Showing 258001 words to 261000 words out of 280244 words

Chapter 87 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1038

fada yazo Kuma a samu akasin hakan, lokacin da suka dawo suka samu momin Kano ma tana fama da nata laulayin ciki wata ukau a watan da suka wuce ta Sami nata itama.
A Nan sokoton ma sun fada mata, da watan haihuwa ya Kama Hajiya Inna da kanta tazo ta saka zainab gaba lokacin baya Nan yaje wani aiki Lagos ai kuwa kwana biya da daukarta cikin dare nakuda ta tashi suka garzaya asibiti a cikin ikon Allah kafin asuba ta haifi yaranta biyu murna gurin Hajiya Inna Kamar ba'a tab'a haihuwa a gidanta ba, kafin gari yayi haske suka koma gida kafin wani lokaci gida ya cika da jama'a bare da abun shima uban gayyar yasha mamaki da Inna tace masa Yara biyu ne Sam cikin beyi wani girman azo a gani ba.
Ranar suna anyi hidima 'yan Niger sunzo tamkar a Niger mai jegon take yaran sunci sunan Aishat da Mahmud, sun Sami Alheri Kamar me Hajiya Inna ta Hana su Hajja zuwaira su tafi da zainab gida dole suka hakura suka tafi ita Kuma taci gaba da wanka a gidan innar har tsawon wata biyu,Saida Alhajin ya gaji yace Mata Wai bazaki mayar Masa da matarsa ba sai hakurinsa ya Kare kice yayi rashin kunya, ke ba bahaushiya bace ko wannan cika daren da yakeyi a gidan nan Bai isheki ki gane matarsa yake So ki bashi ba,dubi fa tamkar baya da wasu matan.
Inna Bata jaba tayi Mata abinda ya kamata ta mayar da ita.
Ranar data koma suka Bata girkinta Amma Saida Inna ta karo Mata da yarinya bayan masu aikinta.
Kafin wani lokaci yaran sunyi bulbul sunyi kyau Kamar ba twins ba, suna wata hudu momin Kano ta haifi Faruq .
Haka haihuwa ta budewa Ammi tayi gambon 'yan biyu Khadija Mai suna Inna ana ce Mata Nur wadda ke Aure a Germany wadda kukayi waya jiya tana kukan ba'a fada Mata ba Dan tana da tsohon ciki.
Sai Baool da suhailat kin sansu sai su Jamal da Auwam suna london secondary.
Mu dawo baya lokaci da za'a yaye mu Hajja ta dauke mu duka badan Inna taso ba ta hakura, da kyar Aishat tayi sati hudu aka dawo da ita saboda kuka takin cin abinci Kuma, Ni kuma naci gaba da Zama a can har na Kai minzalin sakawa a makaranta Abbie yaso na dawo Amma Alhaji Haroon ya Hana yace in dai makaranta ce za'a sakani wadda suke yin turancin ingila hakan Kuma akayi ban baro Niger ba Saida Zan tafi junior secondary school inda aka kaimu Nigerian Turkish a Abuja nida Aisha da Faruq.
A can na hadu da Sameer ajinmu Daya da farko fada mukayi dashi sai Kuma rashin lafiya ta kamani shi da Faruq sukayi jiyyata a sickbay, tun daga lokacin Kuma muka dinke dashi,sai lokacin muka Kara shakuwa da Faruq mutane suyi ta mamaki idan Yana ce min yaya Mahmud sabida suna ganin ya fini garin jiki ma.
