Showing 150001 words to 153000 words out of 280244 words

Chapter 51 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1084

yanda zahra ke tsuma sai yaji ba Dadi, gaskiya oga Bai kyauta ba, da alama ta hadosu ne yake horata ta wannan hanyar wato halinsa Yana Nan na rashin son wargi, itama Bata tsira ba saiya nuna Mata Hali.
Gurin sagir ya nufa, Yana Jin babu Dadi a cikin ransa, ga wadda za'a hada da barbar Nan yayi kaca-kaca da banza, Amma ya wani kyaleta taci bulus sai wannan Mace Mai daraja ze hada da wadannan karnukan nasa masu kama da kuraye su tsare yarinyar mutane, shi ko tausayinta bayaji ya wani yi zamansa a ciki idan ma sumewa zatayi bashi da damuwa, Allah idan ya wuce saiya casa waccan karamar 'yar iskar dan yaga alama tsohuwar Yar duniya ce ta kware a gurin munafurci.
A zaune ya samu sagir Yana jin wakar boda katsina.
"Dallah kashe Mana! Kai ko imani ma baka dashi, ka sakarwa baiwar Allah karnukanku marasa mutunci kazo kana shakatawa,to Bari na fada maka, idan kayi Wasa ka kusa cin taliyar karshe a karkashin oga wallahi, dan ba kowa ka sakarwa karnuka ba sai amaryar oga, idan tayi marking dinka kana zaune za'ace ka Kara gaba".
Ya fada yana Jan tsaki yayi gaba abinsa. Sororo sagir yayi yabi Zayyan da kallo sai Kuma ya tashi da sauri yabi bayansa.
"Dan Allah Zayyan tsaya, fada min gaskiya wallahi na dauka irin masu kawo kansu din Nan ne yake so ya koya Mata hankali, tunda mun shaida oga baya harkar Mata, shi yasa nayi biris da lamarin su".
"Yayi kyau, wallahil azim nasan hankalinsa Yana Kanta dari bisa dari kawai dai so yake ya nuna mata shi din Jan wuya ne baya daukar shirme, tun wuri kasan yanda zakayi ka mayar dasu muhallinsu kafin lokacin fitowarsu yayi su fito patrol"
Fitoh daya sagir yayi musu suka nufo inda suke tsaye, gaban sagir din suka turje gaba yayi suka rufa Masa baya.

Mahmud ne ya fito sharr dashi da gani wanka yayi ya sake wata shigar kananan kayan sai zuba kanshinsa yake as usual, tsaye yayi Yana yiwa Zayyan Wani kallon tuhuma sadda Kai yayi Yana shafa sumarsa.
"Sorry sir, Naga ta takura ne kamar zata shide Ni Kuma Naga kada ta Kira maka ruwa".

"Ok ka fini sanin abinda ya Dace kenan ko?"
Shiru Zayyan din yayi shi dai ai yayi abinda ya dace yasan Kuma yaji Dadi nunawa ne bazeyi ba, gangarowa yayi da sassarfa ya nufi motar dai-dai sagir na dawowa daga mayar da su barbar.
Kamar ze Masa magana saiya fasa.
"Zo ka mayar damu gida bazan iya tukin Nan ba na gaji".
Ya fada Yana satar kallon zahra wadda tayi kalar tausayi da gani ba karamin tashin hankali ta shiga ba.
Key din ya Mika Masa ya zagaya inda Zahra ke zaune ya bude side din yana mika Mata hannu alamar ta Kama ta fito, dauke Kai tayi Kamar bataga abinda yayi ba, ganin yana gyara tsayuwarsa yasa tayi wuf ta fito tasan ba karamin aikinsa bane ya daukota a gaban wadannan garadan.
Ta gefensa ta wuce ta shige can kurya kusa da window ita fa ji tayi Yana wani karni Maimakon kamshin da yake bazawa.
Kyalen after dress dinta ta ware rolling din ta rufe fuskarta tana ci gaba da sharar hawayenta, yau Mahmud yayi Mata karshen wulakanci, wai ita ya sakarwa karnuka.
Tana ji yana yiwa Wanda ya kawo Mata karnuka magana akan abincin karnukan.
