Showing 204001 words to 207000 words out of 280244 words

Chapter 69 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1086

ta Fara dariya shaidar ta ganeta kenan.

Saida Aunty Aishar ta Gama wayar ta shigo tana fadin.
"Au Kice mutuniyar ce ta tashi? Sai ki shirya fita zamuyi yanzu guri ya kure sosai kinsan Hussein shi komai nasa baya fada sai guri ya kure, sosai jibi fa zamu wuce Nigeria shine yace muje kasuwa kiyi tsaraba shi ya wuce Nigeria".
Da madaukakin mamaki Zahra ta dago ta kalli Aunty.
"Ya wuce Nigeria?"
Sai idonta yayi kwal-kwal ta tabbata abinda ya fada gaskiya ne, shikenan ita Kuma haka tata kaddarar take.
Girgiza Mata Kai Aunty Aishar tayi.
"Haba Banda shagwaba Mana, keda kike fushi dashi, yasan ko yazo bazaki saurarasa ba shi yasa ya tafi tunda baisan laifin da yayi Miki ba kike dafa shi da naki salon, Dan Allah a rangwanta Masa shi bako ne a cikin soyayya Bai taba yinta ba ke Kuma Naga taki da zafi ta kamashi batayi Masa da Wasa ba".
Da kyar ta iya mayar da hawayen, da suka so zubowa ta rasa dalili itama tata zuciyar Bata da wani karfi a Kan lamarinsa.
"Shike nan Aunty inda sabo na Saba yayi tafiyarsa Bai fada min ba".
Aunty Aishat ji tayi yarinyar ta Bata tausayi, kenan shima Yana gwada Mata halin miskilancin nasa, nata ne baya iya jurewa.
"Ki rabu dashi tafiyar ce tazo masa ba zato kiyi hakuri dole zamu zauna ya daina Miki irin haka tunda ke ba sanin halin yawonsa kikayi ba, inaga duk duniya Amminsa kadai yake bude Baki ya fada Mata duk inda zaya a cikin duniyar nan kafin yayi fushi kenan".

A hanya ma sosai Aunty Aishar ta dinga bawa Zahra Baki harta Dan ware, sun shiaga manayan shagununan kayan sakawa Ganin Zahra taki daukar komai yasa Aunty Aishar lodar kayan da take ganin sun dace, sunje bangaren jewelry's ma ta dauka Kamar me shoes and bags ta dauka kamar Gori ita Zahra Abu har tsoro ya Fara Bata kashe kudi ake kamar yayi daurin cargo aka yiwa kayan Aunty Aishar ta cike komai sannan suka bar gurin, sun shiga kasuwa nan ma ba kananun kudi ta kashe ba suma awon cargo din tayi musu daga karshe suka nufi gurin gyaran gashi da jiki Aunty Aishat ta saki kudi ba kadan ba anyi Mata gyara iya gyara, suna Cikin Yi Mata gyaran jiki matar Mai gurin tazo tana tambayar Aunty Aishar cikin yaren indianci, tunda su dai basa Jin turanci duk da India suma suna English.
Zaru Aishat din tayi domin ta rasa yanda zata tunkari Zahra da tambayar domin wani Abu matar ta sakawa Zahra a hannu taga yaki Zama kuma a ka'idarsa na matan aure ne kuma an fada Mata matar Auren ce gyara kawai za'a Kara yi mata, magana matar tayi Mata akan taje ta tambayar Mata ita saboda tasan wane iri abubuwan zata yi Mata.
Aunty Aishar ji tayi abun yayi Mata nauyi gaskiya, ai da kunya taje tana titsiye yarinya da irin wannan tambayar,cewa tayi suyi Mata na 'yan matan kawai mantawa tayi tace musu haka ashe Bata tare ba.
Zahra har Saida ta gaji da Shan abubuwa, Miko Mata ake tana shanyewa Saida taji tana neman yin amansu sannan aka saurara Mata aka dosa tureren jiki, kunshi ne tace bata son irin nasu Mai yawan Nan sai akayi Mata Dan kadan Mai azabar kyau, lokacin da aka Gama Mata komai ta fito Saida Aunty Aishar ta shiga wani shock Dan yes matar bros ta wanku iya wankuwa Ina ma Yana Nan da yau dai saiya maida yawu kenan maganar sweet heart da kamshin gaskiya kenan tunda idan ba Rami meya kawo zancen Rami ance an saka Mata abun matan aure yaqi Zama kenan budurwa ce, ita kwamacalarsu nema take tafi karfin tunaninta.
Sun dauki hanya sosai Afnan na jikin Zahra duk tayi laushi da gani ta gaji, sai 'yar mita take Auntyn ce da Dan kallo inda suka tana ci gaba da driving din ta, tamabaya ta jefowa Zahra Wai dazu kun hadu da Sayyid ne da safe?".
Dan Jim Zahra tayi sai Kuma tace "ko wani Dana gani a kitchen daga shi sai boxer short da singlet Yana tsaye a gurin coffee maker?"
"Eh shi nake nufi".
"Na ganshi lokacin Dana fito da zummar na Dora abin break sai na gashi ba yanda ya kamata ba tunda baligi ne shi Kuma ba gidansa bane, Kinga ai Bai kamata Yana fitowa a haka ba,ko Dan bansan ya kuke dashi ba ko mamanku daya".
Wata kwana ta shiga kafin ta danyi tsaki..