Har muka Gama secondary muna tare da Sameer, lokacin da muka dawo gida gaba daya mun Gama makaranta lokacin muka Sami Abbie ya Kara Aure ya cike ta hudu, mace ce wayayya Aunty Sameera 'yar Minna ce Niger state bazawara ce da yaranta biyu na mijin baya Wanda ya rasu, sai kanwarta Sakina wadda ake Kira da Safna, lokacin bazata fi shekara Sha uku ba haka yarinya ce Mai saurin sabo Dan bamu fi sati biyu da dawowa ba muka shaku da ita sosai tamkar mun shekara Bata jin nauyin fada min komai saima Ina kwabarta gata da son kashe kudi Nan da Nan zata rokeni kudi, banajin komai saboda kirki Aunty Sameera Amma Ina ganin bekenta gurin tarbiyya gaskiya saboda ita'yar social life ce.
Lokacin Dana tashi zuwa Niger taso ta bini na hanata har gurin Abbie ta Kai karata nace masa bazanje fa da ita ba dole ta hakura.
A haka Muka share kusan wata hudu a gida ana ta processing na admission din mu inda Abbie ya hada harda Sameer ya Samar Mana a Oxford university ta London inda Aishat suka Bata physiology Ni Kuma business administration inda Sameer yayi Accounting, anan muka hadu da Mutuniyarki Dr Haseenah inda ita Kuma take medicine 'yar abokin Abbie ce tun haduwarmu ta farko ta ringa nuna min sign na soyayya Ni Kuma saina basar saboda Sam Bata cikin tsarin irin macen da nakeso, faruq sun bashi pharmacy haka mukayi ta karatu babu Kama hannun yaro ga Kuma Mr Johnson a gefe Yana kula damu, ba kowace semester ba Mike zuwa gida Muna level two hundred ne Akayi bikin Aishat Dan Kanwar Abbie na biyu Kinsan shi ya Abbas lokacin shima Yana PhD a Nan Auren Aishat ya taimaka Mana kwarai da gaske Dan abubuwa da yawa sunyi min sauki tunda Ina da gurin da inda zan aje abubuwana safe.
Idan anyi hutu ban fiye zuwa Nigeria ba sai idan Hajiya Inna ta matsa,a kwai zuwan da mukayi nida Sameer nayi mamakin girman Safna ta Zama budurwa sosai, lokacin hatta abincina ita take dafa min Bata gajiya da Yi min hidima Saidai idan ban bukata ba haka mukayi ta rayuwa idan na dawo mu dinke idan Ina can muna waya Idan na samu sarari, muna shekarar karshe ne munzo hutu lokacin na Dan Fara gwada business zamuje Istanbul ganin wasu Kaya da nayi magana da kamfanin ta website dinsu a ranar na Fara ganinki keda Abba kina Masa tabara da girmanki Wai Baki son seat din da kike kinfi son saitin window, kin tuna wani yazo yace Miki kije gurinsa ki zauna shiya zauna a naki gurin Yana sanye da facemask?".
Gyada Kai tayi alamar ta tuna "to nine".
Gyara Zama tayi tana kallonsa "shifa wancen yaro ne ba kamarka yake ba".
"Kin jini da yarinya to ke lokacin Yaya kike?"
Zan nuna Miki hoton ki gani, Kinsan a ranar Saida Sameer ya biku tunda yaji Abban na fadin Jordan zai kaiki hutu shi Kuma ya wuce saudia.
Sameer na biye daku har Saida ya tabbatar da inda kujene sannan ya dawo mukayi abinda zamuyi muka wuce London, haka muka ringa juyawa karatun da Dan kasuwanci.
Wani hutun da mukazo harda Aishat mukazo lokacin tana da cikin farko na yarinyar data Haifa ba rai.

