Showing 192001 words to 195000 words out of 280244 words

Chapter 65 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1031

Kuma ita kadai ce bada wasu zasu ringa sakawa ba, sannan ya Bari Shima ya dauki dai dai kun abun bukata irinsu Kayan shaving.
Credit card ya Basu suka cire kudin su ya bada Address din da za'a Kai , Kayan suka wuce.
Suna zuwa train station suka tarar da Mr Salahuddeen Yana jiransu cikin girmamawa ya gaishe da mahmud cikin yaren indianci ita mamakinsa take yi yanda ya iya indianci ga yaren Portugal ma da yake ji can kwanaki taji Yana oyaren french, cikin harshen turanci Mr Salahuddeen ya gaishe da Zahra. Wani card Kamar ATM ya mikawa mahmud cikin ladabi Yana fada Masa magana, shi Kuma sai gyada Kai yake yi, bayan ya gama saurarensa ya Mika Masa key din motar yayi ya juya ya nufi inda motar take, hannunta Mahmud ya riko ya nufi cikin station din.
Gurin Zama ya nemar musu ya kawo Mata fresh milk me matsakaicin sanyi, tunda ta zauna wata yarinya da gani 'yar Africa ce take binsu da kallo ko Ina mahmud yayi idonta Yana Kansa, ganin haka lokacin Daya dawo da Coke na gwangwani a hannunsa ta shagwab'e Masa tana fadin.
"Pls meu amor mu canza guri bana son nan".
Hannu yasa ya dagota daga zaunen Yana fadin.
"Ok muje can ta baya ko?"

Gyada Masa Kai tayi suka nufi inda ya fada, sunzo karya kwana Zahra ta Dan juyo taga still dai ta biyosu da wani mayen kallo Kamar tazo ta rungume Mata mijin, wata uwar harara Zahra ta zabga Mata tana jan tsakin da Batasan ya fito ba.
Dan juyowa yayi Yana Mata wani kallon ke waye?
Dauke Kai tayi tana fadar "ba komai".
Be zafafa ba sukayi gaba.
Bayan sun zamu guri can gefe Zahra tace Masa.
"Wai Ina zamu ne haka?".
Dan lakuce lips dinta yayi Yana wani lunshe Ido.
"Jim Corbett national Park zamuje Yana can Uttarakhand state, Ina son muje huta kuma kiga number one park a India anyi shi tun 1936, lokacin turawan mulkin mallaka".
"Ok, Naga ka kawo mu station na train da nisa a mota ne?".
"Eh Kamar hakan ne dai za'a Kamar tafyar five hours thirty minutes a train".
"Tab da nisa ya akayi kasan Ina son zuwa park ne?".
Saboda an fada min Yana daga cikin abinda Keke so ne".
Shigowar train din da zasu bi yasa hirar tasu ta yanke.
Suna zuwa ya zura katin ya saka musu kudinsu suka shige ciki har zasu zauna wani seat da babu kowa Zahra taga kusa da wannan yarinyar ne tace Masa.
"Pls muyi ciki bana son kusa da hanya kowa ya shigo saiya ganka".
Nan da nan ya nufi inda ta nuna Masa.

