Showing 216001 words to 219000 words out of 280244 words

Chapter 73 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1094

Allah ya tsare hanya".
Kunshin abinda ke hannunta da wani gidan sarka White gold Mai azabar kyau sarkar kudinta sun tasarwa milion hamsin ta mikawa Zahra tana fadin "Allah ya tsare hanya ki gaishe min da mamanki".
Ta bude motar ta sakata ta juya ta koma Bata Kara kallonsu ba saboda ji tayi kamar rabuawar kenan.
Wasu hawaye Aishat taji sun cika Mata ido da gudu tabi bayan Ammi tana fadin .
"Why! Why! Why! Ammai kin kashe min farin Cikin bros wallahi".
Mahmud ne ya fito daga part din Abbie yaji wannan kalaman daga bakin twin sister dinsa.
Yayin da a waje itama Zahra data Gama fuskantar inda aka dosa ta kifa kanta a gefen kafadar mummy Badi'a tana sakin wani marayan kuka tana ayyana shikenan ta faru ta Kare wata sabuwar matsalar kuma.
A Hankali zahra ta bude idanunta sharaf da hawaye Jin motar ta harba da wani irin speed ta nufi main gate, ta juya ta yiwa gidan kallon karshe gidan data kwana Daya Tak a cikinsa da sunan matar dansu wadda a yau kuma bata San wane suna zata Zama ba, wata Kika sunanta ya tashi ya koma bazawa kuma, Dan rashin 'yanci ko Jakarta ta hannu ba'a Bata dama ta shiga ta dauko ba.

* AUREN HUCE HAUSHI*


AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah

99061432330

Or

08056362975

Page 78


.............
Cikin wani irin karsashi mahmud ya riko Aishat Yana fadin.
"Meye haka kikeyi? Kinfi Ammin sannin abinda ya Kamata tayi ne, Ni ne nace Mata idan zahra Bata kwanta Mata ba tayi abinda ya Kamata, ina cewa a gabanki komai ya faru? to meye kuma na daga hankali Allah yasa hakan yafi Alkhairin".
Ya juya ya fice daga part din gaba daya, mota ya shiga yabar gidan gaba daya, isolation yake bukata a yanzu Dan Kansa babu abunda yake sai Sara Masa besan me yasa Ammi tayi hakan ba amma jikinsa be bashi Wai an rabashi da precious bane har abada, akwai wata manufar yin hakan duba da zuwan gaggawa da yaga su mummy Badi'a da Hajja zuwaira matar kawu yusufu sunyi yasan da magana a kasa Kuma ga tafiarma a sirrance akayita ta kofar baya motarma Mai duhun glass ce,
Duk abinda mahmud ya fada Ammi taji shi sarai Amma tayi gaba dole ta nemarwa matarsa uwar 'ya'yansa Qima da mutumci bazata biyewa yarintarsu ba a haifi Dan da babu idanu.
Sama ta Haye tana lalubo number Aunty Surayya matar uncle Mustapha.
Daki Aishat ta koma ta dubo ko Afnan ta tashi tunda Abulkhairi Yana gurin Batool, Amma fa hankalinta yaki kwanciya so take taji daga bakin Ammi din dole su zauna.
Kwanciya tayi tana lalubo number sweet heart dinta dole su ta fada Masa halin da ake ciki saboda a gabanshi Komai ya faru akan yanda ya gigice daga yi masa fushin d'an lokaci to Ina ga anyi Mai dungurungun kuma, ai sai yanda Hali yayi tasan abinda ya fada kawai dauriya ce bawai har Zuciyarsa haka abin yake ba.

*******Tunda su zahra suka dauki hanya tayi shiru mummy Badi'a ke yiwa Zahra Hira da hannunka Mai sanda akan abubuwan da suka danganci zamantakewar aure da irin 'yan dabarun rike miji yaji ba wata sai Kai, ita dai zahra daga eh sai a'a take fada ko hanyar Bata lura da inda suke nufa,ita dai Hajja zuwaira barcinta take Sharawa tunda suka dauki hanyar dodar, tafiya Malam Habu yakeyi iya tafiya ga kuma lafiyayar mota, a Kano sukayi sallar azzuhur da la'asar suka dauki hanya zahra tayi mamakin yanda wannan bawan Allah yasan hanya haka gashi dai ya fara manyanta.