Sannan taji sun fita daga gidan, ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana Fadi "mugu" a cikin zuciyarta, ba Kama Nan da Nan idonta ya Kara cikowa da hawaye Wai itace mijin aurenta ya kawota gidan da yake badala da wasu matan ya ajeta da karnunka ya Gama abinda zeyi harda wanka da canza Kaya Dan ta tabbatar da abinda yayi din.
Tunda ya shigo baiko kalli inda take ba, wayarsa kawai yake ta dandangwala ko kansa Bai dago ba Saida Yana lure da duk motsinta ta kasan Idonsa.
Basuyi tafiya Mai nisa sosai ba idan tayi la'akari da wadda sukazo zuwa nan din taji horn alamar dake nuna anzo gidan, ko Kuna anzo wani gurin a hankali ta bude idonta gidan da sukazo jiyan ne suka dawo har kofar falo zayyan yaje da motar kamar dazu da zasu fita, da sauri ta bude ta fice Bata son yaga weaknesses dinta ko kadan.
Saida Zayyan ya jide kayan cikin motar sannan ya kaita parking lot ya aje ya dawo gurin da Mahmud yake tsaye. Sakon gidan Baba malam ya tura Masa a waya ze saya gobe ya tafi dasu can Azaren.
Zahra na shiga ta Haye sama direct bedroom din data mayar nata ta shige, har dishi dishi take gani saboda tsabar tashin hankali, ko a mafarki Bata taba tunanin zata Sami kanta a cikin irin wannan yanayin ba, wani sabon kukan ne ya balle mata cikin kukan ta Fara rokon Allah s.w.a.
Tana fadin "Ya ubangijina ka shiga cikin lamarina da wannan bawan naka, bansan ko waye shi ba, Kaine ka hadani dashi cikin kudurarka da ikonka, ka jibinci lamurana Dan isar Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w kada ka Bari ya cutar Dani ta kowanne Janibi, Ubangiji Kaine mafi tausayin masu tausayi, mafi jinkan masu jinkai ka tausayawa maraicina kasan halin Dana shiga a baya ka rabani da dariyar makiyana, innalillahi wa innailaihi raji'un Allahumma Ajirny fiymasubati wa aklinli khairin minha".
Tayi rub da ciki tana ajiyar zuciya, Nan da nan Kanta ya Sara Mata sai ciwo da gyar ta iya tashin ta canza kayan jikinta Dana barci, kwantawa tayi ta shiga tariyo rayuwarta tun farkon Fara samun matsalar ta da yanda lamuran suka dunga faruwa kamar a cikin film da haka har barci ya saceta ko Addu'oin kwanciya barci Allah besa tayi ba.
Sai da Mahmud ya Gama komai sannan ya hauro saman Dan Saida ya Gama wasu aikace aikacensa sannan ya shigo dakin, yayi mamakin yanda ya tarar da ita da alama barcin shammatarta yayi, pyjamas ya saka ya dawo ya zauna kusa da ita har lokacin tana sauke ajiyar zuciya a hankali.
" 'yar rigima kawai, maganinki su barbar din, da bazaki Bari na samun bakin zaren da nake son kamawa ba,me bakin tsiwa kawai"
Ya dan shafa sumar Kanta wadda ta kwanta baka sidik da ita sai daukar Ido takeyi.
Jakarta gani a y
Kasa ya dauke mata, sannan ya juyota ga mamakinsa ruwan hawaye ya gani sun gangaro daga idanunta kamar idanunta biyu, take yaji wani rashin Dadi ya shige shi, to meyasa yayi Mata haka ne Wai?.
Harshensa ya saka ya Fara dauke hawayen, Jin hucin numfashinsa a fuskarta da mayen kamshinsa yasa tayi fargigit ta bude Ido.
Da sauri ta yunkura zata tashi jikinta na tsuma.
"Cool down precious nine". Ya riketa Jin yanda jikin ke rawa.
Cikin wani irin kuka Dan ganinsa wani bakin cikin ne ya lullubeta,daya kira sunanta ji tayi Kamar ya watsa Mata wuta,da gaske ya Gama fice Mata daga Rai Sam duk yanda yake smart din Nan ganinsa take bakikkirin kamar bayan tukunya.
