Showing 21001 words to 24000 words out of 185789 words

Chapter 8 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24194

fatan kin wuni lafiya."?

Tace."Lafiya lau Rabi'u ya Alhajin ina fata dai lafiya dan Allah kace masa muna godiya da hidima." Rabi'u yace."Insha Allah zan fad'a masa."

Yana fita ta karaso inda nake tana fad'in "Kai amma naji dad'in wannan aiken wallahi nasan harda nama da kayan miya a ciki kinga na huta 'batar da kudina.

A nutse nace." Gwaggo wai dan Allah me yasa kike da san abin duniya ne inace d'azu kika gama zagin mutumin nan amma yanzu kinga kayansa duk kin gigice."

"Sa'ida kada ki fad'a min magana mana kin san dai ba zan bar nawa na na za'be shi ba, ni nafi kaunar ki auri Khalid amma da babu maganarsa a tsakani zan baki goyan baya d'ari bisa d'ari ki auri Alhaji Nura domin ya cancanta.''

Nace."Wallahi har mamaki kike bani idan naji kina cewa wai na auri Khalid gwaggo kina tunanin ko maza sun'kare a duniya zan auri wannan yaron........"Shima ba zai aureki ba tsohuwar guzama dake." Muryar Ummatu ce ta katse maganar da nake. duk muka juya muna kallonta....Fuska a murtuke ta karaso inda muke tsaye tace."Sa'ida ke har wata cikakkiya ce da har zaki dinga k'yamatar auran Khalid me kike dashi na matantaka bayan duk kin gama rabawa abokanan aikin ki maza."

Gwaggo tace."Rabi wannan wace irin banzar magana ce."? Da sauri tace."Gwaggo ranar wanka fa ba'a 'boyan cibi ke kin sani kuma kin fad'a da bakinki hakanan kuma jama'ar gari sun sani Sa'ida bata da kamun kai to me zai sanya kice lallai sai Khalid ya aureta."

Rai a 'bace Gwaggo tace."Rabi kada ki 'kara yi mata 'kazafi ni kaf zuriyata babu lalatacce idan Allah ya kaddara auran Sa'ida da Khalid babu yanda zakiyi sai hakuri."


Murmushi takaici tayi tace."Gwaggo sai dai kuwa idan bani na haifi Khalid ba." Tana gama maganarta ta bar gurin tana wani irin huci!

Ido jawur! na kalleta nace."Kinga abinda kika janyo min ko."? ''Kinga Sa'ida rabu da Rabi bata da cikakken hankali kuma wallahi sai na fad'awa Ibrahim ayi muku tsakani da ita kada ta 'kara jifanki da mummunar kalma."

Nace.''Gwaggo da Ummatu ba taji kina fad'a min haka ba to ba zata fad'a ba tun farko ke kika nuna kina zargina da iskanci a gurinki taji gashinan kin janyo min cin mutumci."

Tace."Kiyi hakuri na fad'a miki zan had'ata da Ibrahim zata gane bata da wayo." nace"Gwaggo kada ki had'ata da mijinta a kaina ki kyaleta kawai ni zan yanke hukunci da zakuyi farin ciki."

Tace."Sa'ida wane irin hukunci zaki yanke."? Murmushin takaici nayi nace."Idan na yanke zaki gani." barin gurin nayi naje ina duba abinda yake cikin ledojin .....kayan tea ne komai da komai sai uban kayan miya da nama mai yawan gaske a cikin wata katuwar takarda.
Kallonta nayi nace.'' Kinga nayi wanki na gaji ba zan iya dukan sakwara ba zan dafa miki ita kawai kici da miya."

Tace."To shikkenan had'a kayan miyan ni da kaina sai na miqa markad'an gidan Lubabatu." Mi'kewa nayi na dauko d'an maidaidaicin baho da wuka na zauna ina gyara kayan miya ta nufi daki tana fadin" bari na 'karasa d'an abinda nake kafin ki gama."



To duk k'ulafucin Gwaggo ba taci doyar da yawa ba duka -duka uku taci ta ajiye wa mutumin nata miya cikin silba duk ta kwashe masa naman 'kyaleta kawai nayi domin ni nasan abinda na shirya mata.

