Showing 252001 words to 255000 words out of 280244 words

Chapter 85 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1091

min godiya gurin mijinki na gode Allah ya saka da Alkhari".
"Amin" Zahra dasu Sameer suka amsa shi Dan gogan ko tari Bai kubce masa ba tunda ya shigo sai wani kallo yake bin mamar dashi, ji yayi ya Fadi nauyi yayi faduwar sanho a rairaiyi, shi ashe ganin tsoro yake Mata a Dan ganin da yayi mata, sai yaji duk abinda yayi niyyar ya sauke mata yaji baze iya ba ya barta da wannan kaddarar ciwon data sameta kawai ta isheta musiba.
Tun ganin da Mama tayi musu Bata Kara dogo da kanta ta kallesu ba Dan wani irin kunya da nauyi ne suka rufeta yau ga Zahra a gabanta tare da Wanda suka dauka kaskantacce marar galihu a baya Wanda aka dunga fad'a musu da wani haske a tare dashi da yafi na sauran manemanta na baya amma tayi biris da maganar, gata gasu cikin wani irin yanayin da yafi duk wani tunaninta da hangenta.
Sai da ya bushi iska sannan yasa hannunsa na hagu ya zare glass din dake idonsa ya yiwa Mama kallon Kai tsaya cikin muryar data saka zuciyarta kadawa ya furta.
"Hajiya Rabi'aaaa..!!!".

Ba ita daya ambaci sunanta ba su Zahra ma Saida sukaji tasu zuciyar ta kada, Dan Zahra zata iya rantsewa da girman Allah Bata tab'a Jin muryarsa da gautsi irin haka ba.
"Ga Zahra nan ki dubeta ki K'ara kinso ki daqile Mata rayuwa ki Hana ta Kai inda ubangiji ya nufa taje kinyi ta kulle-kulle ki dan kada ta cimma rabonta na rayuwa da Allah ya hukunta a kanta, kin manta tun mutum na cikin mahaifiyarsa yake rubuta duk al'amuransa na duniya daga arzikinsa ajalinsa Dan wuta ko Dan Aljanna, an riga an rubuta alkalamin ya karya tawadar ta bushe, alkawarin Allah gaskiya ne baya tashi,gata Nan KAINUWA ce dashen Allah. Kuma duk kullin da kikeyi Allah ya nuna Miki iyakarki naso da lafiyarki da sai kinyi Dana sanin zuwa garin Nan to Amma sai gashi Abu kadan ya Hana zuciyarsa ta zauna lafiya tana neman bugawa a banza, abinda Kika so ya Sami Zahra sai gashi tun ba'aje ko Ina ba ya Sami yarinyarki, kinso Zahra ta lalace sai Kuma ta Zama Dan tsiron da Allah keso ko babu ruwa Saiya rayu,an Bata Almajiri marar galihu Maimakon tausayawa maraicinta a'a sai Kika gano tunda da Dan rufin asiri ba yanda Kika zata ba kina.cewa sai dai kyau ya qare a banza inda sai dai a kare a yawon kakksbar raba, duk da haka sai Kika dauri aniyar wargaza Mata rayuwar Aure saboda naki yaran Basu samu kamar nata almajirin ba, kin manta ayar da Allah subahanahu wata'ala yace cewa wamakaru "wamakarallah wallahi khairul makirin" Bari na maido Miki da abubuwan da