Karfe shida da rabi suka shigo Cikin garin Azaren katagum, dan rage tafiya Malam Habu yayi ya Dan juyo Yana fadin 'ranki shi dade Ina muka nufa gamu Allah ya kawo mu Azare".
Hanya ta ringa nuna Masa Yana bi har kofar gidan Abba.
"Masha Allah".
Mummy Badi'a ta fada a ranta ganin gidan da suka zo da gani Suma ba kashin yadawa bane da nasu rufin asirin daidai gwargwado dan ko makaho ya Shafa yasan da abun.
Horn biyu malam Habu yayi Baba sani ya leko ganin Bai sheda motar ba ya fito ya nufo su dai dai gurin window din driver ya leko gaisawa sukayi kafin Zahra tace Masa.
"Baba sani nice zahra ka bude Mana".
Da sauri ya juya Yana fadin "sannunku da zuwa ai bangane ba sai yanzu".
Suna sako Kai Cikin harabar gidan magaji na fitowa da sauri da alama wani uzirin ne ya taso masa ganin bakuwar mota Mata na fitowa yaja ya tsaya yaga su waye ganin Bai sheda su ya nufi hanyar ficewa yayi taku kadan yaji maganar Zahra daga bayansa tana fadin.
"Sulaimanu".
Da sauri ya juyo yana dariya.
"Kai Kice cere Bina ce ta shigo garin".
Mummy Badi'a bata san lokacin da dariya ta kubce Mata ba, tana kallon magaji Daya nufosu da sauri.
Gaishe dasu mummy Badi'ar yayi Yana fad'in.
"Sannunku da hanya Bismillah ku shigo, yayi gaba da sauri don ya isarwa da Ammah sako, haba Ashe da dalili shi dai yaga anata faman dafe-dafe Daya tambaya ba Wanda ya bashi amsa, Zahra na gaba su mummy Badi'a suna bayanta cikin gidan shiru ba kowa sai su zilai da sahura suna gyaran kitchen din waje daga nesa sahura ta hango su zahra zasu shige part din Ammah.
"Kai zilai Kinga kamar uwar dakinki sa wasu mata sun shiga part din Ammah".
Banza zilan tayi Mata tana ganin tsabar gulmace kawai irinta sahura wace zahrar kuma wadda bata kasar ma gaba daya, jin tayi banza da ita yasa ta hakura taci gaba da abinda takeyi.
Su zahra na shigowa Ammah da magaji suna fitowa daga kofar baya wadda aka Samar da ita saboda part din Abba.
Cikin farin ciki Wanda har ya bawa zahra mamaki, Ammah ta taresu tamkar tasan da zuwansu, Fadi take "sannunku da hanya kunsha doguwar tafiya nayi ta neman zahra dazu network ba kyau sai hakuri nayi".
Zahra taso ta shige jikin Ammah kamar yanda ta Saba Amman sai taji nauyin yin hakan a gaban bakin Ido sai dai dan kwantar da kanta tayi a jikin Ammah nan da nan taji wata karaya da tausayin Ammah ya kamata tunda ta Zama budurwa Ammah Bata huta da kwaramniyarta ba yanzu ma gashi ana murna anyi auren ga Kuma wata sabuwa ta bullo In "yan caca.
"Bismillah ku zauna Hajiya sannu sannunku fa"
Alawiyya ce ta shigo da katon tray dauke da abubuwan sanyi ta aje tana gaishe da bakin nasu.
Mummy Badi'a ce tacewa Ammah.
"Yauwa sannu Hajiya ya muka sameku".
"Lafiya kalau Alhamdulillahi"
Ammah ta gaishe da Hajja zuwaira.
Ruwa kawai suka Sha kafin a rakasu dakin da akayi musu masauki a Nan part din Ammah din Amma Yana daga can gefe daban ba'a fiye amfani dashi ba tunda da wadatar dakuna.
Magaji ma fita yayi da ruwa da kwalin exotic da Coke na gwangwani yaje ya budewa Baba Habu dakin Baki na waje lokacin Yana gurin Mai gadi suna Hira.
Kayan dake Cikin motar malam Habu ya Fara fitowa da magaji yana fadin.
"Dan Allah shigar musu da kayan nan".
Zahra dakin da take Zama ta shige tana mamakin yanda Ammah Bata nuna tsahin hankalinta ba duk da Batasan dalilin zuwansu ba ita da 'yan uwan Ammi.

Cikin Kan kanin lokaci magaji ya Gama shigo da kayan ya zube su a parlour ya shiga ya fadawa Ammah.



