Showing 210001 words to 213000 words out of 280244 words

Chapter 71 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1023

woman".
Ya fada a zuciyarsa.
Abbie ne ya matso Yana gaishe da Hajiyar Yana fadin. "Haba Mustapha saboda me zaka dauko ta da Daren Nan ku taho basai a barwa safiya ba".
"A'a nice nace baze taho ya barni ba kada ku taru ku nakasa shi a banza yanzu ma zuwa nayi mu tafi ko abinci baici ba, gashi ya laimin kuwa nazo na tarar kunyi ira-ira da gani wani Abu kukayi masa. Kai bude idonka ka fada min waye yayi maka wannan dibar albarkar ya jikeka sharaf haka?".
Abbie ne ya zauna daga gefenta Yana fadin.
"Babu Wanda yayi Masa komai murnar yaga Amminsa ce tasa ya sume Saida aka Zuba Masa ruwa sannnan ya dawo hayyacinsa".
Tabe Baki tayi tana kallon Ammi wadda ta zauna daura da kafafuwan Hajiyar tana saurarenta.

"To Daman zuwa nayi na jawa kowa layi akan rayuawar yaron nan kada naji kada Kuma na gani, anyi Daya babu Kari, Kuma na nazo Kan maganar waccen matar Mai idanu Yana gwarawa wallahi ko bayan raina ka mayar da aurenta ban yafe ba sai Allah yayi Mana hisabi akan,haka me akeyi da wannan matar Mai bakar aniya aini har abada bazan taba yafe Mata ba".
Ta fada tana kallon Abbie fuskarta a hade alamar ranta a bace yake.
Hakuri suka dunga Bata mahmud najinsu Kuma yayi mirsisi ya bude idanunsa.
"Saika tashi mu tafi ka Gama zaman gidan nan gara ma kayi aure inga ta karyar sharri Kuma haka kawai an takura maka kowa neman lika maka 'yarsa yakeyi an mayar da Kai na mamajo, kazo muje Ina da yaran dana zabar maka har hudu idan ma duka kake so saina shige maka gaba a aura makasu Rana Daya inga ta tsiyar kawo maka rida Kuma".
Su dai hakurin dai suke Bata, shi kuwa da goyan tana ambatar ya tashi su tafi yayi wani Dan murmushi a cikin Zuciyarsa.
"Tab ba inda zani yanzu dai da precious ke cikin gigita Sai taji dumina na kwantar Mata da hankali Nima bana son mu zauna guri Daya matsla za'a samu gara muna Dan nesa".
"Wai bazaka tashin bane kayi min kunnen uwar shegu kana wani farfar da Idanu?".
Uncle Mustapha ne yace mata.
"Kiyi hakuri idan ya warware zuwa safe sai ya shigo ai Daman mahmud naki ne, bakiga a gurinki yayi masauki ba daze tafi ma kece ta katshen daya gani kafin yabar gidan, kefa Dan gata har sakawa yake azo takanas a kirashi video call Yana ganinki kofa tsiren da kikace Na Maru yana badawa a kawo Miki saboda Alkawari tunda a gurinsa Mahmud yake sawo Miki Bai daina kawawa ba, da naje nasameshi ya bani bill da adadin kudin tsiren Daya kawo Miki cewa yayi Wai an turo Masa kudin tsirenki na shekara ne, Yana fadin haka nasan aikinsa ne, Dan haka tashi muje na mayar dake gida idan Allah ya kaimu gone saina kawo Miki shi har gida" .
Yunkurawa tayi ta tashi sai lokacin idonta ya Kai Kan Aishat.
"Ke Kuma saukar yaushe Hasana? Ko Kuma ke Kika kawo shi kasar ne?".
"A'a bani na kawo shi ba arashi kawai akayi nazo shima yazo".
Mahmud naji suka wuce ita da uncle Mustaphan da uncle Aliyu.
Abbie da Ammi da Ya Ibrahim suka bisu a baya.
Saida yaji fitarsu sannan ya bude idanu Aishat da Batool kawai ya gani a parlourn duk sauran yaran sun wuce ciki.
"Sannu Ya mahmud".
Batool ta fada tana Dan matsowa kusa dashi.
"Yauwa Batool"
ya fada Yana kallonta, Aishat din ya kalla Yana Mata inkiyar tana Ina?.
'yar dariya tayi tana fadin.
"Saboda Allah ka saka yarinya ta gigice irin haka har ta saki layi irin haka nasan saina amsa tuhuma a gurin Ammi Dan Naga wani irin kallo da tayi min".
Batool ce ta Kara motsowa sosai ta kwantar da murya.
"Ya mahmud Wai da Allah wacece wannan? tunda na ganta naji Ina sonta ina sonta wallahi gata very wise da ita, tana da kirki gashi duk abinda zata fada a Dan zaman da mukayi dazu zakiga da hikima a cikin maganarta, hikimarta ta girmi shekarunta gaskiya, gashi Bata da Jin Kai Sam idan wata ce yanda Allah yayi halitta a gurin ai sai yanda Hali yayi kawai".

