Showing 135001 words to 138000 words out of 280244 words

Chapter 46 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1047

sahun na fadin " Yallabai kudin fa sunyi yawa ka duba kuwa?"
Bai waiwayo ba ya dago masa hannu Yana fadin "kaje ka Kara petrol da sauran". Yayi gaba abinsa, yana jiyo yanda yake kwararo Masa addu'a kamar ba gobe, da yake irin mutanen Nan ne masu kaifin harshe kamar jikan maroki.
Sau biyu Faruq yayi knocking din gate din,malam Musa ya leko ta kofofin dake jikin gate din, ganin shine yasa da sauri ya bude Faruq din ya shigo, sun yiwa juna farin sani tunda sun Sha zuwa da Mahmud suna kwana idan wani Abu ya kawo su kanon, sauda yawa anan gurin malam musan yake zama idan baya son fita ko Ina.
Cikin mutunta juna suka gaisa malam Musan yake fadar "Ashe tare kuke da yallaban Amma kunyi shigowar dare gaskiya, kaga motar can ma a kunne ya barta Naga kamar Matar tasa Bata Jin Dadi, dan da sauri suka wuce ciki ko motar Bai samu damar rufewa ba, nayi mamaki da naga yau yallabai da kansa ma yake tukin motar".
'yar dariya Faruq yayi, Bai tofa ko kalma Daya ba akan maganar tasa da yayi akan Ya Mahmud din, gurin da motar take Ya nufa Yana fadin.
"Ina zuwa Baba Musa Bari na gyara parking din".
Zuciyarsa fari tasss, Daya samu Mahmud a gidan ba kafa ya bashi ya gujewa haduwarsu ba kamar yanda ya yanke hulda da kowa, bai San Yana da irin wanna Zuciyar ba Saida aka samu matsalar, Amma Abu mafi daure Kai yanda Baba Musa yasan matarsa ce har yake fada Masa, ko a Ina ya samu labarin dasu Family dinsa Basu sani ba?.
Saida ya Kai motar parking lot sannan ya dawo gurin Baba Musa ya zauna suka Fara Hira, tunda mutuminsa ne sosai, sai da sukayi nisa a hirar sannan Faruq ya tambayi Baba Musan ko da sabuwar lambar Ya Mahmud a gurinsa shi ya baro wayarsa Mai sabuwar lambar a gida, tunda ya fada Masa ba tafiyar su Daya ba, shi biki yazo garin, shine ya shigo tunda ya fada masa Yana garin.
Ba musu ya Miko masa wayar yana fad'in.
"Duba ka gani Nima jiya jiya nan ya kirani da ita yake fada min za'a kawo kayan gyaran wancen sabon ginin da aka Gama".
Ya fada Yana nuna Masa inda su Mahmud din suka shiga.
Number ya saka a wayarsa ya maida Masa wayar Yana fadin "dauko min keys din wancan part din na shiga na kwanta na gaji sosai".
Dakinsa ya shiga ya fito Yana fadin gasu ka duba niba banbancewa nakeyi ba. Amsa yayi yayi masa sallama ya nufi part din Zuciyar sa fal da tambayoyin Daya Kamata ace ya yiwa Baba Musan Amma gudun bada wata kofa da za'a Sami wata kofar sanin wani abun yasa yaja bakinsa yayi shiru.

Har Mahmud ya shirya cikin pyjamas dinsa sky blue tana kudundune a cikin blanket din, duk Kai kawon da yake tana jinsa amma ko motsin kirki batayi ba, sai ya Gama komai ya nufi kofar ficewa daga dakin ya juyo kadan Yana Kare Mata kallo da gaske ita ce rauninsa yaga alama, a hankali ya koma cikin dakin yaje har inda tayi wurgi da hand bag dinta ya tsuguna ya dauka ya koma gefen gadon ya zauna ya bude jakar, wayarta ce da sauran tarkace irin na Mata sai ATM cards dinta da 'yar robar maganinta a ciki na wajen Hajiyar makwarari, ATM'S din ya dauke da wayar da sauran kudin data Ciro jiya a Hanyar Janbulo, harya mayar da jakar ya ajiye sai kuma yayi saurin Kara daukota kamar Wanda aka tsikara ya Kara budeta cikin wani zip na gefe ya bude takardu ya gani ya cirosu duka passport dinta ya gani da wasu magungunan da aka Bata na Asibiti sai takardun tests da akayi Mata na Azare Dana Nan kanon.