Ganin tana gyangyad'i nace."Gwaggo ki gyara kwanciyarki mana." Da sauri ta bude ido tana kallona tace."Ina jiran Ibrahim ya shigo ne shiyasa ki kaga bankwanta."

Nace."Gwaggo Ummatu ni ta ciwa fuska kuma gani tayi ki nayi min saboda haka dan Allah kada kice zaki fad'awa mijinta ki had'asu." Ta'be bakinta tayi tace."Ai sai kiyi Sa'ida Sai fa na fad'a masa fa Ummatu zata san da ni take zancan."
Shuru nai ina kallonta.........ta cigaba da gyangyadin tana nema ta tintsira nace."To ki kwanta idan ya shigo zan tashe ki." Ajiyar zuciya ta sauke tace."To mi'ko min fillo na d'an matse." da sauri na mi'ka mata ta kwanta tana kiran sunan Allah.

Shuru dakin yayi na tsayin minti goma sha biyar na tabbatar tayi bacci na mike a tsanake nasa hijabina jakar dana san na had'a dukkanin kayana na dauka a hankali na fita daga d'akin.......Kai tsaye babban titi na nufa ina addua a kan Allah yasa ina fita na samu adaidaita sahun da zai kaini hotoro gidan Mahaifiyata......




*Masoya a taimaka da Sharing????*



*IDAN KINA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE....VIP GRUOP#600 NORMAL GRUOP#300.....ACCOUNT...0542382124.....BINTA UMAR GTBANK...IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER.*
*07084653262*
*08089967176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO?????*



*12*
Cikin ikon Allah ina tsayuwa a bakin titin wani adaidaita sahu ya tsaya a gabana. "Hajiya ina zakije."? Ya fad'a yana dan le'ko da kansa. Da sauri nace."Hotoro zaka kai ni." Jim yayi kafin yace."Okey to nawa zaki biya."? 'Kugin da naji a bayana yasa nai saurin juyawa Khalid ne da Salim cikin a daidaita sahu suna kokarin shiga layin....Da sauri na dauki jakata na fad'a babur da fad'in "Muje ko nawa ne zan baka." babur din ya buga da sauri muka bar gurin....Sai da naga munyi nisa sosai hankalina ya kwanta a nutse na fito da wayata daga cikin jaka number ta na shiga nema inaso na sanar da ita cewa gani nan a kan hanya.

A tsanake muka gaisa nace."Umma gani nan a kan hanyar zuwa." Tace."Da daddare nan Sa'ida ina fata dai lafiya."? Cikin rauni nace."Lafiya Umma." Ta amsa da to "Alhamdulillahi sai kin 'karaso." Kashe wayar nayi nasa a jaka kana nayi saurin sa gefan hijabina na goge hawayen da ya fara zuba a fuskata.


Cikin magagin bacci ta tashi tana lalu'ben torchlight d'inta ta kunna tana haske d'akin da fad'in "Sa'ida Ibrahim din be shigo bane."? Shurun da taji yasa tayi saurin kallon inda take kwanciya taga wayam! sai tai zargin ko tana bandaki redion ta ta dauka ta fara kokarin kunnawa wasu tashoshin sun rufe da kyar ta lalubi freedom redio lokacin suma daf suke da rufewa. kimanin minti goma tana zaune ba taji motsinta ba sai ta mike ta fito bakin band'akin ta tsaya tana kiran sunanta. shurun da taji yasa gabanta fad'uwa tana kokarin barin gurin ya shigo gidan ganinta a tsaye a bakin bandaki yasa yace." Gwaggo lafiya me kike anan gurin."?

Murya na rawa tace."Khalid Sa'ida bata gidan nan.'' gabansa ya fad'i da sauri yace."Gwaggo bangane bata gidan nan ba." ? Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin barin gurin tace."Jeka kira min babanka idan ma yayi bacci ka taso shi.''

Khalid da sauri ya nufi gurin nasu itama ta nufi dakinta tana haske haske da torchlight nan taga babu jakar kayanta sai ta sake karaya a sanyaye ta zauna kan shimfid'arta tana fad'in "Wannan yarinya bata da hankali ashe."

