Showing 72001 words to 75000 words out of 185789 words
a tsakar gidan.
Yace."Gwaggo na san ki da son doya shiyasa na siyo miki buhu guda.'' Dariya tasa da fadin"Aikuwa naji dadi d'an albarka Allah ya 'kara maka wadata." ya amsa da ameeen ya rabbi.
Tace."Muje daki kaci abinci ka huta ko."? yace."To uwagidana." murmushi tayi ta rike hannunsa suka kama hanyar dakin....Ummatu kuwa murmushi tayi cike da farin ciki ta shiga gurinta.
Jin motsin shigowarsu dakin yasa da sauri na daidaita nutsuwata ba tare dana dago kaina ba na amsa sallamar shi.
A jikina naji cewar kallona yake a fizge na daga kaina na kalleshi yana sanye da k'ananun kaya kamar ko da yaushe sai kawai na tsinci kaina da kasa dauke idona daka kansa mamakin girmansa nake wata biyar kacal yaro ya sanja ya zama 'kato dashi da gaske ya sake girma da hasken fata.
A nutse ya zauna inda aka tanadar masa Gwaggo sai wani ji dashi take tana gyara masa gurin zama, shi kuma gabadaya hankalinsa na kaina ina kallonsa ta gefan ido sai kallona yake.
"Auntyna ba zakiyi min barka da zuwa." maganarsa naji ta daki kunnena.
Na kalleshi babu yabo babu fallasa nace."Khalid ya hanya."? fuska a sake yace."Alhmdulillahi aunty ya fargaba da alhinin dana tafi na barki dashi.''?
Share maganar nayi na dauki waya ta ina dubawa.
Gwaggo ta hau bude kwanunkan dake gabansa tana fad'in "Jarumi kaci abinci gashinan." Yace."Gwaggo duk wannan nau'in abincin duk ni kadai."
Tana mirmushi tace."Khalid kafi karfin komai a gurina burina kullum ka kasance cikin farin ciki."
Yace."To gwaggo naji dadi sosai ina rokon Allah yaja min da ranki." Tana kokarin zuba masa abincin a plate ta amsa da ameen d'an albarka.
Abincin ta zuba masa da yawa tasa masa miya da uban nama. yace."Gwaggo abincin nan yayi min yawa." Tace."Ka dai ci ka koshi."
Kallona yayi cikin kulawa yace."Auntyna zo ki taya ni ci." Ko kallonsa banyi ba ballanatana na bashi amsa.
Tace."Khalid rabu da ita don Allah kaci abincin ka."
Girgiza kansa yayi yace."Gwaggo ya za'ayi amaryata tana fushi kice na rabu da ita ko dai kishi kike."?
Bani kadai ba Ita kanta Gwaggo sai da gabanta ya fadi! shuru tayi jikinta duk ya mutu data tuna da yaudarar da akayi masa.
Gani tayi ya mike daga inda yake ya dawo kusa dani ya zauna. ni da ita dik jikinmu ya mutu. a sanyaye yace."Auntyna menene? ki fad'a min matsalarki gani na dawo na share miki hawaye."
Kallonsa nayi zuciyata ta dinga tafarfasa! ina tuna irin cin mutuncin da yayi min a ranar da zai gudu! 'kwalla ta cika kwarmin idona! kansa ya girgiza min cikin sigar rarrashi yace."Kada kiyi min asarar hawaye domin yana da mutukar daraja a gurina ki gafarce ni auntyna nasan dole idan kika kalli fuskata ki tuna abinda nayi miki na rashin kyautawa."
Bude baki nayi zanyi magana sai kuma kuka ya kufce min nasa hannu na gumtse bakina hawaye na shatata! jikinsa na wani irin rawa janyo ni jikinsa sosai ya rik'e ni yana kokarin goge min hawayen fuskata...Gwaggo tace."Khalid sakar mata jiki kada kasa mu shiga fushin ubangiji kayi maza!maza ka sakar mata jiki."
Da karfi take maganar tana kokarin mikewa tsaye!
Kasa'ke yayi yana kallonta hakan ya bani damar mi'kewa daga kusa dashi naje na samu wani gurin na zauna ina goge fuskata.
