Showing 213001 words to 216000 words out of 280244 words

Chapter 72 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1088

tana Wasa da gefen gyalen da tayi rolling, ta kasa hada Ido da Ammi din.
Ciki Ammi ta koma tana fadin

"Shigo nan magana zamuyi dake"
Zahra ji tayi gabanta ta yanke ya fad'i, jiki ba kwari tabi bayan Ammi ta shiga gefen gado Ammin ta nuna Mata ta zauna amma ta Kiya ta zauna a Kan carpet din dake gaban gadon tana jiran taji abinda za'a fada Mata.
Zama Ammin tayi tana karewa zahra kallo yarinyar tana wani irin kyau Mai daukar hankali.
"Kina jina Fateemah number mamanki Zaki bani ina son nayi magana da ita".
"To Ammy gata"
Ta Fara karanto Mata harta cika.
"Tashi kije zuwa anjima Ina Jim zakuje unguwan insha Allah Amma Bari nazo muje ku gaisa da Abbie dinku".
Ammi na gaba zahra na binta a baya suka nufi katafaren part din Abbie compound din ba kowa silent da alamar gidan bashi da yawan hayani kowa Yana gurinsa a kame sai munafurci fall a cikinsa a parlour suka sameshi tunda suka shigo zahra ta sadda Kai kasa har kusa da inda yake zaune zahra ta karasa ta tsuguna har kasa ta gaishe shi, Cikin muryarta Mai nutsuwa, albarka dai zahra Tasha ta gurin Abbie da godiyar abinda iyayenta suka yiwa gudan jininsa, cewa yayi ta zauna sosai ta zauna ya ringa yi Mata tambayoyin tun tana dari dari dashi harta dan sake dashi, lokacin da zasu dollars din America ya Bata raffer biyu ya Bata a Leda.
Ammi ta karbar Mata Tama godiya.
Har suka dawo Basu hadu da kowa ba ba Karamin Dadi Ammi taking da faruwar hakan ba, suna shiga suka samu masu aikin girki da share -share.
Zahra Bata koma sama ba gurin Aunty Aishat ta wuce yayinda Ammi ta nufi kitchen.
Auntyn kawai ta Sami ta tashi yaran duk Basu tashi ba, waya takeyi saida taji tace gata Nan ma Bari na Bata, wayar ta mikawa Zahra tana fadin

"Bari nayi wanka tunda Allah ya kawo min ke bana son na shiga wanka ba kowa a Musa dasu*
Wayar ta Kara a kunne tana sallama, amsawa yayi Yana fadin.
"Pls My preccious Kina jina, dan Allah anjima da yamma ki biyo Sister Aishat kuzo tare ki gaishe da Hajiya inna Kuma na cika wani alkawarin Dana dauka tun ranar Dana bar gida nayi shi to shine nakeson cika shi ai asan zaki tayani mu cika alkawarina ko?".
Ya fada da sigar rarrashi.

