Showing 267001 words to 270000 words out of 280244 words

Chapter 90 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1061

Nan guri ya kaure da hayaniya masu Ala tsine nayi masu sharben hawaye nayi masu Ala wadarai nayi, cikin borin kunya Aunty Sameera ta tashi tana zazzaga masifa da hawayenta bibiyu tana fadin wallahi shirya wannan abun akayi ita ba ita bace wadda take magana inpersonate ne akayi Mata bazata yarda ba sai tayi shari'a da masu kamfanin wayar, uncle Mustapha ne yayi Mata zabu -zabu akan idan Bata yiwa mutane shiru ba ze saka a tafi da ita a sakaya masa ita ta jira ai da saura.
Computer aka hada wadda akayi connecting da CCTV tiryan-tiryan aka Fara nuna duk abinda ya faru a part din su Mahmud a Ranar tun daga safe har dare,duk shige da ficen kowa gashi Nan kowa ya gani har abinda ba'a fada ba a wayar Saida aka gani in da uncle saminun ya fasa interlock din kofar shiga part din mu ya binne wani Abu da turaren da akayi da shiga cikin dakin da wayar da yayi lokacin da Mahmud ya taho da shigarsu dakin har da Wasan banza da sukayi kafin suji shigowar su Mahmud, sai lokacin akaga Ashe uncle bayan curtains ya shige ita Kuma ta tsaya gefen da kofa zata karareta idan ya bude kofar, duk abinda ya faru kowa yaga zahiri Nan da Nan hankalinsu ya Kara tashi Dan An yanka ta tashi abinda hankali da tunaninsu Bai tab'a kawo musu ba kenan, Abbie ne ya taso idanunsa sunyi jajur sai huci yake Yana fadin Sameera tazo su fice Masa daga gida ya saketa saki uku minti biyar ya Bata idan suka wuce haka sai sunga kaskancin da Basu tab'a tunanin ana yinsa ba, Nan Sameerar ta Fadi tana birgima tana tuma da fadin ta shiga uku wallahi saminu ne ya sakata yace Dan mu mallake dukiyarsa idan mukayi haka Dole sai yanda mukayi dashi da kowa ma Tunda babu Wanda ze iya bude Baki yace Mana ba haka za'ayi ba.
Kan uncle saminu Abbie ya juya ya nuna Masa hanya Yana fadin ya fita kada ya Kara ganinsa a gidansa yaje yaji da kunyar tonon sililin da akayi masa, Safna kuwa a Nan da sume Saida aka yayyafa Mata ruwa ta farfado tana sambatun ita babu Mai rabata Dani Tunda an daura Aure take Abbie ya rattaba saki ga safna a madadina Tunda Daman bansan da masaniyar Auren ba.
Hajiya Turai ce matar Autan su Alhaji sa'id tasa aka fita da Safna da Aunty Sameera.
Saida aka wuce dasu sannan Ammi ta tashi wadda tun lokacin da aka Fara bayanin take hamdala ga Ubangiji Daya wanke Mata yaro daga zargin Zina Daya karade a cikin family.
