Showing 186001 words to 189000 words out of 280244 words

Chapter 63 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1090

Allah".
"Kai haba Asma'u ki cire wannan tunanin daga zuciyar ma Mahmud Dan mafita ne Ina nan Ina bincken menene musabbabin abinda ya rabo shi da gida dole akwai dalilin dayasa ya baro komai nasa ya taho yayi irin wannan rayuwar".
"Ban gane ba Abban Yara kayi min bayanin da Zan gane".
Dan tunani yayi kadan kafin yace Mata.
"Ki kwantar da hankalinki mahmud ba boyayye bane Dan cikin.garin sokoto ne a yanda aka fada mini nasan mahaifinsa farin sani, sai dai har yanzu ban Gama yarda da shine mahaifinsa ba duk da tun ganina na farko dashi Naga nasan fuskar amma na rasa Inda nasanta Saida aka fada min mahaifinsa Naga tabbas fuskarsa nake gani ata mahmud, Dan haka ki kwantar da hankalinki in Sha Allah uwata saita Zama farin wata Sha kallo duk bacin ran da aka shiga sai ance gara da hakan ta faru ki bani lokaci harna karasa nawa binciken kinje".
Ya fada yana Dan murmushinsu na manya.
"To shi kenan Allah ya rufa asiri, nagode da kulawar ka garemu".
"Kada ki Kara yi min godiya akan al'amarin uwata yiwa Kaine Nina bada aurenta ga wannan yaro hakki nane ba binciko komar daya dangance shi, sai daga baya muka fashinci gidan ne baya muradin komawa yasa yace ya manta komai na rayuwarsa ta baya sai yanzu nake tunano maganar da mukayi ta saka hotonsa a kafafen sada zumunta na zamani ko za'a dace da wadanda suka sanshi amma kinsan yaron nan cewa yayi a''a ayi hakuri a hankali wata Rana ze tuna".
"Au haka kukayi baka fada min ba da wallahi sai ya kawo danginsa sannan za'a bashi ita".
Ta fada tana mokewa.
"Hannunta ya kamo.
Ki dawo ki tayani barcin Mana.
Ba musu ta dawo suka kwanta itama barcin take ji dan Shima Abban ba Sanya ga Ammar mu da daukar gyara.

Karfe tara me kyau su zahra suka dira a famfon shanu, Aunty zilai ce ta dauko baskets guda biyu da Daya na Ammah dayan kuma na Abba ne?
Suna shiga parlourn ba kowa sai buruntun Alawiyya a kitchen, Jin shigowar mutane yasa Alawiyya fitowa.
"Lah sannunku da Zuwa. "Ina Kwanan ku? Ta fada tana karbar ledar hannun Aunty.
"Kawo na Kai ciki"...
Alawiyya ta fada tana fadin sannu da kokari.

*AUREN HUCE HAUSHI *

Maman Fateemah

Page. 67.

...& .........

A nan parlour zahra ta zauna suna kwasar hira da Alawiyya saboda itama 'yar shafta ce ta gaske, suna nan magaji ya shigo yana ganin zahra ya karaso da sauri yana fadin.
"Kai! A gidan nan kika kwana amma?".
"Eh mana da kana tunanin na sallama maka Ammar ne kai kadai? Nima ina son naji dumin uwata".
Wata dariya ya saki yana fadin.
"Naga wannan Allah yasa Ya mahmud ya daukeki ku tafi wata uwa duniya sai naga ta biniyar gida naga alama irin kune matan da idan kuna cikin garinku kuke raba dai dan zama rabi kuma gidan miji rabi kuna gidan iyayenku bare idan kun raina miji".
Maganar Ammah sukaji ba wanda yaji shigowarta ta sha gayu sai zuba kamshi takeyi sam ba zakace su Aunty Hasana 'ya'yanta bane.
"Magaji wallahi ka fita daga idona wai me zahra ta tsare maka ne? Naga alama mun kusa saka kafar wando daya da kai a gidan nan".
Duka suka juya suna kallon Ammah, zahra ce ta tashi ta nufi Ammah tana fadin.
"Rabu dashi Ammah wallahi duk bashi yake ci akwai ranar biya".
Dariya su Aunty zilai sukayi suna gaishe da Ammar itama zahra gaishe da Ammar tayi suna zama zahra ta shige jikinta.
"Wallahi kiji tsaron Allah magidanciya dake ki tsaya kina zuba tabara dan tsabar samun guri".