"Wallahi kanin sweet heart ne, ni kaina bana son zamansa a gidan tunda idan Yana nan bana sakewa nayi duk irin shigar da nakeso tunda Allah yasa shi Mutum ne Mai shegen son Mata dan haka yau a sama Zaki kwana bana son samun matsala Daman abunda yasa na baki daki a kasa Ina muku wani zato ne ashae hasashena gaskiya ne, yanzu kuwa da baya kasar saina shige dake ciki gudun samun matsalar da yaketa jamin kunne a kanta".
Nisawa Zahra tayi tana fadin Allah ya kyauta.
Koda suka shigo Basu huta ba abin bude Baki suka yiwa masa.
A tsakanin kwana biyun nan Zahra ta gaji iya gajiya
Kuma Basu Kara haduwa da Sayyid ba,dan duk wata kafa Aishat din ta toshe ta yayi nacin har yayi zuciya Dan ko kasa Bata saukowa.
Ranar da zasu tafi Mr salahuddeen yazo ya daukesu da kayansu sai a ranar Abulkhairi ya dawo gida, har dashi za'ayi tafiyar.

*AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.

Page 74

............. Mahmud ba Nigeria ya nufa ba lokacin Daya baro India Dubai ya wuce ya samu Sameer a can, lokacin Daya je Sameer ya Gama duk abinda ya kamata ya hada da taimakon matar abokinsa Tajuddeen, 'yar Kano ce Khadija Basu Dade da Aure ba macece wadda tasan Asalin gayu, lefe ne aka hada na garari set din akwatuna ashirin da hudu Banda manyan trolleys guda goma, Gold ma Saida aka ciki wani medium kit dasu, ita kanta Khadija anyi Mata kyautar ban mamaki.
Saida yaga komai sannan yacewa Sameer ya aunasu Nigeria Amma gidansa jikin gidan Hajiya Inna za'a ajesu sai Aishat ta gani Koda abunda za'a Kara ko za'a canza.

Tare da Sameer suka nufo Nigeria sun samu good 8 hours suna reto a sararin samaniya kafi ubangiji ya saukesu lafiya a Lagos, lokacin karfe hudu da rabi na Asuba,tickets suka siya Lagos to Sokoto zasu bi flight din karfe shida da rabi na safe, yayin da jirgin su zahra ya Sauka karfe biyar da rabi na safe a Kano, Suma jirgin karfe Tara zasu bi zuwa Sokoto.
Cikin kamalarsa da kwarjininsa na halitta handsome guy dashi kana ganinsa kasan yana Cikin ganiyarsu kkuruciyarsa a hankali yake gagarowa daga steps din jirgin yayin da Sameer ke bayansa rataye da jakarsa ta laptop. Faruq ne ya tare shi da madaukakiyar murna ya rungime shi ji yake kamar ba gaske ba lokacin Daya kirasa yake fada Masa yazo airport da mota yayi zaton da Wasa yake Masa duk da babu irin wannan a tsakanin su, amma qila wa qala yazo bashi da tqbbacin zuwan nasa.
Dan janye Faruq din yayi daga jikinsa Yana Dan doka kafadarsa.
"Welcome back to Sokoto Ya mahmud, Allah ya tsare gaba yasa kafi haka ya doraka kan makiyarka gashi ka dawo da ranka da lafiyar ka da kuma abinda basaso arzikin naka".
Faruq din ya fada bakinsa yaki rufuwa saboda tsabar farin ciki Dan yayi musu mugun bazata ya shqmmaci kowa Dan jira kawai ake aga su uncle Mustapha sun taso Qeyarsa su kawo shi kamar wani Dan ta'adda, domin duk Wanda Abbie yaso maganar kada ta fita Saida ta Zama abin tsegumi a cikin family.
"Just forget about this charpter ai it's past, bani key din sai kayi waya a kawo maka mota ku tafi kaida Sameer".
Ya fada Yana Mika Masa hannu..