A hankali ta ratso mutane ta fito tsakiya ta Fara fadin ta godewa Allah ko yanzu ta koma ga Allah Bata da sauran bakin ciki saboda Allah maji rokon bayinsa ya amsa Mata addu'arta wadda take yinda babu dare babu Rana, saukar Al'quran ma anyi Mata babu adadi Tunda abin ya faru tana addu'ar Allah ya tona asirin duk Mai Hannu a cikin Lamarin, sannan ta juya ta dubi Abbie tana fadin daga yau kwanan gidan Nan ya qare min abinda nake jira kenan Daman gaskiyar tayi halinta, to Kuma yau Alhamdulillahi gaskiya tayi halinta Dan Haka Nima hanya kasan fita ta. Ta juya ta fice itama, abinda ya tada hankalin Abbaie din kenan ya bita da sauri ya fice shima, Dan Tunda yake a zamanzu magana makanciyarta haka Bata tab'a hadasu ba. "To fa kinji dalilin Daya mayar Ammina niger. Hakan ne ya Kara harzikani saboda anyi min rashin adalci, lokacin fa Sameer yazo min da bayanin na jinjinawa Batool matuk'??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a yarinyar tayi min bazata Sosai, Abu kamar Wasa Duk Wanda sukabi Ammi babu Wanda ta yarda ta biyo da suka Fara rinjar Hajja ne bayan zuwan Hajiya Inna Ammi ta dawo Damagaram gurin Yayanta kafin ya Yanke Mata hukunci dawowa sokoto dole, hummm Amma fa Ina biyiye da duk motsin Ammina Dan Yanke huldar da nayi ta zahiri ce Amma a badini Ina cikin duka lamuranta Dan Ina zuwa Yamai duk lokacin danaso ganinta sai dai su nemeni su rasa a can garin, ganin nesa ta tazo kusa yasa nayi zamana a garin ku dankwali yaja hula, sauran bayanai da yawa Kuma sirrina ne. Kinji kadan daga abinda ya sameni Dan ma na takaita Miki wasu abubuwan da uncle saminu ya ringa nuna min ke dai abar kaza cikin gashinta kawai, idan ana cin B'aure ba'a tona cikinsa Kuma idan ana sallah ba'a magana, wani sanin sirrin cikin ciki sai dai hanji kawai, Dan haka ban Hana ki gaisa da zuri'ar uncle saminu ba Amma na yanke Hulda dasu har abada kamar yanda mahaifina ya cire Shi a cikin duk sabgoginsa sai dai abinda ba'a rasa ba Dan masu iya magana na cewa hannunka baya ribewa ka yanke kayar,to kinji summary na abinda ya faru Dani ya Zama sanadin da yasa na fito a wancan lokacin sai dai ni Alhamdulillahi hakan wata Rahama ce daga Allah.
Jinjina abin Zahra take a cikin zuciyarta ace duk wannan masifa ta dumfari mutum Daya ai sai Wanda Allah ya bawa karfin zuciya da imani ace duk girman family Kamar wannan duk sun maka nak'i Sai mutum biyu kawai lallai anga taskun rayuwa.
A hankali ta sauke numfashi tana kallonsa Banda tasan baya son kuka ba da wallahi saita matse yanda zuciyarta ke Mata zafi, Dan ji tayi ta tsani safnar da yayarta tsana Mai zafi wadda ita dai ko Mama da Salma da suka nuna Mata qin jini bataji su kamar wadannan ba.
"Me amorrrr....".
Ta fada a hankali.
Gyara Mata kwanciya yayi a cinyarsa Yana kallonta cikin Ido.
"Umhummm.... Fadi ya akayi?".
"Allah ya Kara maka juriya da hakuri kaga jarabawa ta rayuwa, lallai Ubangiyi yayi gaskiya da yace shin bazan jarabceku ba?. Amma taka dai Kam sai Mai karfin Imani Dan Mai karamar kwakwalwa sai kansa ya buga koya fada wata harkar Tunda babu ni'imar da Ubangiji Bai maka ba, Allah ya hore maka amma ya baka kariya daga fadawa mugunyar rayuwa, ya tsare min kayana Alhamdulillahi Allah abin godiya".
Dagota yayi daga kwancen ya kafa Mata idanunsa da suke razanata a wancen lokacin Wanda Kuma suke tsumata a yanzu.
"Kice Kayan naki ne ke kadai, to ya za'ayi da sauran dake kokowar shigowa Kuma?".
Wani warrrr tayi masa da sexy din ta Wanda wani irin Abu yake walainiya a cikinsu.
"Ai dagani babu wata a yanzu dai saina cinye na sude kayana tas sai dai su samu sudin kwano".
Rike Baki Yayi Yana wata dariya kasa-kasa.
"Kai yarinyar nan yaushe kikayi Baki haka? "Wato kin Fara gane garin ko?".
Dariyarta Mai shagaltar dashi ta Fara tana nuna shi da hannu.
"Ni Kuma wane garin na Fara ganewa?".
Ba zato yayi Mata daukar jarirai yana fad'in Bari na nuna Miki garin".


*****Tunda su Ammah suka shiga garin Miya kukan Salma ya tsananta tamkar zata shide, Banda aikin lallashi babu Abinda su Ammah keyi daga karshe ne Aunty Hassana ta rufeta da fada ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shi dai malam Bala ko tari Bai kubce Masa ba Dan yasan sakayyar Allah ce kawai ta sauka akan Mama da 'ya'yan ta Dan dashi wani Maci Amana ne da Allah kadai yasan abinda suka shuka shida ita to tun tayin farko ta taka Mata birki da barazanar sanar da Alhajin shine abinda ya kawo basa ga maciji a tsakaninsu.