"Kice kin zurma dai batool irin wannan kodawa haka?"
"Gaskiyar kenan Aunty wallahi tayi, ji nake kamar jinin mu ce ita"
Lumshe ido dan gogan yayi jin yanda ake Koda Masa precious tun Bata kwana a garinba har ta Fara shiga ran kannensa haka.
"Matarsa ce fa bakiga ta rude ba da aka shigo dashi a rirrke ba?"

"Yehhh... Yessss... Wallahi Ko yanzu Ya mahmud ka nuna kai jarimi ne ka dauko matar da babu irinta a dukkan Family ai gara da akayi yunwa halin kowa ya fito".
Ta fada tana tsallen murna kamar Karamar yarinya.
A haka su Abbie suka shigo Amma ba Ya Ibrahim ya wuce parta dinsa da yake a Cikin estate din suke shida saura yayunsa.
"Ke Kuma wane irin sakarci ne wannan da tshon dare kike yiwa mutane ihu haka?".
Jikin Ammi ta fada tana fadin.
"Wayyo Dadi Ammi Wai ashe Aunty Zahra matar ya Mahmud ce,".
Shi dai Abbie gurin mahmud ya nufa ya zauna kusa dashi ya Dan taba gefen wuyansa.
"Sannu me yake damunka yanzu?".
"Ba komai kawai kaina ne yake ciwon kadan".
"Ok.ai na yiwa doctor Hashim waya yace gashi Nan zuwa".

Jin abinda Abbie ya fada yasa Aunty Aishar da Batool suka nufi parlourn da Zahra ke zaune Basu tarar da ita a gurin ba sama suka nufa Batool nata kakabin abin tana faman magiyar Auntyn ta fada Mata ita ce ta hada Ya mahmud da Aunty Zahrar? Amsar Daya ce dai take fada Mata yanda ta ganta itama haka ta ganta.
Knocking biyu sukayi Zahra tace su shigo a kan sofa suka sameta ta Zuba tagumi tana aikin tunani Afnan ta karba daga kafadar Auntyn wadda tayi barci kwantar da ita Zahra tayi.
"Kuma saiki gudo Baku gaisa da Abbie ba".
Sadda Kai tayi dan ji tayi Auntyn ma kunyar hada Ido takeyi da ita.
"Zamu gaisa ne ai yanzu bazan iya zuwa ba wallahi kunya nakeji, ji nake kamar nayi tsuntsuwa na gudu".
"Kaji Aunty meye abun kunyar a ciki keda ba rungumarsa kiyayi ba "Dan kin nuna damuwa a Kan halin da yake ciki ai Kara kankarowa kanki mutunci kikayi su iyayensa, ai Dadi sukaji ko Basu fada ba irin wannan rudewa da antayo soyyaya a gabansu sun San idan aka shiga other room Kuma sai yanda Hali yayi kenan,gaskiya a gurinki zanyi degree harda masters ma akan soyyaya Naga alamar kina Dora Ya mahmud a network".
Riqe Baki Aunty Aishat tayi tana kallon Batool.
"Yaushe Kika lalace haka? Wallahi Zan sami Ammi ayi gaggawar saka Miki Rana kece Mai fadar irin wannan maganganun a gaban idanuna gara a yiwa tubkar hanci kinyi service din a gidan mijinki".
"Kai Aunty Mena fada Ina ce kece ya kamata ki zaunar dani kiyi min Karatun yanda Zan Kama mijin nawa, Amma bakiyi ba sai kuma Kice Zaki hadani da Ammi Wai ayi bikin ko service banyi ba salon laulayin ciki ya hanani yinsa cikin dadin rai".
"Allah ya shiryeki wannan yarinyar da Baki samu miji ba wallahi cewa zanyi Ammi ta fadawa Abbie ya badaki sadaka Naga alamar idan Kika Kara watanni za'a iya samun matsala gaskiya".

