Showing 171001 words to 174000 words out of 280244 words

Chapter 58 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1056

yaga wannan na tsayen ba Mahmud dinsu bane, Dan totally ya canza a idanunsa Bai gaskata shi bane Saida yayi magana lokacin da hadiman gidan ke kwasar gaisuwa.
A gurguje yake amsawa ya nufi bangaren da baba malam din ke ciki,duuuu suka bishi a baya, Koda Wasa Mahmud be yarda sun hada Ido da Habib ba.
Lokacin da suka shiga Malam ya farka Yana sallah, Sauran hadiman juyawa sukayi suka koma dakin ya rage daga su Mahmud sai nurses din da suke kula da shi. Cikin girmamawa suka gaishe da Su Mahmud din.
Saida Baba malam ya shafa Addu'oinsa sannan ya dubi gefen dasu Mahmud ke tsaye, ganin ya idar da sallar yasa Mahmud matsawa kusa dashi Yana murmushi, shima Baba malam din murmushin karfin Hali yake mayar Masa, gefen gadon ya zauna kusa dashi sosai ya riko hannunsa.
"Sannu Baba malam, ya jikin naka?".
"Masha Allah. Alhamdulillahi jiki da sauki kam, Allah yayi Albarka".
"Amin ya Rabbi.Allah ya baka lafiya gobe karfe shida da rabi na safe zamu tafi in Sha Allah".
Dan Jim malam din yayi kafin yace.
"Zuwa Ina Kuma mahmudu?"
Sameer ne ya matso Yana gaishe da baba malam din sannan yayi masa bayanin halin da ake ciki.
Shiru yayi Basu yi zato ba sai ganin hawaye sukayi yana bin gefen idon Baba malam.
Cikin rudewa Mahmud da su Habib suka shiga tambayarsa.
Menene? Ina yake Masa ciwo? Har Daya daga cikin nurses din ya Ciro waya ze Kira doctor Mahmud ya daga Masa hannu alamun ya jira.

"Babu komai, me zance muku yaran Nan Ubangiji yayi Albarka, ya biyaku da Aljanna madaukakiya"
"Allahumma Amin,Allah ya baka lafiya".
Daga nan yaja Bakinsa yayi shiru, Suma babu Wanda ya Kara cewa komai.
Key din motar Sameer ya mikawa Abubakar yace.
"kuje ku shigo da Kaya".
Nurses din Sameer ne ya tambayi nurses din ko akwai abinda suke bukata? Sukace masu babu duk abinda ake bukata daga Nan zuwa safe akwai shi.

Ledoji ne manya suka shigo dasu, da Ido baba malam ya bisu kawai har suka aje, shi tun ganin gidan da aka kawo shi da irin yanda aka dauko Masa manyan likitoci suka zo suka zauna zaman jiran zuwansa da irin yanda yaji Wani Yana fadiwa abokin aikinsa yana Abuja DANGE ya katse Masa tafiyarsa dole ya dawo duba patient dinsa, ga ma'aikatan jinya an aje su duba shi,yasan abun bana Wasa bane, da abinda Allah s.w.a ke nufi da kawo wannan yaron cikin rayuwarsa ya Dade Yana mamakin halayyarsa da yanda yake mu'mala da jama'a zuwan gurin tamkar kofar arziki aka bude musu taimako da tallafi Kota ina, a she ubangiji ya sallad'o wata kaddarar da tafi karfin tunaninsa shi wannan yaron ze zaman sanadin tallafawa rayuwarsa, Hamdala kadai ta kamace shi, a zuciyarsa ya dunga maimaita ta, ya Kara girmama girman ubangiji, wato duk abinda Allah s w.a yayi akwai hikima a cikinsa sai wani abun ya faru kasan wani connection din yafi gaban karamin tunanin mutum.

