Showing 189001 words to 192000 words out of 280244 words

Chapter 64 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1037

a nan gurin ku, duk da irin dumbun arzikin da Allah yayi masa, kinga yanda iyayensa suke da arziki kuwa duk sokoto basu da na biyu, amma sai nasa yacewa na iyayen kau ban guri, ki dafi yarinyarki da kirki dan inda zata shiga bana wasa bane, yanzu haka na taho mata da sakonni daga gurin dan uwana malam na sanka, dan ma yace Alhamdulillah yarinyar jikinta da tsari na gaske".

Tunda Hajiya ta kama zuba Ammah ke binta da aikin kallo wasu maganganu take fada wadanda ko cikin mafarki bata taba hasaso irinsu ba, ita fa ta kasa gane wai akan waye Hajyar ke magana ma tukuna.
"Wai Hajiya waye wannan din da kike bani labarinsa ne ban gane ba".
Wani kallon ina hankalinki yake Hajiyar tayi mata.
"Yo maganarwa zan zage ina miki in ba ta sirikinki mijin diyarki zahra'u ba, ai dalilin da yasa na taso takanas nazo kenan na fada miki ki koyawa yarinyarki iya zama da mutane duk da naga da wayonta yarinyar taki,amma ta koyi kamewa sosai dan naga alama sai kin kara mata karatu sosai na yanda zata rike mijinta sosai dan rirribinsa mata keyi kamar kudi shi kuma dan arzikin ko kallonsu bayayi tunda ya kyalla ido yaga taki 'yar tunfa wata tafiya da inaga mai gidan nan ne ya taba kaita wata kasa ko ina? na manta sameeru dai ya fada min to a tun lokacin yake bibiyar yarki idan ma baki sani ba".
Ruwan mamaki ne ya gama cinye Ammah a zaune yanda Hqjiya ta bude aiki gaba daya, nan da dunga zayyano mata ko waye mahmud har abinda ya shafi uwarsa da inda ta fito saida ta zayyane mata tas.
Godiya dai Hajiya ta shata gurin Ammah, kayan da Hajiyar ta kawo ta bukaci a shigo dasu, Alawyya Ammah ta kira a waya ta fada mata ta shigo da kayan baki sukazo dasu bedroom dinta, ba yanda Ammah ba tayi da Hajiya ba akan tabar bude kayan sai taci abinci amma tace a'a sai tayi abinda ya kawota tukunna.
Bayan ta gama nunawa Ammah komai da yanda za'ayi amfani da komai sannan suka nufo parlour Taci abinci.
Abdul Hakeem ne ya rako sameer suka gaisa da Ammah, ya fada mata zasu yau zasu wuce tare da Zahra saboda an samu canji tashin flight din dole ta Abuja zasu tashi saboda yana yin weather ta kano bata da kyau jirgi baze iya tashi ba, dan haka flight bakwai zamu mu kwana a gidan kanin mommy.
Hajiya ce tayi tsagal tana fadin .
"Wai ku bazaku daina tafiyar katangatse ba sufa mata 'yan tsiri ne bazu fadawa mutum abu ba sai yanzu yanzu a gurguje".
"Ayi Hakuri haka umarnin suke".
"To ni zan fadawa mahmudun yanzu da dah ba daya bane garin irin wannan shima wata rana zata shafeshi dan za'a manta abu mai mahimmanci daya kamata a dauka".
Ammah da kanta ta shiga inda su zahra suka baje kolin hira, fada mata tayi tazo ga sameer ya shigo ta juya.
Tare suka fito da Rukayya, zahra ta gaishe shi yace tazo ya kaita gida ta shirya yau zasu wuce kano, nan yayi mata bayanin canjin da aka samu.
Kamar zata fasa kuka ta tashi ta ahige bedroom din Ammah.
"Tashi kije gurinta abun ne yazo mata bazata".
Ammah bataki ba ta tashi ta nufi gurinta din, samunta tayi ta hada kai da gwiwa tana shsshsheka, dafata tayi a ka tana kiran sunanta, dago sexy eyes dinta tayi wanda suka jike da hawaye, girgiza mata kai Ammah tayi alamar ta bar kukan, tashi tayi ta rungume Ammar tana fadin.
"Ammah wai fa india zan bishi, kuma wallahi bai fada min an samu visar ba".
Bayanta Ammar ta dan bubbuga.
"Kiyi hakuri wasu mazan haka suke ba komai suke fadawa mata ba, kuje da yarinyar nan ta tayaki ki shirya sai kizo nan ma kafin ku dawo na hada miki abunda ya kamata,ke dai kiyi masa biyyayya duk abinda ya sakaki kiyi masa matukar be sabawa Allah ba, duk ida rayuwa ta kaiki ki zama mai hakurin zama da jama'ar da Allah ya hadaki dasu, ki girmama masa iyayensa ki daraja masa 'yan uwansa, kada ki bari kema a raina ki kada ki zama mai nuna halin ko in kula akan lamarinsa ko kiyi farin ciki lokacin da yake cikin halin damuwa, ki zama jaruma mai dauke masa bukatunsa kiyi juriya akan duka binda ya bijiro miki dashi, ki zama mai kauda masa Qishirwa duk lokacin daya bukata. Allah yayi miki albarka ya albarkaci aurenki, kuje kada kuyi dare a hanya".