Away biyar da mintuna shiga Uttarakhand Basu bata lokaci ba suka shiga taxi zuwa I.T.C HOTEL. Wanda yayi booking dinsa tun jiya.
Sun huta sunyi wanka it's Kuma tayi wankan tsarki Dan cikin ikon Allah dif ya dauke, tana fitowa taga Kayan sakawa a saman bed din ta dauki wata abaya baka ta saka ta tayar da sallah, tana ta fatan Allah yasa harta Gama sallar Bai shigo ba, cikin taimakon Allah Bai shigo ba din Saida ta Gama sannan ya shigo Yana fadin.
"Taso muci abinci kisan bana son yunwa"
"Acici shugabannin tauna"
Ta fada kasa-kasa.
"Me Kika ce".
"Nothing"
Ta fada tana tashi tsaye tana Mika tare da salati
Kauda Kai yayi idan tana irin wadannan abubuwan labarin yana iya canzawa.
sunci Abinci sannan suka Dan fita harabar hotel din tana mamakin yanda ake binsu da Ido idan sun wuce, taga sufa kasar ta kyawawa ce ko duniya ta Shaida hakan,amma sai ayi ta kallonta sun zagaya cikin hotel din sosai sun Jima a gurin swimming pool ba yanda Mahmud beyi da Zahra ba ta yarda su shiga ta kiya Wai tsoron ruwa take, Saida zasu kwanta suka dawo daki.
Abin mamaki da suka kwanta ya dai shigar da ita jikinsa amma daga haka babu abinda yayi Mata, da safe da wuri ya fice tana barci, sai written ya aje Mata a kusa da ita ya fada Mata yaje New Delhi gurin Baba Malam, ta Kira a kawo Mata abinci idan ta tashi.
Lokacin data tashi Rana tayi sosai ba Bata lokaci tayi wanka ta nemi abinda zataci.
Ammah ta Kira da sabon sim din Daya saka Mata na kasar sun dade suna Hira har take da fada Mata Abbanta ma ya shigo kasar cikin dare, yazo yaga jikin Malam din, tayi takaici ba kadan ba Daya kawota Nan ya saya yayi komawarsa can.
Ta Kira Aunty Hasana ma Saida tayi Mata fada sosai sannan ta amsa sallamarta akan tahowa Bata fada Mata ba duk da Ammah tayi Mata bayanin yanda tafiyarta tazo, sunyi Hira itama irin ta wayyaun Yaya da kanwarta Nan Aunty ta tinga fada Mata abubuwan Daya Kanata ta rike su zamar Mata makaman yakin Zaman Aure, wani Abu idan Auntyn ta fada sai Zahra taking tamkar ta nutse, Wai Ashe kowa a wannan fannin sai da ka kyaleshi kawai.
Har yamma mahmud bai dawo ba haka tayi wunin kadaici dan ma ta samu mujiba Wadda ungiyar su Sameer suka Samar Mata da gurbin karatu a modibbo Adama University of Technology Adamawa duka batafi wata Daya da tafiya ba.
Sun Dade suna tattaunawa a Kan yanda akayi Sameer yazo har gida da admission dinta tunda sun tab'a karbar c/v dinta tun da dadewa lokacin anyi auren Zahra babu dadewa.
Bayan sallar magriba mahmud ya shigo tana zaune tana lazimi be zauna ba Shima alwalar yayo ya fice Yana fadin "Bari nabi bus naje masallacin dake can cikin gari na samu jam'in insha'i"

