiyar da yake." cikin jin haushi tace."Ke! banyi niyyar bashi ba haba jama'a kin dameni da wani Kawu to bazan bashi ba ga wanda nayi niyyar bawa tunda yace baya bukata gobe da safe naci kayata."
Shuru nai mata na cigaba da abinda nake, dakin yayi shuru na tsayin minti uku, kaina na d'ago kawai muka had'a ido dashi gabad'aya hankalinsa na kaina ya zuba min shegun idanunsa na fitina.
Nace."Naci maka bashi ne da zaka sani a gaba kana kallona." shuru yayi bai ce komai ba kuma bai daina kallona ba. Girgiza kaina nayi na mi'ke na fita daga dakin na barsu.
Kan tabarma na zauna ina duba waya ta ya fito daga dakin yana sanya takalmansa na kauda kaina....."Aunty Sa'ida." naji ya kira sunana cikin sanyi murya. a nutse na kalleshi, ya lumshe idonsa tare da shafa sumarsa yace."Wallahi kin had'u auntyna duk inda ake neman cikakkiyar mace kin kai duk sanda nazo gida hutu da tsananin sha'awarki nake komawa skull."
Gabad'aya ji nayi yawun bakina ya bushe! na dinga kallonsa ina mamakin tsagerancin sa Murmushi yayi ya had'e yatsun hannunsa yayi heart ?? Ilov u auntyna muuuuhhhh!." ya hura min iskar bakinsa. kafin nayi aune har ya fice daga gidan, kaina na sunkuyar 'kasa gabana ya dinga bugawa sosai al'amarin ya firgitani anya kuwa yaron nan bai fara shaye-shaye ba! ? ni kam ina zan kai kaina da wannan abin kunyar dole sai na tasar masa a tsaye zai daina yi min wannan iskancin, jikina a mutukar mace na mike na shiga dakin na kwanta ina tunanin matakin da zan dauka a kansa..
*Masoya ayi min sharing a groups????*
*IDAN KINA BUKATAR KARANTA LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP GRUOP#600 NORMAL GRUOP#300 ACCOUNT... 0542382124...BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO?????*
*4*
Sa'ida cewa nayi fa ki sawa Rabi doyar nan kada mu wayi gari ta dinga yar mana da habaici kin san dai halinta bata da hakuri." Gwaggo ce ke wannan maganar a lokacin da take kokarin shigowa dakin da buta a hannunta da alama bandaki taje.
Zaune na mi'ke ba tare da nace mata komai ba na fara kokarin bud'e fulas din dake kan tabarmar ta. ido ta tsira min a lokacin da nake zuba doyar tace." Bafa cewa nayi ki kwashe mata ba guda biyu kika sa mata ta isa tunda itama idan tayi soye-soyen ta ba bamu take ba."
Nace."Gwaggo dan Allah abin duniya ya daina rufe miki ido mecece doya da 'kwai tun d'azu duk kin damu kanki."
"Sa'ida kada ki fad'a min magana akan Rabi na lura kema asirin nata ya fara tasiri a kanki ai sai kije ki 'karata ke da ita." shuru kawai nayi mata na fita daga dakin.
Ummatu na zaune a gurinta tana saurarar redio na shiga da sallama a bakina, kallon mamaki ta shiga bina dashi, nace."Ummatu doya ce na kawo miki." Babu yabo babu fallasa tace"To nagode." Kar'ba tayi ta ajiye kusa da ita nace"To sai da safe." kamar bata so tace."Allah ya tashe mu lafiya."
Koda na koma dakin gwaggo samunta nayi har ta kwanta bacci kan gadonta redion ta a kusa da kanta tana saurara Gwaggo bata kashe redio kullum a kunne take kwana shiyasa kullum cikin siyan batir take da daddare idan ta isheni da shuuuuu! zan tashi na kashe amma idan ta farka sai ta kunna alhalin ko wace tasha sun rufe, al'amarin Gwaggo nada wuyar sha'ani.
Da wuri na tashi nayi duk abinda na saba karfe bakwai da rabi na shirya tsaf a gurguje na karya kummalo nayi mata sallama domin tafiya gurin aiki.....Shuru tayi min ba tace komai ba nace."Gwaggo kina ji ina magana ko."? kallona tayi da fadin."Me kika ce."? cike da mamaki nake kallonta nasan sarai taji abinda na fada amma wai tambayata take, ajiyar zuciya na sauke nace."Na tafi sai na dawo." a maimakon tayi min irin adduar data saba sai kawai naji tace."Umm!! juyowa nai ina kallonta nace"Gwaggo ba zakiyi min addua ba."'
"Sa'ida kyaleni dan Allah kije kawai ni da wannan aikin naki gwara babu kullum kina yawo a kan titi zagade-zagade babu mijin aure duk wannan