kikayi ta fafutukar su zamar Miki tsanin daze ruguza duniyar gidan aurenta naji garin yayi min zafi na manta da ita har abada sai dai Wanda suka hada su gaji su kwance auren ko?" Ya jefa Mata tambayar duk jikinta rawa dake ga gumi ya tsatstsafo Mata a goshi har diga yake, duk tsiyar da kuke k'ullawa Asabe yarinyarki ta fada min komai har garuwan da Kike aikenta neman tsubbace tsubbacen ku, kinci daraja Daya wadda tasa na kyaleki na Kuma kyale 'yan koren naki, shi yasa na raba yarinyar taki da garin Dan matukar tana kusa zanyi Mata abinda asirin ki ze tonu abinda bazan so ace iyalin Abba itace ja Baga a cikin tafiyar, ko Mai gadin gidansa bazan iya keta masa rigar mutunci ba bare matar da yake aure ance ko a lahira wani Yana cin arzikin wani, Wallahil Azim da sai kunyi Dana sanin Baku santa ba a rayuwarku,Kinga zaman lafiya a kiyaye shigia eighteen dinta Amma duk Wanda ya kuskura ya k'ara gigin saka kansa a cikin lamarinta tofa maganar ba irin wannan za'ayi ba, zakuje asibiti na dauki nauyinki da duk Wanda yake tare dake a tafiyar saboda kinzo rako min princess ne ciwon ya tashi tunda dama da akwai shi,to gara ki Fara sheda wutsiyar ragumi tayi nesa da kasa, idan kin raba kanki da ciwon hassada idan Allah ya taimakeki ki samu waraka idan Kuma Yana Nan tofa Saida ya zamar Miki sanadin komawa ga Allah tunda ita dai wannan dai da aka dunga kokarin daqileta kada ta Kai inda ubangiji ya nufa tifa tayi Miki tazarar da za'a iya cewa tamkar tsakanin sama ne da kasa".
Wayarsa ya mikawa Sameer.
'Kira zayyan ka fada Masa ya shigo da sakon Nan".
Glass dinsa ya mayar a idonsa.
Tunda ya Fara zazzaga maganganunsa wuta da daukewa duk wani mahaluki dake cikin dakin Dan wannan dabi'ar ba kowa ne yasan Yana da ita ba, Idan ka tabo shi saiya rama tun Yana yaro haka yake.
Ba'afi minti uku da gama wayar ba zayyan ya shigo da ledoji guda biyu a hannunsa ya dan risina Yana fadin "gasu sir".
"Ba kowace ta ta".
Nan da Nan ya cika Umarnin uban gidan nasa, ya aje Kayan da asabe ta kawo na turarikan wuta a gaban Mama sai Wanda aka karba a gurin asaben dai Wanda ya Zama sanadin da tabar garin da Kuma tatsar bayanai daga gurinta.
Gasu Nan idan Kuna da bukarsu a gaba saiyi muku amfani, ke Kuma Idan mun fita saiki nuna Mata wadanda bata kaiga ganinsu ba, Kuma yanzu haka Salma ta sauka a Azare zata amsa tambayoyin Abba tunda kinqi fad'a masa irin tarbiyyar da kike bawa yaransa".
Bai Kara tofa komai ba ya janyo Zahra suka nufi kofa su zayyan suna take musu baya, suna Daf da barin dakin suka jiyo kukan Aunty larai tana Fadi "na shiga uku Rabi'a ki tashi"