"Ka Bari Ya mahmud na kaika Mana ai zefi Ina Kai Ina driving daga saukarka, gara na kaika har gida Nima na bada nawa surprised din asan Nima Ina da wani matsayi har yanzu a gurinka".
Ya fada Yana 'yar dariya da shilla kafa kamar Mai Wasa da ball.

"Bani kawai kasan lokacin Dana bar gidan? Ni kadai na fita ni kadai Zan koma I hope you understand".
Kai Faruq ya gyada Masa Yana Mika Masa key din.
Har gurin mota suka raka shi, Sameer ya saka Masa laptop din a back seat ya rufe.
A hankali ya Bata wuta ta Fara tafiya Zuciyar fal da nishadi sabanin lokacin Daya bar garin afujajan babu nutsuwa Kota sisin kwabo a tare dashi. Tintac glass ne a motar a hankali yake tafiya Yana karewa garin kallo ba laifi an Dan samu 'yan canje-canje, gidan Hajiya Inna ya nufa Yana ayyana ta inda aka hau ta Nan ake Sauka.
Dai dai kofar katafaren gidanta ya tsaya sau biyu Yana latsa horn sannan security din ya leko Bai sheda motar ba Dan haka ya fito kafin yazo mahmud ya sauke glass din a hankali, yana zuwa yayi tozali da mahmud ai baisan lokacin Daya juya da gudu ba Yana fadin.
"Allah ya taimakeki barka da Sauka". Nan da nan ya saka remote control ya bude gate din mahmud ya Danna kan motar ciki, wata irin Rahama yaji tana saukar masa kowa ya bar gida gida ya barshi, gidan ya tsaya Yana karewa kallo a hankali ya furta.
"Masha Allah! Alhamdulillahi bi ni'imatihi tutimmussalihat".
Har abinda be fada bama Faruq yasa anyi, sabon part din da akayi daga gefen na Hajiya Inna ya kalla yayi wani murmushi Wanda shi kadai yasan ma'anarsa.
"Shadi....." (My happiness)
Ya furta in a soft voice.
A hankali ya bude kofar ya fito, Nan da Nan Malam sabo security ya karaso ya zubewa Yana gaishe shi, tare da yi Masa barka da sauka, da yake safiyar ce harabar gidan ba kowa sai daga can gefe wasu ma'aikatan su biyu masu shara da ban ruwan flowers suka taho da sauri bakinsu kamar gonar auduga, daman tun shigowar motar suka tsaya da ayyukan su suna jiran suga Wanda ze fito daga wannan walfefiyar motar data shigo.
Ya dan Jima tare dasu daman kusan haka fabi'arsa take, da wuya ya shigo guri ya yiwa ma'aikatansa shaf-shaf ya kan dauki lokaci tare dasu, to bare shi daya dauki dogon lokaci bai hadu dasu ba.