Dr Hashim Bai Bata lokaci ba yazo bedroom din dake kasa wanda mahmud din ya mayar dakinsa suka shiga Dr ya duba shi, ya auna B.p normal yace ya rage saka damuwa a zuciyarsa saboda kada ta shafi lafiyarsa a irin wannan shekarun, tea yasa Ammi ta hado Masa ya Sha yayi Masa Allura ya bashi magunguna Yasha sannan ya tafi.
Ba'afi minti biyar dayi Masa allurar ba ya Fara hamma zuwa minti goma yayi barci.
Karfin A/C Abbie ya rage masa sannan suka fice daga dakin.
Suna fitowa Ammi taja ta tsaya tana duban General.
"Kaga abinda naketa fada maka ko? Game da mafarkin wannan yarinyar wallahi itace zahiri ake nuna mini a Cikin mafarkina suna tare dashi".
Hannunta ya kamo suka zauna.
"Ki kwantar da hankalinki lallai Allah ya nuna Miki wani sirrine da yaso ki fara gani kafin zahiri yazo Miki, tun ranar talata Mustapha ya turo min hirarsa da malamin Daya ya rike Miki yaro lokacin da baya Cikin hayyacinsa da yanda Sukayi ta fadi tashi akan nemar Masa magani da yanda ya fada anyi Masa asirin barin garin na har abada da yanda akayi auka bashi wannan yarinyar yanzu haka dai in takaice Miki labari matatmrsa ce ta sunnan wadda marikinta yayi Mata AUREN HUCE HAUSHI, saboda itama anata samun matsaloli ne a dukkan lokacin da auernta ya tashi, shine markinta Kuma Aminin malamin ya yaba da hankalinsa ya bashi aurenta ba tare da la'akari da irin matsayinsa na bako kuma Almajiri ya bashi ita, babu irin surutun da ba'ayi Masa ba ya toshe kunnensa ana ta fadar Dan ba 'yarsa bace ya Bata marar gata. To shi malamin ne ya gamu da jarabawar matsalar Spinal cord injury shi mahmud din ya fita dashi India lokacin dashi malamin yake kokarin dawo dashi gida sai kuma ya gamu da wannan lalurar yace a bamu hakuri sunyi kuskuren yi Masa Aure Amma mu dauka haka kaddarar take a rubuce gurin Ubangiji shiya kawo aka samu matsalar da tasa mahmud ya tsallake yabar gida har hakan ta faru da ba'a samu wannan matsalar ba da ta Ina zeje Azare ya zauna har a bashi auren yarinyar? Kinga Koda matarsa ce sai dai su hadu ta wata fuskar badai wannan ba tunda Allah ya hukunta matarsa ce".
Jinjina Kai kawai Ammi keyi Tana Kara girmamawa girman Allah s.w.a idan yayi wani abun sai dai bawa ya kalla da Ido kawai.
"Na fashimta bazan ja da hukuncin Allah ba, duk yanda yayi da bawa shine daidai naji Dadi da Allah yasa Dan uwanka yazo da maganar nan bashi Hussein ya fada ba da kuma abinda ita yarinyar tayi yanzu a gaban Dan uwansa Dan haka saika tarasu kasa Mustaphan ya kunna musu suji da kunnensu bazan dauki abinda na dauka a baya ba, Kuma sabon biki za'ayi kamar yanda ake yiwa kowa a gidan Nan maganin tsegumi Dan haka da safe Zan Kira Ya I Ishaq ya bani aron Aunty Badi'a zata rakata har Azare ta yiwa mamanta bayanin sabon biki za'ayi kosu can Basu sake ba su hada jama'arsu za'a zo a dauketa kamar ko wace Amarya da dangin mijinta suke zuwa su daukota, zatafi kima da daraja a Cikin family fiye da a wayi gari ace wai yazo da Mata ai wani ma abin magana ze Zama ko Yaya kake gani? kasan tunanin mace da namji ba Daya bane".
"A maganarki babu gyara hakan yayi Amma idan har hakan za'ayi no need a ce sai kowa ya San gaskiyar maganar kawai Mustaphan yace an daura aure ne yanzu bikin za'ayi kawai Daman suna Shirin dawo dashi gida ubangidan nasa ya samu matsala Yana asibiti a India inda aka kawo labarin ganin mahmud din Ashe jiyya sukeyi a can".