Shi dai Bai juya ba ya dai nunawa su Sameer akan su koma.
A hanyar su ta komawa ne suka hadu da doctor zainab ta fito daga Gyne emergency.
"A'a wa nake gani kamar 'yata? Yallabai lafiya na ganku da daren nan haka a asibiti daba sai a kirani ba".
Gaishe da ita sukayi Zahra sadda Kai qasa Dan ji tayi duk kunya ta rufeta, Mahmud ne yace.
"Ba komai doctor munzo gaishe da marar lafiya ne".
"A to Allah ya qara sauki, 'yata ya jikin naki?"

A kunyace tace "jiki da sauki mummy".
",To Masha Allah, Dan Allah ki kiyaye shanye shqnyen magungunan Nan badan jikinki Mai kyau bane da an samu matsala sosai" .godiya sukayi Mata sannan Sukayi sallama,ta wuce Suma suka wuce, har sukaje gurin mota babu Wanda ya tofa ko kalma Daya a tsakaninsu Dan ita Zahra ji tayi tana wata shakkarsa Bata taba zaton ze iya shafawa idanunsa toka yayi irin wannan rashin kirkin haka ba.

*_ AUREN HUCE HAUSHI_*


AISHAT ISAH MUSAH
(Maman Fateemah)
09061432330
08055362975


Page 91


_________ Tunda suka dauki hanya yake sharara gudu sabanin dazu da suke tafiya a slow, taso tayi Masa magana to ganin Yana yinsa yasa tayi shiru ta zubawa hanya idanu, zuciyar ta fal da mamakin rashin kirkinsa Daman haka yake?.
Har suka shigo rukunin gine-ginen unguwarsu Bai tanka Mata ba Saida sukazo dai dai wani gida Mai farin fenti da ash colour sannan ya Dan juyo ya dubeta, "Kinga gidansu dodanniyarki Nan".
"Wacece Kuma dodanniyar tawa a garinku nida ko one week ban cika ba a garin da har zanji tsoron wata".
"Dr Haseenah ba dodanniyar ki bace?".
"Allah ya sauwak'e wallahi meye abin tsoro a tare da wannan Mai siffara mazan, mace ba gaba ba baya, Kace 'yar garinku?".
Ba zato taji ya fashe da wata dariya Yana duka sitiyarin motar da hannunsa.
"Amma wallahi kin cuceta, tana ganinta Mai zafi Amma ke kina siffantata da maza".
Hannu ya Kai ya Dan shafi gefen cinyarta "ba wannan ko?".
Dan zumburo Baki tayi tana matsawa "to karya naji Kai idonka baya gani, wallahi har naji bana son unguwar".
"Kai! Kuji mu da yarinya haka kike da kishi? Kince kin tsani Kano Kuma my home city din ma sai Kice Bai Miki ba saboda kishi,to Yaya zamuyi dake idan Zan kawo miki 'yar buzuwata diyar Mama filani, Dan ta kirani mun zauna tace idan kin kwana biyu kin Zama 'yar gari ta bani Insiyya in Kara da ita Wai Daya tayi min kadan".
Wani irin kallo ya zuba Masa da sexy eyes dinta.
"Ki rufa Mana asiri mu karasa gida lafiya,kada kisa a tashi damu a social media ace Amare sabbin Aure sun rigamu gidan gaskiya a sanadin hadarin mota suna tsaka da cin amarci".
"To Ni menayi,?".
Ta qara kada Masa idanun tayi, wani smile yayi.
"Naga alama wannan kin wuce tunanina Bari muje gida kiyi min bayani da yaren da zanfi ganewa tunda kin Fara Zama 'yar hannu".
"Meye kuma 'yar hannu?".
Dariya ya qara yi "kije ki tambayi hausawa".
Ya fad'a Yana saka signal na shiga wata kwanar.
"Ina Kuma zamu? Naga ka shigo wani gurin nifa barci nakeji".
",Fadi gaskiya dai yarinya, ko dai...?.
Rufe fuska tayi da tafukan fararen Sol din hannuwanta Wanda suka Sha lalle.
Wani irin kyau tayi Masa ba kadan ba.
"Kunyar wa kikeji a Nan?".
Dai dai lokacin da taji ya Danna horn Sau biyu abinda ya tilasta ta bude idon ta kenan.
Budewar idanunta da bude gate din sai suka Zama kusan lokaci daya.
Hannu kawai ya dagawa securities din yayi gaba, wasu gine-gine ta gani masu azabar kyau ga titi Nan dodar sai haske kamar Rana ga flowers Nan masu kyau an qawata gidan dasu, Bata ankare da Ina bane Saida taga sun karaso main ginin da aka kawota ciki, Bata tab'a zaton girman gidan da Hajiya Inna take fad'a ya Kai irin haka ba,to ai wannan sai a dafa mutum a cinye na wancan gate din ma basujin ko labarin ba, parking lot na motocin gidan Wanda suke tamkar kamfanin siyar da motoci ya nufa da alama ba 'yan milkin bane a kansa Dan tana ganin yawanci sai dai a shigar da Masa da ita ciki.
Kallonsa take galala Kamar wata 'yar kauye.
"Lafiya irin wannan kallon haka? Duk gidanki ne gate uku gareki dayan sai kin kwana biyu kin warke tas mu zagaya kiga inda yake, gasu Nan compartment compartment sai inda kikeso Zaki zauna".
"Ko dai zamu zauna ai Ni Kuma na Gama shiga taitayina nasan wannan gidan mace hudu ne wata kila harda kwarkwara ma tunda da abun".
Bai tanka Mata ba ya bude ya fito, itama ta fito tana Kara waiwayen hanyar da suka biyo sai yanzu ta Kara karewa gidan kallo, ita abin yafi karfin sannin ta gaskiya da data ambaci tsoro Ashe ba tsoron takeji ba sai yanzu.
"Oya let's go".
Ya fad'a Yana janyota jikinsa "Wai tunanin me kike ne haka Kona Dr.din ne?.
"Dan Allah ka daina fada min sunanta".
"Tona daina muje kiyi min wanka kiyi min tausa yanda zanji Dadi Baki labarin nawa wata Kila mu gama zuwa asuba".