I *AUREN HUCE HAUSHI*
09061432330

Or

08055362975


AISHAT ISAH MUSAH


Maman Fateemah


Page 77


.............karfe bakwai dai dai mahmud ya baro gidan Hajiya Inna, bayan yayi wanka,dole tasa yazo gidan tunda a gidan Ammi baya da kayan sakawa ya duba baiga komai ba be sani ba ko canza musu guri akayi ko bayarwa tayi abinda be bi ba'asi ba kenan yaga gara ya taho Nan ya shirya kawai, shigar kananun Kaya yayi ya fito Shar dashi, Bai koma gurin Hajiya Inna ba duk da albishir din da tayi Masa na sinasir da tasa ayi Masa da pepper soup din kafafuwan shanu.
Yaso ya shiga gurin Abbie Amma gurin Amminsa zaya har yanzu bakinsu Bai Saba ba jiya da zummar suyi kwanan zaune ya shigo sai kuma aka samu akasi ya bige da allurar barci.
Ta kofar baya ya shigo part din Ammin har ya Haye sama Bai hadu da kowa ba dakin da Zahra ta kwana ya bude ba kowa sai kamshinta Wanda har ya Fara kama dakin, komai tsab ba tamkar ba'a kwanta gadon ba, kofar ya janyo ya nufi dakin Ammi yasan a irin wannan time din Bata ciki turo kofar yayi da sallama shiru sai kamshi kawai ke tashi a dakin.
Wani sanyin dadi ya ratsa shi jinsa yake kamar an sauke Masa wani katon dutse daga kansa, a tsakiyar dakin ya tsaya Yana tuno wasu lokutan baya da shigo cikinsa tamkar mahaukaci Yana magiya Amma ko gezau Ammi Batayi ba Saima tsallakewa da tayi ta wuce ta barahi a durkushe, Amma yau gashi ya shigo cikinsa da walwala da Aminci ba bacin Rai ba tashin hankali.
Kwanciyarsa yayi a Kan sofa Yana fashi "Alhamdulillahi Ala kulli halin".
Yayi zaman kusan minti talatin kafin yaji alamun bude kofar a Hankali ya cira Kansa daga wayarsa da yake duba sakonnin whatapps, Ammi ce ta shigo tunda ta shigo master parlourn ta tasan ya shigo gurin Bata Kara tabbatarwa ba Saida ta hauro saman Dan kamshinsa na daban ne.
Tsayawa tayi a gurin tana Kare Masa kallo, Masha Allah gani tayi ya Zama Babba ya cika Ido kenan jiya ganin tsoro tayi masa gashi ya Kara yin wani fresh dashi da gani ya samu nutsuwa ba kadan ba.
Aje wayar yayi ya taso ya nufota inda take tsaya murmushi yaki barin Bakinta ta Kuma kasa dauke idanunta daga kansa.
Ba wata wata mahmud na zuwa ya shige jikinta Yana fadin.
"Ammina fushi kike Dani ko? Nasan zakiyi fishi dani, gani Nazo kiyi min duk hukuncin Daya Dace Dani in dai Zaki yafe min, Dan Allah kiyi hakuri Nima bansan me yake faruwa Dani ba, Sam bana kaunar ko sunan garin nan naji an fada bana Kuma son naji ko sunan Wanda na sani in dai Yana Cikin family wallahi".
Zamewa Yayi ya tsuguna ya rike kafafunta sai hawaye.
Dan duk'awa tayi ta kamo hannunsa ya taso jansa tayi kamar Karamin yaro har gefen katafaren gadonta ta zaunar dashi itama ta zauna.
"Waya fada Mata Ina fushi da Kai? Ko alama dama ma banyi fushi da Kai ba sai yanzu da Ubangiji ya amshi rokona ya share min hawayena, bakayi min komai ba ko kayi ma na yafe maka duniya da lahira, Allah yayi maka albarka ya baka kariya daga sharrin dukkan wani abunqi, yanzu Ashe kana Bauchi state kayi zamanka akayi ta nemanka a turai da kasashen larabawa?".
"Ammi Nima fa wayar gari kawai nayi na ganni a garin bansan ta Yaya naje ba, Saida Habib Wanda ya ganni a yashe a kasa karkashin bishiyar gamji ya fada min a halin daya ganni nayi mamakin to ta Ina nabi naje can? da kafata naje ko kaini akayi? duk ban sani ba, Ammi Ina jinfa na rasa hankalina na wasu kwanaki ko watanni, Ammi hatta magana fa daina yinta nayi sai dai Ido Ina Jin abinda ake fada Amma bana iya bude bakina na mayar mutanen Nan ba Karamin jihadi sukayi ba gurin ceto rayuwata, Idan malam dawo har Azare Zan kaiki ki yiwa Baba malam godiyar abinda sukayi min kudi dai bazasu iya biyansu ba sai dai Allah mutane ne su masu karamci". Nan ya zazzage mass
Mata duk irin rayuwar da yayi a Azaren har ya zauna a dakin waje na amajirai.
Baiyi zato ba yaji shashshekar Ammi.
"Subhanallahi ! Haba Ammi me yasa Zaki Bata hawayenki abin fa ya Riga ya wuce, Ina fada Miki ne kawai saboda ki Kara yi min addu'a saboda bamu San me goben zatayi ba".
Knocking din kofa akeyi mahmud ya bada izinin shigowa.
Aishat ce da suhailat suka shigo itace Mai bin batool.
Da murnarta ta Karaso sai Kuma tayi turus tana kallon Ammi dake share hawaye Aishat ma jikinta sanyi yayi.

