Showing 228001 words to 231000 words out of 280244 words

Chapter 77 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1045

Mata wani Shirin na musamman.
" Wow! Masha Allah bestie Allah ya kade bakin mutane kinganki kuwa?".
Dan murmushi tayi kawai.
"Ato gata Nan bansan ya angon naku zeyi ba Naga alamar dan banzan kishi gare shi, wa yace ya kawo ta gidan a haka? Ai dole ya kauda Kai Dan dinner dai sai anjeta babu fashi in Sha Allah".
Ita dai Aunty Nauwarah kallonsu take tunda ba Hausar takeji ba.
Wasu tsaraddun turarika ta shiga fesa Mata masu sanyin kanshi.
Tare suka fito suka raka Zahrar a cikin motar da zasu tafi a ciki, shi Dan gogan kasa magana yayi Dan yana kukan targade saiga karaya ta samu, Yana korafin waccen wedding gown din to Kuma saiga wannan ita ba transference bace Amma ta fiddo da structure din jikinta sosai.
Bai daiyi complain ba suka wuce Sameer na jansu, Suna fita motocin guards dinsa dake waje suna dakon fitowarsu suka saka motar a tsakiya suka wuce. Su Aunty Aishat ma suka wuce da sajeeda.
Suna shiga harabar gurin sajeeda taga yanda motocin Alfarma suka cika wurin tasan ba karya anzo gurin, Dan tunda suka shigo sukaga yanda Families din mahmud suke suketa mamakin abun bare ita sajeedar da tasan komai a game da shi, tayi mamakin mema ya fitar dashi daga irin wannan daular ya gwammace rayuwar da yayi a Azare da wannan.
Ango da Kansa ya budewa Amarya ta fito Yana rike da hannunta suna tafiya Yana gaisawa da jama'arsa suna bin carpet din da a saka musu a hanya photographers sai aikisu suke masu dauka da wayoyin hannunsu Suma suna ta faman daukarsu Dan wani irin perfect match couple ne Wanda kafin a samu irin wannan hadin ana dadewa kyau ne ke dukan kyau.
Suna shiga da tawagar abokansa na kusa Dana nesa sai kawayen Zahra,r music din Larabawa na tashi a hankali sai kus-kus mutane kowa na zaune gentle ba wani hayaniya Dan ba karya an hada manya masu ji da kansu a gurin kowa Yana cewa wane kauce bani guri.
M.C ne ya Fara bazawa Amarya da ango kirari har suka zauna a inda aka tanadar musu, Nan da Nan guri ya dauki surutun mutane wasu suka taso suna daukar video wasu suna daukar photo, 'yan Mata da yawa masu son mahmud sunyi giving up, sun San idan ba wani kwakwkwaran rabon ba babu yanda za'ayi DANGE ya dubesu da sunan soyayya, wakar Auren su wadda Akayi mc ya saka.
A gurguje Sameer ya bada tarihin mahmud har ranar da suka Fara ganin Zahra ita da Abbanta a jirgi ya fada, sai lokacin Abban Zahrar ya tantance inda ya Fara ganin fuskokinsu tabbas anyi haka Dan Mai maganar har Jordan sukaje tare, wato tun lokacin suke bibiyar ta kenan sauran bayanin ne kuma baisan yanda akayi ba.
A bagaren Zahra sajeeda ce ta fito ta fadi tarhinta a nan da yawa suka San ruwa biyu ce Dan duk Wanda ya ganta zeyi zaton gaba daya Arab din ce tunda su ta dauko sak, an tanadi abinci Kala-kala da nama ya Kai Kala goma gashin nan serve your self ne ga drinks Nan tamkar banza, Zahra tayi mamakin ganin su Abbanta Koda Wasa Bata taba kawo hakan ba tunda bece Mata zezo ba yace dai sai daga baya ze shigo ya ganta, taga su Ya Abdul Hakeem dasu ya Hamza bare magaji da taga ya Zama Dan gida ya kasa tsugun.
An saka kidan larabawa wasu Mata Wanda da alama dasu Ummee sukazo suka shigo sukaga ringa rawar larabawa Mai ban sha'awa.
Daga Nan aka bukaci Ango da Amarya suzo su yanka cake Zahra ji tayi duk ta daburce ganin Ido yayi Mata caaaa.