Bayan ya sallamesu ya nufi kofar parlourn yana Kara yaba yanda akayi renovating din gidan tamkar sake ginin shima akayi.
Bude kofar yayi ya shiga gurin yayi masa kyau fiye da yanda yayi zato duk da Faruq ya turo Masa ta whatApps, ya Jima yana tsaye a parlourn kafin yayi kunar bakin wake ya nufi bedroom din Hajiyar.
Dan knocking yayi kadan kamar na munafirci, gyaran murya tayi daga can nesa daga ji Bata Cikin dakin tsayawa yayi tana karewa dakin kallo komai tsab tamkar dakin Amarya. Dan Hajiya Inna badai tsabta ba ga kamshin itama ba'a barta a baya ba, a hankali ya zauna a Kan sofa Yana Dan kishingidawa a kai.
"Wai wane irin rashin Hankali ne irin wannan za'a shigowa Mutum daki baya Nan ana ji Kuma Ina gyaran murya akayi min kunnen uwar shegu Dan an......"
Ai Bata karasa maganar ba tayi wani tsallen albarka tana fadin.
"La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullahi!! Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir Rahamanir Rahim, me Zan gani a nan?".
Tashi zaune yayi Yana Kare Mata kallo, tanan yanda take sai abinda ba za'a rasa ba na karin kwanakin rayuwa Dan ma tsufa ne na Jin Dadi.
"Sai ki karaso Mutum ne ba Aljani ba da kike zabga dogon salati, nine na dawo kizo mu Dora daga inda muka tsaya".
"Kara matsawa tayi kofar toilet din tana Masa kallon rashin amincewa.
"Kai daga Ina idan shedani ne Kai me nayi Mata zaka shigo ka bude min Ido da siffar jikana Dan anga na kwallafa Rai a Kansa".
Tashi yayi tsam ya nufi inda take Yana murmushi yaga alama ba fashintar yaren Bakinsa zatayi ba gara ya matsa taga zahiri.
Saida ya karaso kusa da ita sosai ta tantance shine da gaske.
Hannu ta Dora a ka ta fasa kuka tana fadin.
"Yanzu saboda Allah ka kyauta kenan,kayi tafiyar ka barmu da tashin hankali sau uku ana kwantar Dani a asibiti jinina Yana Hawa ya Kai dari biyar harda dori, nifa duk abinda na fada maka wallahi iya fatar bakina ya tsaya ba har zuciyata na fada ba, Kai Kuma sai kayi fushin zuciya kayi Mana naki ka barmu da tashin hankali munyi nema har mun gode Allah Amma babu ko labarin Wanda ya ganka".
Hannunta ya riko Yana fadin.
"Dan Allah ki daina kuka ai gani na dawo yanzu na sauka a garin Nan Kuma banje ko Ina ba duk yanda nake da kishirwar ganin Ammi amma banje na ganta ba saida nazo na ganki".
Gefen gado ya zaunar da ita tana faman share hawaye.
"Ki daina kuka kinsan kina da hawan jini fa maimakon kiyi godiya ga Allah Daya dawo Miki Dani lafiya harda ribar kafa, kada kisa 'ya'yan ki suce Zan karasa musu uwa daga dawowa ta"..

Ba zato yaji ta Zuba masa dundu, ya Dan gabtsare Yana fadin.
"Kai Ashe da sauranki irin wannan tsohon Kashi saiki karyani ki jawowa matata jinyar da Bata shirya Mata ba".
"Ja'iri dubi yanda ka zama kamar a taba ka jini ya fito, da gani ka Sami kyakykyawan masauki, kana can ka barmu da kwanan zaune da zulumin Ina ka shiga ya kake a Raye ko a mace, Ashe shi yasa wannan uban iyar yazo ya tashi hankalina da aikin gyaran gida da wasu gine-gine anyi Masa tambayar duniyar Nan akan aikin daya tarko Amma sai yace Daman da aikin tuntuni a hannunsa Yi ne Baiyi ba sai yanzu dole aka kyaleshi Ashe da kukus a shinkafa".
"Allah wannan matar bakya gajiya da 'yar cewa ina laifin gyaran da yayi Miki gaki Nan kamar wata amarya, ko Ina sai tashin kamshi yake Ni tashi ki samo min abinda zanci rabona da abinci tun a can inda na baro saboda tsabar son ganinki da nake yi, amma sai welcome din dundu na samu inaga badan nayi alkawarin kezan Fara gani ba da babu abinda ze hanani wucewa gidan mu, da a can ne yanzu da babu masakar tsinke a gabana Amma ke ko Dan pure water ma babu".
Ya fada Yana mikewa tsaye.
" Ina Kuma zaka daga zuwa shanshani, Kai dai har abada baka Zama guri Daya kamar kifi".

"Ni babu inda zani dakina na kusa da naki Zan shiga na danyi wanka barci nakeji".
Wani kallon baka da man Kai tayi Masa tana tabe Baki.
"Ban gane barci zakayi ba kana nufin har yanzu baka Huce bane ko menene? Bazakaje kaga iyayenka ba kake neman Mike kafa a nan!?"

