Showing 264001 words to 267000 words out of 280244 words

Chapter 89 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1020

shiga gari can family house nasu, Nan suka yini da Mama Bilkisu mace ce wadda tasan kanta Dan Mahmud na fita bayan sunyi sallah sunyi lunch taja zahra bedroom dinsu na kasa ta zaunar da ita ta ringa koya Mata dabarun yanda zata rike mijinta ita wani abun idan ta fada sai kunya ta rufe zahrar ita kuwa babu ruwanta sai dai tace ki dai Kade kunne ki kwashe a gaba ze amfane ki, sai kusan magariba suka tafi Zahra ta saka Aunty zilai ta hada musu Kayan biki masu yawa sannan ta bawa 'yan matanta designers din turarika da Dubai abaya tunda kamar gorinsu akayi a gurin kayansu, da kyar Mama Bilkisu ta yarda suka karbi Kayan Dan fur cewa tayi sunyi yawa sai an rage Saida Aunty zilai ta saka Baki ta barsu suka karba.
A nan falon sukaci gaba da Zama suna hira sai lokacin magariba su Aunty zilai suka wuce part din su ita Kuma Zahra ta koma sama, har akayi insha'i Mahmud Bai shigo ba, Zahra na Zaune ta tsula gayunta cikin English wears maroon Mai duhu tayi rolling da farin veil touching din dake jikin coat din sama ta saka maroon din lipstick a Dan bakinta Sai tayi wanu irin kyau kamar ka dauke ba b'oye tana fesa turare wayarta ta dauki kida Mai dadi da sauri ta nufi wayar Kiran na magaji ne, tunda ringtone dinsa shima daban.
Sallama tayi Masa Bai Sami damar Amsa sallamar ba ya Fara fadin.
"Allah ya sauwak'e wallahi idan mutum neman taimakon emergency yake a gurinki Allah Saiya mutu, bakiga missed calls dina ba sun kai dari ina ga, tunda zafin abun nake nemanki Amma ba amsa na Kira oga yace min tun Rana baya gida haba ki daina nesa da waya ai abokiyar Hira ce ko Dan kina tare da Aunty zilai ai kin Gama samun abokiyar hira".
Katse Masa zubar da yake tayi.
"Haba Dan Allah ayi mutum idan ya Fara magana ba comma ba Full stop. Ka fito a mutum sak ka fada min abinda zaka fada ba kayi ta Jan dogon labari ba".
"To yau dai ana idar da sallar la'sar Abba ya rangada daurin Auren Salma da Hameeda Dan yanzu haka Salma har sun dira a Miya, can Aka kaita wani tsohon saurayinta ne Ma'aikacin Nefa da yake yawan zuwa gaida Abba kusan duk sati duk da basa tare da ita shine yazo jiya suna bin gidaje raba bill din wuta, Abban yayi Masa tayin Auren salmar Amma fa Saida ya fada Masa gaskiya idan ze iya yace babu komai Yana so a haka. Yaje ya fad'awa magabatansa, daman an fadawa gidansu mai son Hameeda suzo da sadaki shine ya daura musu Auren yau yace a tafi da Salma gobe kayanta zasu biyota, taimakon da Allah yayi Mata Abba ya Basu gida a can Miya din tunda yana da gidajen haya a garin kuma kwanaki akayi modernizing dinsu. Ita Hameeda ce aka bashi hakuri zuwa wani satin ta tare tunda mijin baya Nan Yana kaduna gurin aiki, to kinji fa abinda Zan fesa Miki kike min surutu, yanzu haka Ammah dasu Aunty Hassana da Hajiya Turan gidan maji dadi suna can, ki Bari kawai saina shigo da labari wallahi buhu-buhu Zan shigo in zazzage Miki su ai anyi dai abun kunya wallahi Ashe duk lullubin biri aje yiwa mutane ai Ni Ya Mahmud ya Gama min komai kindsan bibiyar Salma yasa akeyi Masa Ina gida jiya ya kirani yace min sunyi magana da Abba Zan raka bilyan gidan malam Jos, Ashe asibitin da aka kwantar da Salma ya tura ya daukota Ni Kuma da nasan gari nayi masa jagora wallahi sanda ya kirani ya bani address din asibitin Nasha mamakin me zamuyo wannan asibitin ke........"