Ganin taki motsawa yasa mahmud ya murzawa idanunsa toka Kuma ma dai da biyu yayi hakan Dan yaga wata fuska sanye da musk Kuma ya hakikance Safna ce Dan ko me zatayi bazata taba bace Masa ba.
Tsam ya saka hannu ya Mikar da ita abunda yasa matasa dauka tafi Sai Kuma hasken plasher tako ina.

Shiya Fara Bata cake din sannan ta bashi duk a kunyace, mc Bai Bari suk koma ba announcement ya Fara Yana neman dangin Amarya da turanci tunda yagansu farare tas, ya saka wakar Amr Diab 'yar kasar Egypt.
Ummee ce ta taso wasu Mata biyu suna bayanta dauke da wata jaka tana zuwa ta Fara zazzaga musu ruwan stalling pounds na England sai Kuma su Mama Haneefa dasu Aunty Nauwarah suka shigo suna ruwan American dollars Nan da Nan guri ya dauki tafi, Ummee Bata koma ba saida ta yiwa ango kyautar estate a cikin garin madina sannan aka bashi jajayen rakuma goma da kyauta tickets na kashe biyar na Honey moon.
Aunty Hasana ma dasu Inna mainuna sunzo sunyi rawar gani Dan shanu goma ris ta bawa ango sannan wasu goman biyar uwa biyar uba da kuma zunzurutun kudi har miliyan ashirin na dangin uwa da uba sai karsanoni hudu na abokan zaman Ammi sai guda hudu da million daya nasu Hajiya Inna da Hajja dari biyar biyar.
Abinda ya girgiza da yawa daga Cikin masu ganin Zahra ba 'yar kowa bace irin fakarahun yayan larabawa Nan ne masu azabar kyau din Nan da yawancin mazanmu masu kudi ke aurowa Dan neman irin Mai kyau Cikin zuri'arsu.
Bayan gama tafi da sowar tuwon girman da Ummee tayi aka nemi dangin miji,sun shigo kamar Gori maza da Mata sunyi barin kudi kamar ba gobe Ammi ta fito da tawagarta ta yiwa Zahra liken CFA kudinsu na Niger Hajja ta bawa Zahra kyautar shanu da zunzurutun CFA million goma.
Da sarkar zinari wadda kudinta sun tasarwa million tamanin take aka Miko cheque na eco Bank tunda shine bankin ecowas.
Amarya da angon sun Sha kyautukan girma suna niyyar komawa wurinsu wata Mata cikin sauri take ta yiwa mc magana, Nan da Nan ya dakatar da tafiyarsu Yana fadin.
Ga Mai gayya Mai aiki tazo Fulanin Mai Damagaram aminiya ta hannun damar uwar ango Hajiya zainab.
Wata farar Mace Yar gayu tare da amintattun bayinta sai wata yarinya budurwa dake tare dasu Saida suka matso sosai Zahra ta gane yarinyar Wadda ta kafa musu Ido ce a train station lokacin da zasu Jim Corbett national Park a Uttarakhand state. Take Zahra taji wani Abu ya tsaya Mata a kirji, yanda taga yarinyar na Mata wani kallon kasa kasa irin Mai nuna baka Isa din Nan ba.
Saboda a wancan lokacin taga irin kallon kurillar data kafesu dashi.
Fulanin na zuwa ta rungume Zahra tana fadin.
"Tabarakallah Masha Allah, Zahra diyata sannu da kwaramniya".
"Yauwa Mama, nagode".
Wani kallon banza yarinyar ta gara jifan Zahra dashi tana wani kawar da Kai gefe tana hade rai.
Liken kudi Fulanin ta Fara Yi musu haka 'yan tawagarta ma haka da alama an shiryawa wannan ranar, amma ita yarinyar mahmud kadai take yiwa Saida mummy Badi'a tazo ta janye Fulanin daga gurin ganin lokaci ya Fara ja tasan abokansa da kawayen zahrar suna son Suma su nuna tasu bajintar, a gurin dollars dai da pounds sunyi kuka.
Mama ta Raina kanta iya rainawa taga inda ake maganar arzikin da babu fariyar a cikinsa sai dai idanunka su fada maka, taga yanda matan uba ke kyautar mamaki Dan kowacce ta bawa Zahra tata kyautar.
Ba'a tashi ba sai kusan Sha biyu da rabi.