"Ni ka sake wallahi warin najasa kakeyi, bazan iya Zama da fasiqi ba. Allah saika mayar dani gida ka rabuda dani Kuma, tunda ba tare aka haliccemu ba, daman ance tsintacciyar mage Bata mage, shi yasa ka kawoni nan ka nuna min true colour dinka, kowa kallon mutumin kirki suke Maka ashe kura ce da fatar akuya,tun yanzu ka Fara min haka Ina ga idan zama yayi zama, ai Zina har a gadon barcin mu za'ayi ta, wanda baya Jin kunyar Mahaliccinsa wazeji kunya kuma,? Ai Manzon Allah saww yayi gaskiya daya ce kuyi abinda kukeso idan bakwajin kunya".
Ikon Allah ya tsaya yana kallo da gaske ta rude masa, Bai taba zaton haka take da tijara ba, kalma mafi Muni da take fada Masa ita tafi cin zuciyarsa. "FASIQI".
Janyota yayi da karfi cikin jikinsa, kokowar kwacewa ta Fara tana fadin.
"Ka sakeni niba mazinaciya bace kada ka shafa min masifa wallahi warin Zina kakeyi".
Shi abin nata dariya ya bashi bilhaqqi da gaske take fada Masa kalmar har zuciyarta.
Girgaizata yayi da karfi Yana fadin.
"Zahra ki nutsu! menene haka kikeyi, waye mazinaciya?".
Ba tsoro a idanunta Wanda suka tine sukayi jawur tayi masa wani kallon banza.
"Kaine Mana Wanda baya tsoron taka dokar Allah Wai ka daukeni ka Kai inda zakayi masha'arka dan bani da qima da daraja a idanunka. .
Cikin zafin nama ya matseta a jikinsa, cikin kaushin murya tamkar bashi bane wanda yake ririta ta ya Fara fadin...
"Mai maita min abinda Kika fada? waye Dan iskan fasiqin? Anyi fasiqancin idan da abinda Kika Isa kiyi, Kuma kin Dade bakiji Ina warin najasa ba,zakiga najasa iya ganinki 'yar rainin hankali kawai, Kuma wannan ya Zama na karshen da bakinki ze fada min irin wannan maganar wallahi idan ba haka ba Zan nuna Miki ko wayeni tunda Naga bakinki bashi da linzam ke duk abinda yazo fada kikeyi bakya taunawa, saina Baki mamaki wallahi".
Ya saka yatsunsa biyu ya rike labbanta na sama Dana kasa, sannan ya kafa Mata idanunsa da suka rine da bacin rai, rufe nata idanun tayi dan wallahi gani tayi ya juye ya zamar Mata wani abun tsoro, ga labbanta sai zogin rikon da yayi musu sukeyi, nan da Nan jikinta ya dauki rawa, hannu ta saka tana kokarin banbare nasa hannun daga bakinta yayi caraf ya rike hannuwan nata mutsu mutsu ta shiga yi ga babu bakin magana sai ruwan hawaye ke bin kumatunta kawai, sai da ya tabbatar ta jigatu sannan ya saki bakin Wanda har ya Dan kumbura labban sunyi jajur.
Hannunta ta saka ta rufe fuskarta tana kuka Mai sauti, a haka ya taka ya wuce abinsa baiko karabi ta Kanta ba.

*******
Hajiya Mama cikin tashin hankali ta dubi sahura.
"Ina kike tunanin Asabe na zuwa kije ki dubo min ita".
Dan jim sahurar tayi kafin tace. "Ina na sani Mama, Daman a gidan nan na Santa ta dalilinki bansan komai a Kanta ba, gidan da suke ma ai kece Kika kwatanta mini lokacin da Zaki Fara aikena gidan gurinta".
Tsaki mamar tayi, ita duk lamuran sun lalace Mata, to Ina Asabe ta shiga tun jiya? ga number ta Bata shiga tayi nemanta har ta gaji amsar Daya ce a rufe Layin yake.
Number Aunty Ladi ta nema ta fada Mata ga halin da ake ciki, amma itama layin baya shiga, sallamar sahura tayi, ga abin fada amma ba Hali tunda sahura iya tsegumin cikin gida kawai ta sani bata da masaniyar badak'alar karkashin kasar da akeyi a gidan.
Part din Abba ta nufa duk da ba ranar aikinta bane inda sabo ta Saba irin wannan kutsen, a tufe ta samu part din abinda ya Bata mamaki kenan, juyowa tayi tana tunanin ko wani waje ya fita, to ko bayanan ai ya kamata gurin ya Zama a bude tunda Ammah zata shiga.