Wayar taji an zare daga kunnenta da sauri ta juya Dan kamshinsa ya fada Mata shine Amma koda Wasa bataji sanda ya shigo ba.
Wayar ya duba yaga magaji ne kunnensa ya Kai wayar Yana fadin "ka Adana sauran bayaninka zuwa safe".
Ai kafin ya Gama fada Magani ya kashe Kiran Yana rike bakin Al'ajabin Zahra Daman Yana Nan ya zage yana ta an tayo magana. Wayar ya aje yadan matsa baya Yana Kare Mata kallon ta burge shi matuk'a Dan ji yayi kamar ya sakata gaba yayi ta kallo, hannuwa ya bude Mata alamar ta shigo ya rungumeta, sun Jima a tsaye Saida yaji kamar kafafuwansa Bazasu iya daukarsa ba sannan ya Dan zameta suka zauna a gefen gadon, da kyar ya tashi ya shiga wanka Bai wani Dade ba ya fito ya saka Riga armless da wandonta three quater na Adidas dai tunda sune best kamfaninsa gurin sport wears, tana makake a jikinsa suka fito parlourn farko na sama In da aka aje musu dinner dinsu, sakwara ce da miyar Agushi sai black tea Mai Kayan hadin star anise a ciki, Saida sukaci abincin sannan suka dawo cikin parlour na biyu suka zauna duk ya kanainaye ta ya hanata sakat, nema yake ya ruda Mata lissafi ita Kuma Alla Alla take dare yayi ya karasa Mata labarinsa.
Saida ya mila ya mile Dan kansa ya Dan ragewa kansa zafi sannan ya fara fadin "Bari muci gaba ko" Kai ta gyada Masa Dan ita kam ba baka sai kunne.
"Wato precious Naga gararin rayuwa kowa fa juya min baya yayi babu Mai saurarena sai uncle Mustapha da Batool kawai, abin baqin cikin Wai a tsaya nayi bayani ma abun ya faskara ta ko Ina babu sauki a haka Muka kwana uku idan Kika ganni lokacin Zaki tausaya min a lokacin dukiya ta dai batayi min amfanin ba tunda Bata Hana an wulakqanta ba, a ranar na hudun na tsunci maganar Wai a ranar za'a daura mini Aure da Safna abunda ya yamutsa min lissafi kenan cikin tashin hankali na shiga wurin Ammi wallahi precious Ina shiga Ammi ta Mike tabar parlourn da sauri nabi bayanta Ina hadata da Allah akan ta tsaya taji gaskiyar abinda ya faru Amma kinsan me tace min?
Wai fa cewa tayi inje inyi abinda nake so tunda karana yakai tsaiko gani ga rayuwar Nan tunda fasadi na zaba duniya tafi Dan bagaruwa jima, wallahi a lokacin ji nayi kamar na mutu na huta nakeji,ga wani irin Abu da nake jinsa a jikina, precious wallahi Addu'oin da nake na azkar lokacin da kyar nake yinsu,Dana fito mabera na nufa naje yau dai na fada mata halin Dana tsinci kaina a ciki tunda nasan Bata San wainar da ake toyawa ba, Amma kinsan abun mamakin da tashin hankali itama sammankal duk abun iri Daya ya Zama Bata saurareni ba karshe ma maganganu ta yarfa min masu zafi ga shi Daman wani Abu na min sukuwar sallah a cikin kaina, Nan da Nan naji wani bacin Raina ya qaru ban baro gidan ba Saida naci alwashin saina Bata mamaki kuma kozan mutu saina nemoki duk inda kike a duniya Kuma a dakinta a gadonta Zan Fara saninki 'ya mace, kadafa kice Wai bani da masaniyar inda kike hummmm a'a ana bibiyar min ke ciki da waje, kinga lokacin Dana fito daga parlourn Hajiya Inna ko takalmi kafata babu banbi takan motar Dana shigo ba na Fara tafiya a kasa wani Abu Daya bani mamaki a lokacin precious wallahi Ina ganin kamar mutane basa ganina tunda konaje kusa da mutane bana ganin alamar sun San da mutum a kusa dasu gani ba boyayyan mutum ba, haka na dosa wata irin tafiya tamkar kad'ani akeyi kuma tafiyar wata iri ce Mai cin dogon zango a cikin lokaci k'alilan a cikin abinda Bai wuce minti arba'in ba ni dai sai ganina nayi a talatar mafara na fuskanci mutane suna ganina a lokacin Tunda Ina wuce Ina Jin ana fadar bawan Allah ko daga Ina? haka na dinga tafiya wlh ko gajiya banayi Dana baro cikin gari naji kamar Ina Jin barci na kwanta a wurin wata bishiya, to Ni dai daga lokacin bansan kuma Yaya akayi ba ni dai nasan na farka na ganni a asibiti ta tare da Abubakar wlh nayi zaton ko sokoto na dawo sai Kuma Naga bakin fuska su Malam Abu mafi daure Kai ganin Abbanku da nayi sai Lamarin yafi karfin Dan karamin tunanina na wancen lokacin Dan nasan wannan abun wani connection ne daga Allah Daya hadani dasu yasan abinda nake rokonsa dare da Rana, precious nayi dawafi a dakin Allah na Kai mutane suyi min Addu'a akan wani Abu da nake nema duk a kanki Dan Ubangijina kadai yasan yanda ya jarabci wannan zuciyar da soyayarki tun Baki San meye soyayyar bs, Kinsan Kuma shi maji rokon bayinsa ne Kuma mafi tausayin masu tausayi mafi jinqan masu jinkai Naga Ijaba, bana inkari da lamarinsa Amma na Kara samun yakin Dan Rahamarsa ce ta lullubeni ya kawo Habib ya