Kafin ya dawo ta Shirya ciki wasu kananun Kaya riga da wando masu masifar kyau saita Zama Kamar 'yar Baby a cikinsu turarikan da Hajiya Amina had'a Mata tayi amfani dasu, ita kanta tana Jin dadin turaren ba kadan ba.
Ledojin Daya shigo dasu ta dauka ta bude kifi ne roasted one da kaza sai Kuma fresh milk dasu tarkacen chocolates da biscuit's.
A parlour ya sameta tana kallon wani program da ake a gidan tv na Qasar Mai suna chair Lady sosai Shirin ya dauki hankalinta har Bataji bude kofarsa ba sai kamshinsa taji kusa da ita.
Fuskarsa ya Kai daf da tata ya bata light kiss a chicks dinta.
"You look so cute my previous...'.
Ya fada Yana Zama very close to her.
Wani kamshi ya Shaka a jikinta Nan da Nan ya motsa Masa jamiyya, wata Mika yayi Yana riko hannunta tare da fadin.
"Can I help me plssss....".
"Na shiga uku ni Zahra me Kuma ya kawo irin wanna sauyin Nan da nan".
Ta fada a zuciyarta, hannu yasa ya dago fuskarta ya kalleta da narkakkun idanunsa da suke razanata a can baya.
"Meee.. kakeee sooo..."
Ta fada bakinta na rasa haka ma jikinta, lokaci Daya tayi zuru-zuru da ita.
Sai Kuma ta bashi tausayi yaji ze iya danne duk wani Abu da yake bijiro masa.
"Ba komai bani abinda zanci, yunwa nakeji".
Wata ajiyar zuciya ta sauke Wadda tasa ya dago ya Zuba Mata idanuwansa, yana ayyana.
"Tab za'a Sha drama a gurin yarinyar Nan da alama ta Mike kafa tana neman ta manta menene hadafin auren".
Ya fada a zuciyarsa, suna cikin cin abincin ne yake fada Mata zuwan Abba, tace Masa Ammah ta fada Mata.
A bedroom yau dai Saida ya ragewa kansa zafi sannan ya Sami salama Dan da gaske turarenta ya tashi hankalinsa ba kadan ba.
Satinsu biyu a Uttarakhand suna hutawa sunyi wani kyau ya zagaya da ita guraren tarihi na state din ya kaita River Greek tayi kallon Ruwa sun huta sosai a gurin, ranar da yace Mata zasu koma new Delhi ji tayi Kamar tace Masa su Kara wani sati biyun, da wuri suka baro Uttarakhand din Sha biyun Rana suna New Delhi Asibiti suka wuce jikin baba Malam da sauki sosai Dan har an tada shi zaune saura koyon tafiya Kuma Amma ana tsayar dashi ya rike karfen tafiya.
Bayan sun baro Asibiti tayi zaton leeha palace zasu wuce sai taga Yana fadawa Mai taxi din inda ze kaisu. Bai bar Mai taxi din ya tafi ba yace ya jira su fito,. hannunta yaja suka nufi cikin wani plat house Mai kyau sosai Kati ya zura ya bude main entrance din. Parlour ne Wanda yaji kayan more rayuwa wani corridor ya nufa dasu Yana rike da hannunta har lokacin.
Dakina ne guda uku sai wata kofa Wadda Bata San Kota mecece ba.
Kofar dake hannun hagu ya zura Kati ya bude.
Kayanda suka zo dasu daga 9ja ta gani sai Kuma Wanda suka saya ya bada address din da za'a kawo, kallon ta yayi ki dauki duk abinda Zaki bukata zamuje unguwa ne har abubuwan da Kika dauko na tsaraba ki fito dasu. Ba musu ta shiga dauko luggage dinta da kayyayakin da aka hado Mata da Kuma abubuwan amfani da Ammah ta hado Mata da Wanda Hajiyar makwarari ta kawo Mata.
Shi tsayawa yayi Yana kallonta ganin kayan da yawa.
"Wai Ina Zaki da wadannan kayan haka sai dai kiyi selecting na wasu gaskiya".
Ya fada yana daukan wasu ledoji yayi waje itama luggage din taja ta dauki Karamar jakar da aka Zuba Mata kayan da Ammah ta dunga Mata gargadin yin amfani dasu da Kuma na wajen mommy bayansa tabi tana fadin.
"Ya za'ayi na aje kayan Hausawa tunda Nan dai babu irinsu, kullum mutum yana fama da kananun kaya".
Yana ganin kayan yasan Bata rage ba haka Nan ya kyaleta ya shige ya dauko sauran. Inda ze kaisu da number gidan ya fadawa Mai taxi din.
Tafiya ce Mai nisa daga inda suka baro dai dai gate din wani katafaren gida Dan taxi din ya tsaya, ya fito Yana Ciro musu kayansu, hannu mahmud ya zura ya bude Karamar kofar gate din Yana fadin dauki luggage dinki kiyi gaba kije kiyi pressing din door bell din gani Nan".
Jan luggage din tayi tana rike da handbag dinta ta nufi kofar.
Sau biyu tana latsawa sannan taji alamun an nufo kofar, wata matashiyar mace ce 'yar gayu irin Wanda gayun ya Gama bayyana kansa a jikinsu ta bude kofar tana dauke da wata fine baby Fara sol da ita, kallon kallo na rashin sani suka yiwa juna, Zahra ce ta Fara gaisheta cikin yaren hausa saboda taga doguwar rigar atamfa a jikinta.
A mamakance ta amsa Mata Bata taba tunanin tasan ko zo da hausa ba.
Zahrar ta Dora da fadin.
Tare muke da Mahmud gashi can a waje.
"Mahmud Kuma daga Ina?".
Kafin ta tattaro yanda zatayi Mata bayani ya doso gurin Yana rige da sauran kayan a hannuwansa.
Wani irin Kara matar ta saki ta zabura Banda Allah yasa Zahra tayi azama gurin rike yarinyar ba da Tasha kasa duk da haka Saida ta fasa kuka Dan ta tsorata sosai.
Babu wata-wata tana zuwa ta rugumeshi sai kuka tana fadin "me yasa ka tafi ka barmu? Ko zaka guji kowa Banda ni kayi min alkawarin duk rintsi kana tare Dani me yasa ka Saba alkawarin mu?" Tana fada tana kuka.
Ai Zahra a gurin ta sulale ta zauna Dan ji tayi gaba Daya garin Yana juya mata. Banda innailaihi wa Inna ilaihi raji'un!!! babu abinda take maimaitawa, meye haka Daman da gaske yake da yake fada Mata ba ita kadai bace ta iya ririta shi kada wata ta kwace shi.
Yaro ne ya shigo da alamar daga school yake baze wuce shekaru biyar ba zuwa da rabi, da sauri ya karaso inda suke ya zagayo Yana duba fuskar Wanda yasa mamansa kuka.
Ai Shima kwalla Kiran Daddyyyy....
Yayi ya nufesu da gudu.
Tashin hankalin duniyar Nan ya saukarwa Zahra ji tayi makogwaronta na fitar da wani Abu Mai daci Nan da Nan ganinta ya nemi daukewa.
Janye ta yayi daga jikinsa sai share hawaye take yi handkerchief ya mika Mata fari sol.
Tsugunnawa yayi ya dauki yaron Yana dariya, ya Fara Masa magana da indianci Kai kawai yaron yake gyada masa, yaron ya gyarawa Zama a kafadarsa ya riko hannun uwar suka nufo kofar a zaune a gefen steps yaga Zahra da baby a zauna ba karamin namijin kokari tayi ba gurin hiding din abinda yake Mata tuk'uqi a zuciya.
Kallo daya ya yi Mata ya Gama gane condition din data shiga basarwa yayi Yana fadin.
"Hana Shatu haka ake karbar Baki kin bar yarinya a zube a Nan kin tafi kina yarinta har kinsa min yaro kuka, sauko Babana na dauki bakuwa ko?".
Kai ya gyada.
Yana sauke shi ya nufi gurin da zahrar tayiwa kanta agajin Zama.
Sosai ya tsuguna Yana Mika hannu ze dauki yarinyar magana yayi Mata Wadda daga shi sai ita zasu ji.
" Ki nutsu bana son kuskure duk abinda na fada ki bishi kawai". Canak ya dauke yarinyar daga cinyarta, yayi gaba.