"Meya sameta take share hawaye?
Aishat din ta jefawa mahmud din tambayar.
Ammin ce ta Bata amsa

"Ba komai Hussein ne yake fada min halin rayuwar Daya shiga tamkar marara gata harfa so akayi a haukata min d'a a banza wallahi Ina istigifari ga Ubangiji kafin na fada, dama wani Allah ya bawa dukiyar Nan bashi ba da yake da kananun shekaru irin haka, wallahi da nasan wannan condense milk din itace sila Dana yiwa jama'a unguwa rabonta an wuce gurin,to ba haka zanen kaddarar take ba sai hakuri".

Suhailat ce ta dan matso kusa da mahmud tana fadin.
"Sannu Ya Mahmud ya jikin naka?"
"Jiki da sauki suhailat ya karatun kin Gama ko?".
"A'a da saura sai next year in Sha Allah".
"Allah ya taimaka".
"Amin"
Suka fada gaba daya.
Aishat ce tacewa mahmud "kaje Abbie Yana nemanka a parlournsa na part din nan, Ammi kema yace a Kai masu abin break fast can kamar na mutun bakwai".
Mikewa yayi yana fadin "Bari naje Ammi".
"Jeki ki fara hada abinda za'a shigar part din Abbie din keda sauda da Batool Kice i???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ya Halima ta Zuba pepper soup din kayan Cikin Nan a babban warmer sauran ta saka a fridge".
"To Ammi"
Waje suhailat din tayi da sauri.
Saida suhailat din ta fice shima ya nufi kofar Yana Daf da ficewa Aishat tace masa.
"Ka fada Mata wacece zahra a gurinka Naga alamar ba iya playing match din zakayi ba".
Tsaye yayi shi Bai fice ba shi kuma bai juyo ba, sai Kuma ya juyo ya dawo a Hankali ya zauna a gabanta ya sadda Kai da gaske wani irin nauyinta yakeji Wanda Bai taba tunanin zeji kwatankwacinsa ba a tare da ita, a Hankali kamar baya son yin magana ya furta.

"Ammi ga zahra Nan an bani aurenta a Azare, tun watannin baya nace saina kawo Miki ita idan ta kwanta Miki a matasyin suruka ki saka Mata albaka ki kaita dakinta da kanki idan Bata yiiki ba ki saka a mayarwa da iyayenta ita a Basu hakuri, duk hukuncin da Kika yanke na karba da hannu bibiyu".
Yana gama fada Bai jira yaji abinda zata fada ba ya tashi ya fice da sauri Dan ba Karamin kokari yayi ba gurin kinar bakin waken fada Mata ba.

"Eh to da dai hakan yafi a mayar musu da yarnyarsu tunda akwai alkawarin da nayiwa fulani, Ina ga sai dai suyi hakurin gaskiya"
Abinfa ya iya jiyowa kenan daga bakin Ammin tasa bai it's cewa komai ba ya fice.
Daga shi sai Wanda ya halicce shi suka San abinda yake ji a kasan Zuciyarsa.
Aishat zatayi magana Ammi ta daga Mata hannu dole ta kame bakinta daga abinda tayi niyyar fada.
"Kuje kiyi serving din ku kafin na fito, idan kun Gama ki hadawa yarinyar Nan kayanta Wanda kikece min tsaraba yasa akayi Mata nafi son tabar gidan Nan kafin wani tsegumin ya fito".
Sororo Aishat tayi tana duban Ammi wadda ta tashi ya shige toilet kirjinta na bugawa da sauri da sauri.
"Allahumma Ajirniy fiymusibati, wannan wane irin tashin hankali ne Kuma? Allah ka kawo sauki".
Fita itama Aishat din tayi jikinta a mugun sanyaye, bedroom dinta ta nufa ta yiwa Zahra magana suka fito tare, da kyar Aishat tayi ta maza ta danne zuciyarta sukaci abincin tare da su suhailat duk da basa cin abinci da wuri Amma dole tasa tunda Umarnin Ammi ne.