Yace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."?
Girgiza kanta ta shiga yi tace."Khalid da naso ka zauna kaci abinci ka samu nutsuwa in yaso sai na zaunar da kai na fada maka abinda yake faruwa amma yanzu tunda hakan be samu ba dole na fada maka halin da ake ciki.....A yanzu dai Sa'ida tana da aure kuma ba kowa take aure ba face Alhaji Nura wannan dalilin yasa kaga hankalina ya tashi a lokacin daka ri'keta a jikinka."
Wani irin jiri ya dinga yi a zaune kansa ya dinga juyawa gabadaya ya nemi yawu ya rasa a bakinsa auntynsa tana da aure amma ta yaudare shi a waya tace ya dawo gida zata aureshi shin meye manufarta nayin wasa da hankalinsa.
Mi'kewa tsaye yayi jikinsa na wani irin rawa ya dumfari inda take zaune!.....tsorata nayi da ganin yanda ya tunkaro ni na mi'ke da saurin gaske Gwaggo na kokarin tare masa hanya da sauri ya kauce mata wuyana ya sha'ko ya had'a ni da bango (garu) ya matse ni sosai! ido jajawur! yace."Ni zaki yaudara ko."? Gwaggo hankalinta a tashe tazo tana kokarin janyeshi tana fadin."Haba Jarumi ka sassautawa zuciyarka mana." hannu ya daga mata a fusace! yace."Gwaggo ki 'kyaleni na kashe wannan mara imanin gwara na aika da ita barzahu tun kafin ta aika dani." Yana gama maganarsa ya sake matse wuya na da jikin bangon."
Gwaggo ta fashe da kuka hankali a tashe! ta fita daga dakin............Khalid dai da gaske so yake ya kasheni dan yanda ya matse min wuya gabadaya ya hana ni fitar da numfashi, sai kawai na rintse idanuwana zafafan hawaye suka shiga kwaranyo wa a saman fuskata.
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.????????_*
*51&52*
Ko dana koma d'akin Gwaggo 'kin sakar mata fuska nayi duk wani abu dana san zanyi a dakin nayi na fito nayi shimfida a tsakar gida nayi kwanciyata itama uffan ba tace dani ba, tsakanin ni da ita ban san waye yafi jin haushin wani ba.
Ummatu kuwa itama da bakin ciki ta kwana dan bayan fita ta daga gurin Kawu Iro kiranta yayi itama ya 'kare mata tanadi yace kuma ta jawa Khalid kunne ya shiga hankalinsa idan kuma yasan neman fitina ne ya dawo dashi to sawun sa a likkafa ya koma inda ya fito baya bukatarsa a cikin gidansa....Ummatu taci kukanta ta koshi ba tare da tace masa komai ba ta bar gurin tare da kudirin wani abu ranta.
Khalid yana kwance a d'aki! yaji duk irin cin mutuncin da Kawun kewa mahaifiyarsa ransa ya sake 'baci ya sake 'kullatar Auntyn nasa yana tunanin irin hukuncin da zai yanke mata.
Da zazzafan zazza'bi da ciwon kai ya kwana dan haka yana dawowa daga sallah ya shiga dakinsa ya kulle k'ofa ya kwanta ba tare da yayi tunanin zuwa ya duba Gwaggo mutuniyar tasa ba.
Cikin baccin daya soma fizgarsa ya dinga jin bugu ana kiran sunansa.
Mikewa yayi yaje ya bude kofar dakin, Ummatu ce ya bata hanya ta shiga dakin ta mayar da kofar ta rufe.
Gefan katifarsa ya zauna yana gaisheta ta amsa tana kokarin ajiye fulas din shayin dake hannunta.
Tace."Khalid ina fata jiya duk kaji irin cin mutumcin da mahaifinka yayi min ko."?
A sanyaye yace."Eh Umma naji kiyi hakuri dan Allah kin san halin baba be iya 'bacin rai ba."
Girgixa kanta tayi cikin takaici tace." Ba haka bane Khalid dama haka halin mahaifinka yake wani lokacin idan yayi ra'ayi haka zai zauna yaci mutuncina iya yanda ransa yake so akan wannan yarinyar Sa'ida babu abinda ba zai iya aikatawa ba."
