Showing 162001 words to 165000 words out of 280244 words

Chapter 55 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1062

Qafa ki maida taki duk inda yace ki zauna ki zauna".
"To Ammah,amma fa Kinga mahaukatan gidajen da yake kaini wallahi Sunfi Qarfin kwakwalwata Dan Allah ki taimaka kiyi min gata ki tambaye shi ya fada Miki gaskiya waye shi Kuma daga Ina yazo Kuma meye sana'arsa wallahi Ammah tsoro lamuransa suke bani. Fuska biyu gare shi wallahi ko suturar da yake sakawa a can ba irinta yake sakawa a Nan ba ki agogunansa fa Rolex ne, Kuma duk gidan daya kaini babu abinda babu hatta suturar da Zan saka da akwaita idan zamu shekara bazan nemi suturar sakawa ba shima haka, ban fada Miki ba harfa gidan Nan garin Saida na tarar da mahaukatan kayan sakawa a can".
Wayar dake jakar ta aka Kira abinda ya katse Mata zubar da takeyi kenan.
Tunda ta dauko wayar Ammah ke jinjina Kai da duk abinda zahra ke fada ta dauke shi rashin son Zama da Mahmud ne ke dawainiya da ita Amma ganin iPhone 16 plus yasa jikinta yayi sanyi wayar wajen 1. 46 a gurin zahra? Dole tasan waye 'yarta take aure ko kowa be mata wannan aikin ba ita zata yiwa kanta saboda akwai bukatar sanin waye shi, tunda zilai ma korafinta kenan akan gidan daya saka aka kaisu da Kuma yanda ake kawo Mata kudi ace shiya bada a Bata bayan sutura tace an Bata kusan kala goma babu na banza tace wasu ma Bata taba zaton sata samesu ko a Jace ba an Bata sabbin su.
Jin Mahmud ne yasa zahra Dan kallon Amma taga ko hankalinta Yana kanta sai taga ta Mike ta nufi kitchen ajiyar zuciya ta sauke Dan wasu kalamai yake fada Mata Wanda suka girmi shekarunta kamar bashi bane ya kwana zulumin lalurar Baba malam, wato yazo ya ganshi ya samu 'yar nutsuwa ze ishetq da wannan maganganun nasa masu nauyi a kwakwalwarta.
"Kina jina?"
"Uhmmm ina ji, Dan Allah kayi min Alfarma na kwana gurin Ammah wallahi nayi kewarta sosai".
Abinda kunnuwan Ammah suka jiyo Mata kenan tazo fitowa.
Jinjina Kai tayi tana ayyana bazaki mayar Dani sakaran uwa ba kibi mijinki can ku karata".
Ya koma taci gaba da abinda takeyi Daman fitowa tayi taji idan zataci fattira wadda aka yiwa Imam be Kai ga tashi ba taji ana neman mayar da ita shashasha ta barta ta kwana a Nan mijinta na can rakube kamar gwauro.


Mama ce a daki tana ta faman Kai kawo da waya a hannu ganin zahra ya daga Mata hankali ba kadan ba, a fill ta Fara fadin.
"Jar uba wallahi baze yuwu ba wannan ce matar Almajirin? Da sake wallahi Alhaji munafuttarta yayi yasan ko waye ya dauko agola ya bawa ga 'ya'yansa na cikinsa be Basu ba, wato ni za'a yiwa lullubin biri ko? Wai Ina Kika shiga ne Asabe! Naje gidan,na tura babu ke babu mahaifiyarki na Kira wayarki Bata aiki Kuma mahadin cimma burina Yana hannunki tunda Kika karbo ban Kara jin ko labarin Wanda ya ganki ba"
Ita kadai a daki tana ta buga sambatu kamar sabon kamu, Aunty Ladi ta Kira akace Mata wayar a rufe take jefar da wayar tayi Kan gado tana buga tsaki tana fadin. Wallahil da sake dole nayi Wani Abu yau ba sai gobe ba".

