Showing 6001 words to 9000 words out of 185789 words

Chapter 3 - Ga-irin-ta-nan-complete by binta umar abale

05 Jul 2024

24197

kyawun naki da kyawun surar zai tashi a banza a wofi wannan al'amari yana damuna."

Jim! nayi ina kallonta kafin nace."Gwaggo Al'amarina ya daina damunki komai da kika gani yana da lokaci ki cigaba dayi min addua."
"Umm."! ta sake fada tana ta'be bakinta, kaina na girgiza kawai na kama hanyar fita daga dakin, karo mukaci dashi a lokacin da yake 'kokarin shiga, yana sanye da singlet fara kal da 3qutar fuskarsa ta nuna alamun bai jima da tashi a bacci ba.

Cikin kulawa yace." Aunty Sa'ida ki bari yanzu zamu fita cikin a daidaita sahun Salim sai mu kai ki makarantar taku."

Ba tare dana kalleshi ba nace."Bana bukata." da sauri na ratse shi na wuce! Ina jin sautin muryar Gwaggo tana surutai wanda suke nuni da jin haushin abinda nai masa.


Sai da nayi dana sani akan k'in kar'bar tayin da Khalid yayi min domin nafi karfin minti goma sha biyar a tsaye a bakin titi wani abun hawa na haya bai gilma ta gabana ba motocin gida ne kawai suke wuce wa, dama wani sa'in ina fama da irin wannan matsalar ta rashin abin hawa, wani lokacin kuma ina fitowa titi nake samu yau dai al'amarin sai addua dan tamkar anyi musu gori ko kuma wa'inda suka tafi yajin aiki, agogon dake daure a hannuna na duba takwas saura minti biyar gashi karfe takwas da minti goma nake da Period ajiyar zuciya na sauke ganin adaidaita sahun nasu na kokarin fitowa daga layin duk abuna dole nayi hakuri na shiga mutukar baso nake na makara ba, Motar Alhaji Nura na sake hangowa tana bin bayan babur d'in nasu, saurin dauke kaina nayi ina kallon hanya tabbas nasan sai ya tsaya yayi min magana gashi gabad'aya ban yanke hukunci akan maganarsa ba gabad'aya ma na manta munyi magana dashi jiya.

Aikuwa gabana yayi parking ya sauke gilashin motar fuskarsa dauke da k'ayataccen murmushi yace."Ranki ya dad'i an fito kenan."? sakin fuskata nayi nace"Eh wallahi Alhaji barka da asuba ya kwanan iyali." ? cikin kulawa yace."Lafiya kalau sun tafi skull yanzu me zai hana ki shigo na rage miki hanya." Yafada yana kallon kwayar idona, ina kokarin magana adaidaita sahun nasu ta tsaya kusa dani. da sauri nayi 'yar dariya da fad'in"To nagode Alhaji dama na jima a tsaye babu abun hawa." cike da jin dadin kar'bar tayinsa yasa hannu ya bude mota kofar had'e da fad'in ''bisimillah." ba tare da na tsaya na saurari maganar da Khalid yake min ba na shiga motar da murmushi na mussaman a fuskata duk dan na cuzgunawa zuciyar yaron......Motar ya kunna muka bar gurin ko da wasa banyi kuskuran kallonsa ba so nake na 'kuntata masa dan saboda nasan ya tsani ya gan ni tare da mutumin bayan haka kuma inaso na nuna masa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane ni ba matar 'kananun yara bace.


Khalid iskar dake gurin ya kaiwa naushi! rai a 'bace ya shiga kai kawo a gurin zuciyarsa kamar zata tsaga kirjinsa ta fito saboda tsananin kishi! Salim yace."Khalid dan Allah shigo mu tafi ka rabu da ita." Yana huci! ya shiga motar, Salim ya mika masa pure water da fadin"Kar'bi kasa zuciyarsa tai sanyi kar'ba yayi kamar gaske sai kawai yayi wurgi dashi kan titi lips d'insa ya ciza da fad'in "Allah Salim wannan Alhajin idan baiyi wasa ba sai nayi masa rashin mutunci babu ruwana da wani kud'insa da shekarunsa wallahi mutukar bai fita daga harkarta ba sai na bashi mamaki."!