Yace."Ummatu kiyi hakuri ki saba da halinsa idan kuma nine nake janyo muku sa'bani insha Allahu zan koma inda na fito kamar yanda naji yana fada jiya.
Tace."Khalid idan kai ka cika dan halak ne to dan Allah ka rabu da Sa'ida bafa ita kadai ce 'ya mace a duniya ba shin wai me ka hango a tattare da ita kake kulafunci.
Kansa ya sunkuyar kasa ta cigaba da cewa" A matsayina na mahaifiyarka nake umartarka a karo na biyu ka fita daga sabgar Sa'ida idan kana so kayi albarka a rayuwarka."
Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta a raunane yace."Umma ki taya ni addua akan abinda ke damuna a zuciyata insha Allahu zanyi kokarin ganin na cire aunt Sa'ida daga rayuwata."
Tace."To shikkenan Khalid zan cigaba dayi maka addua sannan inaso ka auri Jamila 'yar 'kanina Garba."
Ya kalleta cikin wani irin yanayi yace."Ummatu ki ajiye maganar Jamila a gefe guda ni bana ra'ayinta.
Tace."Khalid tuntuni fa na fahimci cewa baka kaunar dangi na kafi kaunar dangin mahaifinka yanzu meye aibun Jamila kasan dai tafi Sa'ida kyau ko gata yarinya daidai da kai."
Yace."Umma kin san shi so babu ruwan sa da wani kyau ko muni duk kyawun Jamila bata burge ni ba kuma bana jin sonta ko kadan a cikin raina.
Tace."Ni dai umarni nake baka ba za'bi ba saboda haka idan kana so kayi albarka to kabi umarnina."
Ya jima kansa a kasa kafin yace."Shikkenan Umma zanyi miki biyayya akan abinda kike so." murmushin jin dadi tayi tace."Insha Allahu kuwa zakayi alfahari da auran Jamila.
Shuru yayi bai ce mata komai ba tace."Ga ruwan shayi nan a fulas bari na kawo maka awara da sauran kayan shayin."
Yace."Nagode Ummana." fita tayi daga dakin ranta fari sol babu shakka za tayi farin ciki idan al'amarin nan ya tabbata.
3qutar ne a jikinsa sai kawai ya sanya k'aramar
T-shirt a jikinsa ya fito daga dakin nasa a daidai lokacin da Kawu ya fito daga nasa d'akin da shirin tafiya kasuwa.
'Dan risinawa yayi yace.''Kawu barka da asubah." Ba tare da ya kalleshi ba ya amsa da "Barka dai." ya d'aga labulan d'akin Ummatu yana mata magana. ganin haka yasa da sauri ya fita daga gurun.
Gwaggo na kokarin fitowa daga d'akin ya shiga tace."Ai dama yanzu nake maganarka ina cewa ko da kaina zan shiga gurin naku na dubaka naga baka shigo mun gaisa ba."
D'akin ya shiga babu walwala a tare dashi yace." Na d'an yi bacci ne."
Tace."Koda naji nima nace ko bacci kakeyi to zauna ga guri mu gaisa a nutse." gefanta take karkad'e masa tana marmatsar da abubuwa sai kace barasake ne zai zauna a gurun.
Hankalinsa akanta tana bacci a gadon ba tare da tasan ya shigo dakin ba....Gwaggo ta lura da irin kallon 'kurrular da yake mata sai duk jikinta yayi sanyi itakam wannan jaraba ta isheta wai shin wane irin so yaron nan yake wa Sa'ida.
Labari take bashi wai dan duk ta dauke masa hankali jinta kawai yake amma gabadaya hankalinsa da tunaninsa baya kanta yana can tunani akan Sa'ida duk da yasan ya ga mai mata illah amma yana bala'in kishin Alhaji Nura akanta shi kad'ai yake so ya cigaba da dabdala a wannan ramin amma wani katon banza ya shigar masa gona.
Gwaggo haushi ya bata ganin ya'ki barin abinda yake tace.''Ni kam banta'ba ganin mara zuciya irinka ba."