* AUREN HUCE HAUSHI *

0906143233
My WhatsApp number
Or
08055362975

MAMAN FATEEMAH.

WANNAN LITTAFIN BA MALLAKIN KOWA BANE GURIN JUYASHI ZUWA AUDIO KO WATA SIGA BADA IZININ MARUBUCIYA BA DAN HAKA A KIYAYE.

Godiya ta musamman gareku 'yan uwana
Farida Isah.
Nafisa Isah.
Umma Hani Isah.
Amina Isah.
Fateemah Mabruka Isah.
bisa karfafani da kukeyi a Kan wannan rubutu da nakeyi Allah yabar Mana zumunci ya Raya Mana zuri'a yayi musu Alabarka.

Page 68.



.............
Cikin abinda Bai wuce minti talatin ba su Zahra suka Gama duk abinda ya kamata suyi a cikin gidan, suna parlour ne Aunty Rukayya ta Dan kalli Zahra Wadda ta cika fam.
"Wai ke fushin na menene? Ni na tab'a ganin irin wannan Abu naki, idan wata ce da yanzu ta rasa Ina zata tsoma ranta Dan Dadi gurin your love fa zakije ba Naga kin sakawa number dinsa haka ba? Ko a Baki sunan ya tsaya kawai babu a aikace? Kije ki tarairayi kayanki ki bashi more happiness Mana! Kada kiyi Sanya Ina ganin big bro dina fa me zafi ne, dan haka dole ki Zama irinsa koma ki Dara shi".
Narai narai tayi da idanunta tana kallon Rukayya da walainiyar hawaye a cikinsu sai sukayi wani irin kyau.
"Nifa Aunty Rukayya wallahi tsoronsa nakeji idan yana fada min wasu maganganun sai Naga shi Kansa sun girme Masa ballentana ni, Kuma fa ina Jin Kamar wannan tafiyar zata canza min abubuwa, Kuma ma in fact Ina tsoron haduwar mu wallahi".
"A'a ban fashimta ba? Kina tsoron haduwar ku Kamar Yaya?".
"Aunty bazaki gane ba, nifa still I am a vagina".
Hannu tasa ta rufe bakinta cikin bala'in mamaki.
"Are you sure?".
Kai ta gyada Mata.
"Yes..."
Neman gurin Zama Aunty Rukayya tayi, tana jinjina Lamarin big bro din, nisawa tayi tana kallon Zahra Wadda Kamar ance Mata yanzu Lamarin ze tabbata.
"Amma gaskiya nayi mamaki kwarai da gaske, to shi wane irin waliyi ne akan Mata? Me Kamar ke ya Zuba Miki ido Yana kallonki tsawon lokacin nan, ko dai bashi da lafiya ne?".
Ta jefawa Zahra tambayar.
"A'a wallahi lafiyarsa kalau kawai dai...."
Sai Kuma tayi shiru.
"Ki kwantar da hankalinki ba abinda ze faru, Ina sakon da mommy ta aiko Miki dasu kina kano?".
"Nayi amfani dasu yanda na gani a cikin bayanin".
"Good, yayi yanzu ma kici gaba da amfani da Wanda nazo miki dasu kinsan takanas ta tayo Miki order su daga Birnin inda kanwata ke Aure, magunguna ne na gaske kada kiyi Wasa dasu Kuma idan mukaje Kano zance Ya Sameer ya kaiki mommy tana son ganinki naji suna magana da Maman kwantagora zata Baki Addu'oin da zakina yinsu" .
"Ok Nagode Aunty Rukayya Allah yabar kauna".
"Allahumma Amin".