Ba laifi gidansu Anas din da nasu rufin asirin sai dai da alama rayuwa ake ta babu kwaba a gidan Dan yanda kannensa Mata suka ringa yatsina fuska ga babu tarbiyya Kota sisin kwabo a gidan saboda da kyar kanwarsa Haulatu ta bayar da key din dakinta a sauki Baki cewa tayi ita da kayanta kada a Bata mata, sai wani kanin Anas din yayi Mata Jan Ido sannan ta bada, aka bude suka shiga inda aka kawo musu Abinci ba laifi ta Nan sun yaba, amma dai uwar tasa basuga fuska a gurinta ba, sun dai gaisa shima ganinsu Ammah da tayi ba karya sun jiku da naira gayu ya zauna dole ta mayar da makaman yakinta ta Bari idan sun wuce ta baje kolin abinda ta tanadarwa daga salmar har Anas din tunda 'yar kanwarta yake aure Bai Kuma fada Mata ze auro Salma ba saida iyayensa maza zasu tafi daurin auren suka shigo suka fada Mata Tunda Babansu ya rasu.
A dofane suka wayi gari inda tun karfe bakwai motar Kayan ta sauka a Miya Dan tun dare Abba yasa akayi lodin Kayan abinda babu yasa su sahura da makotansu suka shiga stores suka sawo, Kayan toye-toye ma gidan masu yin na sayarwa akaje aka sawo saboda Basu da matsalarsu a unguwar da Kuma can bakin kasuwa.
Kafin azzuhur gida ya kankama na amarya, Ammah ta saka Salma tayi wanka wadda har lokacin kuka takeyi ga azababban Zazzabi Daya rufeta, a irin kayan da aka dinka na Zahra Wanda magaji ze tafi dasu Ammah ta debo Mata kala kusan goma ta taho Mata dasu Tunda babu Abinda aka tanada bagatatan abun yazo.
Su Ammah sun Kara Kai Salma gurin surikarta sun bada Amanarta sannan suka mikata dakinta tare da yayar Baban Ana's din, tana gunjin kuka suka barota Dan abinda Bata tab'a kawowa bane ko cikin mafarki akayi Mata taci burin auren miji na kece raini ta shiryawa kanta rayuwar Jin Dadi da walwala Amma sai gashi ta Kare a auren yaron kamfanin nefa Zama a inda ko cikin hasashe Bata tab'a kawowa ba, haka su Aunty Hassana suka wuce.
Saukinta Daya gidan da abunda aka zuba Mata ze kankaro Mata mutunci ko banza ta Nan fannin dai babu raini.


***

A cikin sati daya Zahra da Mahmud sunyi wata irin shak'uwa ta ban mamaki,Dan Daya ji yake baze iya rayuwa ba Saida dayan Zahra ta Zama 'yar gari sai tsula shagwaba take Masa shi Kuma duk ya susuce a kanta, ga wani irin fresh da sukayi dan dole idan ka kallesu ka kara, Saida hankalinsa ya nutsu sannan ya zauna dasu Salis da Bashir ya nemi shawararsu akan idan suna ra'ayin aiki dashi to suyi Shawara da gida akan Nan gida suke son Zama suyi aikin ko a waje sannan ya bawa kowa gida a acan Azaren Saida ya fada musu inda gidajen suke Salis yayi murmushi Shima Mahmud din yayi wani Abu suka tuna, lokacin da Mahmud yaja Salis din sukaje ana yiwa gidajen pop Salis ke tambayar ko gidan waye haka sai Mahmud din ke fadin na wani abokin Sameer ne yasa shi ya dube Masa har yake cewa Salis din ko gidan ya burgeka ne Naga kamar kana sonsa? Dariya lokacin Salis din yayi Yana fadin wa zeba Dan rogo rumfa? ai irin wannan gidajen sai wadanda sukaci suka tada Kai. Dariya kawai lokacin Mahmud yayi baice komai ba kawai dai yace Masa ya Taya shi a duba abinda baiyi ba Mai gidan ne yace ayi hakan Nan Salis din ya zage Yana ta fadin Nan kaza ya kamata ayi nan ayi kaza haka suka zagaye gidan har suka Gama bada gyaran, haka suka shiga dayan ma aka rubuta komai, to sai yanzu da yake fadar inda gidajen suka Salis ta tuna da abun, sunyi godiya kamar su Ari Baki Dan Dadi Bashir baisan lokacin da hawaye ya zubo masa sai gani sukayi Yana share hawaye, saboda Tunda ya Gama Karatu Bai Sami aiki ba gashi Dan Mai karamin karfi kullum Yana yawo neman aiki sauda yawa Mahmud Kan fada Masa yayi hakuri da lokaci, in dai aiki ne Saiya zab'a, a lokacin jinsa kawai yake Ashe da gaske yakeyi saiya zaba din tunda gashi ya Basu options na zabar Ina suke da muradin yin aikin.
