Showing 198001 words to 201000 words out of 280244 words

Chapter 67 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1044

ne haka totally ta canza Masa yanda ta nuna tamkar Bata taba saninsa ba ko gaisuwar Daya Raina ta Hausawan baici arzikinta ba.
Remote ya dauka ya kashe kallon Yana fuskantar Aishat.
"Shatu Wai me yake damun yarinyar Nan ne ko magana fa batayi min ba ta wuce, kota fada Miki wani Abu da nayi Mata, wato Naga alamar raini ya Fara shiga tsaninmu.
Zama tayi daura dashi tana fad'in.
"Toni Ina Zan sani ne dazu dai ta fada min mijinta ne ya hanata zuwa Asibitin Wai yace kada a jankwalo Mata wani Abu tunda a Nigeria sun Basu tabbacin babu sauran ciwon".
A zabure ya gyara Zama Yana wani kankance idanu.
"Kikace menene ? Mijinta kome?"

Gyada Kai tayi tana bashi assurance na abinda ta fada.
"Mijinta fa kikace? Haka ta fada Miki?".
"Eh haka ta fada min dazu kafin mu fita kasuwa, harma tace min Bata tare ba sai ta komai gida, gaskiya mijin yarinyar Nan yayi Dace da mace ta gari Naga alama tana jida mijin nata...."
Bai jira yaji abinda zata fada ba ya nufi dakin data ke.
Yanzu ma ta b'ame dakin Yana zuwa yaji shi a rufe, baiyi knocking ba dawowa yayi ya zauna Yana huci, Nan da Nan Yana yinsa ya canza har abun yaso yaba Aishat tsoro.

Ita ta rasa wane irin lamari ne haka idan ma da wani Abu a tsakaninsu to a Cikin gidan Nan ya faru Dan jiya harta kwanta lafiya kalau suka rabu da ita, Amma wayewar garin yau aka tashi da wannan sabon canjin daga gareta.

Har tausayi ya Bata da gani Yana Cikin damuwa..
"Dan Allah Dan sonka da Manzon Allah ka fada min meke tsakaninku da wannan yarinyar dazu naji kana fadar maganganun da suke nuna kamar Kaine ke Jan ragamar rayuwarta wacece ita? Wace irin alaka ce a tsakaninku? Yarinyar Kace? Ko matarka ce? Ka fada min Kona samu nutsuwar zuciyarta,wallahi duk duniya babu Mai Jin wannan maganar".

Bai dago ba harta Gama fadar abinda ke bakinta, yasan Dole ya fuskanci tuhuma daga Aisha dan ya kasa controlling Kansa tun lokacin Daya fuskanci tana fushin da baisan Kona menene ba da Kuma ma'assasar yinsa ba.
Motsin bude kofa yasa mahmud dagowa yaga waye, yasan dole ya kasance ahalin gidan ne.
Abbas ne ya shigo rataye da jakar laptop dinsa, kallon kallo aka shiga yi tsakanin su Mahmud yasan ko rantsuwa yayi babu kaffara Aishat ce ta gargado shi tunda jiya tace masa aikin wata biyu zeyi a Jamaica kafin ya dawo duka jiya kuma satinsa uku a can, inda yake ya tsaya Yana warewa Aishat hannu idan da sabo mahmud ya Saba ganin wannan sabgar tasu.
Hannunta ya riko suka shigo ciki Yana kallon mahmud Wanda ya yi fuska.
"A'a sweetie wa nake gani kamar 'yan gudun hijira?"
"To gashi Nan dau".
"Ammah bansan lokacin da kika Zama Mai fuska biyu ba, shine kika zagaye Mika gayyato min mijinki ko?"
Hannun Aishat Abbas ya saki Yana nifar gurin mahmud, dariyar farin ciki Yana Dan doka kafadarsa.
"My man kace mun ciri tuta tunda mune masaukin bakin, dan duniya wallahi Mahmud baka da dama,kayi masifar bamu kafa Wai ashe kana Bauchi state, Bari na watsa Ruwa na fito nayi welcoming dinka sosai".
Harara mahmud ya Kara zubawa Aishat ita Kuma ta wani dauke Kai ai dai ta samu mataimaki tunda ita ya rainata Yana it's shata Mata layin da bazata iya tsallakewa ba gara maza su shiga.
Suf ta wuce tana fad'in Bari Fara maka preparing na kayan wanka".
Saida ta wuce Mahmud yace.
"Ya Abbas yaushe matarka ta koyi 'yar kasa ta iya fuska biyu, nace Mata fa kada naji kada nagi shine ita Mai mijin ta tattago ka babu shiri kuzo koyi mini taron dangi, dama kayi zamanka daga Nan Sokoto nayi ayita ta Kare".
Ya fada Yana huci, Abbas na ganin haka yasan da abunda ya tunzura shi.
"Koma dai menene Abbie yace mu kaika sokoto dead or alive".
Ya wuce shi yayi strais da sauri.