Mahmud Bai bar gurin Baba malam ba Saida ya matsa din yaci Naman kazo yasha fruits sosai, misalin goma da rabi suka fice daga gidan Muhmud be koma Nasarawa ba Nan Bawo road Sameer ya ajeshi, bayan sameer ya wuce ya dade Yana ta kokarin ya samun visa zahra abin yaci tura, duk Wanda yake tunanin zasuyi masa aikin duk ya rasa su, abin ya bashi matukar mamaki Dan wannan shine first time da irin haka ta faru dashi, dole ya hakura ya sakawa sarautar Allah Ido besan abinda Allah yake nufi da Hana samuwar visar ta taba.
Su Habib ma sunso kwana a gurin Baba malam, Anna kememe nurses din suka Hana sukace aikin da aka biyasu makudan kudi suyi kenan,idan yallabai yaji labarin sun Kwana a Nan za'a samu matsala dan ba karamin warning aka kada musu ba, dole suka hakura suka wuce nasu masauki daura da Inda Baba malam din yake.
Gida ne na Alfarma tamkar gidan want gwamnan komai na Jin dadin rayuwa an tana deshi hatta da suturar sakawa gasu Nan sabbi sai da ka saka Wanda yayi dai dai da kai, Abinci sai Wanda kake bukata za'a kawo maka tunda suka sauka ake hidima dasu Baga Abinci ba Baga snacks ba Baga drinks ba, komai enough gashi nan, gurin malam sule suka koma sukaci gaba da Hira a Nan Habib yaji shima Ashe Abubakar Dan Sokoto ne.
Saida sukayi Shirin kwanciya sannan Habib ya kalli Abubakar.
"Dan Allah ka fada min gaskiya Daman kasan Mahmud ne kafin kaddarar data kawo shi nan Azare? Naji Mai gadi Yana maka wasu maganganun da suka sakani a duhu?".
Dan Jim yayi Yana nazarin maganar Habib, kafin yace.
"kayi hakuri nayi maka Alkawarin fada maka Amma Dan Allah ba yanzu ba".
Jinjina Kai kawai Habib yayi, alamar gamsuwa, Bai Kara cewa komai ba ya kwanta zuciyarsa fal tambayoyin rab'ab'a wanda bashi da amsarsu.


Mama tun Rana da tayi muguwar kwarewa har dare tana fama da kanta duk abinda ya kamata, Tasha ta Sha Amma dai Abun yaki Zama dai faint Dan ji take wani Abu ya tsaya Mata a kirji yaki wucewa, da kyar wurin goma na dare ta samu number Aunty Larai ta kirata cikin nuna damuwa ta zayyane Mata komai da yanda taga Mahmud, da zargin da take yiwa Abba akan Yana da masaniyar ko waye yaron har canzawa da Zahra da Mai aikinsu zilai Saida ta fada mata, bala'i Aunty Larai ta Fara tana zuga Mama dole tayi Abun da zata wargaza rayuwar yarinyar gaba Daya tunda Asabe ta nunafrceta ta gudu da wadannan magungunan da aka kawo Wanda da anyi yanda akace da yanzu ba wannan labarin akeyi ba, kudi masu yawa Mama ta turawa Aunty Larai tace tayi duk abina ya kamata, sun Dade suna tattaunawa kafin suyi sallama da alkawarin da safe zata bazama gurin arnan Kan Dutse.
Aje wayar Mama tayi tana fadin.
"Wallahi Asma'u keda wannan Fara farar yarinyar kun shiga uku, kuda kwanciyar hankali kunyi ban Kwana Ina Raye bazanga bakin ciki ba, wannan yaron ace shine mijin zahra? Wato a baya kallon tsoro nayi Masa kenan,wallahi sai kwanciyar hankali ta gagare ku, Dan karya malam na Bande ze want ce bega rabuwa ba a cikin aurensu Naga kashin awaki saina rabasu yanda naji niyya saina tagayyara rauwar Zahra babu fashi Dan halak ka fasa".
Ta debo wata ashariya ta lafta tana kwafa duk idanunta sun firfito saboda bacin Rai ga azabar data Sha ta kwarewa.



* * * * *

Tun bayan tafiyar magaji zahra da Aunty zilai suka shiga kitchen sukayi simple girki, Aunty zilai ce ta mikawa Naseer,Bayan ta dawo ne take fadin.

