Showing 231001 words to 234000 words out of 280244 words

Chapter 78 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1067

Dan wasu abubuwan ma tare da Ammi suke juyawa irin kayan da ake shigo musu dasu daga kasashen dasu mahmud suke da kamfanoni a can.
Da yamma Zahra na Dakin da ake Mata canjin dress Hajiyar makwarari ta shigo iita da Aunty Rukayya, Hajiyar Tasha wani ubansun lace tayi gwagqgwaron tsofaffi ga jaka da takalmi da gyale duk iri Daya.
"Ina zahara'un take? Zuwa nayi na tofeki da lahaula saboda naji bakin mutane yayi yawa a kanki to kada aje ba'a sani ba Koda Mai kambun baka, gara ki shiga gidanki salin alin salamun qaulin, yo Ina dalili! A sakawa yarinya Idanu kowa wuwww,haba surutu ake caca

*AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH.
Maman Fateemah
09061432330
08055362975


Wannan littafin ba MALLAKIN kowa bane gurin juya shi ko sarrafi shi Audio ko wata sigar Saida izinin marubuciyar.


Page 82.
....... Mahmud na tsaye a compound din gidan motar Alhaji Muhammad ta shigo a hankali har ta tsaya a dai dai steps da ze sadaka da babbar kofar shiga ciki, da sauri mahmud yaje ya budewa Abbie kofar dake tsakiya ya fito yayin da Malam Haruna ya budewa Zahrar kofar karshe ta fito, mahmud ne yaje ya bude kofar Abbie na gaba Zahra na biye dashi.
Suna shiga Cikin Zahra taji wata irin karaya tasan karshen tika tik, duk wani zagaye zagaye yau dai ne final, gata a sokoto a gidan mahmud inda ya ta'allaka duk wani burinsa da yake kanta.
"Ya Ilahiy!"
Ta furta da siririn sauti.
Har bedroom dinta Abbie ya kaita yayi Mata umarni data zauna a Kan gadon ta, ba musu ta dosana tare da Bismillah ta zauna a darare, Abbie din da Kansa ya dunga kwararo musu Addu'oi Cikin harshen larabci mahmud na fadin Amin.
Abinda ya karyawa Zahra zuciya kenan shaukin mahaifanta ya taso Mata yanzu da itama nata suna Nan da watakila shine a tsaye yake kwararo masu wadannan Addu'oin, duk da su Ammah da Abbanta Basu taba Bari tayi kukan maraici ba,amma masu iya magana na fadin gurbin idon ba Ido bane, ita kaunar d'a da mahaifi daban take Allah s.w.a. ke sanyata a tsakaninsu, ba zato sukaji saukar siririn sautin kukanta.
"Haba Fateemah ya zakiyi kuka Kuma? keda nake ganinki jaruma, ai masu babban suna basa kuka, ko su Abban naki da Malam dole sukayi Miki suka hadaki da Hussein? fada min yanzu na koma dake kije ki zabi Wanda kikeso na aura Miki kinji 'yata".
Zuru mahmud yayi yana kallon Abbie din yasan da a wancen lokacin ne irin wannan ranar da Abbanta da Abdul Hakeem suka Kai Masa ita ta samu irin wannan damar babu abinda ze hanata fadar Bata sonsa, sai dai yanzu yasan ko tana Shan giyar wake bazata Fara ba Dan shi Kansa yasan ya Bata darussan da barinsa ze Mata wahala duk talauci kuwa Dan yasan duk shegantaka ce ke sakata wannan koke koken Bata ji dai dai ba da tuni labarin ze canza.Amma a juri zuwa Rafi da sannu za'a fasa tulu.
Shiru Zahrar tayi tana ajiyar zuciya, dan murmushinsu na manya yayi ya nufi kofa Yana fadin.
"Kiyi hakuri haka shine girma kinji Diya ta,idan yayi Miki ba dai dai ba ki fada min nine Zan hukuntashi Allah yayi muku albarka ya Albarkaci aurenku da 'ya'ya masu Albarka ya kade muku fitina ya Baku Zama lafiya ayi ta hakuri kinji 'ya ta Zan tafi, ki yiwa mijinki biyayya ki bashi girmansa da Allah s.w.a ya bashi kinji'.
Kai kawai ta iya gyada Masa saboda kukan da takeyi. ficewa yayi daga dakin Yana Jin wata nutsuwa ko ba komai Dan nasa yayi dacen da kowane uba ke fatan dansa yayi, yasan in Sha Allah za'a samu nagartacciyar uwa a gurin Nan.
Da sauri mahmud ya biyo shi a baya sai ganinsa yayi.
"Yaya ka fito ka barta kaje ka lallasheta Mana kasan mata 'yan lallashi ne".
Sunkuyar da Kansa yayi sai yaji Yana Jin nauyin hada Ido da Abbie din nasa, Dan shafa gefen fuskarsa yayi, Shima Abbie din murmusawa yayi ya nufi mota Yana kissima yanda Dan nasa yake Cikin farin ciki Dan masu iya magana suna cewa labarin zuciya a tambayi fuska, Sai dai yana nuna kawaici ne a gabansa.