Sumar kansa ya shafa babu sukuni yace."Me nayi miki kuma."? Tsaki taja tace."Tunda ka shigo kake kallon Sa'ida alhalin bacci take yi ko gaisawa ba muyi ba hankalinka gabadaya yana kanta to ka dai kiyaye kada ka jefa kanta a matsala domin naga idanuwanka sunyi ja."
Murmushi yayi yana kallonta yace."Waye yace miki ita nake kallo."? Tace."Ai makauniya ce ni." Dariya yasa yana sosa kansa tace."Ka karya kummalo."?
Girgiza kansa yayi tace."To bari na zuba maka abinci." Yace."Gwaggo ba zanci abinci da safe ba ki bani ruwan shayi." Tace."Aa Ni yau kunu nasha ruwan shayi ka tambayi mahaifiyarka."
Yace." Okey na manta ma da akwai a fulas a dakina idan nasha zanzo naci abincin." Tace."To shikkenan.
D'akin ne yayi shuru na minti biyu ya cigaba da satar kallon Sa'ida ta 'kasan ido Gwaggon ta kalleshi tana girgiza kanta Hankali tace."Kasan abinda yake faruwa ko.''?
Girgiza kansa yayi yana d'an ya mutsa fuskarsa yace."Sai kin fad'a."
Juyawa tayi ta d'an kalli inda take kwance ta dawo da hankalinta kansa 'kasa-'kasa tace."Ai *GA IRINTA NAN!* ta guje ka ta auri wanda take so gashinan tana fuskantar matsala a gurinsa da matarsa ya hanata komawa gurin aiki kuma baya biya mata bukatarta.''
Jim yayi yana kallonta kafin yace."Gwaggo ban gane baya biya mata bukata ba."?
Waiwaya wa tayi ta sake kallon inda take kwance tayi 'kasa da murya tace."Bukatarta ta gurin auratayya mana wai baya son haihuwa shine yake inzali a waje ma'ana yana zubar da 'kwayoyin haihuwarsa."
Cike da mamaki yake kallonta! tana so ta 'kara tabbatar masa da maganar na tashi zaune duk sai suka diririce mussaman Gwaggo da gabadaya yanayin ta ya nuna na marasa gaskiya.
Yi nayi tamkar ban fahimci abinda suke ba na mike na fita, brush nayi na dawo d'akin na tarar dasu suna wata hirar.
Ta kalleni da fad'in '"Ga kayan karin kummalo nan." Ba tare da nace mata komai ba na hau bud'e kwanukan...........dakin yayi shuru na minti biyu kafin naji sautin muryarsa da fadin" Kin tashi lafiya."?
Kaina a kasa na amsa da lafiya lau." Gwaggo tace."Kina bacci dazu da safe aka kira wayarki kin san ni ban iya dauka ba shiyasa na barta ta katse."
Hannu na mika na dauki wayar ina dubawa Alhaji Nura ne sai naji wani sanyi a cikin raina text d'inshi na gani da sauri na shiga ina dubawa......Hakuri yake bani akan abinda ya faru wai nayi hakuri insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba kuma idan anjima zai zo ya daukeni.
Zuciyata tayi sanyi kad'an amma dai duk da haka idan na koma sai na nuna masa 'bacin raina.
A nutse nace."Gwaggo Alhaji Nura ne yake baku hakuri akan abinda ya faru yace insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba kuma anjima da daddare zai zo mu tafi."
Ta'be bakinta tayi tace."Ai sai ki zuba ruwa a 'kasa kisha saboda murna."
Kallonta nayi ta gyda min kai da fad'in "Eh mana ai kinga kuka da damuwa ya 'kare zaki koma d'akin ki tunda anan akan qaya kike."
Takaici ya hanani ce mata komai kawai na d'auki kofin kunu na fara kur'ba ina duba wayata.
Katsaham! naji maganarsa a kunnena" Aunty Sa'ida idan kin koma gidan mutumin nan waye zai dauke miki bukatunki na yau da kullum.