"Nayi din, idan fitsari banza ne kazama tayi mana, kaida wannan cinyar sai gani sai hange".
Ta fada tana gyara kanta dake jikin kafadar Ammah.
Zilai ce ta dauko basket daya da leda sai kuma Alawiyya ma ta sauko sauran suka kawo gaban Ammah zilan na fadin.
"Ammah gashi wannan na Abban uwar dakina ne sauran kuma naki ne".
"Masha Allah Allah yayi albarka, kwana kukayi kuna wannan aikin ne?".
"A'a ko daya tun asuba dai muka fara kinsan uwar dakin tawa babu abinda ta aje a halinki Ammah tasan kanta".
Da sauri magaji ya matso yana kokarin bude warmers din yana fadin bari mu gani nasan duk abinda ya fito daga wadannan masu two face din unique ne".
Dan murmushi tayi Ammar tana son zama dasu sauda yawa saboda ko bacin rai take sai taji ta samu farin ciki tamkar Tom & Jerry haka suke.
Aunty zilan sallama ta yiwa Ammah da zahra tace zataje gida, har taje kofa Ammah ta kirata, tashi Ammar tayi ta nufi bedroom dinta ganin haka yasa zilan bin bayanta, itama zahra dakin data mayar nata ta tashi ta shige dan barci takeji bana sosai, tana jin magaji wanda ya cika baki da gas meat daya diba a plate yana fadin.
"Dole ma kafarki kafa ta irin wannan gara ai nan da nan zan canza, ai nasan kin fadawa ya mahmud tare akayi goyon mu".
Dariya zahra tayi kawai, lamarin magaji sai shi shidai yaci nama.
Sako Ammah ta bawa Zilai na ta biya gidan Hajiya Amina ta fada mata tana nemanta tun dazu take kokarin kiranta network yaki bada hadin kai sam.
Parlour Ammah ta fito ba taga zahra ba sai magaji yana ta aikawa.
"To acici ina zahrar kuma?".
Da hannu ya nuna dakin data shiga saboda ya cika baki.
Can ta nufa tayi knocking, da masifarta ta taso zata saukewa magaji sai kuma taga Ammah ce.
"Kizo kije ku gaisa da Abbanku saiki tafar masa da abinda kika kawo masa tunda dama bai kai ga yin break fast ba, idan kin dawo kema kizo kiyi naki nasan ba wani abun kirki kikaci ba".
"To Ammah bari na fito na dauka ya fita da naga duk su Ya Abdul Hakeem basu shigo ba".
"A'a yau inaga basu da fita ko ina kamar Abban nasu".
Ta juya ta koma zahra ma ta gyara rolling dinta ta fito tamkar dawisu tana tafiyar nan das-das.
Basket din ta dauka ta fice bata bi ta kan dan gidanta ba dayake ta zuba mata zance, wani lokacin har mamakin yawan maganar Magaji take shi sam baya gajiya da magana.
Da sallama a bakinta ta shiga parlourn kasancewar a bude ta sameshi, suna dining area sanda ta shiga, directly gurinsu ta nufa,Abba na ganinta ya fara murmushi yana fadin.
"Masha Allah, uwata ba raguwa bace har kin fito? Haka akeso ki zama mai himma".
Itama murmushin tayi tana karasawa gurinsa ta tsuguna har kasa.
"Abbana ina kwana?". Ta fada tana aje basket din.
"Lafiya kalau uwata".
Basket din ta dauko tana fadin.
"Yau dai abincina Abbana zaici gaskiya Ammah".
"Gaskiyarki uwata ai babu wanda zaiki abincin babarsa zuba mini Allah yayi Albarka ya baki masu yi miki kema"
"Allahumma Amin". maganganu yake mata masu harshen damo daga karshe ya rufe da kara jaddada mata mahimnacin hakuri, sannan ta baro sashen nasa duk jiki a mace.
Lokacin data shigo mutumin ya kunna tashar restling yana kallo.
Tana shigowa ya taso.
"Daman ke nake jira kizo na saida miki wannan jaridar".
"Jarida kuma".
Tsaki yayi yana tabe baki kamar mace.
"Ashe ke bakya daukar haske, to labari zan baki".
"Ok. Sai yanzu naje Ghana, bani na sha".
Zama sukayi nan kasa kan carpet.
"Kina jina wai dan Allah me yasa kikace kada na kawo sahura gidanki? Kinga yanda Mama ta damu kuwa akan nace mata kuna kano kamar zata fasa kuka fa, ke bar wannan kada na manta abinda zan fada miki, dazu da Asuba nayi shirin masallaci na saka J/C dina a leda na nufi kofar baya na aje idan an dawo daga sallah na sulale ta baya na wuce training din ball, kinsan tun lokacin dana samu karaya Abba ya hana ball, ni kuma idan babu ita da matsala gaskiya shine nake fita ta baya har na dawo babu wanda ya sani, to dazun ina nufar gurin naga Mama da Ya Hamza da wannan 'yar rainin hankalin tana rusa kuka sun fice ta kofar bayan ita da Ya Hamzan ita kuma Mamar ta dawo ta wuce ta gefen inda nake tana shafe hawaye da gefen hijabin dake jikinta, harta wuce bata ganni ba nasan duk yanda akayi da magana a kasa tunda babu wanda yasan da zuwan salma gidan nan".
Zuru zahra tayi masa tana kallonsa.
"Tab Allah ya kyauta can gasu gada, wai zomo yaji kidan masu farauta, ai idan kace ruwan wani ba zai tafasa ba to in sha Allah naka ko zafi bazeyi ba, ayi dai mugani karya dai fure take bata 'ya'ya, ba dai mugun abu suka zaba ba da saura ma basuga komai ba, kace kai baka son cigaban kowa to kaima yaushe zakaga dai dai".
"Haka ne kam ai so nake Abba ya gama break naje na fada masa ya kira Ya Hamzan yaji meya faru kuma ina suka tafi ko kuma nace Abban yaje makarantar da kansa ko daga can ne aka samu matsalar".
"Kai magaji ina ruwanka da sagbarsu,kasa ido idan tayi wari kowa zeji ne har wani zaka fadawa Abba meye naka a ciki, ka manta hadisin Annabi Asalihissalam wanda yake cewa yana daga kyawun mutum ya bar abunda babu ruwansa? To ka kyautata musulincinka kaima, ka nuna kamar baka san anyi ba idan wani dalili yasa anzo gabar da zaka iya fadin abinda ka gani falillahil hamdu saika fada din".
"To shike nan bari naje nayi wani aiki kinsan mun fara project".
"Masha Allah Allah ya taimaka, ya dai fiye maka da guzirin tsegumi"
.
"Allahumma Amin, gaskiyarki yallabiya"
Yayi waje.