Passport din ya dauke ya hade da abubuwan daya dauka ya Mike ya fice daga dakin yana saka Mata alamar tambayoyi masu yawa.
Saida taji ya fice daga dakin da kusan minti goma sannan ta samu zarafin tashi zaune tana Dan turo Baki tana 'yan matanganunta a ciki Wanda ita kadai tasan me take fada.
Sai lokacin ta shiga bin jikinta da kallo ita fa duk ya dagula Mata Lissafi. Banda taimakon Allah da yanzu ba wannan batun akeyi ba, tsikar jikinta ce ta kara tashi yarrrr kankame jikinta tayi tana sauki wani malalacin numfashi, tare da furta "Narrow escape".
Ta Kai dubanta inda yayi Mata wurgi da kayan jikinta, ita har zuwa lokacin ta rasa meya tunzura shi haka daga ganin Musbahu ita ba ita takai kanta ba, ba ita tace ajeba ballentana yayi tunanin setup ne.
Itama wankan ta shiga yi tana zuwa ta duba jikinta cikin ikon Allah period din ya dauke Daman tun safe taga alamun hakan duk pad din data saka a yinin haka nan take cirewa, ta yanzu ma hakan ce ta kasance, tayi hamdala ga Allah tafi a qirga wato ba karamar kariya wannan pad din ta Bata ba.
Wankan tsarki tayi tare da wankan sabulu ta fito daure da towel, yanzu ta Zama 'yar gari gurin suturar sakawa, gurin kawai ta nufa ta Ciro Riga da wando sleeping dress masu rawa ta saka ta dauko hijabi ta shimfida sallaya ta tayar da sallar magariba da insha'i.

Mahmud Yana fitowa dakin Daya tura zahra dauko Masa magani ya shiga, direct wurin wasu lokoki ya nufa a ta tsakiya ya bude ya zuba duk kayan daya dauko a Jakarta, wayar kadai ya rike a hannunsa.
Kira ne ya shigo wayarsa yana dubawa ya gane number Faruq ce.
"Ya Salam". Ya furta a hankali wallahi ya manta da batun Faruq kwata kwata Saida yaga kiransa ya tuna Daya hadu dashi ma, to Ina ya samu wannan number din shidai yasan be Kira wasu mutane da yawa ba da layin Dan sabo ne jiya ya Fara amfani dashi, sai Kuma ya tuna ya Kira malam Musa dashi jiya yasan a gurinsa ya karba, tasowa yayi ya nufo parlourn farko Yana dealing number din Faruq din.
Yana dagawa yace Masa "ka shigo sabon part din nan ka sameni a parlour". Ya yanke Kiran..
Cikin kujera two seaters ya zauna a kasalance badan Shima Yana Jin kishirwar haduwa da Faruq din ba da Babu abinda ze fito dashi ba.
Fitowa yayi da zummar dauke motar Daya Bari a gurin, ga mamakinsa Bata gurin a parking space ya hango ta, Dan murmushi yayi yasan aikin Faruq ne.
A Nan ya tsaya ya Zuba hannunsa a cikin aljihun rigar Yana shaqar iskar dare da take kadawa a hankali Mai dadi, malam Musa ne ya hango shi a tsaye a gurin da sauri ya nufo gurin Yana fadin "barka da dare yallabai anzo lafiya?".
Hannu ya Mika masa duk da nokewar da malam Musan yakeyi sai da sukayi musibaha. Mahmud din na fadin "lafiya kalau Alhamdulillahi, nagode kwarai, ya iyalin naka da jikin".
"Wallahi Alhamdulillahi kamar ma batayi lalurar ba, Allah yaja da Rai ya Kara daukaka yaja da ran mahaifa ya baka zuri'a d'ayyiba".
"Allahumma Amin".
Faruq ya amsa addu'ar lokacin da yake karasowa.
Komawa bakin aikinsa Malam Musa yayi su Kuma su Mahmud Maimakon su koma Daki sai suka gangaro kasa gurin irin hut (bukka) din Nan ta zamani an wadatata da isashshen haske Mai wani daukar hankali Wanda ya Kara kawata gurin.