Haka ta koma part dinta tana zancen zuci, bayan kamar minti talatin ta sake komawa kamar dazu gurin a rufe dai yake,kiran wayarsa tayi, ta shiga Amma ba'a dauka ba, abinda ya Kara daure mata Kai kenan ta nufi part din Ammah.
Parlourn ba kowa sai TV a kunne volume ta rage tayi sallama shiru ba motsin kowa, wata sallamar ta Karayi daga can kitchen Alawiyya ta amsa Mata ta fito tana gaishe da Mamar.
"Ina Ammah ne na shigo naji shiru inata sallama" .
Cikin girmamawa Alawiyya tace Mata "tana wancan bangaren na bayan nan".
"Wanne kina nufin sabon ginin da akayi?".
Kaita gyada Mata alamar eh.
Mamaki ne ya cika Hajiya Mama.
"kije ki fada Mata Ina son Zan ganta ne yanzu"
"To ai Mama suna tare da Abba ne, kuma tace kowaye yake nemanta kada a kira ta".
Jiki ba kwari ta juya ta koma part dinta, taso taga Abban kwarai sai dai ta tuna da maganar Daya fada Mata kwanaki yace kada ya sake ganin kafarata da dare Idan ba aikinta bane, kome take nema ta fada Masa kafin lokacinta ya wuce karshe ma yace Mata dole ya raba kowa ya mallaki dakinsa a part dinta,wato shine aka tashi wancan ginin saboda matar so, ita Kuma ta zauna a tsohon gurin da suka Gama dabdala su biyu, kwafa tayi tana ayyana wani abu a karkashin zuciyarta.
Har karfe goma Bata samu wadanda take nema ba ga Abba ma shiru be shigo ba, be kuma biyo kiranta ba har lokacin karshe ma network din wayar gaba Daya ya dauke abinda ya tilastawa Mama hakura Dole Kenan.

**


Zahra barci dai sai barawo amma kusan yanda taga Rana haka taga dare, tayi Dana sanin zamanta a Nigeria ma kwata-kwata da ba'a nan ta rayu ba da wataqila kalar kaddarar ba haka take ba, tunda tayi sallah ta Gama arzkar ta nade a gado wani irin barci yayi awon gaba da ita tunda shi ba'a cin bashinsa sai an biya.
Har karfe bakwai Mahmud be shigo gidan ba anyi meeting ne na 'yan unguwar yanda za'a Zuba matakan tsaro saboda b'atagarin dake neman damun mutanen unguwar, Mahmud ya bada kaso mafi yawa na gudunmawa da alkawarin bada salary ga "yan vigilant din da zasu rinqa patrol din, abunda ya bawa wasu da yawa mamaki Kenan dan ba Wani zama yake a unguwar ba sai ayi wata shida ba'aga giccinsa ba, ballantana wannan karon ya kusa shekara ma be zo ba sai yanzu.
Baibi takan Zahrar ba duk kuwa da yanda zuciyarsa ke azalzalarsa akan yaje din, yaga Idan ba da gasken gaske ya iya danne son da yake Mata ba Nan gaba baze iya sarrafata ba Idan ta gano itace weakness dinsa akwai damuwa.
Sameer ya Kira ya fada masa yayi musu order din break fast madam Bata Jin dadi, ze Fara masa surutu ya kashe wayar Yana fadin.
"Allah ya shirya ka Sameer kayi zaton kowa irinka ne mayen Mata kawai".. Wanka ya shiga so yake su fita da wuri akwai abubuwan da yake so suyi su Gama kafin yabar kanon.
Awa Daya Mai kyau Sameer ya diro gidan da abincin da Fateeha ya hada, da yake itama gwanace gurin girkin Kuma Mahmud yana cin abincin ta.
Saida Mahmud yaci ya koshi sannan suka fice daga gidan,Sameer beyi karambanin tambayar Zahra ba duba da yanda yaga fuskar Mahmud din kamar baya cikin walwala, sai Shima ya Share kawai.
Zahra ba ita ta tashi ba sai gurin Sha Daya da rabi,tayi mamakin yanda lokaci yaja haka, wanka tayi ta shirya ta saka wata rigar shadda purple dark saita fito da asalin kyawunta da hasken fatarta sosai, Bata daura dankwalin ba ta yafa gyale tayi gaba tana Zuba nata kamshin. Tunda ta fito taji kamshinsa ya cika mata hanci tasan Yana gidan kamar zata koma sai Kuma tayi ta maza ta gangaro stairs din.