_AUREN HUCE HAUSHI_



08055362975



* MAMAN FATEEMAH*



Page 59




.......... Abincin kawai Ammah ta zubowa zahra ta fito mata dashi, lokaci Ahmad din yazo zahra ta bashi kudin da za'a sawowa Auta kayan kwalam, Ammah ce ta tsawatar Jin yawan abinda za'a sawo.
"Ki Bari a sawo masa kawai Ammah ba sai ya rinqa zuwa makaranta dasu ba tunda yace nasa kinyi kyauta dasu"
Tana Ciro kudin magaji ya shigo da manyan ledoji a hannu Yana fadin.
"Ina Ammah Bari kiga Aunty zilai yanda ta zama inaga supplement Tasha ta Zama haka naga alama harda bleaching takeyi Kinga yanda ta ...
Bai karasa ba yaja birki Yana ware idanu.
"Kam bala'i! Wannan yarinyar yaushe kikazo? Gaskiya kinci Amana koki nemeni duk amincin dake tsakaninmu dake har kizo garin nan ki mike kafa kiyi awanni Baki bada cigita ba,wato kin Zama DONE ko? yanzu na baro mijinki a Asibiti shima ya wani zama Jan wuya,da gani Yana Gane garin Dan ba haka yabar garin Nan ba, ku fad'i gaskiya dai ko kun danne Kan dollars din America na qungiyoyin da kuke yiwa aiki?".
Pillown kujera karami zahra ta jefa Masa daga inda take zaune.
"Allah ya shirye ka magaji, Kai Kullum baka girma, shi yasa nafi son Zama da Ya Imam wallahi saboda komai nasa gentle yake yinsa, amma Kai kamar rikon kauye,gaskiya da a kauye akayi ka da anga tabargaza, Wai nice yarinya ka tafi ka nemi yarinya ni yanzu yayarka ce dole kace min Adda, sauran amsar Kuma sai mun kebe Zan baka ita".
Dariya ya dauka Yana tafa hannu.
"Very good, inye yaushe kikayi Baki irin haka? Da sake wallahi Nima azo ayi maganar manya auren nan zanyi, kuga yarinya ta zanzare tayi bulbul sai magana fal cikinta".
"Magaji! Magaji! Wallahi ka fice kada na Bata maka Rai yanzu, daga zuwanka zaka damu mutane, ka Dade bakayi auren ba mutumin musawa".
Hannuwa ya hade irin yanda indiyawa sukeyi.
"Sorry Ammah idan na fita dawa zatayi Hira ki Bari mu Dan cukusa kadan dan Allah".
Sallamar zilai ce ta katsewa Ammah hanzari abinda zata fada.
"Lah! Aunty zilai har kun karaso? Sannu da hanya".
Zahra ta fada, tana kallon magajin.
Yara ne suka shigo da Kaya suka sauke suna gaishe da Ammah, sannan suka gaishe da zahra.
Da sauri magaji ya fita Yana Fadar.
"Ina Zuwa ya fice.
Wasu kayan ya dauko, zahra na ganinsu ta gane Wanda Zayyan ya aje a gidan dake BAWO ROAD ne, sai yanzu taga Ashe kilishi ne dasu dabino da cukui sai tarkacen kayan zaki dasu BAMA.
Sauran Kuma suna cikin ledoji.
Gurin da Ammah ke zaune Zilai ta karasa ta tsuguna tana fadin.
"Sannu da gida Ammah mun sameku lafiya? Ashe Kuma Baba malam haka tsautsayi ya sameshi, Allah ya bashi lafiya, Kuma nagode Ammah Allah ya jikan mahaifa ya yiwa zuri'a Albarka a tayani godiya gurin yallabai nagode, nagode".
Sai hawaye.
"Ikon Allah! ku kuma da 'yan kuka kuke shigowa garin? itama mutuniyar da kukan ta shigo min, amma na fashimci kukan Dadi kukayi gaku nan kun zama wanke hannu ka taba".
Yar dariya zilai tayi tana goge hawaye.
"Wallahi Ammah duk yanda Zan fada Miki karamcin da akayi min Ni kaina baze misaltu ba Kinga waccan jakar wallahi duk suturu ne babu ta karamin kudi a ciki Kinga yauma abinda oga Sameer ya bani".
Ta dauko envelope brown ta dora a gefen kujera inda Ammar ke zaune.
"Tab Aunty zilai kice shagalinku kuke a kanon kun ninke mu a nan, da gaske Ammah wannan yarinyar ma kukan tayi Miki?".
"Innalillahi! Magiya fice Dan Allah".
" Kiyi hakuri Ammah, Amman fa ba inda zani nabar wannan sabgar Arzikin Kinga fa".
Ya fada yana nuna kayan dake zube a tsakiyar parlourn.
"Allah ya shirya"
"Amin" suka fada, gurin zilan Ammah ta juya.
"Lafiya kalau muke, wallahi kuwa Haka Allah ya kawo wannan kaddarar sai fatan Allah ya bashi lafiya, ki dauke abunki an gode madallah".
Harta yunkura zata tashi ta koma tana fadin.
"Ga kayan tsara Nan inji oga Sameer yace a kawo Niger sukaje aiki".