Baba Iro da Khalid suka shiga dakin a tare......Tace."Ibrahim matarka ta tunzura Sa'ida ta had'a kayanta ta gudu."

Kawu Iro yace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."? Fashewa tayi da kuka tace."Iro d'azu Rabi ta zauna ta 'karewa Sa'ida cin mutunci tana kiranta da Karuwa tsohuwar guzuma saboda kawai ina maganar auransu da Khalid shine fa ta fito tayi mata wannan cin mutuncin a cewarta wai d'anta ba zai auri lalatacciya ba wannan dalilin ya fusata zuciyarta ta had'a kayanta ta gudu."

Baba Iro yayi shuru yana jimanta al'amarin! tace."Yanzu ni babban tashin hankalina da damuwa ta inda ta nufa a cikin daran nan."


Yace."Gwaggo hakika raina ya 'baci da wannan al'amarin kuma duk irin hukuncin dana dauka akan Rabi kada kice don me ta riga ta gama fusata ni ace wai 'yar d'an uwana na jini take kira da Karuwa."

Gwaggo tace."Ibrahim ba zan hana ka ka dauki mataki akan Rabi ba domin ko baka dauka ba ni zan dauka ba zata dinga la'antar zuria ta ba."

Yana kokarin fita daga d'akin Khalid ya dafa kafad'arsa a tausashe yace."Baba kada ka yanke hukunci cikin fushi Annabi ya hana."


Rai a 'bace! yace."Saboda mahaifiyarka ce ko? yanzu kai a tunaninka abinda ta aikata tayi daidai."?

Kansa ya girgiza a sanyaye yace."Nima banji dadin al'amarin ba amma dan Allah kayi hakuri." Ba tare da yace masa komai ba ya bar gurun.


Khalid dakin ya shiga jikinsa duk a mace babu shakka yasan wannan hargitsin dake faruwa shine sila da baya shiga sabgar auntyn nasa da mahaifiyartasa ba zata samu hanyar zaginta ba.

Number ya nemo a wayarsa ya fara kira, Gwaggo tace."Yawwa dama yanzu zance ka kira ta a waya mu ta fad'a mana inda ta nufa duk da dai nasan watakila tana can gurin uwarta mai hure mata kunne."


Jin wayar tana shiga yasa da sauri ya d'aga mata hannu. shuru tayi tana kallonsa, wayar ta 'karaci ringing ta katse bata dauka ba.

Hannu na rawa ya sake kira nan ma babu amsa Khalid ya dinga kiran wayar tana katsewa ya kai sai goma, jiki a sanyaye ya kalleta da fad'in "Gwaggo aunty Sa'ida tayi zuciya taki daukar wayar."

A sanyaye tace."Khalid dole tayi fushi! bayan fitarka Uwarka sata tayi a gaba taci mutuncinta ta dinga zaginta tana kiranta karuwa." Tana share hawaye take maganar ta cigaba da cewa"Wai yau zuria ta Rabi takewa wannan cin mutuncin."

Yace."Gwaggo idan Ummatu tana da laifi kema kina dashi kada fa ki manta irin takura mata da kikeyi Gwaggo keda Ummatu kune kuka kori auntyna Sa'ida daga gidan nan."

Shuru tayi tana share hawaye tace."Dan Allah sake kiran wayar ko zata dauka idan kuma bata daga ba ka kira wayar uwartata idan kana da number ta."


Yace."Ni bani da Number Ummah Habiba amma bari na sake kira naji ko zata dauka...sake kiran wayar yayi har sau biyu babu amsa, ya sauke nannauyan ajiyar zuciya yana tunanin yanda za'ayi......."Khalid ka fito kaje gidansu abokinka ka kar'bo mukkulin adaidaita sahunsa ka kai ni babban gida.'' Muryar mahaifiyarsa ta katse masa tunani.

Da sauri ya mike ya fita sai ya ganta a tsaye da hijabi a jikinta. agogon dake daure a hannunsa ya duba sha d'aya shaura yace."Ummatu me zakije kiyi a babban gida da daddare haka."

hawaye ta share tace."Babanka ya kore ni a gidan wai naci mutuncin 'yar d'an uwansa har ta gudu sabida haka nima ba zan kwana a gidan ba.''