Har Abbas suka sauko Yana inda suka barshi,.bayan Abbas yaci abinci ya dawo kusa da mahmud ya zauna.
"Wai me yake damunka ne ko baka da lafiya mu wuce asibiti? Ko Kuma malantar ce tasa ka zama haka? Kasan ku alarammomin nan da izza kuke".
Ya fada Yana dariya, shima mahmud din dariyar yayi.
"Kai Amma Aishat kin kware gurin kinibibi yanzu har kin fada masa wannan maganar gaskiya min Dena sirri dake tinda yanzu babu Aminci a tsakaninmu kina da naki ma'amincin".
Itama dariyar tayi tana nufar corridor din dakin Zahra, tana tunanin wayon yarinyar da gani akwai abinda suke boyewa su duka Dan da alama horo ne take Masa a Cikin ruwan sanyi Dan ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba da wata a kasa.
Cikin ikon Allah tana kokarin knocking taga Zahra ta bude kofar tana sabe da Yar gidanta Wanda ta tashi daga barci.
"Sannu Aunty, gata ta tashi tun dazu batayi dai kuka ba na Bata fresh milk dai sai Naga gara Tasha natural nata dai".
Ta fada tana Mika Mata Afnan din, abun mamaki sai yarinyar taki zuwa gurin uwar.
"Huta roro Nima na huta da tsotsa, amma kuzo muje ki gaisa da sweet heart ya dawo shine ma yake tambayar Afnan din tunda yau Abulkhairi baya Nan yaje week end gidan Dr Suraj abokin Daddynsa".
"Allah sarki shi yasa banganshi ba Ashe baya gidan".
Bata bukatar komai Dan ta yafa wani veil Amma karamine ta saka abaya Dubai maroon Mai adon stones kanana saita haskata sosai yarintarta ta Kara fitowa da wani sirrin kyau Dan asali ga kanshin turarenta da Kuma irin Wanda Hajiya Amina ta hada Mata masu janyo Hankalin oga duk irin kamewarsa kuwa.
Tare suka Jero suna magana wadda tasa Zahra yin wani tsadedden murmushi sai akayi dace duk su biyun suna facing din hanyar.
"Tabarakallahu ahasanil kaliqin".
Abbas ya fada.
Shi Kuma Dan gogan ya kasa dauke idanunsa daga kanta sai yaga murmushin kamar da gayya take yinsa.
Cikin takunsu na matan da suka San takan gayu suka karaso parlourn, sallama Zahra tayi.
Abbas ne ya samu zarafin amsawa shi kuwa mahmud tamkar an rufe Masa Baki, ai shi Abbas Bai zaci haka zahrar take ba yanda sweetie ke bashi labarin ta Sai yaga ai Sam Bata iya fasalta mutum ba.
Afnan na ganin Daddy ta shiga irin rawar murnar kaga abinda kake so din nan da Yara sukeyi tana zillo gurinsa zahrar ta nufa da nufin ta kaita.
Ita da duk saura ba Wanda yaga lokacin da mahmud ya diro gabanta Dan ja da baya tayi da sauri tana fad'in.
"Subhanallahi! Lafiya meye faru?".
Baiyi wata wata ba ya rungumosu ita da Afnan din dake hannunta.
Kici kicin kwacewa take Dan Bata taba tunanin zeyi irin wannan danyan aikin ba.
"Na shiga uku! Aunty ku taimaka min Dan Allah ku janye shi inaga bashi da lafiya kada yayi Mana illah Ni da yarinyar nan".
Ta fada tana kuka.
"Wallahi bazaki sakamin ciwon zuciya ba kin hanani sakat tun safe kin Hana ko fuskarki na gani,kinki yarda muje asibiti, me nayi Miki Mai zafi haka har kike ikirarin Wai mijinki ya Hana kije Asibiti, waye mijin naki bayan ni? Fada mini!!!..????"
Ya fada Yana hargagi abinda Bata taba gani ba kenan a iya zamanta dashi,kuka Afnan ta kwallah saboda yanda ya matsesu ga Kuma hayaniya da yake musu.
Da sauri Abbas ya taso yaga mahmud din kamar baya cikin nutsuwarsa.
Hannunsa Daya ya kamo sai yaji jikin nasa na tsuma.
Daidai kunnensa Abbas yayi magana.
"Pls sakarta kaga ka saka yarinya kuka, ka nutsu ta fada maka me yasa tayi hakan kowa ai yasan taka ce Ina ga da abinda kayi Mata Mai ciwo".
Da kyar ya yarda ya saketa ita da yarinyar. Zaunar dashi Abbas yayi ai Zahra na Dora yarinyar a cinyar uwarta lokacin Abbas na can Yana bashi Baki ta fice.
Tana shiga tayi locking din door tana sauke numfashi tare da goge 'yan hawayenta na karya data kakarosu.
"Wallahi saina rama zakayi bayani da bakinka guy ni zaka yiwa cin fuskar da ze Zubar min da daraja da kimata sai zuciyarta da Bakinka sun Fadi gaskiyar da kake boyewa, Kuma Wallahil Azim addu'ar tsamiya yanzu na Fara har FAHAZAMUHUM BI'IZIMILLAHI YA WADUDU YA JAMI'U MALIKIN NASI MALIKI YAUMIDDIN zanta zabga maka sai ka Raina kanka kasan Dan an baka kyautar zahra ba Yana nufi Zan Zama matar shige ba, sai duniya ta shaida zahrar Zahra ce, tayi kwafa ko yanzu na rage tension ko ya yake tunda kaima kaji a jikina ka Kuma karyata maganar daka fadawa 'yar uwarka jiya, Wai bakaga wadda tayi maka ba, sai kasan bayanin da zakayi musu Kuma tunda magana zarar bunu ce bata komawa.