**

Ammi najin fitar Aishat ta fito daga toilet din ta dauki wayar ta Kira number data karba a gurin zahra, Bata so Kira a irin wannan lokacin na safiya ba amma dole tasa hakan.
Lokacin Ammah na kitchen Musaddiq ya kawo Mata wayar yace kiranta akeyi, tana wanke hannunta wani Kiran ya shigo Saida ta goge hannunta ta karbi wayar, bakuwar number ce.
Dauka tayi tana amsa sallamar tana ficewa daga kitchen din ta barwa Alawiyya aikin, gaisawa sukayi da Ammi kafin Ammin tace.
"Ko Hajiya Asma'u ce maman Fateemah Zahra?".
Sai Ammah taji gabanta ya Fadi ana ambatar sunan zahra.
"Eh nice, Allah yasa lafiya?".
Dan murmushin da Bata shirya ba ya kwacewa Ammi.
"Lafiya kalau sai Alkhairi,sunan Hajiya zainab daga Nan sokoto mahaifiyarsa Mahmud mijin Fateemah".
Cikin nuna jin Dadi da tsantsar fari ciki Ammah ta Fara fadin.
"Masha Allah! Hajiya ya gida ya akaji da jama'a ai jiya ta fada min suna Nan naso na karbi number ki mu gaisa sai tace min wai bazata iya tambayar mi ba, to yau naso na karba a gurin shi mijin nata mu gaisa".
"Kai haba babu komai muya Kamata mu tako muzo muyi godiya yanzu ma bamu fasa ba wata dai Alfarma nake nema akan 'yata yau komai dare suna Nan bisa hanya zasuzo tare da 'yan uwa na sai anzo daga Nan an daukar min ita an kaita dakinta kamar kowace Amarya ba Wai a wayi gari a ganta a matsayin matarsa ba bana son ayi Mata wani duba na daban kinsan Yana yin kowa ne family da irin nasu matsalolin,duban irin kalubalen da aka fuskanta a Nan din kafin barinsa gida, naso ace wani nawa yayi Miki wannan bayanin to basa kusa kiyi hakuri nayi rashin kunya akan Dan Fara".
Ta fada tana 'yar dariya irin gentle din Nan.
Itama Ammar yin tata tayi, tana fadin.
"Na fashimta kina dai son kankarowa diyar taki mutunci ne ko?"
"Gaskiya dai Kam Allah dai ya saka Miki da Alkhairi kinyi abinda duk uwa ta gari zata yiwa yarinya mace Hussein ya fada min komai, mun gode da Karamancin ku garemu kin dauki yarinya kamar wannan kin bashi ba tare da kunsan asalinsa ba, sai nazo har gida nayi godiya in Sha Allah".
Sukayi sallama kasake Ammah tayi tana lissafo maganganun su da mahaifiyarsa Mahmud daga ji ba wata Babbar bace sosai sai dai tasan kanta da alamar Allah ya karbi Addu'oin ta Wanda take ba dare ba Rana akan Zahra na neman dace da kwanciyar hankali a gidan Aure, sai Kuma tayi murmushi wannan sirikar ta Zahra za'a da ita tasan ta Kan duniya wato sai ansan yayi aure ba Wai yazo da Matar ba kamar Auren bariki.
Part din Abban ta nufa na bangaren ta, tana shiga Yana aje wayarsa da ya gama. Ganin fuskarsa da wani irin annuri yasa ta fasa fada Masa abinda tazo dashi gara ta Fara Jin nasa tukunna.
"Wane irin albishir akayi maka haka Mai Dadi Daya saka Zuciyarka a irin wannan Nishadin haka?".
"Zoki zauna yanzu muka Gama waya da sirikin uwata Wai ashe yaron Nan mahmud Dan wajen General Muhammad Dange ne, Saida ya kirani yanzu na gano inda nasan fuskarsa Kullum na kalleshi sai Naga nasan fuskarsa ko a wani gurin ne daban Ashe fuskar mahaifiyarsa nake gani a tasa fuskar, kinsan kuwa waye General Dange? To babu abinda zewa Ubangiji sai godiya ya sakawa uwata da abinda hankali da tunanin mu Bai taba kawowa ba mijinta fa shine Dan general din Wanda ake hasashen Yana Daya daga Cikin matasan masu kudin Africa sahun farko duk fa yanda family dinsu sukayi popular a kasar nan ta fuskar arziki yaron yayi musu wata irin tazara, Abu Daya yake bani mamaki yanda ya iya jure rayuwa irin ta Cikin Almajirai ba kyamata ko kadan Abu Daya ne dai kawai ya ringa sani a tunani yanda tun bayan samun lafiyar yaron komai na makarantar ya canza akace NGOs sun shigo suna wannan mahaukatan ayyukan Wanda ba'a yinsu a sauran makarantu Dan ma daga baya sun canza salo sun shigo da wasu makarantu harma Dana Karkara".
Jinnina Kai kawai Ammah takeyi tasan wannan ba tsuminta ba ba Kuma dabararta ba Rahamar Allah ce ga bawa kawai da yake yinta ga wanda yaso a lokacin da yaso, lallai sun kunshi takaici da yawa a baya Amma Cikin Rahamaniyya ta Ubangiji sai gashi abun ya zamo wani haske daga karshe abinda babu Wanda ya zata Koda kuwa a Cikin mafarki ne.
"Abban Yara Nima abinda ya shigo Dani kenan na fada maka munyi communicating da mamansa yanzu".
Nan ta fede Masa daga biri har wutsiyar yanda Sukayi da Ammin mahmud.
Dariya Abban yayi yana fadin "Nima ya fada min har Yana bani hakuri da halin Mata na bidi'a Wai ita uwar sai tayi bikin danta kowa yasan yayi aure"