Watsa hannunsa yayi Yana Dan canza fuska.
"Tunda nazo ai kinsan magana Kuma ta kare,.Abbie din ne baya Nan shi yasa Amma fa da dare Zan shiga in Sha Allah".
"Ai kuwa kafarka kafa ta bazan Zuba idanu ba a wannan karon su Kara Kora min Kai wata uwa duniyar gara naje ayita ta Kare, tunda Naga alamar da niyya ake maka wannan makarkashiyar Dan anga Allah ya fitar da Kai zakka kasan haka kakanka yayi ta fama da irin wannan abun banbancinsa da Kai shi jarimi ne baya guda baya ja da baya Amma Kai ragon maza ne daga ' yar magana ka kwashi jiki kabar gida, to me tafiyar taka ta dad'a maka yanda ka tafi haka ka dawo babu kayan ka babu na rataya sai uban fari da mirjewar jiki dai gata nan".
Wani smile ya saki yana lumshe idanu.
"Ai kuwa ni na samo kayan ka na samo na rataya, ki Zuba idanu ki Sha kallo kece ma Mai masaukin bakin Dan a Nan saina mayar Miki da maganar da Kika fada min, kin tuna da ita ranar da zanbar garin?".
Kafin ta Sami zarafin yin dogon tunani kira ya shigo wayarsa. Ganin Aishat ce yasa ya fice da sauri Yana fadin.
"Eh kuje gidan Ammi din Mana ki kaita amma bance Kice komai ba ki bar sauran abun a hannu na".
Dan Jim yayi Yana sairarenta daga can bangaren.
"Ok hakan yayi kuje sameer din ya kaiku gidan shi yasa nace ya biyoni yayi min wannan aikin nafi son sai dai a bude ido a ganta ba'asan sanda tazo ba kafin Kuma a fashinci wacece ita din".
Wayar ya cire Yana furzar da iska daga bakinsa.

* AUREN HUCE HAUSHIN*

. AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.

09061432330
Or
08055362975.

Page 75

......... Tunda jirgin su zahra ya sauka a filin jirgin sultan saddiq Abubakar dake Sokoto gabanta ke faduwa,tasan a Nan ne komai fa ze iya tabbata ko ayi ko a fasa gata a Sokoto sai Kuma abinda Rabbi Izzati ya hukunta shi ne ze tabbata, Afnan ce a sabe a kafadarta tana takawa a hankali tamkar Bata son taka kasar Dan da gaske ta Gama yin giving up a cikin Lamarinsu da mahmud.
Aunty Aishat ce tsaye a Kan kayan da sukazo dasu Saida komai ya kammala sannan ta nufo inda Zahra suke ita da Afnan yayin da Abulkhairi yake biye da ita kafa ya kafa.
Kamar tare Aishat din suke da Sameer Dan tana karasowa shima Sameer Yana karasowa da waya a kunne da alama doguwar waya yakeyi, saida ya Gama sannan su zahra suka gaishe dashi har Aunty Aishat na fadin.
"Nayi fushi kaje har India amma ka kasa zuwa mu gaisa".
"Kiyi hakuri kinsan halin kayanki bashi da lokacina a lokacin Kuma infact ma dai bai barni na zauna ba".
"Ai shikenan Daman ku Ina kuke Zama guri Daya tamkar marasa gaskiya Baku da standard gurin Zama dole ku canza yanzu kun aje iyali suna da hakki a kanku baze yuwu ki ringa Abu babu lisafi ba Daman kasan tun farko Ammi Bata son wannan dabi'ar taku ko misqalazarratin Sai dai da yake Abbie ya tsaya muku ne yasa dole ta hakura".
"Wannan gaskiya ne Auntyn mu za'a gyara in Sha Allah ko Baki fada ba zakiga canji ke dai kisa Ido kawai zakice na fada Miki".
"Allah yasa hakan ta kasance".
"In Sha Allah".
Sameer ya fada yana Dan kallon zahra ta gefen Ido tana ta yiwa Afnan Wasa.
"Madam barka da sauka sokoto Allah yasa mun shigo kenan, yasa Albarka a cikin rayuwar da zakiyi a cikinta".
Dan murmushi tayi, yayin da Aunty Aishat ta amsa da. "Allahumma Amin, ni jikina ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login