"Uwar dakina wato lamarin yallabai Yana bani mamaki gashi dai yaro Karami amma fa Naga alamar kowa a Karkashinsa yake,dan oga Sameer na fuskanci a nan ne yake oga amma a waje yaron oga ne". Ta fada tana dariya.
Dan yatsina fuska zahra tayi.
"Nifa na aje lamarin su a gefe,ita dai ai karya ai fure take Bata 'ya'ya, ni meye nawa tunda Kika min fada a kano na sakawa Raina salama na iya kaina tunda Naga abun nasu ba Mai karewa bane, Kullum da wani sabon salon da Zaki gani a gurinsu basai mitum ya Zuba musu idanu ba Randa suka shirya magantuwa sai su magantu".
"Gaskiya dai kam, Nima da farko na shiga razani lokacin da aka Kaimu Kano Amma Dana ji bayani daga bakin Iya Rahane saina fashimci duk Inda mijinki ya fito ba daga Karamin gida ya fito ba,Kuma naji kishin-kishin din bacin Rai ne ya fito dashi Dan iya ta fada min sai dai tace Bata San takamaimai menene ba itama tsintar zancen tayi mommy da oga Sameer sunayi ta shigo ta kofar kitchen ta baya, abunda nakeso dake uwar dakina duk Inda rayuwa ta kaiki ki Zama Mai takatsantsan da mutane yanda naji labarin nasa dai sai kin nutsu sosai Dan na fuskanci mijin naki ko a cikin dangain na daban ne shi gaskiya, bare yanda naji iya Rahane na fada sai Wanda ya gani, Kinga dai yanda akayi ta samun akasi akan Aurenki Kuma Billahillazi asirai ne aka dunga yi nasan Allah ne ya nunawa ko waye ma iyakarsa ya Baki miji Daya da daya, wallahi a gaban idona anyi dariya an Kara akan an aura Miki Almajir Qolo Wanda Bai aje ba Bai bada ajiya ba, ance sai aga ta taqamar kyau an Kare a Almajiri mane min tsaba".
Ta fada cikin nuna bacin Rai.
"Kai haba Aunty zilai meye na tuna abinda ze Bata Miki Rai, ba gashi ya Zama fast ba, Ni nasan mutum be Isa yayi min abinda babu Shi a cikin kaddarar da Allah s.w.a ya rubuta min ba. Daman haka take kaddarar sai dai a jahilci irin na mutum yaga abinda yayi ne yayi tasiri,sun manta Alkawarin Allah baya canzawa". Kai Aunty zilai ta jinjina tana fadin.
"Wannan gaskiya ne Allah ya Kara Miki tawakkali da qarfin imani ya doraki a Kan mak'iya da mahassada, yasa wata Rana ki Zamar musu kadangaren bakin tulu a barka ka bara ruwa a karka a Kar tulu, Allah ka nuna min ranar da karya zata Kare gaskiya tayi halinta in Sha Allahu sai kin zamar musu ciwon Ido ba yanda za'ayi dake sai hakuri, in Sha sai munga karshe masu hassada da muna furci".
"Allahumma Amin".
Sun Dade suna hira kafin zahra ta nunawa Aunty zilai wani daki a cikin parlour na biyu daga cikin corridor da yake fitar da mutum waje, daki ne comfortable yaji Turkish bed Mai shegen kyau yasha ubansun bedsheet sai sanyi A/C da kamshin roomfreshner dake tashi, sallama zahra tayi Mata ta wuce nata bedroom din.
Wanka tayi ta Saka sleeping dress tayi shafa'i da wutiri sannan ta kwanta, lamban tayi a gado, duk kewarsa ta dameta Amma tana Jin nauyin kiransa a wannan lokacin rabonsu da waya tunda ya kirata yace Yana Dutse, da magariba tayi ta try Bata same shi ba tasan yanayi network duk da tayi marking da wuya a Kira wayarsa Bata shiga ba.
Data ta bude tana duba sakonnin da suka shigo Mata ba tunda ta mayar da master layinta Daya Bata dazu.
Reply din sajida ta Fara dubawa, saina Aunty Rukayya data tura mata sallama ta fada Mata itace, sakon karin jajanta rashin lafiyar malam ta turo mata har tana tsokanar ta akan meya Hana balarabiya taje India ta Sami ruwa biyu tunda kyau ne ke dukan kyau, Emoji na rufe Ido da hannu ta tura Mata.
Ba zato kawai kiransa video call ya shigo, wani Abu taji ya tsirga Mata tsikar jikinta ta tashi, data tuno moment dinsu na dazu.
Dauka tayi tana lumshe sexy eyes dinta.
"My previoussss.."
Ya fada a hankali, Yana bin fuskarta da kallo gani yayi Kamar Kara Mata kyau akeyi matukar zeyi some hours Bai ganta ba.
Cikin nata salon ta bude idanunta dake Rita Masa lissafi ta saukesu a Kan nasa.
"Yesss.. meu Amorrrr..."
"Ya Salammmm.."
Ya furta a hankali tamkar Mai tsoron wani yaji abinda yake fada, da gaske yarinyar Nan so take nayi ta sakin layi a gabanta.
"Cikin muryar data saka zahra a cikin wani yanayi yace.
"Inaga na fasa tafiyar Nan har sai kin samu visa Kona tafi akwai damuwa gaskiya".
Tashi zaune tana cire blanket daga jikinta tunda tana jingine da pillow ne a jikin face din gadon, rigar irin transparent din nan ce Mai siririn hannu baqa sai ta Kara haskaka fatar Qirjinta sosai Nan da Nan ya nemi nutsuwarsa ya rasa.
Cikin shagwabar data Fara zamar Mata jiki ta Fara fadin.
"Haba dai Dan Allah me Amor... kuje kawai babu Dadi Baba malam ne fa ba Wani ba,! Idan ma kazo to me zanyi maka sai dai fa ka raba hankalinka biyu, Amma idan kuka tafi zakafi samun nutsuwar data Kamata, kaji plsss.. Dan Allah".
Mak'e kafada yayi tamkar yaron goye Yana Mata wani kallon Daya sakata rufe idonta dole.
"Bude idonki bana son kinibibi, Kamar ba ke bace...... Bari dai nayi shiru kada na kirawowa kaina Ruwa ko?".