ganni a wancen lokacin, ga wata sabuwa Ina Jin maganar mutane Amma Ni Kuma bana iya magana, lokacin na shiga tashin hankali ba kadan ba Dan ji nayi na koma mutummutumi, asibiti sunyi iya abinda zasu iya suka sallameni Baba malam da Abban ki su suka dunga Fadi tashi akan lafiyata Dan abun babu dadin ji na shiga wata irin rayuwa lokacin na Kara gane mahimmancin lafiya da tasirin Addu'a, su Habib su sukayi jiyyata a dakin soro na gidan malam har Allah ya bani lafiya, lokacin ne Abubakar ya fada min ai aikin da yake komai na tafiya dai dai, dan dai lokacin kina syprus to Nima ganin nesa tazo kusa saina nemi gurin Zama naje Bauchi nayi duk abinda ya kamata akan layikan waya da dasu system da credit card na bank da duk abinda ya kamata banyi kasa a gwiwa ba na Kira Sameer da Bilyaminu muka zauna dasu a dakin Dana Kama a hotel, Abu na farko Dana Fara shine kad'a musu warning akan inda nake kada naji kada na gani duk da Sameer ya fada min hankali fa ya tashi na barina gida gashi uncle saminu ya assasa daura min Aure da Safna, banji komai ba nasan suda ganina ba Nan kusa ba ko zan waiwayesu ba lokacin ba, aiki na bawa Sameer na Nemo ma'aikatan wata ngo's suzo mu zauna Ina son muyi aiki dasu a zahiri Amma ba sune zasu ringa harkar kudi ba, kinsan k'asar mu indai Zaki bada budi to kome kike nema kin samu Nan da Nan suka shigo muka Fara aiki Ni Ina gefe Sameer ne oga, ba Saina Baki labari ba Kinga yanda makarantar Baba malam ta Zama, ke kuma a can syprus din bamu barki sakaka ba sai Dana tura Omer ya shiga jikinki a can ya Zama idanuna ya Kuma yi Miki tayin soyayya sai akayi Dace kince Masa a'a sai dai kuna mutuncin da ta Kai ko siyyaya kikayi shi yake biya koba haka bane? Kuma 'yan Nigeria sai ake Baku wasu kudin scholarship daga wata kungiya MMD anyi haka? Ke naki yana ninka na sauran kunyi bincike kun rasa gano meyasa hakan yake faruwa haka ne? Kai kawai Zahra ta gyada Masa Dan ya kasheta da mamakinsa, cheeks dinta ya shafa a hankali Yana Mata smile har dimful dinsa ya Dan lotsa kadan Kinsan Allah da ban Aureki ba ina ga hummm.... Allah dai ya kyauta da dai Kam.. za'a Sami matsala Dan inaga maza biyu Zaki aura Dan Ni dai bazan hakura ba to sai Ubangijin Daya dasa soyayarki a zuciyar ya ta kaita al'amuran, Kinsan Muneeb Dan yayar mummy Badi"a ne?".
Wani kallon warrr tayi Masa na nuna mamaki, ban gane ba kasan shi kenan?.
Bar wannan maganar ta wuce sirrina ne bazakiji yanda aka haihu a ragaya ba, Sameer ne ya Zama Dan leken asirina duk yanda kaso aji wani Abu Sameer yaki fadin komai shima nunawa yake Yana zuwa ne Koda hasken da ake samu a Kan tafiyar tawa, Kuma duk abinda nake yiwa Hajiya Inna nace ya Dora Dan a Dan tsakanin jininta Saida yayi mahaukacin Hawa har Egypt sukaje da Uncle Mustapha da Mama mainuna surukar Aishat Ina da masaniyar komai Dan hatta bill dinsu na Asibitin Ina daga can nayi komai abinda ya darsa zargin Sameer yasan inda nake a zuciyar uncle Mustapha.
Sameer ne ya kawo min labarin Ashe lokacin Dana bar gida Batool rikicewa tayi a gidan ta Hana kowa zaman lafiya ta Fadi duk abinda ya faru a Ranar da lokacin Dana kawo musu Kaya da lokacin da aka Fara fitinar sai lokacin Sajjad ma yayi bayanin shima abinda ya sani, Kuma aka shiga bincike har gurin securities Suma maganar iri Daya ce data batool sai lokacin mutane suka Fara dawowa cikin hayyacinsu aka shiga tuhumar Safna da tambayoyi na hankali Wanda ya kamata ace tun Ina Nan akayi su, inda ta kafe kaida fata ita maganarta babu canji, Kamar batool ta hakura Ashe gidan uncle Mustapha yaje ta nemi ya shige Mata gaba tana son aiwatar da wani aiki, baiki ba yace ta fada masa menene? A nutse tayi Masa bayanin kamfanin waya na MTN da AIRTEL ze rakata zata bada aiki duk da zata iya amfani da sunan family din ko ID card dinta na dalibar koyon aikin shari'a Amma tafi son suje da Babba yanda za'ayi Mata aikin a Kan Kari.
Ba qaramin mamaki uncle Mustaphan yayi ba lokacin da sukaje kamfanin Dan lambobin wayar Sameera da Safna da uncle saminu da wata wadda baisan Kota waye ba ta bada tace wadannan takeso a bibiyar Mata tun daga Kira chart , messages dinsu duka daga Nan zuwa wata Daya haka sukaje Airtel ma ta bada suka caji nasu suma, shi dai uncle Mustapha Dan kallo ya Zama sai lokacin yayi nadamar Hana ma'asuma yin karatun law gasu Nan ridi-ridi babu Wanda yayi irin wannan tunanin sai 'yar cikinsu wadda take dibace ma a fagen karatun Amma harta iya irin wannan nazarin da aiki da hankali Wanda suka kasa su.