*********Tunda su Abba suka sauka a Bauchi yake Kiran wayar magaji Amma amsar Daya ce not available, malam Bala ne yaje dauko su tare suka taho dasu Aunty Hassana da Inna mainuna da Hameeda. Dan daga gidan zahrar airport suka wuce inda suka samu su Aunty Hassanar, tunda su Abba suka baro gidan Zahra Bai Kara kallon Hamza ba Dan idan ya dube shi ji yake zuciyarsa tana wata irin tafasa, Bai tab'a zaton haka daga gare shi ba, yayi zaton hankalinsa da tunani sun wuce haka kenan da hadin bakinsa aka munafurce shi anyi masa lullubin biri.
Karfe biyar saura suka shiga cikin garin Azaren katagum.
Gidan shuru kamar babu mutane a cikinsa su Aunty Hassanar suka shigo, parlourn Ammah ba kowa sai kamshin turaren daki Dana girki Daya cika shi.
Saida Aunty Hassanar tayi sallama sau biyu sannan Alawiyya ta fito daga kitchen tana amsa sallamar tare da fadin
"Lah Aunty, Inna sannaunku da zuwa mutanen sokoto ya hanya?".
"Hanya Alhamdulillahi mun dawo lafiya, ya muka sameku?".
Inna maimuna ta fad'a tana zama a Kan two seater.
"Lfy kalau Inna ya aka baro Amarya? mu ai mun tsufa a gida, Ashe Mama bataji Dadi ba a can?".
"Wallahi kuwa jiki kam babu Dadi tunda har za'a fita da ita can misira".
"Allah ya Bata lafiya, sannu Hameeda ya Mai jikin?".
"Jiki da sauki Alawiyya nagode".
Ammah ce ta fito daga cikin corridor din bedroom dinta.
"A'a Masha Allah! Inna sannunku da hanya, ai tun dazu nake zaman jiranku da naji shiru Baku karaso ba na shiga daki gurin wayata da ake Kira".
Abinci Alawiyya ta kawo musu da drinks.
"Waini Hajiya Ina su Hanifa ne naji gidan shiru alhalin an bar Miki 'ya 'yan Amana".
'yar dariya tayi "suna gurin Babansu tun safe dayazo gurin Abba suka tattara suka bishi".
Aunty Hassana Yi mamaki ba Daman tasan za'a rina Banda ta taushesa da kalamai masu dadi cewa yayi sokoton ze biyota ya gaji ta barshi ba matallafiya. Gaishe da Ammar tayi ta tashi ta shige ciki ta barsu da Inna suna Zaune suna Kara jajanta jikin Mama yayin da Hameeda ta nufi nasu part din ta aje luggage dinta da sauran tarkacenta na biki da aka basu.
Kiran sallar magariba ya tashe su daga hirar da Inna ke yiwa Ammah na irin daular arzikin da Allah ya Kai yarinyar su wadda ko a mafarki Basu tab'a zaton hakan ba.
Suna sallah sukaji kamar hayaniya daga parlour da sauri Aunty Hassana ta fito tana fadin.
"Menene haka nakejin hayaniya?".
Ai batasan lokacin daka kwalla Kiran" Daddyyyy....ka Bari wayyoooo Allah Ammah ku fito za'ayi kisan Kai a gidan Nan".
Da gudu ta karasa gurin dasu Ya imam da ya Abdul Hakeem keta kokarin banbare hannun Abban daga wuyan Salma wadda take wani irin kakari kamar na fitar Rai.
Magaji ne ya shigo da gudu baiyi wata wata ba ya girgije Abban ya raba hannunsa da jikin wuyanta ya dauketa cak kamar yarinya yayi Kan three seater da ita Yana fadin "ku bani ruwaaa..". Da gudu Aunty Hassana ta shige kitchen dauko ruwan sukayi kicibus da Alawiyya ta nufo parlourn da gudu da ruwan hawaye na bin Kumatunta.
Da kyar su Abdul Hakeem suka zaunar da Abban sai huci yake Yana fadin.
"Wallahi banga amfanin haihuwar ki ba Salma kinci mutuncina kin tozartani kunci amanata keda uwarki da Dan uwanki, damena rage ki? A gidan Nan abinda kukayi min na barku da Allah sai munyi shari'a da Rabi'a a gaban zatin Allah, Kuma a gobe ba jibi ba a gidan miji Zaki kwana ko wanene, Kuma karatu kin Gama a gidana har abada, itama Hameeda su kawo sadaki ko Bai Gama gidan ba ya zaba cikin nawa su tare".