Ba kowa a duka parlours din da alama kamar baya gidan , gurin dining din ta wuce ganin kayan abinci a Kai, tana zuwa taga anci abincin, kenan shiya nemo yaci nasa ya fice daga gidan Bata cuci Kanta ba ta zauna tana duba abubuwan dake cikin sinasir ne da miyar agushi sai Naman Kan saniya da kunun gyada, ba karamin Dadi taji ba sai taji tana kewar Ammah kusan haka take yiwa Abba duk weekend idan Yana gida yafi son abincin gargajiya, zubawa tayi taci Mai isarta ta koshi ta kwashe sauran ta Kai kitchen ta saka a fridge ta dawo ta gyara gurin.
Ta nemi guri ta Zauna tana jiran ta inda Mahmud ze bullu ayita ta Kare zama dashi dai ta Gama duk yanda za'ayi sai dai ayi.
Wayar Daya Bata ta bude ta Kira number Ammah. Auta ne ya dauka Jin muryar Zahra ya Fara murna da tsalle yana Kiran. "Ammah ga Adda zahra a waya".
Ya falla da gudu a kofar kitchen suka hadu ita ta fito Jin yana kwalla Mata Kira Yana ambaton zahra Shi Kuma ze shiga, wayar ya Mika Mata.
Jin Ammah ta karba zahra ta Fara magana.
"Ammah ina kwana".
Dan Jim Ammar tayi Jin muryar Zahrar tayi ba yanda ya kamata taji ba.
"Lafiya kalau, Kuna lafiya dai ko?"
Ammah ta tambayeta tasan zahra Bata Mata karya matukar da damuwa zata fada Mata Koda ba directly ba.
"Eh, amma Dan Allah Ammah kisaka Baki a fada masa ya dawo dani gida wallahi nan din babu dadi tafiya yake Yana barina a gidan ba kowa gashi yaki mayar Dani inda Aunty zilai take ko waya bamayi tinda ban rike sabuwar number dinta ba, Kuma ya karbe wayar da layin". Ta fada kamar zata fasa Mata kuka Dan zuciyar a kusa take Banda Bata son dagawa Ammar hankali da kukan zata saka Mata.

Shiru Ammah tayi tana saurarenta har ta Kai Aya.
"Zahra ta Kira sunanta ki fada min meye asalin damuwarki wannan ba hujjar dazan tinkari Abba da ita bace Wai Yana fita Yana barinki ke kadai ai hankali baze dauka ba, idan wani Abu yake miki ki fada min Baki da Wanda Zaki fadawa damuwar ki sama dani kinji menene? fada min".
Shiru tayi me zata cewa Ammah, Mahmud na neman mata, wallahi saidai ta mutu da wannan sirrin ai maganar Bata fada bace.
"Ke nake saurare".
Ammah ta katse Mata tunanin data fad'a.
"Ba komai Ammah kawai dai Bana son zaman Nan din ne"..
Badan ta yarda ba ta kyaleta kawai.
"Ai kuwa saidai kiyi hakuri da yanda mijinki ke so mu yanzu yafi mu karfi a kanki sai yanda yake so zakibi matukar Bai sabawa shari'a ba,kiyi hakuri kowa da haka ya girma Ina cewa yayanku Hassan yana can wata duniyar da tasa matar Ashe sai nata iyayen suce a dawo musu da 'yarsu,ai aure ba inda baya Kai Mace kowa da tasa kaddarar, kinsan Zaki hadu da shi Mahmud din? Ina cewa Allah be ya kawo shi cikin rayuwar Taki ba, kiyi ta addu'a nima Ina nan ina yi Miki Babu abinda ze faru dake Sai Alkhairi in Sha Allah".
A sanyaye tace to Ammah nagode ki bani Musaddiq din".
Mika Masa wayar Ammah tayi ta Kara gaba, haka nan taji zuciyarta ta kasa nutsuwa da yanayin zaman Zahrar a Kano daga tafiya ganin likita saiya sauka a kanon ya makale Mata yarinya ya Kuma rabata da kowa yayi nasa guri da ita, zatayi magana da Abba a dawo da Zilai gida tunda zaman ta bashi da amfani a can sun tafi Dan kula da Zahrar tunda mijinta ya dawo ya dauke abarsa itama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login