Luuuu tayi da Idanu, sai Kuma ta hura Masa iskar bakinta saitin bakinsa Kamar Yana kusa da ita.
"Ki jirani komai dare dole nazo na biya wannan bashin".
A razane ta wartsake tana marairaice fuska, tana Dan jijjiga jikinta a hankali jikin Yana wani irin shaking a hankali".
"Dan girman Allah da darajar Manzon Allah kayi zaman ka wallahi Zan nemi visa da kaina Zan biyo ka".
"It's too late, kiyi Shirin tarbar bako da safinsa".
Kafin ta Kara rokonsa ya kashe wayar.

_AUREN HUCE HAUSHI_

08055362975
____

My WhatsApp number
09061432330

*MAMAN FATEEMAH*




Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da daukaka da Aminci su tabbata ga shugaban mu Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w

Allah ka jikan iyayen mu da sauran musulmin da suka rigamu gidan gaskiya.

Page 62.

_______Karfe shida dot mahmud suka shiga Malam Aminu Kano international airport shida safwan Daya kawo shi, kafin su Kai ga gyara parking motar su Baba malam ta shigo wadda zayyan ya tukosu, kafin Safwan ya fito tuni Mahmud ya bude ya fice da sauri cikin wasu hadaddun suit army green sai wani wani sanyi kamshi yake fitarwa idonsa sanye da siririn eyeglasses Mai haske sosai abinda wani be taba gani a Azare ba kenan ya fito a mahmud dinsa, cikakken Dan boko da ganinsa kasan yes ba karya.
Wadannan nurses din ne tare dasu Habib suka kamo gadon daukar marasa lafiya suka fito da Baba malam din. Gurinsu ya Karasa Yana fadin.
" Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
Sallamar suka amsa Masa a tare, gaban gadon ya matsa yana fadin.
"Barka da Asuba Baba yaka kwana?".
"Jiki da sauki cikin Rahamar Allah, sannu da kokari kaji mahmudu Allah ya baka ya saka maka da Alkhairi".
"Allahumma Amin"
Ya fada sannan ya amsa gausuwar dasu Abubakar ke Masa, sukayi gaba shi Kuma ya koma mota ya zauna yana Kiran wayar zahra. A Nan Sameer ya same shi tare da abincin break nasu Habib.
A cikin reception bangaren vip aka shiga da Baba malam, lokacin da Mahmud ya shigo su Habib suna gurin screening, gurin Baba malam suka shiga da Sameer din ya duba shi har lokaci yaran Nan nurses suna tare dashi.
Ma'aikatan jirginne suka shigo suka fita da Baba malam, Sameer ne ze koma da yaran ya sallamesu duk da tun jiyan sunji alert me nauyi a account dinsu.
Har cikin jirgi Sameer ya raka Mahmud ya Kara duba Baba malam yayi Masa fatan Alkhairi tare da fada Masa Shima ze shigo Daya Gama abinda yake yi.
A ciki ma vip Mahmud da Baba malam suke yayin da Abubakar da Habib suke a cikin jama'a.
Tunda suka tashi Mahmud ya bude Qur'an din cikin wayarsa Yana karatu lokaci bayan lokaci Yana duba Baba malam tare da tambayarsa ko da abinda yake so? abincin da ake ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????rabawa ma cewa yayi baze ci ba.
Bangaren su Abubakar,Habib kam ba baka sai kunne domin an shayar dashi mamaki ba kadan ba, yanda ya fuskanta Mahmud dai uban gidan su oga Sameer ne harda Abubakar ma tunda a airport din Nan yaga zahiri ba Wani boye-boye a ogansa ya fito sak, hatta ma'aikatan wani irin girma suke bashi.