Abbie na barin gidan Shima ya shiga motar da yazo da ita ya fice Yana fita motocin Ammi suka doso gidan Daya Aishat ke ja sauran Kuma be tantance ko su waye ba, fitila Aishat tayi masa tayi gaba itama ta gane shi.
A Cikin motar Aishat su Ummee ne sai Mama sauran Kuma su Hajiya kaltume ne 'yan tawagar Ammah sai tawagar Ammi dai saura motocin gidan Kuma jama'ar su Mahmud ne da matan gidan.
Tun a kofar gate din gidan Mama ta Raina kanta balle da aka shigo ciki, take taji kirjinta ya Fara ciwo har wani jiri yake daukarta a daddafe ta shiga ciki a Nan Kuma taga abin al'ajabin Daya so ya zautata Dan abinda Bata taba tunanin ze faru bane take gani. Wai wannan gidan na zahra ne itace mamallakiyarsa ita zata rayu a cikinsa. Lungu da sako ba inda Aishat Bata shiga dasu ba,master bedroom dinsu ne kadai Bata bude ba,da yawa sun Zama 'yan kauye a gidan, dan sunga abinda Basu taba gani ba, dakin Zahra da kawayenta Wanda suka shigo Babu dadewa suka shiga suna ta rarinarsu da dauke dauken hotuna. su Hajiyar suka shigo ai ganin da gaske Zahrar ce a zaune a Cikin dakin Kuma da sunan mamallakiyarsa.
Wani Abu Mama taji ya soketa a kahon zuci da kyar ta iya sulalewa ta zauna a bayan wata Mata tana dafe kirjinta.
Babu Wanda ya lura da halin da Mamar ta shiga tafi minti uku a haka kafin ta samu rangwamen ciwon ta Mike ta fice tana Jan kafa Dan ji tayi sunyi Mata wani irin nauyi.
Har goma da rabi gidan da jama'a Amma da yawa bakin sun wuce sai danginsu na Cikin garin sune suka nemi gurin suna baza hajarsu ta yin hotuna, sai Aunty safiya wadda gidansu babu nisa da unguwar da aka Kai zahrar. Yawancin kawayen duk kasa suka sauko ya rage daga Zahra sai sajeeda da Amatullah. Aunty safiya Batasan lokacin yaja haka ba Saida ta duba wayar hannunta taga quarter to eleven sannan ta ankare ta cewa Amatu ta taso su wuce.
Sallama suka yiwa Zahra Amatu na?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? fadar.
"Kiyi Masa biyayya dai yauwa kada naji kada na gani, ko Aunty safiya?"..
Ta fada tana kallon zahrar wadda ta sadda Kai kasa tana Wasa da siririn zoben gold da yake hannunta.
"Dan Allah Amatu ki rabu da ita tun safe kika damunta, ba gara ita ba Dan an kusa shatanta ta warke ba, ke kuwa kece a kwana Dan Naga wannan Tajuddeen din da yake dama-dama dake guda ne da alama kema garin namu Zaki shigo".
"Ki rabu da ita Aunty safiya Zan rama ne, wallahi yanzun ma Ina Jin kunyar Aunty na ne baiwa bani da bakin magana ba ki Bari dagani sai ke kiji magana, Naga alamar ko irin Jan aji Nan bazakiyi ba Daya kiraki kike Fara tsuma kamar wata tsohuwar kilaki".
Ta saka gefen Alkyabbar ta rufe fuskarta dashi tana Mata dariya.
"Wallahi kinci bashi saina biya Shi kuwa Dan tsabar iya sharri Zaki wani ce Daya Kira nike kama tsuma".
Hannun Amatu Aunty safiya ta janyo tana fadin.
"Zomu tafi ramawa tayi tun farar safiya kike Mata Dan biki ai kadan ma tayi miki".
Suka fito parlourn farko na sama ba kowa a ciki sai wani irin kanshi da sanyi Mai kwantar da hankalinki a tsakiya Amatu ta tsaya ta rike Qugu tana karewa gurin zuwa dayan parlourn kallo ta Dan busar da iska daga bakinta tana kallon Aunty safiya dake tsaye tana kallon Amatu data ja ta tsaya.
"Wai lafiyarki Kika ja tunga Kika tsaya?".
"Bari kawai Aunty aini lokacin da kike bani labarin Families din su mahmud jinki kawai nake gani nake kamar kina kurarasa ne kawai. Amma yanda Naga gidan kakarsa kadai sai Naga ai Bakima iya bada labarin ba ban Kara sarewa ba Saida na shiga gidan mahaifiyarsa to ga Kuma Mai kankat, Dan Allah Aunty safiya waye mahmud din Nan nifa na sare da Lamarinsu gaba Daya dole kiyi kokontonsa a wancen gidan Daya sakani Santi Ashe akurkin kaji na gani".
Tafin hannuwanta ta bude ta Fara kwararo Addu'a.
"Ubangijin sammai da kassai ka zauna da Zahra lafiya a gidan Nan Dan isar Annabin Rahama ka tsareta daga dukkan qalubale na rayuwar Aure ka dubi gwagwarmayar data Sha a baya ka Zama gatanta, ubangiji ka jibinci lamuranta Dan soyayyar ka da Manzon Allah ka dorata a Kan duk wani mahassadi da 'yan bani na iya ka dauwamar da soyayyarta a zuciyar mijinta, ubangiji ka dubi maraicin baiwarka ba Dan ta rasa gata ba".