Zama sukayi a tare kusa da kusa tamkar Muhmud din ze gudu cikin murye me rauni Dan har idanunsa sun cicciko da hawaye Faruq ya Fara fadin "why me yasa kayi haka Ya Mahmud? Kasan yanda kabar baya da kusa kuwa? Rayuka da yawa sun baci Kasan Ammi ma zazzagewa tayi tayi tafiyarta Niger, sai fa a wancan satin ta dawo sokoto. Lamarin babu Dadi ko kadan ga Hajiya Inna ma ta tashi hankalinta Wai itace tayi silar barinka gida tunda ita ta kara tunzuraka da maganganunta, ga Abie ya Kori Aunty Samira da Safna har da masu aikin part dinta Dan sai daga baya maganganu suka dunga fitowa har da asiri fa sukayi maka akan kabar Sokoto har abada ko sunanta kada kara tunawa, Kuma Duk abinda kake dashi ya lalace,kasan wani abun mamakin Wai a cikin masu tayata wannan shirkar harda uncle Saminu".
Sai lokacin Mahmud ya dago da Kansa ya kalli Faruq dan tunda ya Fara maganar yaji kamar a lokacin abin yake faruwa.
Cikin cikakkiyar kamalarsa yayi wani murmushi kafin ya bude bakinsa cikin Jin Kai Dan maganar ma kamar baya son yinta Dan har lokacin jikinsa ba daidai yake jinsa ba yace "Na sani mana sosai ma kuwa, ai kome akace yayi ba zanyi mamakinsa ba, kasan ya tareni gaba da gaba yace min ba dai Ina takama da nafi 'ya'yan su rufin asiri ba shi yasa nace bazan auri 'yarsa Asma'u ba, shima ai ba matsiyaci bane to sai yayi min sanadin da sai zaman sokoto dama kasar Baki Daya yayi min wahala, Sam ban kawo komai ba akan furucinsa Dan nasan ba abinda ya Isa yayi min Saida Izinin Allah, Kasan Abu mafi yi min ciwo a duk cikin jumurdar da akayi tayi?" Kai Faruq ya girgiza Masa.
"sharrin zina da akayi min Wai harda Cikin shege, ko Ina Zina me zaci da Safna kazama kawai yarinyar data Zama karya ko wane kare binta yakeyi har ayi kokarin hadani aure da ita, wallahi Dana auri yarinyar nan gara na mutu a gwauro babu aure, sannan Abu mafi ciwo babu Wanda ya ji view dina an dauki abin da zafi kowa bakinsa yana kaina har Ammi Taki yarda Dani, tana ganin D'an yanzu babu abinda baze iya aikatawa ba, shi yasa na nufi gurin Hajiya Inna Nan ma gurinta babu sauki shi yasa naji gara nayi nesa da gida tunda kowa ganin mutumin banza yake mini. kasan kuwa duk abinda yake faruwa Ina da masaniyarsa? har barin Ammi sakoto, kawai dai na Kai zuciyata nesa ne sau uku Ina zuwa Yamai amma sai naji bazan iya tunkararta ba saboda tana ganina wannan badakalar zata sake dawo mata a zuciya duk da gaskiya tayi halinta, so nake kowa ya ji yanda naji lokacin da akeyi min nak'i aka juya min baya! Kamar bani da gata, wallahi nayi Dana sanin Fara business dina da kananun shekaru Dana San idan na Fara haka Zan Zama yanda na Zama da ban yarda uncle Ishaq ya dorani akan kasuwanci ba, Allah swa yayi gaskiya Daya ce dukiya da 'ya'ya fitina ne, da Ina level irin na kowa a family din ba Wanda ze dameni tunda duk familyn wanda baya da rufin asiri da nasa wadatar? To ni abin ne yayi min waya wallahi ga kananun shekaru, kasan uncle Saminun dai ya taba fada min ko kungiyoyin matsafa dai na shiga, shi yasa na Zama abunda ba Zama cikin kankanin lokaci, a gaban Hajiya Inna da uncle Mustapha akayi har Saida suka samu mugun sabani da uncle Mustaphan Dan ma Hajiya Inna ta tsawatar kasan Bata da Wasa a gurin 'ya'yanta, sosai ta ciwa Uncle Saminun mutunci tace ze Bata Mata zuri'ar ta, na rasa mena tsare masa haka da zafi Sam baya kaunata ko alama, haka Sam baya ko shiga part din Ammina sai dai idan guri ya kure su gaisa Dan dole".