Lokacin da Abbas ya juyo da zummar yiwa Zahra magana yaga sai filin gurin kallon Ina take ya yiwa Aishat..
"Ta gudu Ina zata tsaya ya nakasa ta yayiwa mijinta asara,kuma saboda Allah sai ka kakume Matar mutane da yammacin gari yaushe ka Zama haka yarinya da aurenta da komai wannan kasan haramun ne basai an fada maka ba, Ina cewa gida Daya kuka zauna ba diyar malaminka bace me yasa kasan kana sonta kayi shiru har wani ya aura ni Naga kokarinsa Daya amince ka taho Masa da irin wannan diamond baby din wata uwa duniya baya tsoron sharri shaidan ya gitta tunda gashi a gaban mutane ka iya rungumeta yaya idan daga Kai sai ita ne ai labarin ba irin wannan bane ki.."
"Stop!!!..... Aisha, ni kike fadawa abunda yazo bakinki? to Zahra halaliyata ce matata ce ta sunna".
Ya fada a zafafe tashi yayi ze fice da sauri Abbas ya riko shi.
" Dawo magana zamuyi ta fashimta".
Baiyi gardama ba ya dawo ya zauna, ita dai Aisha rasa ta cewa tayi wai barawo a hannun Mata.
Very close dashi Abbas ya zauna ya riko hannun mahmud Yana fadin.
"Munji matarka ce amma yanda sweetie ta fada min kace matar ubangidanka ce me yasa ka boye mata Bata cancanci haka ba, kasan irin wahalar Dana Sha da ita lokacin da case din Nan ya taso? yanda kasan zata zautu wallahi Amma sai ka dawo Mata da wata fuskar daba taka ba duk rintsi bakwa rufewa junanku komai, kasan ta fada min cewar wallahi matarka ce Dan ta shaida bazaka taba yarda kayi tafiya da mace irin wannan da mace kamar wannan babu alaka Mai karfi a tsakaninku".
Mahmud ji yayi duk ruwa ya cinye shi yarinya karama ta dagula masa lissafin da tasa ya saki layi duk yanda yake shirya nasa planning din ta rusa a lokaci daya yayi amansa ya lashe.