Babu walwala a tare dani nake kallonsa, shima ya 'bata rai da fad'in ''Kin kawo 'kararsa akan baya biya miki bukatarki ta aure sannan baya so ya haihu dake amma sabida rashin sanin ciwon kai zaki koma gidanshi meye amfanin zama dashi a haka kodai kwad'ayin kud'insa kike."?
Na dinga jin wani irin gumi mai zafi na tsatstsafo min a jikina shin ko dama maganar da sukeyi kenan a lokacin da na tashi na ga sun nuna alamun rashin gaskiya! "Yanzu Gwaggo meye amfanin yin wannan maganar da Khalid? me ya shafe shi a ciki da har zaki zauna kina fada masa halin da nake ciki a gidan aurena."
Shuru tayi bata tanka min ba, naji wasu hawaye masu zafi suna kokarin zubo min na kalleshi raina a 'bace nace."Wato dai ba kaji gargadin da mahaifinka yayi maka ba ko."
Cikin rashin tsoro yace."Ai magana ta wuce aunty Sa'ida na rabu dake kije kiyi rayuwar auranki wannan magana kuma da ki kaga nayi miki ba wai da wata manufa nayi miki ba ina jin tausayin halin da zaki shiga anan gaba."
Nace."To ina ruwan ka da dukkanin halin da zan shiga a gidan aurena bana so ka nasa bakin ka akan al'amuran da suka shafe ni ka tsaya a matsayin ka."
ta'be bakinsa yayi yace." To shikkenan aunty Babbah na daina saka bakina akan abinda ya shafe ki tunda bakya bukata."
Nace."Hakan shi zai fi maka alkairi." Shuru dakin yayi kowa yana sabgar gabansa.....Yace."Gwaggo kin san wata yarinya Jamila 'yar Kawu Garba 'kanin Ummatu."
Da sauri tace."Eh kwarai kuwa nasan yarinyar ko ba wata 'yar fara siririya ba."
Yace."Eh ita ce Ummatu take fada wai na nemi auranta."
Gwaggo ta rangwad'a buda tana washe baki da fad'in "Kai Alhamdulillahi amma naji dadin wannan al'amari tabbas wani hanin ga Allah baiwa ne Khalid nima na goyi da bayan ka auri Jamila domin ta cancanta.
Murmushi yayi yace." To shikkenan Gwaggo ku cigaba dayi min addua akan Allah ya tabbatar mana da alkairi.'' ta amsa da ameeeen ya rabbi.
Gabad'aya ji nayi na kasa nutsuwa a gurin jikina yayi bala'in sanyi jin maganar da sukeyi fita nayi na bar musu dakin na zauna baki soro ina dube-dube a wayata gabadaya na rasa abinda yake min dadi.
To koda Kawu ya dawo da yamma na fada masa sa'kon Alhaji Nura sai yace."To Alhamdulillhi dama jiya na fada miki cewa yau ne karshe idan baiyi magana ba zamu tattauna da Alhaji Shamsu to tunda yace zai zo ya daukeki zan zauna zaman jiran zuwan nasa.
Nace."To shikkenan Kawu........Bayan sallar isha'i Alhaji Nura yayi parking din motarsa a kofar gidan ya fito daga motar cikin lafiyayyar shadda sai maiko take yana baza 'kamshin turarensa Khalid dake zaune cikin abokinsa ya dauke kansa dan koda Alhaji Nuran ya 'karaso gurin yana musu sallama bai amsa ba su Salim ne suka amsa Ya kalli Khalid da fad'in ''Ko zaka kira min Sa'ida ne." Kai tsaye yace."Alhaji ka kirata a waya mana."
Ya duba wayar hannunsa da fad'in "Tun kafin na karaso nake kiran wayarta bata daga ba mybe tana wani uziri ne."
Jim yayi na minti biyu kafin ya miqe ya shiga gidan.....Lokacin na fito daga wanka ya tsaya yana kallona tsaki naja zan wuce shi yace." Sai kiyi maza ki kimtsa wancan lusarin mijin naki yazo yana jiran ki a waje."
Uffan bance masa ba na wuce shi na barshi a gurin a tsaye. dakin na shiga a gurguje na soma shirya jikina...
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600