Khalid jikinsa yayi bala'in mutuwa da saurin ya jingina jikin bango (garu) Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un ya shiga kira yana jimanta masifar dake kokarin kunno musu....Gwaggo kuwa tana cikin dakinta a zaune tana jin duk abinda ke faruwa ko gezau ba tayi ba tana zaune babu abinda ya dameta.

Yace."Ummatu ba zaki je ko'ina ba ina zuwa." da sauri ya nufi gurin nasu hankalinsa duk a tashe.....a kwance ya samu mahaifin nasa a tsakar gidan ya tsuguna gefansa hade da fad'in "Baba dan Allah kayi hakuri matakin daka dauka akan Ummatu bai dace ba."

Hannu ya d'aga masa rai a 'bace yace."Khalid tashi ka bani guri bana bukarar jin wata magana daga gareka, Rabi ta kaini karshe kuma dama ba tun yau ba nasan da cewar bata kaunar yarinyar nan Sa'ida alhalin abinda yayi ubanta shi yayi ni mu biyu kacal iyayenmu suka haifa muka haifeku me zai sanya ta d'orawa yarinya karan tsana akan wane dalili? ita ko tausayin maraicinta ba tayi to shikkenan yanda tayi sanadin barinta gidan itama sai ta barshi idan kaga mahaifiyarka ta dawo gidan nan to ka tabbata cewa Sa'ida ce ta dawo."


Khalid jikinsa yayi sanyi yace."To Baba dan Allah kayi hakuri dare ne yanzu ka bari da safe kome zai faru sai ya faru." cikin tsawa! yace." Khalid ba zaka tashi ka bani guri ba."?

Mikewa yayi ya fita daga gurin ransa a tsananin 'bace...Babu Ummatu a gurin da sauri ya le'ka dakin Gwaggon yana tambayarta tace itama bata san inda take ba, fita yayi da saurin gaske.

Can ya hangota tana tafiya yabi bayanta da sauri yana kiranta, tsayawa tayi ya karaso gurin yaga tana share hawaye yace."Ummatu kiyi hakuri dan Allah ki daina kukan nan bari na shiga gidansu Salim d'in na kar'bo key din."

Kanta kawai ta d'aga masa zuciyarta na tafarfasa tunda tayi aure tsayin shekara ashirin da biyar wani sa'bani mai muni bai ta'ba shiga tsakaninta da mijinta ba, sai gashi yau akan Sa'ida yarinyar tayi sanadin da mijinta ya koreta daga gidan auranta.

Khalid ya karaso gurin cikin adaidaita sahun a sanyaye ta shiga ta zauna yaja babur din suka tafi.

Sai da suka hau titi sosai ta sauke ajiyar zuciya da fad'in "Khalid kaga irin tozarcin da mahaifinka yayi min akan Sa'ida ko."?


Yace." Ummatu kiyi hakuri amma kema mai yasa kika zageta ki ka kuma yi mata kazafi na zina."

Cikin 'bacin rai tace."Ai ba sharri nayi mata ba gaskiya na fad'a me yasa kun san gaskiya amma gabad'ayanku kuke kareta ni nasan Sa'ida mazinaciya ce."

Yaji kansa ya sara! gumi na yanko masa yace." Ummatu zuciya takan dauki zafi a duk lokacin da zaki jefi Auntyn Sa'ida da wannan kalmar wallahi ita d'in kamila ce bata bin mazan banza a waje."


Tace."To shikkenan tunda kana jin zafi sai ka dauki mataki a kaina kamar yanda ubanka ya dauka wallahi Khalid mutukar ni na haifeka to ba zaka auri Sa'ida ba dan duk na gane take-taken ka."


Shuru yayi wani irin gumi! yana tsatstsafo masa .

Tace."Idan ka bijirewa umarnina ka auri yarinyar sai nayi maka baki ka lalace gwara tun wuri ka cireta daga cikin zuciyarka."


Murya na rawa yace."Ummatu me yasa kike wannan maganar me yasa kika dauki zafi da al'amarin nan kada kiyi min haka dan Allah aunty Sa'ida itace farin cikina."