* * *

Baba malam bashi ya farka ba sai kusan hudu da 'yan mintina, lokacin Mahmud ne kadai a dakin Shima ya rigasu fitowa daga masallacin ne, da sauri ya taso ya karasa kusa dashi.
"Sannu Baba ya jikin?"
Mahmud ya fada Yana rik'e hannun malam Daya Miko Masa.
"Alhamdulillahi Ala kulli halin, duk abinda Ubangiji ya yiwa bawa akwai hikima a cikinsa, Kuma bawa baya wuce K'addararsa sai dai neman sauki,Haka Allah ya hukunta tun ran gini tun ran Zane rubutaccen al'amarine baya canzuwa,ita kaddara haka take sai dai fatan Allah ya bani juriyar da dangana, inaga iyakar takawar kenan wadda akayi a baya na gode da kokarin ku naji jiya kaima bakayi barci ba, Allah yayi muku Albarka ya saka muku da mafificin Alkhairinsa, ka shigo cikin rayuwarmu ka zamar Mana fitar data haske Mana duhu, Ina hadaka da girman Allah kayi hakuri bisa abinda akayi maka ka koma ga mahaifanka nasan ba manta garinku kayi ba na dai kyaleka ne saboda halin bacin ran da nake ganinka a ciki,naso idan ka dawo na sakaka a gaba muje ga iyayenka kodan halin damuwa da nake ganin mahaifiyarka a ciki, gata da matsakaitan shekaru sai a tausaya Mata, Mahmuda ba'a fushi da iyaye kaji, sun 'yan lallabone, to sai ga kaddarar data sameni Kuma lallai naso yin wannan Alkhairn Amma bamu San abinda Ubangiji ke nufi da hakan ba shi Allah s.w.a baya da sabon aiki".
Tunda Baba malam ya Fara magana Mahmud ya sadda Kansa kasa Bai dago ba Saida yaji ya saka aya a maganarsa, amma fa maganar ta doki zuciyarsa ba kadan ba.
A hankali Mahmud ya dago idanunsa Wanda sukayi jajur badan Yana namijin duniya ba da kuka ze fasa kamar mace, hannun Baba malam ya Kara rik'ewa cikin nasa.
"Baba ka daina fadar haka in Sha Allah saika cigaba da taka kafafunka Kuma niyyarka ta Alkhairi saika idata da izinin Allah in dai akwai inda suke magance matsala irin taka da Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w sai an kaika, daman Nima nayi tunanin fada maka asalina idan na shigo garin sai Kuma wannan ibtila'in ya faru, kayi hakuri Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne, yanzu ka kwantar da hankalinka ka cire damuwa in Sha Allah zaka warke, ai sunce ba wata damuwa Mai yawa bace bayan ne ya Dan bugu, harma oga sameer yazo ya gana da likitocin bansan dai yanda suyi ba, sai ya shigo muji yanda za'ayi"

Habib da Sameer ne suka shigo tare da zugar dattawan unguwa masu zuwa dubiya tun safe Dan mutum be yanke ba tafe suke maza da Mata, Dan ma iya Abu na gida tunda tazo da safe taga jikin ta Fara koke koke Habib ya mayar da ita gida.
Sun Jima suna Masa Addu'ar samun lafiya sannan suka tafi tare da ajje Masa kudi masu Dan kauri.
Mahmud da Habib suka Kai shi toilet suka taimaka Masa yayi alwala suka dawo dashi suka kwantar yayi ramuwar sallar da ake binsa.