Ya fada cikin bacin Rai sosai Dan idanunsa sun kada sunyi jajir, kwantar da Kansa yayi jikin kujerar yana sauke ajiyar Zuciya, da ganinsa kasan yayi famun ciwon da yake Zuciyarsa.
Dan muskutawa Faruq din yayi shima abin saiya dawo Masa sabo.
"Kayi hakuri Dan Allah Ya Mahmud kasan idan Allah yayi maka daukaka zaka gamu da kalubale kala-kala ba cikin family ba ba cikin jama'ar gari ba ba cikin abokai ba dole hakan ta faru yanzu dai ka koma gida, ayi duk wacce za'ayi duk da gaskiya tayi halinta an banbance tsakanin aya da tsakuwa, wallahi rayuwa lami ta zamar min da baka Nan, kofa a email na turo maka sako baka bani amsa nayi magiyar har naba uku lada, amma baka kulani Nima fushin ya shafeni ko? Wallahi yanzu ma nasan addu'ar da nakeyi ce ba dare ba Rana Allah ya amsa min ya kawo dalilin zuwana kanon Nan dafa harna cewa mamee ba, Kuma wallahi Allah kenan harna kwanta naji uncle musbahu ze fito sayan wasu abubuwan na amfani da mamee ta bashi ya list ya sawo Mata shine fa nace Bari na rakashi na Jima ban shigo garin ba na Dan Zagaya tunda ba dadewa zanyi ba, Ashe farin gani zanyi Dan Allah Ina ka shiga a kasar nan? Wallahi babu Wanda ya taba kawo kana kasar Nan ko alama Dan anfi maida hankalin nemanka a European countries da Asia wallahi ba Wanda ya kawo zaka zauna a 9ja".
Girarsa Daya ta gefen dama ya Dan dage Yana yiwa Faruq wani kallo.
"Au kunyi zaton Ina waje kenan ko? To Ina gida Bauchi state, cikin garin Azare katagum local government, nasan ba sai nayi maka bayanin komai akan Zahra ba, an fada maka wacece ita tunda Wanda na ganku yasan komai a Kanta watakila Abu Daya ze bashi mamaki ganin mu tare a Nan tunda ya sanni ko ba sosai ba a can tunda time to time Yana shiga gurin malamina suna gaisawa idan ya shiga garin, sai albishir Daya Zan maka itace yarinyar da nake fada maka mun taba haduwa da ita a cikin jirgi ita da Babanta wadda na tura Sameer ya bisu Zuwa Jordan,ai ka gane bayanin ko?"
Kai Faruq din ya jinjina Yana fadin "Yes". Ya fada yana mamakin abun sosai wato shi Mahmud komai ya sake a gaba saiya cimma burinsa. "Sai yanzu ya gane ka har hotunan daurin auren ya nuna min a phone dinsa, Shima ya Dade Yana tunanin a Ina yasan fuskar ka tunda ba farin sani yayi maka ba sai dai a hoto, shi yasa Sam be ganeka ba tunda ta Ina za'ayi tunanin zakayi irin wannan rayuwar, Dan Allah fada min ta Yaya hakan ya faru harda Auren irin wannan yarinyar haka wato ribar kafa kenan ko?"