Sun Dade sun tattaunawa na Suma dole su nuna Mata gata tunda inda Allah ya kaita ba gurin Wasa bane na take Abban ya turawa Ammi makudan kudi ayi abinda ya Kamata Dan ma da furnitures a aje Wanda Ummee suka turo ba'a sakaba saboda babu guri Kuma Kaya ne na garari.



******** Tunda su zahra suka Gama Break fast suka koma parlour na uku suka zauna suhailat ta kunna musu tv ana yin wani series na 'yan Lebanon, manyan jakunkuna taga masu aikin Ammi suna fita dasu daga dakin da aka aje kayan da suka zo dasu ba dadewa Kuma taji maganar mutane daga dayan parlourn, sai kuma taga suhailat ta tashi da sauri tana fadin.
"Kai su mummy Badi'a ne yanzu da safen Nan haka kamar Wanda suke daga wata unguwar"
Ta wuce ta nufi inda suke.
Da gudu suhailat ta fada Kan mummy Badi'a tana fadin.
"Sannunku da zuwa mummy keda Hajji zuwaira, ina kwanan ku Ya hanya? Amma zuwan Cikin dare kukayi ko? Naga duka yanzu Sha Daya fa".
Gaisuwar suka amsa sannan mummy Badi'ar tace "ko kadan dazu muka zo wurin karfe Tara da rabi ta baya muka shigo muna sama ne gurin Ammi itama yanzu zata sakko".
Aishat ce ta shigo daga wata kofa wadda zahra Bata San ko Ina bane, ranta a hade ta cewa Zahra ta taso suka nufi gurinsu su suhailat.
Suna shiga bakin suka fara fadin.
"Masha Allah, wannan ce Fateemar? Matso mu gaisa Hajja zuwaira na fadin "nice dai ta karfen keta katako ce" mummy Badi'a na tare mata, cikin Jin nauyi zahra ta tsuguna ta gaisheni su Cike kunya da girmamawa.
Aishat sai taji tana jin haushin maganar Hajja ita ana ga yaki tana ga k'ura, Ammi na maganar a mayar da Zahra gurin iyayenta a Basu hakuri ita Kuma tana maganar wani itace ta karfe. Ammi ce ta shigo rungume da wani Abu anyi rapping dinsa tazo ta zauna kusa da mummy Badi'ar tana fadin gara ku tashi komai ya Zama ready kada kuyi dare tunda tafiyar mota ce".
Tashi tayi tana fadin .
"Hasana kuje kofar baya gamu Nan zuwa".
"Taso sister muje"
Ta fada tana taba kafadar zahra.
Ita fa Bata gane ba an sakata a duhu Ina zata kuma taji ana fadin kada ayi dare to suwa zasuyi Daren? Ita Kuma meya hadata da bakin Ammin da taji kamar da ita zasu tafi.
Ita dai bin Aunty Aishar takeyi wadda taji kicin kicin da rai kamar ta fasa kuka.
Wata lafceciyar GLK Mercedes-Benz 2024 model Parke a kofar baya sai daukar Ido takeyi Baba Habu drivern Ammi na Amana Yana gefe Yana jiran Umarnin Ammi.
Da saurinsa ya matso Yana gaishe dasu zahra, fa sauri zahra ta Dan duqa ta fadin.
Lafiya kalau Baba"..
Su Ammi ne suka fito har inda su Zahra suke tsaye Ammi ta Karaso, ta Kamo hannun Zahra ta dankata a hannun Hajja zuwaira tana fad'in.
Gata Nan Hajja na Baku Amana ku damkata hannun mahaifiyarta Dan Allah,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login