* * * * *

Tunda Mama taga shigowar zilai da yanda taga zilan ma ta koma, sai hankalinta ya qara duguzuma ya tashi, nan da nan ta shige toilet dinta dole ta nemo malam na Bande.
Cikin sa'a ringing Daya ya dauka Yana fadin.
"Idan kin Kira ta baci kenan, yaya ake ciki!?"
Babu Bata lokaci ta Fara bayanin.
"Malam da matsala sosai Dan komai nema yake ya cukude, da Alama Alhaji munafutta yayi ance an bawa yarinyar nan Almajiri Qolo,amma wallahi kaga yanda ta koma kamar matar shugaban Qasa, ko Mai aikin mu da suka tafi tare ta Zama abin kallo duka a cikin 'yan satiitka Dan Allah ayi wani Abu kada bakin cikin su ya kasheni, malam ga Kuma na nemi Asabe na rasa duk komai Yana neman lalace min".
Wata dariyar marasa nutsuwa yayi duk da yawan shekarunsa Yana fadin.
"Ai daman na fada muku ayi duk yanda za'ayi ta turara turaren wutar nan sai kukayi sake kayan suka fada a hannun yaron mijinta, sannan Kuma Kika kasa hakuri mu karkare Kika canza guri, wannan shiya rusa duka ayyukanki na baya,maganar Asabe Kuma bana Jin zaku Kara haduwa da ita nan kusa dan naga tayi nisa sosai da nan din, naga alamar kamar korarta akayi daga garin saboda Wani asirinki Daya tuno ban dai fashimci abunba sosai gaskiya amma Yana da nasaba da ita wannan yarinyar gaskiya sai dai itama kanta yarinyar Bata sani ba".
Karkarwa jikinta ya dauka ta Fara hada jibi.
"Dan Allah malam ka taimaka mini kada maganar nan ta fito har abada, kayi duk yanda zakayi ita kanta Asaben a dauke Mata hankalinta daga garin dama jahar Baki Daya. ko nawa ne Zan baka fatana kada asirin ya tuno, ita Kuma kayi abinda zakayi kada ya Kara marmarin Zama da ita har abada yanda ya kawota ya tafi ya barta a nan kada ya Kara tunawa da ko sunanta dama garin gaba daya".
"Ki kwantar da hankalinki, Naga tafiya Mai nisa da zeyi Kuma gaskiya banganta a kusa dashi ba, zata zauna Dan Zama kam Amma Kamar yanda nasha fada Miki Banga rabuwa a cikin aurensu ba in dai shine ze saketa to bangani ba".
"Zan turo maka da sako ayi duk abinda ya Kamata kawai".
Ta fada tana sauke wayar daga kunnenta, iska Mai zafi ta buso daga bakinta tana fadin.
"Haba biri yayi Kama da mutum shi yasa na nemi Asabe na rasa kaura wambai tayi batan dabo, to waye ya Kamata har malam yace asiri ya tuno kenan wayarta ma ankwace tare da sauran sakonnin da zata kawo min, Kuma sakon farkon ma hannun yaron mijinta ya fada".
Ta maimaita yaron mijinta yafi sau biyar.
"Me hakan ke nufi kenan? Ina ga ko cikin yaran makarantar ne, amma a cikinsu waye ze budewa Asabe Ido har ya iya koreta daga garin irin haka afujajan da gaggawa?".
Haka ta zauna tana faman kullawa da kwancewa babu Mai Bata amsa.
Abincin kusan kala uku Ammah ta saka Alawiyya tayi tunda itama ba laifi Ammah ta horata, zilai ce ta shiga ta tayata duk da Ammah tace ta huta ita da ta dauko hanya, Amma Sam taqi Zama ta shiga sukayi tare, a manyan warmers aka Zuba abinci, magaji Ammah ta Kira yazo ya Kai Asibitin.
Zahra bacin da Bata samu ba jiya ta shige bedroom din Ammah tayi kwanciyar ta daga ita sai vest da Wani wando skintight ta saka wata hula Mai budedden Baki ta zubo da gashinta baya ta Fara barci hankalinta kwance.
Sai da Ammah ta Gama sallamar magaji ta shigo dakin, tsayawa tayi tana Qarewa zahra kallo, yanda ta ganta komai nata ya kara cikowa kirjinta da kasanta suka ciko sai zuciyarta ta shiga kokonton anya babu yaron ciki a jikinta kuwa? duk da bangaren ta ne da yake abin anzo Kan 'yarta ne sai ta samu confused.
Abinda zata dauka ta dauka ta fice daga dakin.
Sai kusan magariba zahra ta farka, wanka tayi ta shirya ciki rigar Atampha royal blue da ratsin Baki Mai manyan ganye, dinkin yaso ya matseta daga kirji abinda ya Bata mamaki ke nan dan kasa fitowa tayi Saida ta rufa da gyale sannan ta iya fitowa, sabanin da rigar har Dan yawa tayi Mata daga wurin breast cup din.