"To tayi hakuri ni kaina bansan me yasa na kasa fada Mata ba Ina Jin nauyin yanda Zan tunkari Ammi da Abbie da wannan maganar ba wallahi, sai Naga nayi wani Abu Daya sabawa al'adar mu ta Malam bahaushe, Kuma ita na rasa abinda nayi mata lafiya kalau mukazo gidan Nan Amma ta sauya min na rasa abinda yake min dadi wallahi Ya Abbas yarinyar nan itace weakness dina a rayuwa ni kaina nasan hakan, itace fa wadda nake fada maka na gani da dadewa a jirgi ita da Abbanta ka tuna?".
"Off cause anyi haka,Amma how comes hakan ta faru?".
Furzar da iska yayi daga bakinsa.
"It's long story, idan ka huta zamu tattauna akai, yanzu dai ki tashi like kiyi min Biko tunda Naga alamar kina da masaniyar laifina".
Baki Aishat ta dafe da hannu Wallahil Azim ban sani ba, nifa duk abin Nan hasashe nake yi ban tabbatar ba sai yanzu, ni wannan aikin ba nawa bane Kai zaka gyaro kayanka da abinda kayi Mata tunda Naga Bata da kwaramniya Sam, Kuma ya zakayi da ita kenan? Zakaje kace ga matata nan tsaraba fushin da nayi ko Yaya za'a kayi?".
"Ki Bari kawai alkawarin da nakeso kuyi min mu rufe maganar nan a nan duk da Faruq ma ya sani amma nasan tunda na kada Masa warning bazeyi karambanin fadawa kowa ba, nina taro match dina Ni zanyi playing din kayana kawai kuyi min addu'ar samun nasara kada Ammah tayi min nak'i".
Ya fada Cikin raunin murya.

*AUREN HUCE HAUSHI*


MAMAN FATEEMAH

09062432330

Or

O8055362975.



Page 72


........... Cikin kankanin lokaci mahmud yaji ya Dan samu nutsuwar Daya rasa, yarinya karama ta saka shi sakin layi a gaban mutane, ita dai Aishat sai jijjiga Afnan takeyi wadda har lokacin take 'yar mita, tashi Mahmud yayi da nufin barin gurin, Ya Abbas ne ya riko Masa hannu Yana girgiza masa Kai.
"Dawo magana zamuyi ta fashimta, baiyi gaddama ba.
"Kana ji yanzu ka Bata sarari ta huta ta Kuma Huce daga fushin da tayi da kai, idan so Samu ne ka koma gidanka ka kame kanka, kada ka Bari ta Kara ganinka Nan kusa har sai an Kai wani limit da zata nemeka ruwa a jallo ta rasa yanda ko kun hadu babu saura fishi sai dokin ganinka dole ba Zama very strong a fannin soyayya Kaine namiji kada ka yarda ta gane itace rauninka, sannan dole ka koyi takatsantsan kasan inda na dosa idan ba haka ba za"ayi amfani da wannan damar a cutar maka da ita Koda ta furucin Baki ne".
Shiru mahmud yayi Yana saurarensa wato shi kansa zaman takewar auren sai an shirya mata, Dan rausayar da Kai yayai yana fad'in.
"Anyway shike nan,Amma da so nake ta yarda muje asibiti su dubata tukunna sai na wuce din".
Wani kallon me yake damunka Ya Abbas yayi Masa.
"For God sake! Ashe bazaka Zama Mai karfin ba kenan? Tunda nace ka kame kanka ai sai kayi yanda nace ko, tashi mu fita ja rakani na dubo patient din namu ma ida discussion din a hanya tunda Naga alama ka rifta da yawa".
Ya fada Yana Masa dariya, sumar kansa ya shafa shima Yana murmushi.
Bayan fitarsu Aishar Goya Afnan tayi so take tayi barci, Bata Kara bi takan Zahra ba ta shige kitchen ta Dora ruwa ta dauko kaza ta Fara gyarawa ta Dora a wuta ta debo fresh fruits ta wanke ta Fara hada fruits salad ta saka a fridge tayi lemon kankana da Madara pepper chicken tayi da chicken rice sai coslow data hada ta dafa ruwan tea Mai hadin spices masu Dadi na dafa tea kafin magariba ta Gama komai, Babban tray ta hadawa zahra kayan bude Baki ta aje a gefe sannan ta ringa fita da nasu zuwa dinning tana jerawa Saida ta Gama komai ta dauki na zahra lokacin har duhun magariba yayi, knocking Daya tayi Zahra ta bude Mata ta matsa gefe tana fad'in.
"Sannu Aunty da aiki Aunty".
Ta fada tana karbar kayan Amma taki yarda su hada Ido.
"Zanje nayi sallah idan na Gama zamu zauna dake Ina so mu tattauna wasu abubuwa".
Aishat ta fada tana juyawa.
"To Aunty zanzo basai kin dawo ba".
Dan dakatawa tayi da tafiya ta waiwayo.
"Kiyi zamanki ai Amare 'yan lalashi ne, ni zanzo on behalf of my beloved brother".
Ta fada tana dariya, itama zahra murmusawa tayi.