***
Su zahra basu fi minti ashirin da tafiya ba Part din Ammi ya fara karbar Baki matar Aliyu Halimatu ita ta fara zuwa Ammi batayi mamaki ba tasan karshen maganar kenan duk wanda ya samu labarin mahmud ya dawo zaiyi kokarin zuwa ya gani da idonsa ballantana tasan maganar zahra zata karade dangi shi yasa tayi wannan Kandagarkin ta turata gida duk masifar mutum da iya gulmarsa Saida ya koma da gwiwa a sage Dan Mai Kama da itama baze gani ba, kafin azzuhur part din ya dinke da jama'a 'yan taya murna, na gida Wanda suka Isa sai yan leke-leke sukeyi basa sama basa kasa, irinsu Habiba matar uncle saminu har gidan Hajiya Inna sukaje ita da Matar Ya Abdallah first born din Abbie, tasu tazo Daya da Habiba itama 'yar adawar mahmud ce ta gaske sai dai ita ta iya takunta ba lallai ne lokaci Daya ka ganeta ba,haka suka dawo ba wani labari sai Kuma suka shiga kokonton gaskiyar maganar yarinyar da aka fada yazo da ita.
Aishat na kwance Kiran Aunty Surayya ya shigo.
"Wai kina Ina ne tun Dan hantsi nake gidan Nan sai yaran nake gani Amma ke ko duriyarki Babu".
Yunkurawa tayi ta tashi zaune tana fadin.
"Ina masaukina a kasa bana Jin Dadi ne shi yasa, Aunty Ina wuni".
Dariya Ammi tayi saboda wayar a speaker take, tana ayyana kina min dacin Rai dai na tura muku Mata gida,Baku San nemar muku daraja nake yi ba duk wannan taruruwar murnar da ake zuwa ba domin Allah ake yinta ba saboda aga yarinyar da aka Kai musu labarin ta.
" Lafiya kalau, kizo sama yanzu Ina bedroom din Ammi".
Ta kashe wayar, saukowa Aishar tayi ta zura takalma ta fice tana hawan strains taji Kira ya shigo Mata tana dubawa Sameer ne.
Ta daga da sallama suka gaisa sannna ya Dora da fadin.
"Dake da waye zakuzo gidan oga na arkilla zaku duba wani Abu kuga Koda abinda za'a gyara".
"Ok Bari na fadawa Aunty Surayya sai muzo tare".
Ta fada tana tura handle din kofar bedroom din Ammin.
A zaune ta samesu su Aunty Surayya nata faman rubutu a Cikin wata jotter.
Da sallama a bakinta ta shiga ta gaishe dasu Ammin ta nemi guri ta zauna, Saida Aunty Surayya ta Gama rubutun ta dago tana kallon Aishat din.
"Ungo duba kin gani Koda gyaran da za'ayi".
Jotter ta karba ai Bata San lokacin da tayi super ta Haye jikin Ammin su ba.
"Allah ya Kara sutura Ammi, ya jikan mahaifi yanda Kika faranta Mana Allah ya haskaka qabarin Alhaji Haroona ya yalwata Masa, mun gode Amminmu sai yanzu na samu kwanciyar hankali wallahi".
Murmushi Ammin tayi.
"Allahumma Amin, da kin dauki fushi Dani Dan Ina nemar muku daraja da kima kinsa yau har sama Hajiya Babba ta hauro saboda taga kwakwaf tunda nasan yayan ki Ibrahim ya fada Mata komai har dakun Nan ta shiga Wai sau Daya ta taba shigarsu Ina jinta dasu Batool Suma da Taya bera Bari har kciki suke shiga Kuma jikin ba kwari ta sauka da kyar fa take taka kafar Amma gulma ta hauro da ita saman Ina jiyo wash wash dinta tana sauka".
"Allah ya kyauta ai ba Karamin Basu kafa mikayi ba Ammi sai yanzu na gane plan dinki na gaggawar ficewa da zahrar daga gidan Kinga kin kashe bakin tsanya babu batun mutum ya bugi kirji yace ya ganta da idanunsa, yanzu Sameer ya kirawo ni yace muje gidan bros na Arkilla muga wani Abu ko da abunda za'a gyara".
"To Kuma da boutique dina zakuje a hado lefen da za'a Kai musu can nasan ba wani abun azo a gani akayi Mata ba duba da yanda abun ya faru kinsan halin kayanki Kuma".
"To Bari mu Fara zuwa Arkillar in yaso sai mu wuce can din ko Aunty Surayya?".
A gidan suka Sami mahmud da wasu abokansa biyu sai sameer.
Suka gaishe da Aunty Surayya har tana zolayar mahmud.
Sameer ne ya shiga ya bude musu inda kayan da suka zo dasu daga Dubai da Kuma akwatunan.
"Auntyn mu gasu Nan ku duba idan da abinda babu ko za'a canza ko karawa sai a fada"..
Ya ja musu kofar, kayan suka Fara dubawa ba karya komai yayi harda abinda ma ba'a sakawa an saka sunyi santin kayan kamar me Dan naira da taci gidansu a gurin ba Bata lokaci suka shiga zubawa a Cikin akwatunan abinda ya daukesu kusan awa hudu suna Abu Daya.
Saida suka Gama komai sannan Aunty Surayya ta Kira Ammi video call lokacin Ammin tana gurin Hajiya Inna Dan ana shiga magariba ta fice ita da suhailat wadda ke driving dinsu suka nufi mabera gidan Hajiya Inna taje ta fada Mata komai ake ciki ta Kuma Bata hakurin yanke hukuncin da tayi ba tare da ta nemi Shawarar ta ba,nuna Mata Hajiyar tayi ba komai idan akace sai an tsaya ciccira maganar abin baze Zama sirrin ba hakan da tayi shine dai dai.
To Kuma saiga Kiran WhatsApp tunda duk gidajensu da wifi suke amfani.
Akwatunan Ammi ta Fara gani gasu Nan birjik sai da suka Kai karshe sannan Aunty Surayyar ta dago da wayar tana fadin .