"To abubuwan da yawa Dan Ni dai nasan na baro gidan Hajiya Inna cikin fushi kofa takalmana ban iya tsayawa na saka ba kawai dai nasan duk phones dina suna jikina na kamo hanya a kafata Amma Abu Daya nayi noticing kamar jama'ar da nake wucewa basa ganina sam, nayi tafiyar da bansan iyakarta ba daga Nan Kuma ban Kara sanin abubuwan da suka faru ba na dai tsinceni ne a gadon Asbiti bana magana ko kadan amma Ina Jin abinda ake fada mayarwar ce Bana iyawa, Wanda suka shinceni wani babban malami ne da marikin zahra da d'an Kanwar Malam din, shifa Malam din ya dage min da Addu'oi a kaina Dan har Taraba Saida yaje akan matsalata gurin wani tsoho malaminsa, a haka har Allah ya bani lafiya, sai Kuma nayi arba da Zahra a garin duk da Daman a bincken Sameer ya gano mazauna Bauchi state ne, sai naji Naga gurin Zama na dage da Addu'a da sadaka amma fa ban fadawa kowa ba ko Sameer saboda a lokacin maganar aurenta akeyi na shiga wani Hali a lokacin sai dai nayi Alkawari sai halarci daurin aurenta Kuma sai nayi Mata kyauta ta ban mamaki kafin nabar garin, sai kuma ubangijin da yake amsa addu'ar bayinsa ya juya lamarin cikin kankanin lokaci, aka bani aurenta lokacin Dana yanke kauna da samunta a matsayin matar aure uwar 'ya'yana".
Ba karamin mamaki Faruq yayi ba ya Kuma Kara jinjinawa girman Allah swa, wato duk gwagwarmayar da aka Sha Rabon wannan yarinyar ne ya rantse Kuma ya kaddaro shine ze taka da kafarsa ya karbi aurensa ba tare da wakilcin iyayensa ba sai iyayen Amana.
"Wato Ni duk lamarin ya juye min wallahi".
Dan murmushi Mahmud yayi Yana fadin.
"Kaima kenan da ba a kanka hakan ya faru ba, sometimes idan na zauna sai naga kamar Almara wasu abubuwan da suka faru, kasan abinda zakayi min".
Kai Faruq ya girgiza alamar "A'a.
Fuska ya hade Sosai Yana kallonsa Ido cikin ido.
"Kada naji labarin ka hadu Dani a Sokoto Koda wasa, Nina fita da kafata Kuma ida kafata Zan koma Amma ba yanzu ba, Kuma kada naji labarin nayi aure a gurin kowa koda nazo da Zahra kada ka nuna kasanta ko a fuska, Nina taro match din ni zanji da kayana".
Kai kuwai Faruq ke gyadawa tunda ya Fara maganar yasan ba Wasa a cikinta.
"In sha Allah hakan bazata faru ba".
Sun Kai kusan karfe uku suna tattaunawa akan abubuwan da suka ringa faruwa bayan bayanan, kafin kowa ya nufi NASA gurin kafin lokacin sallar asuba. Ba karamin mamaki Faruq yakeyi ba idan yaji Mahmud Yana fada masa wani abun Dan shi sai gurinsa yaji wasu abubuwan duk da Yana cikin gidan.

Itama zahra Bata kwanta ba sai kusan biyu da rabi bayan ta gama karatun Alqur'ani ta Fara nafifili sannan ta kwanta, harta gama addu'ar kwanciyar barci sai Kuma ta canza Shawara ta tashi ta dauko Jakarta tana fadin "Bari na kunna wayar nan ba turawa Ammah text na ban hakuri tayi breakfast dashi sai Kuma da Dan hantsi na kirata nasan zata huce ta saurareni lokacin, sannan na Kira bestie musha hurar yau she gamo".
Jakar ta dauko ta koma saman gadon Tana gyara Zama, duk iya binciken ta tayi Babu duk wani Abu Mai mahimmanci data saka a ciki, zazzage jakar tayi wayam kamar ba'a taba ajewa a cikinta ba.
Tagumi ta buga tana tunanin, to a Ina suka zube wadannan kayan? Kuma me yasa sauran Basu zube ba? ko jiya lokacin da suka fito daga gidan mommy komai Yana ciki Kuma ai ko daga motar Bata fito ba lokacin da sukaje sahad din.
Jiki ba kwari ta matsa tsakiyar gadon ta kwanta ita duk lamarin ya tsinke Mata wa zata tambaya Ina kayanta na jaka suke da wannan tunanin barci yayi gaba da ita.
Hudu da rabi Mahmud ya tashi as usual, duk da Daren da suka raba da Faruq besa shi ya makara ba, nafila yayi sannan yayi raka'atanul fajri ya fito Jin an Fara Kiran sallar na biyu, harya nufi Hanyar fita daga corridorn sai ya dawo baya ya tura kofar dakin da take, a kwace ya ganta tsakiyar gadon hular data saka ta cire gefe guda Ribom din shima yayi nasa gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login