Showing 147001 words to 150000 words out of 280244 words

Chapter 50 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1053

Mai mashimmanci ne, after dress din ta Dora ta gyara rolling din suka nufo kasa sai kallonsa take kasa kasa Dan ba karya yayi wata irin haduwa sak matashi Dan hutu ajin farko, duk Wanda ya kalleshi Saiya kara, Sumar Nan Tasha gyara tayi kwance sai walkiya takeyi.
Motarta ta gani a kofar parlourn, da alama da ita zasu fita duk da taga bakin motoci a gidan, da kansa ya bude Mata ta shiga ta zauna.
Gurin malam Musa yaje sukayi maganar sannan ya dawo ya shiga motar ya tuqa suka fice daga gidan, malam musa na fadin A dawo lafiya yallabai.
Direct hadejia road ya nufa suna tafe yana Mata bayanin abubuwa da guraren da Bata sani ba.

Be tsaya a ko Ina ba sai welcare, tare suka shiga bangaren magunguna suka nufa wani magani ya dauko.
A bangaren kayan kwalam da makwalashe lodarsau yasa tayi kamar ba gobe, yaje ya Basu Kati suka cire kudinsu.
Aka Kai musu mota, ta dauka gida zasu koma sai taga sun Kara gaba, Ring road suka shiga basuyi nisa ba Sosai taga sun shiga wata kwana bata tantance Ina sukazo ba Saida taga sign board din Asibiti M.D.S.
Abin ya Bata mamaki to me zasuyi a Asibiti?. A mota ya barta ya shiga Cikin be Dade ba ya dawo Yana fada Mata ta fito tazo, ba musu ta fito suka jera wasu majiyyata sai kwllonsu suke, ofis din Dr. Suka shiga.
Mutum me fara'a ya karbesu hannu bibiyu suka gaisa da Mahmud sosai, da alamar ba wannan ne haduwar su ta farko ba, da sanayya.
Zahra ma ta gaishe da likintan. Sannan suka zauna, Mahmud bayanin Dan abinda ya sani yayi masa.
Tambayoyi Dr din ya Fara jerawa zahra daga karshe shima yace Bari ayi hoto da wasu test a Nan ze tabbatar da abinda yeke tunani.

A Nan ya sake Mata scanning da tests na jini.
Zahra tayi mamaki kwarai da sukazo Nan din itafa ta dauka be damu da matsalarta ba tunda taga be Kara Mata maganar ciwon ba tun bayan Wanda suka tattauna.
Suna zaune wata nurse ta shigo da result din da sakamakon test din jinin ta bawa likitan tayi gaba abinta, ya dauki lokaci Yana nazarin abin Wanda har Mahmud din ya tamabaye shi ko matsalar tayi zafi ne?
Kai ya girgiza masa kafin ya aje takardar dake hannunsa ya kalli Mahmud din Yana fadin.
"Tabbas da matsalar fibroid a mahaifarta, sai dai wani abun mamaki Dana gani ya Fara narkewa sakamakon wani Abu da take Sha harma jinin jikinta yake wankewa, Dan haka ba maganar aiki a yanzu dai gaskiya mu jira zuwa next month idan lokacin period din yayi a Nan zamu tantance Yana Nan Yana functioning ko Yayi dissolving, amma Zan Dan Kara mata da wasu antibiotics din Wanda zasu taimawa jikinta in Sha Allah".
"Ok Dr nagode kwarai".
Tambaya likitan ya jefowa zahrar.
"Ko kina amfani da irin maganin Islamic chemist ko na gargajiya haka? Ma'ana kike Sha da sunan magani ko kuma haka Nan amma yayi miki maganin wannan babbar matsalar?".
Dan Jim tayi tana tunanin to ko abinda Hajiyar makwarari ta Bata ne ya Fara aiki? Hannunta Mahmud da Dan murza kadan daga kasa ta dago ta kalle shi, Kai ya gyada Mata alamar tace wani Abu.
"Eh Dr kakata ce ta bani magani lokacin da aka gano matsalar shine nake amfani dashi".
Biron dake hannunsa ya aje a Kan table din ya gyara zama

"Kika ce kakarki ta Baki magani da aka gano matsalar?".
Kai ta gyada masa alamar tabbatarwa.
"Anyway ba damuwa Bari mu gani daga Nan zuwa ending this month din Nan idan munga da progress shi kenan,idan Kuma Yana nan zamuyi surgery mu cire shi kawai, Allah ma yasa big brother dinki ya yi tunanin zuwa a duba da wuri irin wannan ba'a fiye ganewa ba sai anyiwa yarinya aure anga Bata haihu ba sannan ake bincike a gano meye matsalar".
"Ok mun gode doctor, kome ke nan zamu dawo zuwa next month din in Sha Allah".
Mahmud ya fada yana mikawa Dr din hannu.
Tare suka fito da Dr din a haraba sukayi sallama shi ya shiga ciki ward su Kuma suka fice daga Asibitin.