Sai da aka tashi sannan Ammi suka gaisa da Fulani wadda ta sauka a Daren Dan Bata kasar lokacin da Ammi ta kirata ta fada mata danta ya dawi har da tsarabar Daya dawo musu da ita.
A gajiye aka dawo gida danma an kamawa mutane da yawa dakunan hotels Dan duk matar da tazo daga Azare a mota ta biyu duka hotel aka kaisu shi yasa sai a gurin dinner Zahra taga wasu mutanen harda su Aunty zilai dinta Dan har liken Yan dari biyar sabbi tayi Mata. Duk yanda mahmud yaso ya wuce da Zahra Aishat da Aunty Nauwarah sun kasa sun tsare,dan Aishat ce tayi Mata tsegumin abinda take zaton ze aikata Dan taga dazu ya birkice da yawa idan aka barshi ko budar Kan baza'ayi ba ga momin Kano kuma ta shirya masa Dan lokacin da akaje da maganar ko a hakura dayin wunin tsalle tayi ta dire akan babu fashi sai anyi me zata yiwa mahmud ta biya shi kaunar da yake yiwa Faruq ya dauke shi tamkar uwa Daya ta haifesu ya bude Masa yanda ya kamata hatta karatun da yayi mahmud ya zabar Masa saboda ya ringa yi Masa ayyukansa.

Mahmud yana ji yana gani Sameer ya wuce dasu zahrar ita dasu sajeeda da Amatu.
Zahra a gurin su Ummee ta zauna sun Kai kusan biyu Aunty Nauwarah na saka Zahra a wasu irin ruwan magunguna masu azabar kamshi ga turaren jiki Wanda sai da kamshimsa ya game part din gaba daya, abin isar Zahra yayi Dan idan ba so suke yayi Mata lahani ba ya kamata a kyaleta haka ita kadai ranta sai abubuwa ake Mata Babu sasaauci,ko Dan Basu San abinda idanunta suka gani bane. Kawai a Riga suke ganin mutum Basu San sirrin dake lullube bane.
Gado Daya suka kwana da Ummee Zahra nata mitar Ummee ta manta da ita, data isheta da magana Ummeen ta fada Mata Abbu ne bashi da Lafiya ai mijinta ya sani Dan yaje har London ya duba shi, shine yayi blocking din layinta a wayoyinsu yace idan aka Bari Kika sani Zaki tada hankalinki gashi kema lokacin yace Baki da lafiya.
Gyara kwanciya Zahra tayi tana mitar abun, kamar ta hakura sai kuma tacewa Ummee.
"Wai Dan Allah Ummee a Ina Mika san...."
Sai Kuma tayi shiru.
"A'a Fadi Mana a Ina nasan mijinki".
Dariya tayi tana rufe Ido.
"Makocinmu ne a can Jordan gidansa Yana kallon namu".
Tashi zaune Zahra tayi tana duban Ummee.
"Badai wannan gidan da nake cewa yayi min kyau ba gashi Naga an saka Masa suna a samansa GIDAN ZAHRA".
Dariya Ummee tayi to ai daman gidan na zahrar ne haka Shima ya fada min tun kafin nasan ke zahrar tawa yake nufi, ko aikin gyaran gidan Abbie ne ya samo Masa masu yin duk sadda ya shigo Jordan Yana gidan mu, Bai Kuma taba fada Mana ya sanki ba Koda wata manufar da take kawosa gidan, sai bayan an bashi ke ya kirani yake fada min an bashi Mata idan ya shigo ze kawo min hotonta na gani.
Ranar Daya zo da yammaci ya shigo yaci abinci sannan ya bude ya ringa nuna min hotunanki tun kina 'yar matashiyar ki har na girmanki, ba Karamin mamaki hakan ya bani ba Daman yasan kina da alaka da Dani ko Kuma arashi ne kawai.
Dana tambayeshi ba wani rufa-rufa ya fada min yasan matsayinmu a gurinki.
Zahra tayi matukar mamaki Amma Dan tahalikin Nan Bai taba nuna Mata yasan su Ummee ba Koda Wasa, Sai dai Daman tayi matukar mamakin yanda taga suke mu'amala abun kwarai ya bata mamaki babu wani bakunta a tattare dasu.
Sun Jima Ummee na Bata labarin yanda suka shaku da mahmud din sai taga ita ai ya fita shiga jikinsu ma sosai.