"Hakan yayi Allah ya Kara sutura"
"Allahumma Amin" Abbie ya fada, muje ki bani wani Abu marar nauyi naci tunda Naga Alamar murna ta hanamu yin dinner a gidan nan, ki kawo min can part dina".
"Kaiiii Yallabai ayi min afuwa yau Daya dai Ina da bakuwa ai nayi entertaining dinta".
"Babu wannan kizo Ina jiranki ki bar musu Nan din kinsan dai zasu iya abinda zesa ki kusa nutsewa a kasa Dan kunya kuma ma ke Ina ruwanki dasu ba tare Kika gansu ba kinsa auren nasu ya dauki watannin da yinsa?".
Dan murmushi Ammin tayi.
"Ni fa Banga alamar yarinyar nan an mayar da ita mace ba gaskiya budurwa ce".
"Kamar yaya, yarinya da mijinta ki ringa fadar haka?"
Shiru tayi masa ita dai taga abinda ta gani tun ganinta da tayi dazu kafin ta sauki daga steps ta kiduri duba abinda Hajjo ta fada Mata da yake nuna yarinya budurwa ce ko tana ma'amala da maza, da niyya taje da niyyar daukar Afnan Saida ta gani sannan taji ta Samu nutsuwa.
Lokacin da Ammi ta haura saman shiru da alamar sun kwanta,Saida ta Gama duk abinda zatayi ta rufo kofarta kamar zata shiga gurin zahrar saita juya ta nufi downstairs kawai tasan idan ta shiga kinya zata Bata gara ta Bari abun ya Dan bi jiki tunnna, downstairs ta nufa tana ayyana sai ta Dan yamutsa musu lissafi ko Yaya ya ne Dan su Kara sanin darajarta itafa tana kishin mace ganin an bashi yarinyar Nan a sama saiy
Zahra ta Dade tana tunanin makomar aurenta baran barama dai tariga tayi sai Kuma yanda ta yuwu Wai Dan daudu a lahira.
"Koyaya jikin nasa?"
Ta fada a zuciyarta, ta Jima tana sakawa da kwancewa, gashi duk yanda taso ta Kira Aunty Hasana abun ya faskara haka Ammah duk network yaki bada hadin kai. Sai wurin Daya saura tayi barci, can a Cikin barcinta taji Kamar ana tabata, kwanciyarta ta gyara ba tare data bude Ido ba sai tajita a jikin mutum da wata irin zabura ta yunkura zata Mike taji an mayar da ita Baki ta bude zata zabga ihu taji carab ya hade bakinsu sai lokaci taji kanshin turarensa a hancinta, wata ajiyar zuciya ta sauke, tayi lif a jikinsa da gaske sunyi missing din juna Saida yayi Mai isarsa sannan ya dan saurara Mata ya yanye bakinsa suna maida numfashi.
"Previous kin azabtar Dani whyyy... Me nayi Miki Kika haramta min ganinki kwata-kwata? Fada min kinsan halin Dana shiga kuwa? Kikasa na kasa controlling kaina a gaban elder brother dina kin kyauta min kenan?".
Ita dai mukus tayi to me zata fada masa tace labewa tayi taji shirarsu da Aunty Aishat ko tace Masa me shirun shi yafi Alkhairi. Juyin duniyar Nan taki magana dole ya kyaleta ya koma wata shirar da ban.
"Wai dazu da rungumeni zakiyi a gaban su Ammi?".
Saka kanta tayi a kirjinsa Cikin kunya tana gigiza Masa Kai.
"Kin dauka Zan tafi na barkine ko? To muna Nan sai kin haifo Mana fine babies masu Kama dake".
Ya fada Yana Kai hannu akan cikinta Yana Dan shafawa.
"Ka Bari Dan Allah Ammi fa tana Nan ka tashi ka tafi Dan Allah kada wani ya ganka ka shigo yayi zaton wani Abu fa".
"Kwantar da hankalinki ai kin Gama Mana aikin Dana kasa yinsa a Cikin kankanin lokaci meya rage kuma? sai mu tattara mu tafi inda mukafi wayo Nima nasan nayi aure na huta da ragaita mu fuskanci rayuwa kuma, badan nayi alkawarin kawowa Ammi ke a yarinyarki ba Aida yanzu muna Shirin tarbar babyn mu ko ba haka ba?"