Sun dauki titin da ze fitar dasu HOTORO NNPC ne wayar Mahmud tayi K'ara alamar shigowar massage.
Ciro ta yayi ya duba, gefen titi ya gangara yayi parking.
Sannan yayi dialing din number da akayi Masa text din da ita, ba Bata lokaci daga can aka daga.
"Yi min cikakken bayani".
Abinda Mahmud din ya fada kenan, daga can Daya bangaren aka Fara Masa bayani sai jinjina Kai kawai take yi har ya aka gama fada masa duk abinda ya nema a fada masan.
"Kana jina Zan fadawa Bilyaminu ya kawota Nan Kano can sallari za'a ajeta zanzo in Sha Allah ayi Mata duk abinda ya kamata".
Ya yanke kiran, ita dai Zahra ido ne nata, wani zance yakeyi Wanda ta kasa fahimta, wacece me za'a kawota tayi shi me zeyi idan yaje gidan da yace a kaita? Nan da Nan taji faduwar gaba kada fa ko Yana harkar mata, taga ba sauki idan ya rikice, ko zuwa zeyi yayi... Da sauri ta girgaiza Kai tana runtse Ido.
"Ya akayi ne 'yan Mata naga kin shiga dogon tunani?".
Kankance idanu tayi tana Masa wani kallo na tuhuma.
"Wa kenan za'a kawo maka". Wata dariyar rainin wayo yayi Yana kallonta kasa - kasa.
"Mace Mana, tunda kin hanani ai gara na nemi mafaka inda Zan rage zafi, ko so kike na kasa amfanuwa, idan har ban samu nutsuwa ba saina kwanta gadon Asibiti, kinsan ya nakeji kuwa?".
Ya wani Yi mik'a Yana kokarin janyota jikinsa.
Da sauri tayi baya tana fadin.
"Allah ya tsari gatari da Saran shuka,ni me Zan baka ai ban cika mace ba, Daman ni me zakayi Dani da aka k'ak'aba maka sadaka bani da wata qima ko daraja a gurinka tunda bakasan darajata ba, da bakinka fa kace an fada maka duk Wanda suka nemi aurena sai sun Gama Dani suke barina kaga kana min kallon fasiqa Mai ma'amala da maza kenan me ze Hana ka Kira a kawo maka mace a gabana, wallahi tallahi bazan zauna da fasiqi ba sai dai ka rabu dani wallahi ban taba kebancewa da wani namiji ba a duniyar nan bayan Kai, bazaka shafa min wahala ba ka gudu ka barni, tunda har gobe ba Wanda yasan daga ina kake, Kuma rayuwar garin Nan ai mun santa komai ma na haya ne, haka kawai ka cuceni ka gudu ka barni da Jangwam idan da gaskiya wa yake gudun asalinsa ai duk lalacewar gida yafi daji ka koma Mana idan ba fitsare gurin kayi ba da abin kunya ba ka gudo nan".
Tana kawowa Nan sai kuka, shi ikon Allah ya tsaya Yana kallo yanda ta zage tana tsula Masa rashin kunya wato Mata ba sauki gurin kishi, Dan murmushi yayi yana ayyana 'yar daru kawai.
Dauko ta yayi cak kamar 'yar baby ya kwantar da kujera ya sakata cikin jikinsa ya zagaye ta da hannunsa.
Tana ta mutsu-mutsun kwacewa Amma yayi Mata kyakykyawan riko.
"Mai maita min abinda kikace waye Dan iskan? Ni zaki kalli idona kina fada min abinda ranki ya Raya miki? Idan matan zanbi kin isa ki hanani ne, nace a kaita sallarin Kuma Billahillazi mace ce kuma gurinta zanje ko Zaki hana ne, an fada Miki ina sonki ne kunya da kawaici yasa na karba amma badan kinyi min ba, Kuma ki rubuta ki aje har abada bazan taba sakinki ba idan ma kinayi dan naji haushi na rabu dake ne ki sake dabara, Kuma dake zamuje can din na ajeki na shiga nayi abinda nakeso mu koma Kuma kiyi min wanka, gida Kuma eh abun kunya nayi na gudo nan, yarinya na yiwa ciki Dan haka ki shirya rike yarinyar da aka Haifa min nan gaba kadan".