******Daga gida direct Asibiti su Mahmud suka nufa, sun samu Habib da Abubakar, Ya Abbas yayi mamakin ganin Abubakar a gurin sosai Amma baice komai ba kenan da wadanda mahmud yayi hijirar dasu.
Lokacin Baba malam Yana zaune suna Hira, har gabansa su mahmud suka karasa suka gaishe shi da Kara suba shi, sannan su Habib suka gaishe dasu mahmud, Ya Abbas ne ya kalli Abubakar Yana fadar.
"Wato har Kai gurin kufe Mana gaskiya ko? Kana ji ana ta Fadi tashin nemansa kayi fumfurus kana kallon kowa daga karshe ma akace ka canza gurin aikine".
Sadda Kai yayi yana Dan sosa gefen wuyansa, gyaran murya Baba malam yayi Dan duk da bayanin matsayin Ya Abbas da mahmud yake basa baisa ya dauke hankalinsa daga maganar da Abbas din fada ba.
Jin gyaran muryar Malam yasa suka juyo gaba Daya suna kallonsa.
"Ayi Masa Afuwa shima Mai bin umarni ne,sai yanda akayi dashi kada aga laifinsa amanar kenan da baya da Amana baze yarda dashi irin haka ba. Allah yayi albarka ya kiyaye gaba, ai karfin addu'a ne yasa komai ya Zama tarihi naji dadin ganinka sosai Malam Abbas Dan Allah kayi min aikin Dana kasa ka maida min Dana gida tare da iyalinsa ka bawa mahaifinku hakurin karambanin da mukayi musu wallahi nagarta muka duba ba komai ba tunda Bamu San gaibu ba, in Sha Allah idan lafiya ta Samu Ina Nan zuwa sokoton da kaina".
Waje su Habib suka fice, ya Zama daga Malam din sai su Ya Abbas.
"Babu komai Malam Allah ya baka lafiya, muke da godiya ya fada min duk dawainiya da kayi dashi tunda kuka tsince shi har kawo yanzu ai kaima ubane ka Isa kayi yanda kaga dama dashi, Allah ya Kara lafiya da sutura yasa kaffara akeyi in Sha Allah amanarka Zan idata, ai mu bamu da Bakin godiya sai dai ubangiji ne ze biyaka".
Sun Jima suna tattaunawa anan Malam yake farawa Abbas yanda kayiwa mahmud makaru abinda Bai taba fada Masa ba sai yanzu yakeji, har wasu hawayen gefen Ido Mahmud yaji sun taro Ashe haka akaso a kassara Masa rayuwa Allah yayi Masa gada da Rahama ya kawo Habib ya gashi a gurin da yake a yashe a kasa.
Anan sukayi magariba sukayi insha'i sannan sukayiwa Baba malam sallama, mahmud ne yace suje su duba jikin Alhajin su Aunty surayyar uncle Mustaphan Shima Yana nan.
Shima sun samu 'ya'yansa maza biyu sunzo duba jikin nasa, sun gaisa tare da jajanta musu, shima Alhajin jikin da sauki sosai Dan har Yana takawa shima da karfe.
Gida suka koma mahmud yayi dinner tare dasu, haka Nan yayi ta maza bai nemi zahra ba Suma babu Wanda yayi maganar ta har suka gama, Mahmud Bai wani zauna ya shiga dakin da ya mayar nasa tun ba yanzu ba ya dauko laptop din da wayoyinsa ya fito.
"Ka Bari na saukeka Nima Ina son fita ne".
Ya Abbas ya fada.
"No, ka barshi kawai nayi waya da Mr salahuddeen Yana kusa da isowa, kawai dai Alfarma za'ayi min twins zasu shiga Nigeria a tsakanin kwanakin nan harna Fara musu processing na visa harda yaran duka".
"Ba damuwa Nima Ina son suje Nigeria din to saboda makarantar Abulkhairi ne, Amma yanzu dole suje tunda ta Kama amma naji kana fadar kana nemar musu visa Kai kana Nan kenan?".
Kai ya girgiza Yana fadar "A'a akwai dalilin raba tafiyar ne jikina Yana bani wani Abu da bansan ko menene ba".
"To Allah ya rufa asiri, Zan fadawa sweetie ka wuce tana can gurin 'yar daru ita da dare take tata rigimar amma da Rana lafiya kalau za'a wuni da ita".
Dan murmushi Mahmud yayi Yana ayyana Wai babyn su ce da zahra suna tarairayarta.
Yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login