Washe gari da wuri Aunty Hasana dasu Aunty Nauwarah da sauran mutanen Ammah Hajiya kaltume ta turasu tare da Aishat wadda zatayi musu jagora suje a duba abinda ya kamata a gyara a gidan da za'a Kai Amaryar tunda company ne sukayi jeren kayan da akazo dasu na zahrar duk da mahmud yace ba gurin saka komai, dole ya bada part dinsa na gidan Hajiya Inna aka zuba kayan tunda baiyi niyyar saka masa komai ba a lokacin domin guda biyu aka Gina Daya na zahrar to an Riga an saka masa furnitures sai dayan da dole tasa aka yi Masa paint da abinda ya kamata aka saka kayan a can. Basu wani Dade ba suka baro can din tunda babu bukatar yi masa komai sai dai turarukan daki da aka saka, Basu dawo gida sai da aka kaisu gidan da za'a Kai Zahra, permanent gidanta gidan Hajiya Inna temporary ne na week end da yada zango Idan an dawo daga tafiya Dan Alkawari ne duk inda yaje ya dawo gidanta ne farkon sauka.
Sunyi santin gidan tamkar ba'a Nigeria mutum yake ba Dan Maman mujiba kasa shiru tayi da bakinta lokacin da Aishat ke shiga dasu guri guri a kasa taga parlours sun Kai hudu ga sama sun hau taga common karfen dake Jikin stairs shi Kansa tamkar na zinari sai daukar Ido yakeyi ga gidan ko Ina daukar Ido yakeyi ga haukatan bedrooms ga toilet ga gani na fada Dan wani abun ko a hoto Bata taba ganinsu ba. Ja tayi ta tsaya tana kallon Aunty Hasana.
"Dan Allah Hasana Wai Yaya Aljanna take ne?"
Ba Wanda baiyi dariya ba a gurin kuma ita har zuciyar ta tayi tambayar.
Ganin suna dariya yasa ta Kara fadin.
"Wallahi da gaske nake tambayar Nan, ki dubi gidan Nan Wai a sokoto yake? Ni tunda Allah ya halicceni ban taba shiga makamancinsa ba, Nan gidan zahra ne wadda ake tsegumin an aurawa Almajiri kolo marar galihu marar komai, ana ta zunden Alhaji idan ya wuce a unguwar, a cikin gidan Kuma ana sakin habaici an ce kyau ya Kare a Wanda ba'asan asalinsa ba, to yau kowa yazo yaga inda Allah yasa Alhaji Jafar ya kawo marainiyar Allah gidan da hasashe be taba hasasowa ba, tunani Bai taba tunanowa ba, Hasana saka wayarki ki daukar min gidan Nan ciki da waje sai masu tsegumi sun gani da idanunsu, 'yan bakin ciki kuma su mutu tunda Alkawarin Allah baya tashi idan yace Kaine sai kakai, lallai Dan tsiron da Allah keso ko babu ruwa saiya rayu, yau Zahra ta Zama farin wata Sha kallo. Masha Allah Arzikin mutum a jikinsa yake Kuma dare ga Mai rabo hantsine".
Guda ta rangada har sau uku tana Kara fadin . "Idan Rana ta fito tafin hannu baya kareta, walkiya inta haska wanene ze iya kareta? Hadari In yayya tsawa rufe kunne baya Hana jinsa ga Zahra ikon Allah sai kallo".
Kudi Aunty Nauwarah ta Ciro dollars ne saura Wanda ta zubawa Zahra ta Zubawa maman mujiba Dan ko Bata Jin abinda take fada tasan kurare 'yarta takeyi, ko ita da suke a kasashen da sukaci gaba gidan Zahra ya tafi da ita Dan babu karya anyi gidan tamkar baza'a mutu ba Dan dukiya dai an kasheta tamkar ba'asan ciwonta ba.


******

Saida zahrar tayi barci Mai isarta sannan ta tashi, lokacin wurin Sha Daya. Wanka ta shiga tayi data fito tayi break fast sannan ta shirya, Aunty Nauwarah tayi Mata makeup mai daukar hankali. Doguwar rigar atamfa green Mai milk din fulawoyi ta saka tayi amfani da gyale milk da takalma plat milk, wayarta ta dauko wadda ta sakata a silent tun daren jiya saboda message din data gani na mahmud da yake son dole ta fito Yana ta bayan part din Ammin, idan ta fita akayi Dace wani ya ganta ai noway out, cewa za'ayi har satar jiki take tana zuwa gurinsa, dubawa ta shiga yi na meu amor ta Fara bi kasancewar Aunty Nauwarah Bata Jin hausa yasa hankalinta kwance ta kirasa.