AUREN HUCE HAUSHI.

Naman Fateemah.



Page 54.



...........Sun Kai kusan minti goma a haka, tana jikinsa a haka tayi kukanta Mai isarta, baris yayi da ita Yana Jin tana ajiyar zuciya, Shima da gaske ta tunzura Masa zuciya Wai "fasiqa"
kalma mafi Muni Daya tabaji daga bakinta, dole ta karbi hukunci Wanda ko Nan gaba ba zata Kara marmarin fada Masa makamanciyar irinta ba.
Sauke ta yayi daga jikinsa ya gyara kujerar ya tada motar, baiko Kara kallon inda take ba ta fisgeta da wani irin mahaukaciya gudu.
"Wayyo Allah Nan Dan Allah kada ka kashe mu, na shiga uku". Ta fasa masa kuka Dan da gaske ta tsorata da yanda ya saki motar.
Bai tanka Mata ba amma ya sassauta gudun, shiga Nan fita can taga sun shiga wata unguwa Mai karancin gine-gine duk tayi zuru-zuru da ita kofar wani katafaren gida ya tsaya ya Danna horn da karfi da gudu aka bude gate din ba wata wata ya Danna Kai cikin gidan.
A tsakiyar gidan ya Parker motar, wasu kartin maza ta gani sun nufo motar da sauri kusan su shida dukkansu majiya karfi, take jikin zahra ya dauki rawa, Yana kallonta ta gefen Ido yanda take mazari, Amma ya share ta.
Kofar ya bude dai dai lokacin da suka karaso suna kwasar gaisuwa.
"Sagir tana Ina?".
Mahmud ya fada Yana duban Wanda ya kira da sagir.
"Tana ciki yanzu ba dadewa bilya ya kawo ta".
"Ok.kuna iya tafiya Amma kafin Nan ku sako min little da barbar tsakar compund din nan. Yayi gaba abinsa ya nufi wata katafariyar kofar parlour.
Zahra tayi mutuwar zaune Dan gaba daya tsoro ya cika Mata zuciya ganin wannan mutanen kawai tasan ba abin arziki ake qullawa a gidan Nan ba, Wanda taga ya nufi wani guri can baya ya taho tare da wasu irin karnunka masu wani irin gashi a jikinsu bula bula dasu, wani irin kara Mai Kama da fito yayi musu suka Fara zagaye motar suna wani irin gurnani, wata mota hilux taga sun shiga sai mutum biyu suka Bari a gidan suka wuce.
Zahra idanunta na ganin karnukan na zagaya motar hantar cikinta ta Kama rawa, a duniya tana tsoron Kare bare wadannan data gani masu Kama da kura ai Bata San lokacin da jib'i ya rufeta ba duk da sanyin AC dake motar, wannan wane irin wulakanci ne yayi Mata Yana can Yana aikata masha'a ya sakar Mata karnuka wadanda zasu hanata fita ko Nan da can.
Daya daga cikin biyun da suka rage a gidan ne ya nufi cikin gidan ya Zama daga Zahra sai Wanda take tunanin Mai gadi ne sai Kuma masu gadinta Dan taga alama saboda ita aka kawo karnukan nan, Bata San lokacin da kuka ya kwace Mata ba tana fadin.
"Wayyo Allah! Abba kazo kaga yanda ake wulakantani karnuka ke gadina Kamar wata criminal".
Motsin kirki ta kasayi gani take kamar idan ta motsa zasu fasa glass din su shigo ciki, ba abin tashin hankali irin gurnanin da sukeyi.