* AUREN HUCE HAUSHI*


08055362975

09061432330

MAMAN FATEEMAH.

Page 70.

.........& ..
Luggage din da Zahra ta aje matar ta dauka tana fadin "taso mu shiga,wallahi nayi loosing control dina ne wallahj abun ne da mamaki ban taba tunanin Zan ganshi a irin wannan lokacin dana hakura na sallama".
Jiki ba kwari Zahrar tabi bayanta suka shige ciki, a zaune suka same shi, yaron yana lik'e a jikinsa ya lafe sai Karamar da yake yiwa wasa tana balbala dariya Kamar ba yanzu ta Gama tsandara kuka ba.
Suna shiga matar ta karasa inda ya zauna tana fadin.
"Yanzu ina alkwarin mu? Haka mukayi alkawari da Kai, ka bace bat a cikin duniya ka manta da kowa? Ba waya ba sakon Email? Wallahi ka dauki Alhakin Ammi ba kadan ba, kasan yanda Hajiya Inna ta rude kuwa? Abbie ma ba karamin tashin hankalin ya shiga ba, da farko ya dauka fushin 'yan kwanaki ne Saida yaga tafiyar ta mik"a yasan da gaske ne, har nan ko ya taso takanas ta kano, Wai yasan ko baka fadawa kowa in da kake ba yasan ni dole nasan inda kake".
Hannu ya daga Mata.
"Pls Aisha Dan Allah ki rage surutu, kin bar yarinya a tsaye ki kaita daki ta huta kinsan long journey din da tayo? Ki tayata shiga da kayanta zata nuna Miki abinku na Mata da bakwa iya tafiya Saida tsaraba".
Wata harara ta wurga masa.
"Ai duk Kai ka jawo na manta da ita, sorry sister kinsan abin ne da al'jabi wallahi twins dina ne yayi batan dabo a duniyar nan, nayi kukan rashinsa har naba uku Lada, zo muje".
Wata ni'ima Zahra taji tana shiga jikinta, sai lokacin ta Kare Mata kallo kamarsu Daya Dan dai shi namiji ita mace.
"I am coming".
Ta fada tana haura stairs da sauri.
Tana bacewa ganinsu ya juyo Yana kallon Zahra.
"Precious".
Bata amsa ba Amma ta dago tana kallonsa kafin tayi magana Aishat ta sauko da sauri da keys a hannunta.
"Muje ko bakuwa ni ko introducing dinki Bros Bai yi min ba".
"Kije ki rakata Mana tunda na kawo Miki ita ai magana ta Kare, diyar uban gidana ce Bata da lafiya ne zataga likita, sannan malamina ma Yana Nan anyi Masa aikin spinal cord ne da sauran fractures Daya samu.
Ya fada Yana fuskewa.
Daki ne comfortable yaji komai, na bayan more rayuwa.
Aisha Bata fita ba Saida ta Taya Zahra saka komai a muhallinsa sannan ta fito.
Zama Zahra tayi a gefen gadon tana nazarin maganganunsa, me yake nufi da diyar uban gidansa, Amma zata raka shi taga iya gudun ruwansa Shima namiji ya iya danne abunda ke ransa bare ita mace.
Aishar ce ta Kara shigowa da tray an dora snacks da Ruwa da drinks.
Da murmushinta ta karaso tana fadin.
"Ashe Fateemah ce, sannu da hanya zahra, ya jikin naki nagi Bros yace Baki da lafiya, Ni Sunana Aishat Muhammad Dange, twins din Al-husasain".
"Masha Allah, Aunty nagode kwarai sannu da kokari".