Wannan furucin nasa shi ya ankarar da ita akwai fa sauran Rina a kaba, Nan da Nan wani tsoro ya kamata Nan ne fa karshen maganar, a Nan ne me afkuwa fa zata afku,tunda gata a sokoto har dakin mahaifiyarsa saura da me ya rage kuma?.

Cikin shagwaba ta Fara fadar "Ni dai ka daina wannan maganar gaskiya wallahi ni Ina Nan kusa da Ammina ai ba muyi haka da kaiba nifa tsoro nakejiiii..."
Wani special smile ya sakar Mata duk da dakin dimmer light ce Bata hanata ganin yanda dimple dinsa ya lotsa ba.
"Wani abu nace zanyi Miki ne da zaki Fara tsorona? Ki zana feel free Dani har abada babu cutarwa a tsakanin mu, kin manta Abba da Baba Malam Amanarki suka bani?".
Kai gyada Masa alamar eh.
Cikin jikinsa ya sakata Yana fadar muyi barci da sauran lokaci duka yanzu one thirty five am".
Kafada ta make tana kallonsa ta gefen ido ita fa da abinda yake figitata gaskiya.
"Dan Allah ka tafi kada kaja mini Ammi fa tana Nan kada ta ganka nidai babu ruwana wallahi".
"Nace Miki ki kwantar da hankalinki Amma Bata Nan fa tana gurin mijinta itama to Kinga Kota ganni ai ba wata damuwa ko?".
Ita dai barci rabi da rabi tayi a kunnenta aka Kira sallar farko data biyu tana jinsa ta tashi ya shiga toilet ya fito ya zura jallabiya Daya zo da ita Cikin ledarta ya Dan shafi gefen fuskarta wadda tayi fayau a Cikin Dan hasken dake dakin.
"Tashi lokacin sallah yayi, Zan wuce masallacin daga can zanje gurin Hajiya inna, jiya Baki ganta ba ko lokacin kin gudo tazo gidan Nan Wai zata tasani a gaba mu tafi Wai na daina zaman nan. Kin amince nayi nesa dake?".
Jin za'a tada sallah yasa yayi sauri ya fice daga dakin, Karan rufe kofa yasa Ammi dawowa ta bude kofarta wadda shigarta dakin kenan Dan yallabai na tafiya masallaci ta nufo part dinta, bayansa kawai ta iya gani saboda saurin da yakeyi na kada ya rasa raka'ar farko, jinjina Kai tayi tana fadar.
"Dole ayi yanda za'ayi ku tattara ku Kama gabanku badani za'ayi wannan dibar Albarkar ba, wato abinda general ke nufi kenan Daya tilastani zuwa gurinsa"
Sallah ta tayar ta zauna zaman azkar da lazimi Ala ala take shida da rabi tayi ta Mira Niger, Saida ya dai daici lokacin dawowa daga masallacin yayan nata sannan ta Kira shi.
Yana ganin Kiran yasan ba lafiya ba Dan Yana dagawa ya Bai saurari gaisuwar da take masa ba ya Fara fadin.
"Zainab lafiya? Meya faru kuma?".
"Wallahi ba komai Yaya sai Alkhairi".
"To Alhamdulillahi, lfy kalau ya yaran da Mai gida"
"Kowa lafiya, daman Mira nayi na fada maka danka ya dawo harda tsarabar Mata aka Mata aka bashi tana nan sunzo ita da 'yar uwarsa can ya Kai Mata ita"
Sai kuma ta dauko masa Asalin dalilin kiran nasa shima supporting dinta yayi harma ya Kara da fadin dole a hada da babbar mace su tafi tare kamar zefi girma da daraja a gurin Iyayen nata, sunyi sallama akan idan an samu tickets dinsu damagaram to sokoton zasuyi waya wata irin nutswa taji ta saukar mata, gara ayi a wuce gurin.
Da gari ya Fara haske zahra ta tashi daga Kan sallayar da tayi sallah ta ninke ta kintsa gurin wanna tayi ta shirya Cikin rigar material Mai budedden dinki San rigar Bata Kama Mata jiki ba tayi rolling da gyalen material din Nan da Nan ta gyara dakin ta fesa roomfreshner ta fito Cikin so take ta gaishe da Ammi Amma Bata San takamaimai Ina ne dakinta ba sannan kuma Batasan da wane Ido zata dubeta ba, tana kokarin juyawa ta koma kenan kofar dakin Ammi ta bude ta fito Shar da ita tana baza kanshinta da mamaki a fuskaerta ta fito tana fadin.
"Masha Allah, harkin tashi kenan?"

Ta tambayi Zahra.
Da sauri Zahra ta tsuguna tana fadin.
"Ina kwana Ammy".
"Lafiya kalau ya bakunta?".
"Lfy kalau".
Ta fada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login