Ita kuma zahra ta tashi zata koma ciki taji ana knocking din kofa ta nufi gurin, tana budewa taga Hajiya Amina mutuniyar Ammah ce sosai, tana sayar da turarika na jiki dana daki da kayan gyaran Aure dasu dilkar Amare. Jakar hannunta zahra ta karba tana bata hanya tare da fadin.
"Sannu da zuwa Hajiya"
"Yauwa Amarya ya gida?".
"Lafiya kalau Hajiya, ina kwana?".
Lafiya kalau Alhamduliahi ya mai gidan naki?.
"Lafiya kalau" ta fafa tana sadda kai kasa.
"Bari na fadawa Ammar kinzo"
Kafin ta bata amsa har Ammar ta shigo, tana fadin.
"Lale marhabin da Hajiyar kamshi, lallai kinaji da wannan 'yar taki, nan da nan haka har kinzo".

."Ai ba'a bori da sanyi jiki" ta fada tana dan murmusawa".
"Haka ne kam"
Ammah ta fada sannan suka gaisa.
Tashi zahra tayi zata tafi ta basu guri.
"Dawo ki shiga da wannan jakar, ki bude ki dauki fallan sabon zani ki cire kayan jikinki ki dauwa shi gani nan shigowa".
Dauka tayi tayi gaba da jakar babu halin tambaya tunda ita dai bataga wani dalilin da ze saka ayi mata wani gyara ba tana zaman zamanta ita da ko mijin baya kusa bare yaji ko kamshin ne.
Saida ta bacewa ganinsu sannan Ammah ta bawa Hajiya Amina hankinta sosai.
"Kina ji abun ne yazo a gurarran lokaci wai gobe zatabi mijin india sai jiya da dare Abbansu ya fada min, shine na tura kizo kiyi mata dan abunda ba za'a rasa ba, to kuma sai a dazu Zilai ke fada min wata magana, na rasa ta inda zan bullo mata, wai sunje asibiti an tabbatar wa da zilan wai zahra har yanzu wani namji bai santa a diya mace ba, dan da farko an dauka ciki ne ya lalace sai da akayi bincike aka gani fibroid ne ya narke a sanasiyyar maganin da tasha, shine zilan tace wai ko mijin ne bashi da lafiya sukayi shiru ko asibitin da sukaje hanawa tayi a fada min wai kada hankalina ya tashi".
Jinjina kai hajiyar tayi.
"Babbar magana dole ayi bincike gaskiya, bari na shiga naji yanda abun yake daga bakinta"