Tace"Humm! dama abinda nake so na gazgata kena gashinan kuma ka furta da bakin ka saboda haka daga yau sai yau na rabaka da yarinyar nan wallahi tallahi ka sakeyi mata magana Allah ya isa."!

Ji yayi kansa yana juyowa kan babur din na nema ya kufce daga hannunsa da kyar ya aro dauriya yasa a ransa ya cigaba da driving din yana nanata kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.!


"Hakika Sa'ida banji dad'in wannan abubuwan da suke faruwa da rayuwarki ba amma kuma bai kamata ki yanke wannan hukuncin ba dalili kuwa shine kin san halin Gwaggo baud'ad'd'iyar macace zata iya zargina kan cewa ni nake zugaki ki bijire musu."

Ajiyar zuciya na sauke a raunane nace"Umma wallahi hakuri na ya 'kare a gidan nan dan saboda bana so watarana su tunzura zuciyata na fad'a musu magana mara dad'i shiyasa kawai na yanke wannan hukuncin."

Girgixa kanta tayi tace."To shikkenan ai Allah yasa hakan shi yafi alkairi bari da safe sai na shedawa Alhaji halin da ake ciki idan yaso duk hukuncin da ya yanke miki sai kiyi hakuri dashi."


A sanyaye Nace."Tom shikkenan Umma Allah ya kaimu lafiya." kallona tayi cikin tausayawa tace."Naga duk kin rame ko duk fargabar ce."? Murmushin takaici nayi nace."Umma zama da Gwaggo da Ummatu ai sai jarumi mai kuma hakuri sosai suke takurawa rayuwata."

Murmushi tayi tace."Ba tun yau ba na san halin Gwaggo macace wata iri wacce baka gane gabanta da bayanta haka nima nai hakurin zama da ita Ummatu kuwa dama can ba muyi wani zaman arziki da ita ba."

Nace."Hakane Umma tace." to saboda haka sai kiyi hakuri ki cire damuwa daga cikin ranki ki fuskanci abinda yake gabanki aure idan Allah ya kawo lokacinsa babu wanda ya isa ya hana."

Nace."Kwarai kuwa hakane." Ta kalli kwanukan abincin dake gabana a nutse tace."Da alama ba ki bude abincin nan ba."? Nace."Eh ban ci ba tukunna." Tace."To ni zan shige na tafi dakin Alhaji sai ki nutsu kici abincin ki kwanta." nace."Tom shikkenan Umma sai da safe." Ta mike a nutse ta fita daga dakin, cikin nutsuwa na bud'e kwanukan abincin towon farar shinkafa ne da miyar taushe taji gyada sai kamshi take.....dama tsabar fargaba da tashin hankali bata bari naci wani abincin kirki ba saboda haka lokaci guda yunwa ta taso min nasa towon a plate na zuba miya akai a nutse na fara ci ina tunanin halin da Gwaggo zata shiga idan ta farka daga bacci taga bana nan.....



*Masoya a taimaka da sharing??????*


*IDAN KINA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE....VIP GRUOP#600 NORMAL GROUP #300 ACCOUNT... 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK...IDAN KATI ZAKI TURO #400 SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER.*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE**GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO?????*


*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna min????*_


*13*
A daran ranar Gwaggo kasa rintsawa tayi asubar fari ta tashi tai alwala tayi sallah da carbi a hannunta ta fito kai tsaye gurin baba iro ta nufa ta shiga bubbuga musu kofa. Lokacin shi yana massalaci bai shigo ba, bugun kofar da take ya tashi khalid a firgice ya mike zaune dama shima sai dab da asubah baccin ya daukeshi agogon da yake kafe a bangon dakin ya kalla shida da rabi da sauri ya dauki brush dinsa ya fito.....kallo ta bishi dashi da fadin."Kada dai kace sai yanzu ka tashi."? kansa ya daga mata ya ratseta ya wuce bayansa tabi da kallo kafin tace."Khalid me yasa kake wasa da sallah ne."? ba tare da ya tanka mata ba ya dauki buta ya shiga bandaki, sai itama ta bar gurin ta nufi dakinta ta zauna cikin alhini da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login