Salim girgiza kansa yayi yace." Khalid idan da zan baka shawara ka d'auka sai nace maka ka rabu da Aunty Sa'ida saboda nasan kai kanka kasan ba tsaranka bace aunty Sa'ida matar manya ce ganin idonka babu wani gajarabul d'in mutum da yake tunkararta duk masu nemanta manyan mutane ne kana dai kallo da idonka duk kudi da muqami irin na Alhaji Nura idan ya ganta rawar jiki yake mata."


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yana kallon abokin nasa yace."Salim duk abinda ka fad'a akan auntyna gaskiya ne wallahi ni kaina ina mamakin tsaurin idona a kanta Salim na rasa yanda zanyi wallahi aunty Sa'ida ta shiga zuciyata tayi kakagida! a cikinta, Salim bari na fad'a maka wani sirrina da ba kowane yasan dashi ba, tun inada shekara goma sha takwas a duniya na fara mafarki da ita haka zan wayi gari jikina a 'bace! to tun daga sannan na gane cewa na balaga na zama cikakken namiji wallahi Salim babu ranar da zan kwanta bacci banyi mafarkinta ba kuma kai idan kaga irin rayuwar da muke da ita a mafarkin sai kayi mamaki wallahi sosai nake sex da ita ina jiyar da ita dadi tana jiyar dani! na rasa yanda zanyi da wannan masifar Salim ko a skull haka nake fama da wannan jarabar dan dai kawai adduar iyaye na tasiri a kaina amma da badan haka ba da tuni na nemi hanyar da zan biyawa kaina bukata.''


Girgiza kai Salim yayi yace."Gaskiya Abokina na tausaya maka domin ni tuntuni na gane son maso wani kake yi domin jikina na bani aunty Sa'ida bata sonka duba da irin halin ko'in kulan da take nuna maka me zai hana kayi ya'ki da zuciyarka akan abinda kasan ba zaka samu ba."


Ranshi a 'bace! yace."Salim idan kaga na daina bibiyar Aunty Sa'ida to aure tayi kai wallahi ko aure tayi ba zan hakura da ita ba saboda bata da wani miji sai ni wannan dalilin ne ma yasa na samu gwaggo na fad'a mata maganar ina ganin ko kowa ya'ki amincewa ita zata goya min baya."


Salim yace." Khalid ina jiye maka wahala wallahi na fada maka Aunty Sa'ida tafi karfinka ka hakura kawai." a fusace! yace." Salim wai wannan wace irin magana ce kake? a'ina ka ta'ba ganin mace tafi 'karfin namiji! Auntyna nada 28year ni ina da 23year sai ka fad'a min ina tazarar take kai ni a yanda nake jin jarumta idan an had'a min iri-irin ta goma zan iya dasu ballantana ita da tun a mafarkina na gama da ita na fad'a maka a mafarkina fa tuntuni na gama mata aiki." Salim ya fashe da dariya yana dukan sitiyari yace."Kai Khalid wallahi baka da mutunci wato dai yanzu kana nufin fanko kake kallonta."

Murmushi yayi ya d'an sosa tarin sumarsa yace."Aa mafarki daban Zahiri daban yanda nake sarrafa ta a mafarkina to inaso na sarrafata a zahiri wallahi sai na 'kure duk wata fitinar ta." Salim ya dinga dariya yana fad'in Khalid baka da dama wallahi Allah ya baka aunty Sa'ida ka more 'kuruciyarka dan wallahi nima ina son mace mai kyau da tsarin jiki irin nata kullum kamar 'kara mata 'kuruciya ake."

Murmushi yayi yace."Nagode da addua abokina." Wasu mata ne suka tsayar dasu, Salim yace."Hajiya ina zakuje."?
"Gidan Murtala." matar ta fada tana kallonsa, yace."To ku shigo muje." da sauri suka shiga, shi kuma yaja babur din suka bar gurin.