Ta mike ta nufi dakin, a zaune ta samu zahra tana lallatsa wayarta.
Da sauri ta aje tana gyara zama.
Gurin da aka aje jakar ta nufa ta bude ta fara ciro kayan aikinta ta shinfida table mat a kasa ta fita ta dawo da cups da cokali, hada wancan zuba wannan tana zuba madara tana bata tana shanyewa sai da tazo kan wani bakin magani sannan ta dago tana fadin.
" Wamnan saidai na baki ki tafi dashi dan buduruwa bata sha sai matar auren da suke haduwa da mijinta kinga ke dai ba zakiyi amfani dashi ba tunda naga ke har yanzu baki fara naki amarcin ba ko?".
Hannu tasa ta rufe fuskarta shike nan tasan ko rantsuwa tayi babu kaffara Aunty zilai ce ta fadawa Ammah shine aka biyo mata ta nan gurin.
Shiru zahra tayi in dai ita zata bada amsar tambayar za'a shekara ba'aji amsar ba.
"Kinyi shiru baki bani amsa ba? Ko mijin naki bashi da lafiya ne akwai irin nasu magaungunan sai a baki ki tafar masa dasu".
"Hjy shifa lafiyarsa kalau wallahi".
"To ai shikenan daman ana gudun kada kuyi yarinta wannan shine zaman auren"..
Kayan hadin data hado ta shiga shafa mata dilkan dasu kurkur, bayan ya bushe aka murje ta shiga wanka tun a toilet din taga an samu banbanci yanda jikinta ke fitar da wani irin shining ga wani irin kamshi mai saka nutsuwa, data fito ta samu an hada burner kan wata kujera ta zauna Hjyr ta tufeta da blanket tace ta cire towel din ta bata wani magani me azabar kamshi tace ta zuba ta bude kafarta sosai ya shigeta, a dan kunyace tace mata
"Ina period fa".
Dafe kai tayi, kafin tace ba komai ki barshi ya shiga jikinki kawai, daya gama haka ta ringa bata kalolinsu tana turare jikinta dasu har aka gama wasu mayika da humra ta aje mata ta fice tace ta shafe jikinta dasu. Lokacin data fito ko amma kasa dauke idonta tayi daga kan zahra.
"Tabarakallahu Ahsanaul khaliqin"
Ta fada a hankali dan wani irin kyau tayi na ban mamaki.
Tana karasa shigowa cikin parlourn kanshin jikinta ya canza yanayin gurin gaba daya.
Sannu ta yiwa Ammah ta shige karamin parlour tayi zamanta saboda taga alama maganar sirri sukeyi da Ammah.
Ya Imam ne ya shigo parlourn da sallamarsa yana dauke da manyan ledoji guda biyu, ya aje yana gaushe da Hajiya Amina, sannan ya yiwa Ammah sannu da gida.
"Wannan kuma daga ina?".
Ammah ta tambaya, baki ne daga kano gasu nan shigowa".
Ya fada yana juyawa, tasowa zahra tayi da sauri tana fadin.
"Ya Imam ina yini?"
Dawowa yayi yana fadin.
"Lafiya kalau zahra ashe kina gidan na shigo dazu banganki ba, ya gida? Ya kuma jikin baba malam? Jiya na kirasu na duba shi lokacin ana masa aiki sukace".
"Eh wallahi anyi aikin sai fatan samun lafiya".
Ai kafin Ya imam ya fadi abinda yayi niyya yaga zahra ta kwasa kamar wata.'yar baby ta nufi wata fattijuwa da suka shigo da wata budurwa sai magaji daya riko sauran wasu kayan, tana zuwa ta shige jikinta tana fadin.
"Wayyo dadi yau ga Hajiyarmu a Azare, wallahi nayi zaton da wasa kike min".
Dariya Hajiyar tayi tana fadin.
"Kada ki kadani tsohon rai ki ida laifin daba naki ba fa".
Dariya itama zahrar tayi, tana rike hannun Hajiyar makwarari, sai data dago taga Aunty Rukayya na musu dariya.
Hajiyar zahra ta saki ta nufi Aunty Rukayya da saur tana fadin.
"Kin shammaceni Aunty Rukayya sai ki fada min gaku nan zuwa".