A hutun ne Ubangiji ya bude min kofar nawa arzikin Dan Ina sokoto uncle Ishaq ya kirani a waya yace min ga condensed milk Nan wani abokinsa yayi order dinta Kuma kafin ya Kai kasuwa wasu Kayan nasa da sukafita mahimmanci suka shigo shine yake son ya sayar dasu a tsaye shine ya bani rancen kudin idan an sayar na maida masa da kudin.
Kamar wasa aka kawo Madarar da Sameer muka shiga kasuwa muna yiwa mutane talla kafin sati Daya gaba Daya ta kare sai Kuma costumes ta ko Ina ana booking dink Kayan nan da nan uncle Ishaq din yayi magana da kamfanin suka saya lokacin harda powder milk yayi order shi yazo har Nan sokoton ya Kama min store sai daga baya Alhaji kakana yayi ta fadan Dan me za'a Kama hayar store Alhalin gasu Nan kamar banza hakuri uncle Ishaq din ya bashi yace saboda kada abun ya Zama fitina shi yasa Amma idan kudin sun kare ba za'a sake ba.
Kafin wani lokacin abubuwa sun bungasa Kota Ina kudi shigowa suke Nan da Nan jari yayi karfi na ban mamaki, da kyar muka koma london saboda kasuwa ta kankama.
Cikin ikon Allah muka Gama jarabawar lafiya muka tattaro muka dawo aka Dora daga inda aka tsaya, lokacin su Aishat suka koma India da zama.zuwa lokacin munyi wata irin shakuwa da Safna komai ta nema take zanyi Mata tunda kudi dai Allah ya hore,da taimakon uncle Ishaq muka dunga fita kasashen duniya sawo Kaya da bada aiki a kamfanoni.
Kafin shekara biyu Ni kaina bazace ga abinda na mallaka ba lokaci Daya saida muka bude kamfanoni a cikin gida da manya manyan stores na Kayan abinci yawanci a states din mu na arewa muka Fara muke diban yaran mu na gida muke Kaiwa suna aiki sayar da Kayan mukayi musu tsarin kamar makaranta Dan harda Mai gadi idan suka dawo daga sallar insha'i Kuma ba Mai fita Saida lalura saboda yanda zamani ya Zama abinda ya Zama.
A cikin shekara ta hudu ne komai ya fito Dan lokacin ne aka bude kamfanin riguna abaya a Dubai da materials da laces na garari aka bude na jewelry a India sai wasu Kuma a China wallahi precious Ni kaina bansan ta ina na samu wannan dukiyar ba nasan dai condensed ce sanadin.
Kinsan har lokacin Sameer Yana bibiyar min ke duk inda kikayi makaranta Ina da masaniya ke har korar masu son Aurenki gaskiya mune Abu daya ne bamu da Hannu na yaron Nan Dan uwan momin Kano shi ne dai bansan inda aka haihu a tagayar ba.
Wata zabura Zahra tayi, janyo yayi jikinsa.
Wata ranar lahadi Ina Zaune a gurin da aka tanada Dan hutawa Ina ta faman aiki saiga Safna ta nufo inda nake da system a hannunta, tayi kwalliya sosai tunda Ni kaina nasan Ina Mata hidima Dan duk abinda na bawa kannena to tare nake Basu da ita Dan irinsu kudi ma saina Bata sau biyar ban Basu sau Daya ba.
Sannu Tayi min tana zama daf Dani har breast dinta Yana Dan tabani, ta tashi daga gurin nace Mata saita shagwab'e fuska tana fadin Dan Allah na barta ta zauna kusa Dani wani Abu Zan nuna Mata, kamar rufin Baki saina kasa musa Mata cikin Jin Dadi ta furta Thank you dear.
Wani website ta shiga ta Fara nuna min wasu tsala-tsalan sarkoki na gold masu Azabar kyau tana fadin na tayata zabe Wai Aunty Sameera ce zata saya Mata Wanda zata saka tanar bikin kawarta 'yar ministern Albarkatun kasa, ba zato mukaji salati daga bayanmu da sauri na juya sai Naga kawu saminu Yana tafa hannu Yana fadin wane irin rashin mutumci ne haka da yammacin Allah wata'ala na shigewa yarinyar daba muharramata ba irin haka Ashe Nima lalataccen ne.
Saboda bakin ciki ko kallonsa banyi ba na dauki wayoyina nayi gaba, ko akan wani bana son a jefe shi da kalmar Nan bare Ni a kaina.
Ina gurin Ammi sai gashi ya biyoni Nan muna Zaune ya shigo Yana huci Yana fadin har yaushe nayi arzikin da Zan wulakantashi Yana min magana kada na lalata yarinya tunda giyar nera na dibata shine nayi tahowata na barshi ga banza.
Hakuri Ammi ta bashi ya juya ya fice Yana kananun maganganu.
Fada sosai Ammi tayi min lokacin tace kada ta Kara Jin makamanciyar irin wannan magqnar a gidan Nan idan son yarinyar nake ayi magana ita Bata son kananun maganganu, na fada Mata babu wata soyayya a tsakaninmu da safna.
Abu kamar ya wuce da dare saiga Kira daga Abbie a waya naje Yana nemana.