Harta yanke be daga ba sai taji wani irin ba Dadi a zuciyarta.
Ya Abdul Hakeem ya Nemo wayar taji a Ina suka kwana.
Dauka yayi suka gaisa kafin ta Dora da fadin.
"Ya Abdul Hakeem a Ina kuka kwana ne? Kuma Ina Abbana wallahi kunyi surprised dina banyi zaton zakuzo ba wallahi".
"To Ni dai gani Nan a wata unguwa Wai kome? Na manta Abba kuma sunbi jirgin bakwai da rabi yanzu haka ya sauka a Bauchi sun dauki hanyar Azare".
Wayyo Ya Abdul Hakeem yanzu Abbana yazo garin Nan na kasa gaisawa dashi".
"Kinsan halin Abba ai yace ze dawo special yaga masaukin ki, kinsan ya w
Sun jima suna waya daga baya sukayi sallama.
Aunty Hasana ce tazo ta raka Zahra Dakin Ammi ta gaishesu sannan ta mayar da ita masaukin da Ammi tayi mata.
Sai wurin karfe biyu mai yin makeup wadda momin Kano ta dauko takanas tazo Shirya Amarya, tayi Mata makeup light, ta Zuba Mata wani material Mai ubansun kyau ta daura Mata head sai zahrar ta fito a tauraruwarta dan komai hassadar mutum ya kalleta ya Kara kallo Dan da gaske zaharar ce.
A Hidima event center Wanda ke bodinga road, behind Nipost sokoto south za'ayi yinin, lokacin da aka shiryata photographer yazo anyi hotuna kamar me sunje part din momin Kano ma anyi hotuna a Nan Zahra taga kanwar maman Musbahu Aunty batayi mamaki ba tunda taga musbahun da Faruq tare a Kano da alamar sun jada relation dasu.
Daga bangaren Momin akazo tafiya da Zahra gurin da za'ayi event din Mai gayya Mai aikin ya Kira momin da Kansa yace suje za'a kawo ta.
Abinda yaso ya Zama na magana a Cikin family kenan sai da momin ta tsawatar saboda momi ba Wasa tasan kanta yanda ya kamata Bata daukar wargi domin itama daga babban gidan sarautar Kano aka daukota, shi yasa tasu tazo Daya da Ammi ma Dan itama Ammi tasan ciwon kanta Kuma da fadarta gurin miji, Sam Bata shiga shirgin tsugune tashi na family din.
Sameer yazo ya tafi da Zahra su Amatu sunso subi Zahrar Amma Sameer yace ba can suka nufa ba yanzu da inda ze kaita, dolensu suka hakura da bin motar Amaryar.
Direct kalambaina road suka nufa ita dai Zahra ikon Allah take kallo.
Gaban wani plat house mai wani irin gini na daukar hankali taga sameer ya tsaya Yana yin Horn har suka Karads shiga ciki wayar Sameer ta dauki kida da sauri ya dauka Yana fadin.
"Har munfa karaso".
Da yake a handsfree take sai Zahra taji yace .
Ku wuce kawai akwai mutane a gidan".
Wani sanyin dadi ne ya rufe Zahra Daman tunda suka taho addu'a take haka Nan Bata San kebewarsu a tsakanin Nan dan salon da yake fito Mata dasu yafi karfin dan Karamin tunaninta.gaskiya, hamdala dai tayi tafi ciki carbi.

Guri yinin ya hadu ya kuma Tara matan da suka amsa sunan su mata, Dan momin kano ba Karamar gayya tayi ba tunda ita Ammi ta bawa wannan bangaren, mutanen Ammi na Niger sunzo kamar Gori, gurin ya dinke da matan gayu sai sabgogin arziki akeyi an sakata Zahra a wata kujera a tsakiya hall din ga kidan wakokin bikin na tashi Dan a kalla su Kai kala biyar Dan ma abun ne yazo a Qure.
Kafin yamma an sakewa Zahra dress ya Kai sau biyar da mahaukatan laces na makudan kudi duk karkashin momin kano tunda itama 'yar kasuwa ce ta gaske

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login