"Allahumma Amin".

Sukaji an fada daga bayansu.
Da sauri Aunty safiyar da Amatu suka juya, Mahmud suka gani ya shigo ciki ta wani corridor Basu San ta Ina ya biyo ba.
Kunya Aunty safiya taji abinda take ta gudu kenan kada ya shigo da abokansa su sameta a gidan duk da ba wani girmansa tayi da yawa ba Amma ita ai Yaya ce".
Cikin daburcewa Aunty safiya ta gaishesa tayi Masa Allah ya Sanya Alkhairi, Amatu ma gashesa tayi.
Zasuyi gaba mahmud din yacewa Aunty safiyar.
"Auntyn mu ko ta Nan Zakibi sai zayyan ya mikaki gida mun gode kwarai".
Tana Jin haka tasan abokansa suna kasa da sauri ta juyo tana fadin.
"Nagode jazakumullahu khairan".
Saida ta gangara kasa sannan ya Ciro waya ya Kira zayyan.
"Ga Auntyn mu nan ka mikata gida a fadawa Sameer ya Bata itama".
Kit ya kashe wayar Yana kallon Amatu yana murmushi.
"Ashe dai sai wani yayi min iso gurin previous din kenan,ai nayi zaton dukkan ku kuka yoye kun bar min ita kadai".
"A'a wane mu da barin sarauniyar Mata a daki ita kadai yanzu haka suna tare da sajeeda".
Gaba Amatu tayi ta nufi kofar ba wani knocking ta tura ta rike kofar tana kallonsu, sajeeda ce tace.
"To uwar iya wace gulmar Kuma ta dawo dake dakin Nan yanzu dai ba kyaleki zamuyi ba tunda babu idanun kunya".
Shigowa tayi tana fadin. "Alheri ya dawo Dani Mai gayya Mai aikin ne na rako dungurungun Dan haka kema tattarko ya naki ya naki Mai gurin yazo".
Wani irin Ras zahra taji, Ita fa abun Nan ya Fara Bata tsoro Wai me yasa a baya Bata jin haka ne Sai yanzu? turo kofar da yayi ita ta datse Mata tunanin data fada.
Shine Cikin shigar shadda sky blue sai walkiya take tamkar a matse Mai a jikinta ga wani ubansu kamshinsa na dindindin Daya kashe na kowa a dakin.idanunsa yana kanta wani irin azababben kyau tayi Masa Ganin ya shagala da kallonta kada a saki layi a gabansu sajeeda yasa tayi magana.
" Yallabai barka da dare, ya hidima? Allah ya Sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyuba. To zamu tafi gata Nan Zan baka Amabarta a karo na biyu, kamar wancen karon, kaji tsoron Allah a Cikin zamantakewar ku ka tsare Mata mutuncinta a da Basu San waye Kai ba, Amma a yau ko baka fada Mana ba mun gani da idanunmu, nasan bestie zata iya fuskantar hari daga masu burin samun matsayi irin nata a gurinka, ko ba'a fada ba tunda a Dan kwaramniyar bikin Nan naji views din Mata da yawa a kanka. Gata Nan Bata da kowa a garin Nan daga Allah Daya halicceta sai Kai daka