Cikin ikon Allah komai ya kammala suka Kira uncle Mustapha suka fada masa shi Kuma ya Kira Ammi yace ta turo Masa batool, tare sukaje kamfaninin kusan babu banbanci a aikin nasu sai ma na Daya kamfanin Daya Dara Daya fito da hujjojin zahiri Alfarma suka nema a Basu ma'ikacin da zeyi aikin Ranar da suke son abun ya kasance to kinsan dai yanayin Qasar indai zaka bude bakin aljihu yanzu ne zakaga biyan bukata, suna fitowa uncle Mustapha ya cewa Batool to ita nata aikin ya kare tabar sauran a gurinsa yashi Mata Albarka kamar me,ita fa batool ko Ammi Bata fadawa komai ba duk Fadi tashin da takeyi saboda haushin kowa tajeji gidan.
Kwana biyu da zuwansu kamfanin taji ana maganar Abbie na Kiran meeting na duka family a Babban hall din Nan da kukayi walima.
Mutane sun amsa Kiran kamar ba gobe Dan sun San da walakin goro a Miya, Uncle Mustapha ne yayi Addu'a da jawabin maraba ga jama'a sannan yace wani Abu yakeso kowa ya maida hankali ya saurara yaji sai mu yiwa kanmu adalci a ciki game da maganar Mahmud da yarinyar Nan safna, Jin haka yasa su Aunty Sameera da uncle saminu zasu tada Zaune tsaye, Abbie ne ya taka musu birki yace ko shi baisan menene ba tosu meye zesa su tada hayaniya Kan abinda bakasan menene asasinsa ba, dole suka hakura Amma zuciyar Safna kamar ta fito Dan mugun bugawar da tajeyi.