****
Cikin murya mai taushi yace."Ranki ya dad'e har yanzu banji daga gareki ba inaso ki sha'ku da iyalina kafin Allah ya kawo ki cikinsu shine babban dalilin da yasa nace kina shiga gidan a cikin ranaku biyu kinayi musu lesson itama matar gidan tuntuni nayi mata bayani kuma ta amince da manufata.''
Alhaji Nura ne ke wannan maganar a yayin da suke tafiya a motarsa.


Ajiyar zuciya na sauke na d'an kalleshi da gefan ido mamaki sosai nake da maganarsa yana sona da aure amma kuma yana kawo wata gurguwar magana mara ma'ana Ta yaya zan dinga shiga gidansa da sunan yiwa yara lesson bayan da maganar aure a tsakaninmu hakan sam bai dace ba, ita kanta matar gidan da ta amince da hakan nayi mamaki amma dai nafi zargin gatse tayi masa tunda mafi akasari maza basu sanshi ba.

A nutse nace"Alhaji ni ina ganin ba lallai sai na shiga gidanka nayi wa yara lesson zamu sha'ku dasu ba, hakan kamar bai dace ba tunda har magana aure ta shiga tsakanina da kai a yanzu sai mu bari muga abinda Allah zaiyi idan har Allah ya kaddara aure a tsakanina da kai yara basu da matsala insha Allah zan tsaya na kula da harkar karatunsu amma maganar na dinga zuwa nai musu lesson ka ajiyeta."

D'an murmushi yayi yace."Sa'ida kenan ai da amincewar matar gidan nake miki wannan maganar ina ganin hakan duk ba wani abu bane tunda duk an riga an zama d'aya.''


"Alhaji kenan na yarda da amincewar matarka amma ni a ganina hakan ba kamata ba dan Allah kayi hakuri da wannan maganar domin ina ganin hakan shi yafi alkairi." Yace."To shikkenan tunda kince haka yanzu a'ina maganarmu ta kwana? inaso wannan karon ki bani dama na turo da magabata na akan maganar auranki." Jim! nayi ina nazarin maganarsa "Insha Allahu zan kira wayarka idan na koma gida." Cike da farin ciki yace."To masha Allah Nagode 'kwarai Sa'ida sai na jiki.'' Murmushi kawai nayi ban sake magaba ina dai jinshi yana ta bani labarin yaransa sai da dariya yake gaskiya yanda na fuskance shi yana da son yara sosai........cikin wannan halin ya sauke ni bakin gate din makarantar da nake koyarwa a nutse nace"Alhaji nagode kwarai." kokarin bud'e mota nake yace."Idan kun tashi ina iya turo direba ya dauke ki." Da sauri nace"Aa Alhaji bani da matsalar abin hawa idan zan koma gida domin 'kawata Hauwwa tana da mota tana rage min hanya." Yace."To shikkenan ranki ya dade a fito lafiya." Nace."Insha Allah nagode." motar na bude na fita da sauri na daga masa hannu hade da fad'in "A sauka lafiya." cikin sauri na nufi cikin makaranta kafin na shiga sai da muka gaisa da masu gadi cikin mutunci sannan da sauri na shige ciki.......



*Masoya ayi min sharing a groups??????*




*IDAN KINA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE......VIP GRUOP#600 NORMAL GRUOP#300 ACCOUNT.. 0542382124...BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE**GA IRINTA NAN!!!?????¡â?*
_(LOVE STORY??)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE??_
*MANAZARTA WRITES ASSO?????*


*DUNIYAR HAUSA NOVEL*

_*Cannal ne na mussaman da zaku samu littafan hausa ko wane iri ne maza ku tafi YouTube kuyi sarcing d'in Cannal din zaku samu 'kyatattun littafai masu dadi! kada ku manta da sunan channal din *DUNIYAR HAUSA NOVELS*_


*5*
"Sa'ida tun kafin mu fito daga ofis nake miki wani irin kallo sai nake ganin kamar kina da damuwa a ganina bancanci ki 'boye min abinda ke damunki ba tunda nima duk wani abu da yake damuna bana 'boye miki."
Hauwwa ce kenan wannan maganar a lokacin da suke cikin motarta domin komawa gida.