**
Cikin takunsa na mazantaka ya shigo parlourn sai da yazo tsakiya yaja ya tsaya Yana karewa gurin kallo kamar yau ya Fara shigowa, ba motsin komai, da sassarfa ya Haye steps din da ze sada shi da dakunan barcin, kofa ta farko ya bude da karfi abinda ya sakata zabura kenan ta Dora hannu a ka jikinta ya dauki karkarwa tana fadin.
"Wallahi Allah sani akayi bani nake Mata wannan abun ba".
"Shiii! Kept quiet!".
Ya daka Mata tsawa, Yana kusanto inda ta takure a jikin katafaren gadon, kafa Daya ya Dora a Kan gadon dayar tana dire a kasa Yana Kare Mata kallo tun daga sama har kasa sai wani bashi yake tashi daga jikinta.
Sadda Kai tayi kasa tana tsuma.

Cikin izza da rashin son wargi ya bude bakinsa da kyar yace Mata.
"Meya hadaki da rayuwar iyalina? Meta tsare miki? Keda waye kuka saka rayuwarta gaba? Waya sakaki bibiyar lamarinta gurin kawo sakonnin mugun Abu? Waye ya sakaki jefo abinda Kika jefa a gidan ranar da Zayyan ya kamaki? Kada ki kuskura kiyi min karya duk da kin haifeni Zan nuna mini true colour din yanzun nan, sai kinyi Dana sanin sanin Wanda kikewa aiki wallahi Dan Allah sai nasa an wulakantaki".
Zayyan ne ya shigo.
"Sir akwai damuwa Naga hankalinta ya tashi kamar tana kuka, da alama tsoronsu takeji ko a mayar dasu ne?".
Wani banzan kallo ya watso masa.
"Sorry sir".
Ya fada Yana sadda Kai kasa.
Kuka ta fasa tana fadin "Dan Allah kayi min Rai yallabai wallahi bani nake Mata wadannan abubuwan ba, wallahi Hajiya Mama ce duk Aurenta da ake fasawa ma ita ce take yin asirin da ake fasawar saboda an fada Mata duk cikin yaran gidan Zahra tafi kowa sa'ar rayuwa,mijin da zata aura ba ita ba wani ma saiya huta a jikinta,uwa uba Kuma tafi duk yaran gidan kyau da cika irin ta Mata ga nasaba ta bangaren mahaifiyarta,ko rashin zuwan kakarta kasar Nan da hannun Hajiya mamar a ciki, abinda nakai na farko Wanda wannan ya karba, ta nuna Zayyan, Shima maganine a cikin turaren wutar Wanda akace idan ta turara ka shaki kamshin bazaka Kara Zama a Azaren ba har abada, zaka kuma manta da ita Zahrar sai dai kotu ta raba Auren, na ranar Nan Kuma wallahi bansan Kona meye ba tace daga Jos aka kawo Mata wayata ma babu caji har gida tazo ita da dureba ta aikeni naje Tasha na karbo ta fada min duk yanda zanyi ta bani duba hamsin tace ladar aikina ce, wallahi iya abinda na sani kenan, kayi min Rai wallahi na daina har abada ka rufa min asiri wallahi na baro mahaifiyata babu lafiya ni nake kula da ita, kudin da nake samu a gurinta dasu muke cin abinci na Kuma sayawa tsohuwa ta magani".
Ta fada tana yarfe gumi daga fuskarta duk da sanyin AC dake ratsa dakin.
Tsayuwarsa ya gyara Yana jinjina maganganunta a zuciyarsa, shi yana Jin chakwakiya kala kala Amma ta zahra ta bashi mamaki wannan wace irin kiyayya ce haka.
"Kinsan abinda yasa Zan kyaleki?"
Da saurinta ta girgaiza Kai.
"Saboda ke 'yar aike ce, shi Kuma jakada Bai taba laifi ba sai ke kin bada gudun mawa gurin cutar da marainiyar Allah Wadda bataji ba Bata gani ba, kunyi ta kokarin kada ta cimma abinda Allah ya hukunta a Kanta Ashe Taki kuke zubawa gonarta,ku Baku isa ku Hana Allah s.w.a ciki Alkawarinsa ba a Kanta, hassada ga Mai rabo Taki ce, Kuma dare ga Mai rabo hantsi ne, duk da ta auri Almajirin malam baku saurara Mata ba dole sai ta wulakanta ko? To Allah ya nuna muku Kaidin ku ba komai bane da sannu zaku girbi abinda kuka shuka, babu abinda zanyiwa Hajiya Mama taci darajar mijinta.Amma ke gargadi na farko Kuma na karshe da Zan Miki kada naji ko labarin ki a Azare duk ranar da naji labarin an ganki saina saka an batar dake har abada, ga Bilyaminu nan ze mayar dake kutattara ku nemi wani gurin ko arear Bauchi kada naji labarin an ganki, na bashi sako ze Baki idan dan talauci ne kika Zama jakadiyar yada barna to ki nemi sana'a ki Kuma tuba ga Allah Mai gafara ne Mai jinkai".