"Ammi kin gani? To Dana ya Gama aikinsa Kaiwa kadai ya rage ba'a bukatar komai Ina za'a kawo Kayan? Can ko kuma a barsu a nan kawai?".
"Masha Allah, Kice kun hutar dani? Ki fada musu su kawosu gidan Hajiya kawai sai a fadawa Wanda ya kamata suzo su gani a Nan kawai".
Sukayi sallama Hajiyar ke tambayar.
"Me za'a kawo Mini Nan kuma?".
A kunyace Ammi ta fada mata".
"A'a kirawo su azo a kaini Arkillar na gani yaushe za'a wani kawo min Kaya da wani kiran jama'a su ringa dodon gani Abu guri yana neman kurewa ga Azumi Yana karatowa gara ayi a Mika Masa matarsa ai yayi rawar gani ma wallahi a 'ya 'yan zamani ba kowa ne zeyi abinda dan Albarkar Nan yayi ba, shi yasa yaki zuwa gidan kenan yayi min zaune a Nan yake min wasu maganganun a bai-bai".
Ita dai Ammi Dan murmushi kawai takeyi.
Daga Arkilla gidan Ammi su Sameer da Tajuddeen suka nufa da lefen har lokacin Su Habiba suna nan Wai suna neman Ammi suyi Mata sallama da momin kano Maman su Faruq wadda ta dawo da gefin magariba daga Dubai inda takeyo oder din Kaya, tana zuwa yaran ta suka fada Mata dawowar Ya mahmud din shine bayan tayi sallah ta shigo sai Kuma Bata Sami Ammin ba sun dauka ko tana part din Abbie ne.
Suna zaune aka Fara shigowa da akwatuna ana ajewa Saida aka shigo dasu gaba daya Nan kallo ya koma sama suna mamakin daga Ina kuma wannan su Aunty surayya ne suk shigo daga karshe Nan suke fada musu lefen mahmud ne, Akayi caaaa kowa na fadar Albarkacin bakinssa aka Fara daddagawa, ana wannan rarumar Ammi ta wuce ciki.
****
Saida su Aunty Badi'a sukayi salllolinsu Alawiyya da zilai wadda tayi suf ta baro sahura ta shigo, dazu Sarai ta gane zahra ta gwasale sahurar ne Dan kada tayi halin nata na kinibibi tunda Bata San menene dalilin zuwan ba ga Kuma Bakin fuska suna tare tana gani zata shiga gurin Mama ta Kai tsegumu Dan ma kwanan nan ta rasa me yake damun Mamar duk ta fada sai idanu gashi ta rage wannan izzar da wulakancin nan na ganin kowa a banza.
Sai da suka Gama suka kimtsa wannan Ammah ta shiga suka gaisa sosai tayi musu sannu da zuwa.
Aunty Badi'a ce ta Fara Kora bayanin dangantakarsu da Ammi sannan ta Dora da fadin dalilin zuwansu duk da Ammi ta yiwa Ammah a takaice.
"Hajiya ga yarinyar mu Nan mun kawo ta badon mun Raina iyawarku ba a'a bisa wasu dalilai na abinda ya faru da yaron muke son azo a daukar Masa matarsa a Cikin mutuncinta da kimarta kamar ko wace yarinya budurwa da ake aurarwa a gaban iyayenta,kinsan ko wane family akwai tasu matsalar da fatan bamu Bata muku ba".
"Kai haba wannan ai gyara kayanka ne kuma kun nuna Mana yanda kuke kaunar zahra da gaskiya mun gode sosai, ku huta kafin Abban nasu ya shigo ku gaisa".
Har Ammah taje baking kofa ta dawo tana fadin.
"Na shafa'a ga waya Hajiya zainab zata Kira tace min layinku baya shiga a nan kasar".
"Wallahi kuwa haka ake fama idan Suma suka shiga sai dai su sayi sabon sim na can wallahi".