Ajiyar zuciya na sauke nace."Wallahi Hauwwa ba 'karya kikayi ba ina damuwa na kuma rasa yanda zanyi na warware ta al'amarin dai sai godiyar Allah.

Murmushi tayi tace."Haba 'kawata abokin kuka shi ake fad'awa mutuwa ki fad'a min damuwarki ko akwai shawarar da zan iya baki."


Murmushi nayi nace"Dama ina tunanin fad'a miki kikayi magana Hauwwa kin san wannan yaron na gidanmu ko.''?

Tace."Khalid ko bashi kike nufi ba."? Nace."Shi nake nufi Hauwwa Khalid ya takura min a gida wallahi wai saboda tsabar rashin mutunci da raini kamar ni zai duba yace yana so."


Hauwwa dariya tasa tana kallona da mamaki a tare da ita, tace."So.''? Ta'be bakina nayi nace."Kwarai kuwa Hauwwa Khalid sona yake dan duk wasu alamu ya nuna harda fad'awa Gwaggo wai zai aure ni yaron da a gabana ya girma meye nasa ban sani ba amma da yake yanzu yaga ya fini tsayi da girman jiki shine yake furta min wannan kalma.''


Hauwwa draving take tana girgiza kanta tace."Sa'ida Khalid yayi tsaurin ido amma kuma idan an duba tarihi za'a ga baiyi tsaurin ido ba tunda hakan kamar sinna ce mai zai hana ki aureshi tunda hakan ba haram bane."


Wani irin kallo na watsa mata "Hauwwa wannan wace irin magana kikeyi me zan aura a tare da Khalid bana tsammanin zan iya auran 'karamin yaro a yanda nake a haka nafi bukatar cikakken namijin mai kima wanda yasan rayuwa amma auran yaro mai 'karanci shekeru akwai kalubale a ciki."

Murmushi tayi tace."Sa'ida wane 'kalubale kike hangowa a tattare da auran Khalid? Yaro kyakykyawa da siffar mazantaka Khalid bai da makusa matsalar kawai kice bashi da kudi sannan kuma bashi da aikinyi in banda haka menene abin'ki a tare dashi."?


Girgiza kaina nayi nace."Hauwwa Ra'ayi na ne kawai haka bana sha'awar auran k'ananun yara dan sai nake ganin kamar basu san meye aure ba wannan dalilin yasa gabadaya bana kulasu nafi tsayawa na saurari magidanta masu iyali da suka dad'e a cikin harkar."


Hauwwa ta'be bakinta tayi tace"Sa'ida mazan fa suna suka tara kamar yanda matan ma suka tara duk kallon kitse kike musu ni zan fad'a miki wannan kinga dai ni bazawara ce ko to wallahi ba zan auri namiji ba sai na tsaya na duba tukkuna saboda ni kad'ai nasan bala'in dana shiga a gidan aurena kafin na fito."


"Hauwwa kenan kin san kowa da tunaninsa amma gaskiya bana yi miki sha'awar auran 'karamin yaro domin kinfi 'karfinsu ki auri namiji daidai dake dan Allah kada kibi son zuciyarki daga baya kizo kina nadama."


"Sa'ida kin san Allah ko d'an 20years ne yazo da niyyar aurena na gamsu da shi sai na aureshi domin hakan ai ba haramun bane akan naje na auri babba nazo na sake shiga wata matsalar gwara na auri yaron na cigaba da rainonsa har yayi 'kwari."


Cikin wani irin yanayi na mamaki nake kallonta.....tasa dariya da fadin"Kina mamaki ne.''? Girgiza kaina nayi nace."Sosai kuwa idan kin auri dan 20years kin auri d'an cikin ki ko ba haka bane."

Still tana dai dariyar tace."Aa Sa'ida bana san sharri a ina na haifi dan shekara ashirin Walid yarona na farko duka shekaransa tara Safna kuma shekararta bakwai."

Nace"Kin gani ai tunda kika haifi dan shekara tara kin zama uwa me zai baki sha'awa a gurin auran karamin yaro dan shekara ashirin.