Su dai sauran na parlourn kallon ikon Allah suke tunda basu san bakin zahrar ba.
Tasowa Ammah tayi tana fadin.
"Sannu da hanya Hajiya karaso ki zauna ki rabu da shiriritar zahra".
Gurin zama Ammah ta bata ta zauna suka gaisa da Hajiyar sannan Hajiya Amina ma ta gaisheta tare da yi mata sannu da hanya,su zahra ne suka karaso Rukayya ta gaishe dasu Ammah zahra ta matsa ta gaishe da Hajiyar makwarari, sai kakabin abun takeyi.
Alawiyya dake aiki a kitchen ce ta fito da tray babba da ruwa da drinks dasu snacks a kai ta kawo ta aje tana gaishe da Hajiya da yi mata sanni da hanya, sannan suka gaisa da Rukayya.
Hajiya Amina tashi tayi tana fadin.
"Zan tafi Hajiya duk komai suna gurinta na nuna mata yanda zatayi".
"To nagode in sha Allah sai munyi waya".
Hajiyar makwarari ta yiwa sallama ta tafi.
"Hajiya kusha ruwa sai kuyi sallah kafin kuci abinci ko?"
Ammah ta fada tana tashi ta basu guri.
"Zuba min ruwan nasha kinji zahra'u, kinga Rakiya nan sai dacin rai take mini dan nace zanzo naga jikin naki, kinsan kirkinta kadan ne, banda barbada har yaushe zata nuna adawa a zuwa gurin matar mahmud yaron daya zamar mana fitilar daya haskemu da ita yo ko ubanta ai da tallafin mijinki yake juya tashi kasuwar".
"Ayi hakuri Hajiya banda gori, ina laifi tunda ta rakok".
Ammah ta fada lokacin ta shigo parlourn daga kitchen.
Baki Rukayya ta zunbura.
"Wallahi da nasan haka zakiyin da ban fadawa Ya sameer ya taho dake ba na barki wanda ze kawoki ya kawoki ku gama bulayinku ku koma tunda ba sanin inda zaku kukayi ba".
"Kar nan 'yar Ashatta, ai wannan yarinyar babu irinta a garin nan dana kwatanta za'a kawoni gareta ko kinji".
"Hajiya rabu da ita, zahra ku shiga can dakin kije ki dauko mata nata ruwan a kyale Hajiya ta huta".
Tsam suka mike kamar daman jira sukeyi suka wuce ciki.
Magaji ne ya shigo yana kara gaishe da Hajiya, sannan ya fadawa Ammah a kawo abinci da ruwa a mikawa Oga sameer shiya kawo su.
Kitchen suka shiga tasa Alawiyya ta hada abinci da duk abinda ya kamata magajin da Alawiyya suka fita kai masa.
A dakin Ammah Hajiya tayi sallah sannn suka kara gaisawa, Hajiyar ke fadin.
"To barka fa anyi ta barka da wannan ciwo ya rabu da yarinyar nan, ina amfanin ace sai an yanka yarinya ace za'a cire ciwo".
Kasake Ammah tayi wato abinda Hasana da zulai suka fada haka yake ita kawai taki fadawa wai kada ta tada mata hankali.
"Eh wallahi Hajiya anyi ta barka kam babu abinda zamuce sai dai Allah ya saka da Alkhairi yasa a gama lafiya, mun gode kwarai da gaske".
"Kai! Kada na karajin godiyar nan daga bakinki, ai duk abinda zamu yiwa yaron nan bazamu biya shi ba,yanzu fa Allah ke rike damu amma da bazarsa muke rawa, sau biyu fa yana kaini masar akan lalurar ido data kafa ya, kaini umar sau biyu ya gyara mini gida ga jikana ya janyo shi jikinsa duk inda ya aje kafa sameeru yana maida tasa ko wannan fushin zuciyar da yayi babu wanda yasan inda yake sai sameerun, su iyayen sunfi maida karfin nemansa a kasashen turawa da larabawa basu san yana nan ba,ai wannan yaron uwarsa tayi farar haihuwa gashi Allah ya bashi mata wanke hannu daka taba, gaku kuma mutanen arziki kun bashi irin wannan yarinya ba tare da kun dubi halin da yake ciki ba sameeru yace min Almajirin malam ya zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login