'yar tv jikin seat din kujerar gabansa Habib ya kunne Yana ganin location din da jirgin kebi, sun kwashe awa bakwai da minti hamsin da biyu a sama kafin suyi lending a Ethiopian, an fito da Baba malam ma ya huta yaci Abinci yayi sallah, Habib sai kallon Abubakar da Mahmud yake mamaki na neman kashe shi da ransa, rayuwarsu a Azare yake tunawa duk iya kwakwar mutum baze taba sanin da wata sanayya a tsakaninsu ba ballantana kaga wani Abu Daya danganci yaro da uban gida.
Shi kuwa gogan yayi fuska Kamar be gane kallon da Habib ke Masa ba.
Awarsu Daya da minti goma suka sake tashi, jirginsu sai karfe shida da minti arba'in da biyar ya Sauka a INDIRI GANDI INTERNATIONAL AIRPORT new Delhi India.
Suna fitowa suka iske ambulance din Max na jiran saukarsu Dan tun tasowarsu suka Fara communication da Sameer, sai a Ethiopia ne sukayi da Mahmud, ba karamin mamaki mahmud ya bawa Habib ba a lokacin Jin yana yaran indianci tamkar harshen tsohuwarsa.
Ma'aikatansu suka shigar dashi cikin, Mahmud ne ya bisu, yayin da yace Abubakar ya jira Mr Salahuddeen zezo ya tafi dasu ya Kai Habib gida ya huta.
Shi dai Habib yaga abinda ya girmi nasa wayon nesa ba kusa ba.
Saida motar Asibitin ta bacewa ganinsu sannan Abubakar ya Dan daki kafadar Habib kadan yana fadin.
"Don't mind, in Sha Allah Baba malam da kafarsa ze dawo nan,shi yasa oga ya dage azo nan din yasan suna da qualified doctors, kada ka damu yanzu muje gida ka huta tunda baka Saba da irin wannan doguwar tafiyar ta kusan twelve hours ba".
"Nifa ba wannan bane damuwata ba yanda naganku da Mahmud daga jiya zuwa yau shi yafi bani mamaki abin Kamar a Shirin film".
Dariya yayi Yana fadin.
" Share kawai lalura fa ta gitta ai babu maganar wani boye-boye Kuma kasan yanda oga yake son malam kuwa?".

"Na sani Mana tunda tare muke dashi, kawai dai abin ne da mamaki yanda ko kadan babu wata kafa da Wani ze fashimci hakan da kuka bada".
Dariya kawai Abubakar yayi ya basar da maganar, Shima Habib shiru yayi Bai sake cewa komai ba, Basu jima a gurin ba kira ya shigo wayar Abubakar, picking yayi ya Fara magana cikin harshen turanci Yana yiwa Mai Kiran kwatancen ta Inda suke.
Shi dai Habib lamarin naso ya Fara bashi tsoro, gaba Daya sun juye masa daga asalin yanda ya sansu sun koma Masa wasu na daban.
Suna gurin Mr Salahuddeen ya karaso, musulmi ne mutumin Pakistan, da sauri ya fito ya rugune Abubakar Yana fadin Daman Yana Nan lafiya ya yiwa india yaji tunda boss baya zuwa Shima ya dauke kafa. Dariya sukayi Abubakar ya gabatar Masa da Habib a matsayin Dan uwan Mahmud, suka gaisa da fara'a sosai a fuskarsa, Abubakar ya gabatar da Mr salahuddeen a matsayin drivern Mahmud ne duk lokacin Daya shigo kasar Kuma
kamfaninsa na jewelry a Nan kasar.
Har sukaje gidan da zasu Sauka Abubakar suna Hira da Mr Salahuddeen yayin da Habib ya Zama Dan kallo.

Su Mahmud suna shiga Asibitin direct suka wuce zuwa vip ward inda Sameer yayi musu booking kenan, sai suka da gyara baba malam tsab sannan suka wuce suna fadawa Mahmud yanzu masu bashi Abinci zasuzo.
Kana ganin baba malam kasan ya jigatu ba kadan ba, Mai lafiya ma Yana gajiya da Zama ballantana Wanda yake a kwance, sallah suka rama kafin masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login