Hauwwa baki ta ta'be tace."Ke Sa'ida bari dai na fito miki a mutum! ni Hauwwa ina da tsananin bukata wannan dalilin ne ya janyo mutuwar aurena domin babansu Walid bashi da maida hankali a wannan gurin yafi mayar da hankalinsa gurin neman kudinsa nasha wahala a hannunsa Sa'ida ina fada miki Walid da Safna tsanani rabo ne yasa aka haife su saboda babansu sai ya shafe wata biyu ko uku bai had'a shimfida dani ba, kullum yana yawo a jirgi sai kace tsunsu shi dai ya samu kud'i ni kuma ya barni cikin wahala da bukata wannan dalilin yasa na yankewa kaina shawarar yanke zama dashi dan ba zan iya da halinsa ba."

Na jima ina mamakin maganarta kafin nace."To Hauwwa shi 'karamin yaron da kike 'kulafuci a kansa kina da tabbacin zaki samu abinda kike bukata mazan fa duk kusan haka suke tunda dai ba 'kwan'kwasawa zakiyi ki gane daidai dake ba ."


Murmushi tayi tace."Sa'ida ana ganewa wallahi shiyasa ai nace miki kafin nayi auran sai na tantance tukkuna kuma ina rokon Allah ya bani daidai dani."


Nace."Ta ina zaki gane jarumin namiji Hauwwa." murmushi tayi tace."Sa'ida kenan." draving d'inta ta cigaba dayi ta barni cikin tunani nima irinta ce mai yawan sha'awa da son soyayya shiyasa gabad'aya na shiga tunanin ta inda zan gane jarumin namijin da zai iya daukar lalurata......Alhaji Nura ne ya fad'o min a rai na dinga tunanin siffofinsa dogo ne mai ma daidaicin jiki kwayoyin idanunsa jajaye ba irin na Khalid ba da kullum suke da haske, nace"Hauwwa tunda kin'ki fad'a min ai na gane."

Tace."Yawwa ai dama so nake ki gane sai kiyi min bayani." Dariya nayi nace."Kamar dai Alhajina ina nufin Alhaji Nura ya cancanta da wannan sunan.

Shuru tayi tana nazari tace."Eh gaskiya kam kwayoyin idanunsa ma sheda ne ina miki sha'awar auransa gashi yana bala'in sonki to amma ai matarsa ce matsala Sa'ida a rayuwata bana san kishiya wallahi."


Ajiyar zuciya na sauke nace."Hauwwa ni wallahi kishiya bata firgita ni za'bin Allah kawai nake nema idan Allah ya kaddara Alhaji Nura ne mijina babu ruwana da matarsa tunda ba itake aurena."

"Hakane Sa'ida to ina rokon Ubangiji Allah ya za'ba mana abinda yafi alkairi." na amsa da ameeeen ya rabbi......Da wannan hirar ta sauke ni a bakin layin mu ta juya kan motar hannu na daga mata da fadin"Nagode 'Kawata sai gobe idan Allah ya kaimu." ta amsa da "Ameen Allah ya kaimu lafiya." sai da ta bar gurin sannan na nima na bar gurin........


Tunda na hangoshi a zaune a kofar gidan naji gabana ya fadi! hakika Khalid ya zame min 'karfen 'kafa, kici-kici nayi da fuskata, kafin na karasa naga ya mi'ke ya shiga gidan, ajiyar zuciya na sauke naji dad'in hakan saboda na tsani kallon da yake min......Ina shiga soran naji an fizgo hannuna kafin nayi aune naji ya ru'kun'kume ni ta baya! numfashinsa naji yana fita da sauri da sauri ya d'ora kansa a kafad'ata sosai ya ri'ke 'kuguna! gabana ya dinga fad'uwa! murya na rawa nace."Khalid wane irin iskanci ne wannan? zaka sake ni ko sai nai maka rashin mutumci d'an iskan yaro kaw......Kafin na 'karasa naji yayi cikin bayan k'yaure ('kofa) dani, a zabure! na juyo fuskokinmu suka had'u guri guda!

Hawaye ne naji suna kokarin kufce min wane irin fitinan nan yaro ne wannan? matseni yayi a kirjinsa yana kiran sunana cikin wani irin sauti "Aunty Sa'ida kina so na mutu ko? ki taimakawa rayuwata kada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login