*_AUREN HUCE HAUSHI_*

AISHAT ISAH MUSAH.

(Maman Fateemah).


09061432330
Or

08055362975


Page 95.


______Ba'a dauki dogon lokaci ba ma'akacin kamfanin wayar ya hada komai ya saka microphone yanda na nesa zasuji magana, cikin abinda Bai wuce minti biyu ba maganar Aunty Sameera ta karade gurin ita ta Kira uncle saminu ta nemi ganinsa a lokacin take tamyarsa yaje gurin data fada masa a Nan ya fada Mata yaje har ya bada turare Wanda safnar zata shafa taje gurina idan na shaqa ban Isa nayi Mata musun duk abinda ta buqata Koda kuwa kwanciya da ita ne, shine suka hada tazo da system tayi min wannan shishshigewar Dana kasa hanata a Ranar da uncle saminu ya samemu Ni da ita da yamma Wanda yaso tun a Ranar ya hada min gwarama sai Kuma Allah ya Kare abun ya shashance, sai kuma sauran maganganu Wanda Basu shafeni ba, haka aka dunga sauraren yanda suka ringa kulla makirci kala-kala ita da uncle din har turo min Safna daki, Ashe duk setup ne.
Sai Kuma wayata da Safna a mabanbantan lokuta babu komai sai gaisawa da zumunci da Kuma requesting na kudi da dai sauransu sai Kuma wayar Safna da number din da Batool ta bada,a Nan kowa ya shiga shock Dan abin ba tsabta Dan duk abinda sukayi tun daga chart dinsu har Kira da voice note har video call ba'a rage komai ba Abu mafi tada hankali a cikin wayoyinsu sunyi maganar zubar da ciki ya Kai sau biyu, da irin yanda suke shirya haduwa a lokutan da take zuwa makaranta, a lokacin ne aka gane Ashe duk lokacin da tace ta tafi Niger state saurayin nata take bi har outside country suke fita, ta Nan aka gane tana amfani da layukan waya hudu da wayar ta yanda idan ta fita makaranta take rufe wayar tace saboda suna lectures ne.
Daga karshe aka dawo kansu uncle inda aka dunga sauraren makirci abun dai babu Dadin ji, har na karshen nan Wanda suka hada karfi sukaje har okene gurin wani matsafi suka karbo abinda aka turara min a daki da wasu tsubbace_tsubbacen da akayi Dan kowa yayi min naqi, duk ta waya suke shirya komai Dan a zahiri bazaka tab'a cewa da wata alaqa irin haka a tsakaninsu ba, a Ranar da abun ya faru sun jima suna waya da hada yanda abun ze kasance Dan turaren maganin da aka saka Aunty Sameera ce ta shiga da kanta tayi lokacin yaran sun fice sallah sannan Safna da uncle saminu suka shigo dakin lokacin da uncle din yayi waya da security din gidan Hajiya Inna yace Masa mun fito da zayyan, shine fa suka shirya min wannan makircin Wanda kowa ya kasa gane meye gaskiyar Al'amarin sai batool da Allah ya tsareta ita da uncle Mustapha, tunda aka Fara wannan fallasar su Safna da Sameerar ke zufa Shima uncle sadda Kai kasa yayi, mutane kuwa Nan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login