Dariya sosai Mahmud ya ringa yiwa Bashir ganin yanda yake shafe Ido kamar Mace.
"Haba bash meye haka be strong mana Dan Allah, kuka kuma? To in banyi muku ba suwaye Zan yiwa kun riqeni Amana lokacin da bakusan daga wace duniyar nake ba, kun ciyar Dani kun dinka mun suturar sakawa, kun bani kudin da kuka nema da karfin jikinku, kun tsaya a gurin jinyata lokacin dasu Habib ke yinta ga abin Hawa an sakar min babu shamaki duk inda zani, an bani Mata kunyi uwa kunyi makarbiya gurin hidima da jikinku da aljihunku to ni kuwa ai bani da abinda Zan biyaku dashi sai dai nace Ubangiji ya biyaku da madaukaliyar Aljanna wallahi tuni na cireku daga abokai kun zamar min 'yan uwa yanzu ga wannan" ya mikawa Bashir Daya fi kusanci dashi E.passport ne yace su saurari visa Sameer ze kawo musu ta umarar Azumin nan Mai kusantowa, yace Kuma kowa ya duba akwai sako a wayarsa, sunyi tsaraba ya Kuma fada musu tickets dinsu na zuwa Bauchi Yana hannun Sameer, bakin godiyar ma rasawa sukayi Dan wata kyautar tafi gaban godiya, Dan ya gigita musu lissafi ba Dan kadan ba.
Sameer ne ya shigo da sallama lokacin kwanansa biyu da dawowa daga Egypt gurinsu Mama Dan Saida akayi Mata aiki sannan ya juyo ya barosu a can, Mama tayi kuka tayi kuka akan wautar datayi a baya na nuna hassada da ganin kyashin yarinya marainiyar Allah wadda aka mutu aka Bari ko kanta Bata sani ba Amma shedan yayi Mata katutu a zuciya ta dunga kulle-kullen mugun Abu Tunda masu dubanta suka barbasa Mata yarinyar tana tare da wata irin sa'ar rayuwa duk sai ta rude tana ganin ta Yaya hakan ze faru gata Mai kyau na ban mamaki sannan ace sa'arma tatace tun daga lokacin zuciyarta Bata huta ba, to gashi Alkawarin Allah ya tabbata gata a gadon asibiti a wata k'asar tare da ciwon zuciya Wanda bakin ciki da hassada sukayi sanadinsa, ga Kuma wadda take abun a kanta taje inda Ubangiji ya nufa taje din,tunda Alkawarin Allah baya tashi ga shi Kuma mijin da taketa kangewa kada yazo gurinta shine ya Zama silar samun waraka ga ciwonta, ga mijinta Tunda sukazo bai Kira ba ya bawa banza ajiyarta Bata Kara Jin ko duriyarsa ba tun lokacin da yaje sokoto tana barcin Allura batasan yaje ba,yau ga dan 'yar uwarta Mai ingizata tayi komai Dan Hana Allah ikonsa itace Dan cikinta ya yiwa yarinyar ta cikin shege.
Da kukanta share-share ta ringa fadawa Sameer ya nemar Mata yafiyar Zahra akan abubuwan data yi Mata.
Kusa da Salis sameer ya zauna ya gaishe da Mahmud sannan suka gaisa dasu Salis din, sannan ya dauko musu tickets dinsu na jirgin Sha biyu da rabi na Rana, godiyar dai suka Kara yi musu har Mahmud na fadin "wallahi idan ya Kara Jin godiyar na zasu bata.