Wani kukan ne ya kwacewa Asabe Bata taba tunanin ze Zama me rangwame a gareta ba,duba da yanda Zayyan da bilyamu suka ringa surfa Mata Mari har Saida kumatunta suka Haye kamar ta kunsa biredi a ciki.
"Na gode! Nagode! Yallabai Allah ya saka maka da Alkhairi lallai ka cika mumini Mai imani ka saka sharri da Alkhairi in Sha Allah gobe zamu koma gida Zuru daman nina Kiya da innata tace mu koma mahaifarta Ina kwadayin abinda nake samu da Mama".


Bai Kara tofa ko kalma daya ba ya juya ya fice daga dakin Zayyan ya biyo shi a baya.
Wani bangaren ya nufa yayin da Zayyan yayi waje, har lokacin su barbar suna nasu aikin, sagir Zayyan ya kwalawa Kira ya taso daga bakin gate ya nufo shi.
"Dan Allah meyasa baka da lissafi ne Wai? Kasan wacece a motar Nan daka bawa karnukan ku umarnin nan?"

Motar ya kalla yana fadin.

"A'a ban sani ba".

Kwafa yayi to matar oga ce wallahi idan ta ganeka sai tayi maganinka, da alama wani abun tayi masa kasan boss ba sauki idan aka taba shi, kasan meye bani mamaki besa nayi bij-biji da wannan matar ba saima ma makudan kudi da ya bada a bata".
Ya fada Yana tsaki.

"Kai rabu da wannan muyi magana Mai mahimmanci. Dan Allah da gaske ne da ake fadin oga yayi aure? Wallahi na dauka duk shafta ce kawai".
"Matsa Nan, naka Wasa ne yanzu ka janye su salin alin ka tafi dasu gurinka yanda baze gane Kai ka janyesu sai yayi zaton sun gaji ne suka zo gurinka".
"Haka za'ayi Bari ka gani".

Ya juya da sauri Yana wani irin fito a hankali, da gudu sukayo gurinsa ya nufi gate suka bishi suna kada jela.
Wata ajiyar zuciya zahra ta saki Dan tayi kukan har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido.
Bayan fitowar Zayyan Mahmud yakai minti Sha biyar sannan ya fito cikin sabuwar shiga ta wasu kananun kayan, ash colour T.shirt da black trouser Yana baza kanshinsa kamar ko yaushe.
Da sauri Zayyan ya nufo shi, ganin Basu little a gurin motar yasa Mahmud din yiwa Zayyan Wani kallo, shafa Kai yayi yana fadin.
"Tuba muke oga, hukuncin yayi tsauri".
Be ce Masa komai ba har suka karasa gurin motar saida ya bude sannan ya dubi Zayyan din Yana Mika masa key.
"Ungo bari mu koma baya kayi driving din mu na gaji bazan iya mayar damu gida ba".
Ya zagaya ya bude side din zahra take zaune Yana fadin.
"Precious" ya Mika Mata hannu alamar ta kama ta fito...

Tun wayewar gari Hajiya Mama ke jiran Asabe ta kawo Mata sauran magungunan da zatayi amfani dasu mahadin Wanda ta tura a jefa gidan Zahra, har akayi sallar azzahar babu labarin Asabe, la'asar shiru gashi har bayan insha'i babu ko duriyarta a gidan gashi wayarta a rufe. Ganin zaman tsammani baze yuwu ba yasa Mamar fitowa neman sahura, can inda dakunansu suke ta nufa tana tufka da warwara, tashin hankalinta Daya Bata aiwatar da abinda akace tayi tun safe ba, a daki ta samu sahura ta Bata kudin adaidaita ya kaita gurin Asabe ta fada Mata tazo tana nemanta.
Labarin da sahura ta dawowa Mama????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
dashi yayi matukar daga Mata hankali, Dan 'yan gidan abokan hayarsu sun tabbatarwa da sahura tun fitar da sukayi Hajiya Mama Bata dawo gidan ba har lokacin.

AUREN HUCE HAUSHI.



Maman Fateemah.

Page 55.

_____Zayyan Yana fitowa yaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login