Su Aunty zilai ta samu suna gyara parlourn, Zama tayi tana tana musu sannu, Alawiyya ce tace.
"Aunty zahra a Zuba miki Abinci?".
Dan yamutsa fuska tayi.
"A'a bana Jin yunwa duk cikin ma bana jin Dadinsa, ki hado min salad kawai ya isheni sai ki hado min da fruits salad ya isa".
"To Bari naje na hado miki" .
Ta fada tana barin gurin.
"Aunty zilai Ina Ammah ne naji shiru ba motsinta?".
"Tana sabon part din Abba na bayan Nan kinsan Ammar mu Bata daukar raini ta dawo da Abba nan ta raba musu turaka ita da Mama, kinsan halin Mama har Saida takai hakurin Ammah karshe ta yiwa part din can yaji ta nuna sai dai a raba ko Kuma ta hakura ta barmata mijin duka shine ya dawo sabon nan".
Baki zahra ta rike tana kallon Aunty zilai.
"To ke Aunty zilai waya Baki wannan dogon labarin naga daga ni har ke bama garin Nan?".
"Sahura ce ta bani labari dazu Dana shiga part din mu Zan aje kayana".
Tsaki zahra tayi tana fadin "Kai Allah wadaran naka ya lalace, har abada sahura bazata daina gulma ba na tsani mutum Mai fuska biyu".
Hira sukaci gaba har Alawiyya ta kawo Mata hadin salad din.
Kiran sallah ya tashe su daga parlourn.
Zahra na sallah Ammah ta shigo, cikin sabuwar kwalliya sai kamshi take bazawa, Abu ta dauka a wardrobe dinta ta fice, zama zahra tayi tana Addu'ointa har aka Kira sallar insha'i.
Tana cikin sallar ne wayarta ta dauki Kara, sau biyu ana kira tana tsinkewa, Saida ta Idar ta dauka *Amor mue* ta gani Dan murmushi tayi.
Kiransa tayi lokacin ya fito harabar Asibitin duk ya gaji so yake ya kwanta ya huta kiranta yayi ya fada Mata ga Zayyan nan ze daukota ta duba Baba malam din shine Kira biyu Bata dauka ba Yana niyyar na uku saiga kiranta ya shigo.
Picking yayi tare da amsa sallamar ta.
"Ina sallah ne ka kira, ya jikin Baba malam din?"
"Jikinsa Alhamdulillahi, ga Zayyan nan na turo shi ya daukoki kizo ki duba shi".
Shagwab'e fuska tayi kamar yana ganinta.
"Nayi zaton sai gobe tunda dare yayi, pls ka kirashi kace ya dawo Dan Allah kaji".
"Do what I said".
Ya kashe wayar gaba Daya.
Ta gumi ta Zuba tana zancen zuci.
"Yanzu ko kwana dayan baze barni nayi a gidan nan ba saboda Allah shi yafi son Kullum Yana manne Dani kamar yaron goye"
Dago Kan da zatayi taga Ammah tana tsaye ta Zuba Mata Ido.
Karasowa tayi tana fadin.
"Lafiya Naga kin hade rai?".
"Ba shine yake Wai ya turo a daukeni naje ba duba Baba malam ba, nace ya Bari Saida safe yanzu dare yayi shine yace A'a".
Godiya ga Allah Ammah tayi a zuciyarta yayi maganinta yarinya da muhallin ku kice bazaki tafi ba.
Amman a zahiri sai tace.
"Aida kinsan Baki duba shi ba da tun yamma zilai ta rakaki kunje tare, nima Abbanku ne da baya garin da tun safe naje naga jikin nasa, Amma Zuwa safe in Sha Allah Zan shiga na duba shi tunda Abban naku Yana hanya".

Badan ranta yaso ba ta hakura zata bi Zayyan din.
Handbag dinta ta dauko ta bude ta Ciro rafters na 'yan dubu dubu guda uku ta zube a gadon Ammah.
"Wannan fa? Ammah ta nuna da hannu.
Kiyi amfani dasu, ni babu abinda zanyi dasu dazu ya Zuba min a jaka".
Daga parlour suka jiyo sallamar Ya Hamzan Mama,Ammah ce ta leko ya gaisheta yana fadin.
"Ammah a yiwa zahra magana ta fito ana jiranta".
Ya juya ya koma, shigowa tayi ta zauna gefe Daya kusa da zahrar.
"Ki debe kudin ki mayar jaka waya fada miki haka akeyi daga kinga miji ya aje Abu kice naki ne ke aka bawa? Ba haka akeyi ba ko zasu shekara baka tabawa duk ranar Daya waiwayo yace bani ki dauko Masa, to Wai mema yake sayarwa da yake Wasa da naira haka Nima fa lamarin ya Fara sani a cikin kokonto kuje yanzu Amma dole a fadada bincike a Kansa, ki duba akwai sakon da Hajiya kaltume ta bada a kawo Miki a ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login