"Lah ba komai, ki Sha ruwan kiyi sallah saiki fito lokacin an shiya muku abinci"
Sallar zahra tayi ta Jima tana addu'ar neman mafita daga wata sabuwar rigimar da take hangowa.
Nan Kan sallayar ta Dan kwanta barci yayi awon gaba da ita.

****
Zaune suke Yana cin abinci ita Kuma tana duba sakonni whatApps har zata wuce salon Faisal saita dawo saboda Basu fi minti goma da Gama ways dashi ba Yana Mata magiyar ta turo da kudi suyi sarin Kaya, ta nuna masa ya jirata zasu shigo ganin jikin Abban nasu sai ayi abinda ya kamata, sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta akan ta duba ita me majiyyaci ai share sako ba nata bane.
Ta maimaita karanta sakon ya Kai sau biyar tana ganin kamar ba gaskiya bane.
Dialing din number Faisal Aunty Surayya tayi, Yana dauka Bata jira komai ba ta jefa Masa tambaya.
"Shin text din daka turo min gaskiya ne".
"Eh wallahi Aunty ko jiya ma yazo gurin Abba mantawa nayi na fada Miki bakiga yanda yake kula da Abba ba kinsan har daki ya canza Mana mantawa nayi na fada Miki ayi Mana godiya gurin Auncle Mustapha".
"Ok shi kenan ina zuwa".
Ta fada tana yanke Kiran.
Auncle Mustapha ta juya tana kallo Wanda Shima ita ya zubawa idanu, batace Masa komai ba sakon ta bude ta Mika Masa.
Yana Gama karantawa ya dago da sauri yana neman Karin bayani.
"Nima shine na Kira Faisal din ya bani tabbacin haka ne, Wai ya Kai wani Babansa ne".
Spoon din ya aje ya mike ya zari hularsa da key din mota ya fice, Surayya na Masa magana hannu kawai ya daga Mata yayi gaba.

Duk yanda Aishat taso mahmud ya Bata hadin Kai suyi magana ya Kiya yace ta Bari sai dare zasu zauna suyi magana sosai.
Abincin ta shirya a table ta nufi dakin da zahra take, samu tayi barci ya dauketa a saman sallar da tayi sallah, Bata tasheta ba dawowa tayi tana fada Masa tayi barci da alama ta gaji.
Shida Abulkhairi sukaci abincin, yayin da Aishat ta dauki Afnan Wadda tayi barci ta haya da ita sama.
Kamar jira ake ta shiga bedroom dinta Kiran sweet heart ya shigo.
Tana dauka ya Fara fadin.
"Sweetie Ina Mahmud din yake Dan Allah?"
Saida taja fasali sannan tace Masa.
"Yana down stairs, wallahi sweet heart kamar Almara nake ganin abin duk na rude Dan Allah kazo kada ya Kara tafiya... Yace matukar na fadawa Abbie ko Ammi Bazan Kara ganinsa ba".
Ta fada tana share hawaye.
"Cool down your temper my sweetie Babu inda zaya, ban tsoro ne kawai yake miki yasan idan yayi Miki haka bazaki fadawa kowa ba, ki jirani zuwa gobe da safe in Sha Allah, ki daina yi min asarar hawayenki a banza, a gurina suna da mahimmanci , ki kyaleni dashi yanzu basai an Jima ba zanyi informing din Abbie gara ayita ta Kare tunda shi Abu baya wucewa a gurinsa".

"Gaskiya dai Kam ki shiga cikin Lamarin kuyi Masa taron dangi, kasan da wata yarinya yazo Wai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login