AUREN HUCE HAUSHI

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateenah

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Page 92.






_______Ba bata lokaci na shigo mota ni da Abubakar muka nufo gidan ban shiga dakin kai tsaye ba tunda naga kusan takalman mutum biyar, ina nan tsaye saiga uncle mustapha ya fito yana waya saida ya gama ya karaso inda nake tsaye yake tambayata meya farau tsakanina da safna ban rufe masa komai ba na fada masa duk abinda ya faru, girgiza kai yayi kawai cikin bacin rai yace na koma kawai ba saina shiga ba, haka na juya ba musu na nufi mota muka fice daga gidan, ni dai bansan yanda suka kaya ba tun daga lokacin wata magana bata kara tashi ba amma na janyewa safna sosai sai abinda baza'a rasa ba, amma dai ban fasa yi mata hidima ba duk abinda zanyiwa su yaran gidan babu bambanci da ita wani abun ma sai nayi mata ban yiwa su Batool ba tunda Aunty sameera samunta bai kaina su Ammi ba tunda suna business sosai ita da momin kano.
Wani sabon salon da safna ta dauko kuma na zuwa part dinmu wai zatayi min gyara ko kuma ta dafa abinda tasan shine favourite dina ta dauko ta kawo min, nayi nayi ta bari amma saita ringa min magiya akan ita bada wata manufa ba takeyi, wannan yawan shige min din da tajeyi saiya kara mana shakuwa da kusanci sosai har ya kasance wata rana Dana dawo da dare na sameta tana barci a dakina sai abin ya daure min kai na juya na futa daga dakin na shiga part din Abbie na sameshi shida uncle mustapha saboda tare muka shigo gidan, kiransa nayi muka fito tare kafin na kaiga yi masa bayanin komai uncle saminu ya nufomu afujajan yana fadain su dai an haifo musu masifa a cikin zuri'a daman duk namiji mai aure aure hakance ke faruwa to azo aga ga yarinya can a dakina na gama lalata da ita.
Wani wawan Mari uncle mustapha ya sauke masa yana fadin ban taba sanin kai mahassadi bane kuma masharranci sai Yau wallahi ka guji Fushun ubangiji a kanka yaushe ka zama haka haba ka rasa Wanda zaka ringa jifa da qazafin Zina sai dan zumunka kabar jaki kana dukan taiki, me yaron nan ne ya tsare maka? kullum idanunka da bakinka basa nufin alkhairi a kansa, to ka sake wata dabarar wannan batayi ba tun nagariba muke tare dashi a mabera sai yanzu muka rabu ya nufi nasu gurin Nina na shigo kiran da Alhajin yake mini,ko maganar bamu fara ba ya shigo ya kirani kafin ya kaiga fada min dalilin kiran kazo kana yiwa mutane shirme da girmanka da komai to kaddara ma abinda kake fadar gaskiya ne bazaka iya daukar matakin da saidai a wayi gari a ga ka dauka ba,amma ka zama jakadan yada munafurci da son hada husuma ka yiwa kanka fada wannan ba rayuwa bace,ka bawa shedan dama yana walagigi da kai haba meka nema ka rasa da har samun dan cikinka ze tsone maka idanu ne ayeh?.
Tunda uncle ya shara masa Mari ya dafe kunci bai kara dago da Kansa ba, bai kuma kara tofa wata ba yayi min wani kallon qasqanci yayi gaba, tsaki uncle mustaphan yayi yana fadin wahalallan banza Wanda hassada ke dawainiya dashi, gurina ya juyo yana fadin kayi hakuri Mahmud kaji babu wani Abu na batanci daze sameka in sha Allah, lokacin na fada masa safna Dana gani tana barci a bedroom dina, yayi mamaki kawai da gaske tare mukaje amma abun mamaki bata dakin ko alamar mutum ya kwanta a gadon babu, dan murmushi yayi kawai ya juya yana fadin take care.
Wallahi a Daren banyi barcin kirki ba saboda damuwa na rasa mena tsarewa uncle saminu ne yake bibiyata da irin wannan Abu na bacin suna? Sai kuma zargin da hadin bakin wani ake min wannan bita kullin.