"Haba Alhaji idan Rai ya baci ai hankali baya gushewa kada a hau dokin zuciya sai ayi aikin Dana sani, ka Bari abi komai a sannu Allah zeyi maganin komai,kowa da irin jarabawar da ubangiji keyi Masa, wasu ta 'ya'ya wasu ta dukiya wasu ta lafiayrta jiki ayi hakuri dan Allah ka taushi zuciyarka kada kayi aikin Dana sani".
Ba zato sukaga hawaye ya zubo Masa abinda Ammah Bata tab'a gani ba kenan duk iya zamansu, sai itama nata Hankalin ya ninka na dazu tashi ta matso kusa dashi tana fadin.
"Dan Allah Dan darajar Manzon Allah kada ka Zubar Mata da hawaye kayi hakuri kamar yanda Inna ta fada abi komai a sannu sai kaga an samu masalaha a Kai".
"Haba Asma'u wane irin tashin hankali ne wannan ace Dan daka Haifa kake lokarin Kare duk wani haqqi nasa da ubangiji ya Dora maka, amma a ce an wayi gari ya kangare ya Zama fasiqi duba medical report din Nan ki gani"..
Ya Mika Mata takardar dake cukuikuye a hannunsa.
Jikinta na Bari ta shiga warware takardar,bayani ne tiryan tiryan na adadin cikin da aka Zubar a baya da nasu bincikrn da sukayi da tambayoyin da likitan yayi mata da Kuma irin matsalar da aka Samu garin Zubar da wannan cikin.
Zuface keta ketowa Ammah ba qaqqautawa, wannan wace iriyar masifa ce a gidan Nan?.
A hankali ta furta "innailaihi wa inna ilaihi raji'un".
Ta manta dasu Inna da Yara ma a gurin ta zauna kusa dashi daf tana shafe hawaye..
"Kayi hakuri Abban Yara kowa da tasa' jarabawar Kai taka a haka tazo ka karba kayi hamdala a kowane yanayi sai ubangiji ya saukar maka da Rahamarsa"
Su Abdul Hakeem ne suka Fara fita kafin inna ma ta koma daki,Alawiyya ma ficewa tayi daga part din gaba daya, ya rage daga Salma dake mayar da nunfarfashi ruwan hawaye na Mata anbaliya ba sassauci,sai Kuma su Aunty Hassana da magaji sai Kuma su Ammar.
Ban Baki Ammah ketayi akan ya janye furucinsa Amma ya kafe ba canji.
"Haba Asma'u karuwa a gidana,a cikin 'ya'yana, wace irin masifa ce wannan, Kuma Dan yayarta uwa daya uba Daya ace yayi min irin wannan abun su kansu Dame na ragesu Banda tambadaddune sunki karatu sai sakarci, da sun msayar da hankali da yanzu Basu Samu tudun dafawa ba? Ina cewa tare suka Fara karatu da imam ba ya kasa akayi withdraw dinsa daga makarantar, to Aure babu fashi Kuma kowaye na samu saina aura Mata shi in Sha Allah.
Su Aunty Hassana suka shiga da Salma dayan bedroom din Ammah tana ta rusa kukan da baya fitowa.sabida wahala ga zafin ciwon da Bata Gama warwarewa ba.
Abban ma bangarensa a part din Ammah suka nufa da kyar Ammah ta lallashe shi yayi wanka ya Sha tea kawai ta bashi pcm ya sha, saida ta saukar da fushinsa Mai zafin sannan ta fito ta nufi parlour lokacin wurin Tara da Arba'in da biyar na dare
A Nan ta iske magaji da Aunty Hassana wadda har lokacin Bata tafi ba, dan Ammar cewa tayi magaji kada ya tafi ya jirata a nan.
Fuska babu annuri Ammah ta karaso inda suke Zaune.
"Me kayi kenan sulaimanu? Ka kyauta kenan ka hada tashin hankalin mutane banda Allah ya tsare me kake tunanin ze faru? kasa ayi Mana kisan Kai a gida, to kaji Dadi hankalinka ya kwanta wato Kai koje sarkin labari ko Kuma suda Mai bakin magana, to kaji dadi ka hada husuma saika zuba ruwa a qasa kashe burinka ya cika Abbanku ya sani sai me kuma?".
"Kiyi hakuri Ammah wallahi gani nayi idan nayi shiru naci Amanarsa yanda yake tsaye a kanmu, Kuma ni bada gulma na fada Masa ba kawai dai nace Naga sun fita ta baya da asuba tare da Ya Hamza Mama ta rako Salman tana kuka, daga Nan ban qara ce masa komai ba, bansan Wanda ya fada Masa sauran zancen ba, sai dazu da safe yace min sunyi waya da Ya Mahmud yace Zan raka Bilyaminun gidan Baba Malam Jos, shine fa muka tafi a hanya Ya Mahmud din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login