**

Ranar da suka cika kwana goma sha biyu Mahmud tun dare ya fadawa Zahra ta shirya da safe ze kaita gidan Ammi shi kuma zeje Lagos wani aiki, Bai barta tayi barcin kirki ba a Daren,dan daga baya ma cewa yayi ta shirya ta raka shi suje su wuni su dawo, da kyar ta samu ta lallabashi da kalamai sannan ya hakura Amma Saida ya Kara rage tafi.
Tun asuba zahra ta Kira Aunty zilai suka Fara aikin dabun kaji dasu cake sai da sauran tarkacen snacks Tunda su duka gwanayene kafin takwas da rabi sun Gama hada har breakfast, sama Zahra ta koma lokacin Mahmud ma ya farka Dan nine thirty flight dinsu ze tashi daga sokoto zuwa Lagos. Tare suka fito sukayi break sannan yace ta dauko gyalenta su tafi ya ajeta ya wuce, fada Masa tayi tare zasu tafi dasu Aunty zilai, waya ya yiwa zayyan ya saka wani ya kaisu Aunty zilai can family house nasu, lokacin da akace su fito sai gani yayi ana ta fitowa da manyan warmers ana sakawa a boot din mota, Bai nemi Jin abasin menene ba itama Bata fada masa ba.
Su suka Fara yin gaba sannan suma suka fice daga gidan, sunzo wucewa ta kofar gidansu Dr Haseenah ya Dan shafo cinyarta, tsuke fuska tayi tasan abinda yake nufi.
"Komu shiga ku gaisa tana garin har yanzu Tunda Nima Ina garin kinsan lokacin da Ina Nan ai a Nan take aiki Saida nabar garin ta koma Kano da aiki Tunda daman a kanon aka riketa kuma masu fada aji ne, jiya da har zatazo ku gaisa sai tace sauri takeyi gurina kawai tazo wani lokacin ida ta dawo ta shigo ku gaisa".
Hade Rai tayi ta hade gabas da yamma tayi kicin-kicin duk yanda yaso ta kulashi tayi banza dashi har sukaje gidan.
Abbie baya k'asar yaje Benin republic akan wasu Kaya nasa da aka rike a can.
Direct part din Ammi suka nufa duk yanda yaso ta saki ranta abun ya faskara Dan da gaske ya Bata Mata rai ita fa ta tsani matar Nan ba kadan ba shi Kuma ya kasa ganewa.
Yana tsayawa tayi wuf ta fice Bata tsaya ya fito ba ta wuce Abinta tana ayyana itama ai Amminta ce bazata tsaya shi ba,Amma kafin takai ga kofar parlourn ya cimmata.
"Ke meya faru Wai kike ta hade min Rai haka?".kauda Kai tayi tana jin zuciyar na Mata zafi.
Janyota yayi ya rungumeta a Nan da sauri ta dago tana rarraba idanu.
"Dan Allah ka sakeni kada wani yazo ya ganmu a haka wallahi ba komai,Dan Allah ka Bari kada ace bamu da kunya plssss...."
"Baki San anyi min tambarinta ba a gidan Nan wannan ai ba wani Abu bane,nida kace nayi abun a gidan Nan ko kin manta?".
"Ai sharri ne wancen, wannan Kuma gamu in reality ne".
"To shine me? Ai ba haram bane ko.....,"
Bai karasa ba yaji alamun za'a bude kofar da sauri ya saketa Dan bazeso kannensa ko Ammi su gansu a haka ba,ko maid din Ammin sai girma ya Fadi.
Sahalatu ce 'yar Babban yayansu Abdallah da Afnan da hannunta suka fito, ai yarinyar na ganin Zahra ta Fara zillo tana dariya, itama zahrar dariya tayi Mata ta nufesu da sauri ta karbeta daga hannun sahalatun tayi wuf ta shige tana amsa gaisawar yarinyar.
Ammi ce dasu Aunty Aishat a parlourn farkon sai Aunty zilai daga gefe a zaune bintar dai Bata gurin Zahra batayi mamaki ba Tunda ita 'yar gida ce, gaba Daya suka amsa sallamarta cikin nutsuwa Zahra ta karasa kusa da Ammin ta tsuguna har kasa tace "Ammy Ina kwana?".
Ammi wadda bakinta yaki rufuwa saboda farin ciki ta amsa Mata "Lafiya kalau Zahra ya gidan naku?".
A kunyace ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login