kawota,ka zamar Mata bangon da zata jingina dashi ka zamar Mata suturar da zata Kare Mata martabarta, kada ka cutar da ita Dan girman Allah Zahra marainiyar Allah ce duk da Bata rasa komai na gatan gidan duniyar Nan ba Amma tana bukatar samun nutsuwa tunda a can akwai 'yar kasan da ake soya Mata Aya a tafin hannuwanta ba tare da an ankare ba Saida tafiya tayi tafiya, Allah ya amintar dake bestie a Cikin gidan Aurenki ya Baki kariya irin wadda yake Kare bayinsa salihai da ita, ya amintar dake kamar yanda ya amintar da Annabinsa Ibrahim A.S daga wutar Namaruzu. Dan Allah kiyi Masa biyayya ki rufe masa sirrinsa kinji, Allah ya Baku zaman lafiya Mai dorewa ya kauda muku fitina"..
Sai Kuma muryarta ta Fara rawa, sai hawaye, da sauri ta nufi kofa ta fice. Zahrar ma share hawaye take haka Amatu itama idanunta sun cicciko da hawayen,Shima Dan gogan tunda yarinyar ta Fara magana yaji kamar ta Dora Masa bulo inci Tara a kansa, ya yarda kaunar precious da yarinyar Nan ta gaske ce babu algus a cikinta saboda yayi wani Abu Wanda ya gaskata hakan, Dan ranar Daya bijiro Mata da maganar soyyyarsa dan Karamin hauka sajeedar tayi Masa da kyar ya fahimtar da ita cewar gwaji ne yayi Mata ba Wai da gaske yake ba, duk da haka Saida ta nuna Masa kada ya karayi Mata irin haka za'a iya samun matsala.
A can main parlour kuwa abokan angone tare da kawayen Zahra sai wasu 'yan Mata na family din, tun a can ya fada musu Bai Hana zuwa sayen Baki ba Amma babu Mai shigar Masa dakin barci babu Kuma Mai Kara gane Masa Mata Ganin gurin dinner ma Ala amfana.
Yasha caccaka gurin friends dinsa yayi kunnen uwar shegu dasu shine dalilin Daya saka yayi amfani da kofar baya ya hauro stairs din shi kadai.
A Nan su sajeeda suka Sami su Khadija dasu Aneesah da sauran mutanen, Tajuddeen ne ya taso ya nufi Amatullah yana fadin. "Daman kina sama duk Kiran da nake Miki bakya amsawa?".
Dan bude hannunta tayi alamar babu waya a gurinta.
Jinjina Kai yayi suka nufi waje.
Addu'a sukayi aka shafa sannan kowa ya fito da wata Leda Mai shegen kyau a hannunta da alama kyautar girma ce daga bangaren anguna.
Saida suka fito sannan salis ya Kira mahmud Yana fadin .
"To yallabai ango mu zamu wuce asuba ta gari".
Wani Abu mahmud din ya fada Masa ya fashe da dariya wadda ta janyo Hankalin da yawa daga mutanen gurin Yana fadin. "A'a kayi zamanka wasu har sun Fara ficewa daga cikin gidan ka duba time lokacin yaja da yawa".