Tunda zahra ta shige Bata ko leko waje ba, kwanciya tayi duk abun duniya ya taru yayi Mata yawa, ga Ammah ma bata ko leko ta ba tana ta bakinta shima meu amor shiru Bai nemeta ba haka Aunty Aishar itama shiru Sai taji Zuciyarta ta tsinke tasan shikenan sai yanda Hali yayi tunda har zuwa lokacin Bai kirata ba tasan Amminsa Bata sonta gashi harda mutane ta hadota a bawa iyayenta hakuri.
Aunty zilai ce ta shigo taga zahra ta rabsa uban tagumi ko daga inda take Bata tashi ba, ga abincin da aka kawo mata ko taba shi batayi ba.
Matsowa tayi tana fadin.

"Haba uwar dakina tagumi ai ba naki bane, wane gata ne Ubangiji baiyi Miki ba ai ke sai hamdala ta kamace ki".
Dago aexy eyes dinta tayi ta watsasu akan Aunty zilan tana fadin.
"Kayya Aunty zilai idan ana cin baure ba'a tona cikinsa Kuma daudar gora ciki ka shata, gida fa Ammimsa tace a rakoni a bawa Ammah hakuri Kinga abinda ma ta bani da zamu taho tace min sai wata rana".
Sai kukan da take rikewa ya kubce Mata.
Hakuri Aunty zilan ta Riga bata, tana Cikin kukan ne wayarta ta dauki Kira harta tsinke Bata daga ba da gaske abin yayi Mata ciwo da tasan karshen abun haka ze Zama da Bata yarda tayi irin wannan sabon dashi ba.
Wani Kiran ne ya shigo Aunty zilai ce ta dauka da sallama muryar yallaban taji duk sai ta daburce ta rasa abun fada, Cikin in Ina ta furta."yal..labai Ina wuni".
"Lafiya". Ya amsa mata in short.
"Ina zahrar take ne?".
Da sauri tace "gata Nan yallabai bansan meye ya sameta ba sai kuka takeyi"
"What! Kuka kuma?".

"Wallahi kuwa yallabai nayi lallashin nayi lallashin taki ta saurareni".
"Pls Bata wayar".
Duk abinda suke zahra na jinsu ita fa wani Haushinsa takeji su baro wannan garin nasu Mai shegen nisa tun Dan hantsi Amma ya kasa kiranta sai da ya mula ya mule da tsohon Daren Nan ze wani kama kiranta tayi masa me.
Kin karbar wayar tayi ai ba bakuwa bace Aunty zilan da zataji nauyi ta dauka ko Dan kunyarta.
"Ta tashi ta fita yallabai Sai hakuri kasan da yarinta a Cikin Lamarin ta".

"Ok shikenan"
Wayar ya dangwarar a Kan bed side yana lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya.

"Haba uwar dakina yallabai baici irin wannan hukuncin ba, kiyi hakuri kome yayi Miki ki daga wayar kiji meye ze fada miki".
Autane ya leko Yana fad'in.
Aunty zilai kizo inji Ammah tana bedroom dinta".
Ya juya ya fice daga dakin.

**

S.K.T
Saida kowa ya Gama iya nasa iya yin gurin ganin lefen Amma dai mutum ko shine hasidin Iza hasada Bai Isa ya mushe kayan Nan ba, Saima korafin sunyi yawa yarinya Kamar wata diyar sarki, ba dai Wanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login