Naso na fadawa Ammi amma saina share, amma naje har part din Aunty sameer, tana ganina ta tarbeni da murnarta asual muka gaisa kafin nayi korafin abinda ya kawoni Auntyn ta rigani da fadin kasan kuwa jiya mutuniyar a dakinka barci ya dauketa tana jiranka wai tayi maka coconut drink ta zauna zaman jiranka saida naga shirun tayi yawa na tura safara'u yarinyar da take min aiki ita ta taso ta, ai kuwa nayi mata fada sosai irin haka ai sai zargin wani Abu ya shiga dan haka nace ta saina shiga part din tunda duk maza ne, wallahi precious duk saita daureni da jijiyoyin jikina na rasa abin fada haka nan na fito daga part din nata.
A cikin satin tafiya ta samemu nida sameer muka tafi, a lokacin shares na saya a manyan kamfanin motocin duniya na zuba large share sosai a lokacin ne na canzawa kannena mata sabbin mitoci abinda ya ruda da yawa daga yara mata na family din mu 'ya'yan da iyayen sukayo min caaaa da kowa burinta ace muna tare da ita sai kuma safna ta fara fuskantar yan hamayya daga cikin dangin saboda ta saje da yaran gidan babu bambanci.
Lokacin da muka dawo ne aka fara magabar bikin Gambon mu Khadija wadda ke Germany.
Aishat ce ta bani bill na duk abinda suke bukata ni kuma na bawa sameer nace yaji dasu, sun kace raini a bikin nan dan komai unique Aishat ta sawo musu a Dubai da sukaje tunda dai kin ganta 'yar gayu ce ta bugawa a jarida kuma duk abinda ta sawo babu bambanci tare da safna tayo shi hatta da gold na mahakatan kudi saida aka sawo da ita.
A wannan bikin ne idanun safna suka bude fiye da dah, ta zama babbar yarinya tayi sabbin kawaye tunda ta shigo gari ga motor ta alfarma tana shiga ga suturu na kece raina ga 'ya'yan banki basa mata wahala.
A cikin wata hudu tayi wani irin fice a sokoto sai kuma lamarin ya zama marar tsabta ta shiga sabgar samari 'ya'yan Hutu, koda yaushe bata zaman gida ga yawan kawo samari gida barkatai, sabanin yaran gidan,dana samu Ammi da maganar ta takamin burki tace babu ruwana ai mai gidan da sauran yayuna suna gani, haka na zuba ido ina kallo amma bana jin dadin abun ko banza ina kaunar safn tunda zuciya tana son mai kyautata mata,amma dole na dauke idanuna nayi kamar bana gani mataki daya na dauka kawai na saina daina shiga sabgarta na daina tura mata kudin da nake tura mata special na daina mata komai hatta da tsaraba idan nayi tafiya na Dawo wadda sameer ke assasa ayowa yaran na fada masa a daina yi da ita, abun saiya dameta ya tada mata hankali duk yanda tasan zatayi mu hadu ma nayi blocking dinta.
Previous Ashe wannan matakin shine ze zaman mafarin faruwar Marsalar shine zaren da aka kulla kaddarar tawa dashi. Ashe shine sanadin da za'a samu sabani mai girma Wanda yasa mahaifiyata barin gidan aurenta na tsawon watanni ya dagula rayuka da yawa ya kawo sanadin da aure ya mutu murus.

AUREN HUCE HAUSHI_*

_AISHAT ISAH MUSAH_

Maman Fateemah

Da sunan Allah mai Rahama Mai jinqai salati da Daukaka da Aminci su tabbata ga shugaban mu Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w.

Page 93.


_____ Precious wato Ranar wata talata 1/6 ranar da ta Zama baqar Rana a gareni da duk wani Mai kaunata, ranar da aka sak'a zaren mummunar kaddarata ranar data rikita Mana zaman lafiya ta Zama ranar da wani ko wasu suka dagula lissafin mahaifina ya Zama sai yanda akayi da shi dama duk wani Mai fada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login