Tun bayan fitar su Amatu zahra tayi tsilli-tsilli, sai taga yau ya Kara Mata wani kwarjin da girma gani tayi kamar ya cika dakin, numfashi ma neman tsaya Mata yayi wallahi wani irin Abu take gani a cikin idanunsa.
Yana sauke wayar daga kunnensa ya nufo zahrar Yana sakin tsadadden murmushi, ya Dan tsuguna a gabanta ya saka hannu ya dago fuskarta wadda hawaye ya bata.
"Ya salam!"
Ya fada Yana Zama kusa da ita, tafin hannunta Daya Sha lalle ya rike Yana Dan matsawa kada dayan hannunsa ya saka ya zare Alkyabbar daga kanta Yana karewa fuskarta kallo, be tab'a Jin ya gaji da kallonta ba shi dai ya yarda Allah ya jarabcesahi da wata irin soyyaya a kanta shifa ji yakeyi ko baze kusanceta ba ze iya rayuwa da ita har iya rayuwarsa.
Wani irin kanshi ne ke fita daga jikinta na musamman ba Wanda ya Zama constant ba a'a an samu Karin wani na musamman a Jikin.
"Welcome to Dange's house Mrs Mahmud Muhammad Dange, Alhamdulillahi bini'imatihi titummus salihat, Fateemah Allah yayi Miki Albarka yau gaki a gidan Mahmud Kuma gidanki da Zaki rayu a cikinsa ki dasa Mana bishiyar Zuri'armu a cikinsa ta girma ta yadu har asha inuwarta, Fateemah duk burina na duniyar Nan game da mace a kanki na ta'allaqa shi ki zamar min bargon daze lillib'eni ki hanani Jin sanyi sai dumin jikinki, ki daukemin duk wata kishirwar data addabeni akan diya mace kinji my princess, duk duniyar Nan da ke kadai na aminnta na bayyana Mata sirrina ciki da waje ke kadaice macen data tab'a gani ainishin waye ni tunda nayi Hankalin kaina, ki tallafeni kada ki Bari na shiga rubibi a hannun Mata kinji my previous, na baki amanar kaina da kaina tunda ni babu Wanda ya Baki Amana ta amma ke kowa fada min yake gaki Nan Amana na kula dake to nima ki kula Dani Dan tamkar marayan da bashi da uwa bashi da uba haka nake a gurinki ki bani dukkan kulawa kinji, kuma Dan Allah ki daina tsorona nifa babu abinda Zan Miki na cutarwa idan na cutar dake Nina cutar da kaina, duk wani burina nandora shi a kanki".
Ya fada Yana shigar da ita jikinsa Yana sauke ajiyar zuciya a jajjjere, lif tayi a jikinsa Amma fa yaji yanda heart dinta ke beating very fast. Lumshe ido yayi ya rasa meya canza Masa ita take irin wannan Jin tsoron nasa yasan ba dabi'arta bace hakan ko ranar Daya Fara fito Mata a mutum sak ba tayi irin wannan tsumar ba kawai dai ta Dan rikice Masa na dan lokaci Amma Daya saka Mata pressure dole ta nutsu tayi Masa abinda yake so a lokacin harya saida ya samu relief, Amma yanzu duk ta rikice Masa a Hankali yayi Mata magana a kunnenta.
"My previous me kike tsoro a tare dani, fada min kinji?".
Ya fada Yana Kara shigar da ita jikinsa yana kuma Dan shafa gashin kanta Daya Sha gyara na musamman, sanyi da salama da wata irin nutsuwa suna sauka a cikin zuciya da gangar jikin a lokaci daya.
Lif ta qarayi a jikinsa dan da gaske tana Jin wani irin Abu da ada Bata jinsa a tattare dashi, sai yanzu take jin da gaske fa auren ne a kanta sabanin da da take jinta dai gata nan.

*AUREN HUCE HAUSHI*

_AISHAT ISAH MUSAH

_*Maman Fateemah_*

08055362975
My
WhatsApps number.




*Page 83.

______Kara shigar da zahrar yayi jikinsa, nan da nan yaji labarin Yana neman canza salo shi Kuma harga Allah Yana bukatar privacy saboda matukar ya tab'a wannan shugwababbar 'yar raki sai abinda Hali yayi. Don yasan za'a Sha danger da ita ga mutanen biki suna Nan yasan da safe baza'a rasa masu zuwa suyi Mata sallama ba, yafi son sirri gaskiya. Amma dai zasuyi nafilar da Manzon Rahama yayi umarni da ma'aurata su yita.
"Cikin nasa salon da yasan Yana yin rinjaye a kanta ya Dan fara shafa cikinta a Hankali.
"Da yunwa a cikin Nan gaskiya, Bari na kawo Miki abinda zaki?i kada Nan gaba ayi min gorin ranar da akazo gidana ko abincin tarba babu Ina ta kurin sokoto aga nayi failing ko ba haka ba?".
Ita dai zahra shiru tayi masa shi ya kasa ganewa yau jinta take tamkar Bata taba wata kebewa tare dashi ba,taga sai wani rawar jiki yakeyi abinda ba halinsa ba, duk wannan kanewar ta nemi nata gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login