Lokacin da suka dawo Ammah ta hadawa Zahra komai harda abubuwan amfanin kitchen kayan da Hajiyar makwarari ma ta kawo Saida ta Zuba musu fin Rabin kayan.
A gurin Abba Zahra ta tarar da Hajiyar makwarari suna ta Hira dashi tamkar d'a da uwa, wata nasihar ya Kara yiwa Zahra sosai Wadda ta karasa karyar Mata da zuciya sai taji tamkar yau ne zata rabu dasu zuwa gidan auren nata. Lokacin da suka fito zasu tafi ne sahura ta dawo daga Aiken da Mama tayi Mata wani gari a cikin Jigawa area din gwaram, da sauri tayi ciki ta nufi dakin Mama wadda duk yau babu Wanda ya sakata a Idonsa idan ka dauke magaji, ko knocking Bata tsaya yi ba ta tura kofar ta shige ba kowa a parlourn corridor din bedroom din ta shiga da sauri Kamar zata tuntsira knocking ta dunga yi Amma shiru tamkar babu Mai rai a ciki haka ta gaji ta dawo parlour.
Har gurin mota Abba da Ammah da dasu Auta Saida motar tabar harabar sannan su Ammah suka koma ciki,sun rabu da Hajiyar makwarari da alkawarin zataje kano har gida ta gaisheta.
Tunda suka taso Hajiya ke Zuba ita ta zauna a kusa da Ya Sameer har Kano bakinsa Bai huta ba ko yayi shiru saita nemo abinda dole yayi magana.
Karfe biyar da kwata suka shigo Kano Hajiya yaso ya Fara saukewa tace ya wuce da ita gidan mommy sai da dare direba ya kawo ta gida, ba yanda ya iya dole yayi yanda take so.
Kamar mommy ta goya Zahra haka ta dunga nan nan da ita.
Dakin Aunty Rukayya Zahra ta sauka, a nan mommy ta shigo ta sameta tayi tagumi tayi nisa cikin tunani.
"Meya faru ne diyata ko kina da damuwa ne?".
Mommy ta fada tana Zama kusa da Zahrar.
"Babu komai mommy".
"To Masha Allah, kina jina abinda Zan fada Miki ki rike Mijinki da kyau kada kiyi sakacin da wata zata samu damar shige Masa suna da 'yan Mata a wannan families din nasa Kamar me Kuma kowace uwa gurinta mijinki ta shinshina ta samu damar lika Masa 'yarta ga Addu'oi da Hajiya Mama tace na baki lokacin Dana fada Mata a kawo Miki salon da Rukayya ta kai Miki, kina jina dauko wayarki ki rubuta a notepad din ciki".
"To mommy nagode".
"Kina jina da farko Zaki samu tsamiya Mai kyau ki jika da jiku da dare idan Zaki kwanta ki taci kadan ki tofa YA WADUDU kafa bakwai duk kafa Daya ki Fadi sunan mahmud ki tofa haka zakiyi harki Gama saiki shanye, haka Zaki ringa yi in Sha Allah soyayya dai Zaki gamta a gurinsa kinsan duk yanda kike a zuciyar mijinki kina bukatar Karin samun daraja da soyayyar mijinki yaji babu kamarki a zuciyar kinji".
"Naji mommy in Sha Allah zanyi".
"To Allah ya kaiku lafiya kiyi ta hakuri Lamarin Zama da wasu dangin Saida hakuri zakiga abubuwan da suka Sha banban da naku al'adun da dabi'u to sai kin nutsu sosai kin Zama Mai kula da koma da lura".
Karfe bakwai flight dinsu ya tashi daga Kano zuwa Abuja, harda Fateeha akazo airport din sai a lokacin Zahra tasan da Oga Sameer zasu tafi.
A gidan kanin mommy suka kwana matar gidan yarinya ce duka haihuwarta biyu tunda Aunty suhaima taga Zahra taji yarinyar ta kwanta Mata a rai da gani ta samu tarbiyya Bata da rawar Kai irin na yaran yanzu more especially idan Allah yayi musu baiwar kyau zaka samesu da iyayi da fadin rain Koda ba 'ya'yan kowa bane. Sun Dade suna Hira kafin Zahra ta kwanta saboda zasuyi sakkon fita tunda flight din seven fifteen zasu bi.
Duk wani Kai kawo Fadi tashi Sameer ne yayi musu ga Zahra ta dauko kayan sakawa abinda basu Saba ba a dabi'ar tafiye-tafiyensu, Aunty Rukayya ta zuga Zahra tace ki dauki duk kayan da kikasan kina sonsu kinga dai wasu ba samunsu zakiyi a can ba,idan ma kin Sami to dinkin zakiga baiyi dai dai da ra,ayinki ba.
A VIP suka zauna, ko a Adis Ababa da sukayi lending Zahra batabdamu data fita ba, Saida suka kusa tashi ta fito ta Sha minerals kawai da snacks.

Cikin da???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?re suka Sauka a Indiri gandi international airport.
Lokacin suka sakko mahmud Yana gefe ya nade hannunsa a kirji a gurin da ya zuba Mata Ido shifa yana kishin yanda take fita mutane suna ganinta, ko shida take mallakinsa da kyar yake iya control kansa idan ta doso inda take to Yaya Wanda ba muharramanta ba, ga wani abun mamakin Sam Sameer Bai fada masa tare zasu zo ba.
Dube dube Sameer yake da waya kunnensa yanaji tana vibrating a jikinsa yaki dauko ta, a hankali yake doso inda take ta baya shi kuma Sameer ya juya Yana kallon gefensa na dama, scent dinsa ya fada Mata ya kusanto ta kafin ta ya saka hannunsa ya rugumota ta baya.
Luuuu yayi da idanu lokacin da taji ta a cikin jikinsa take taji wata irin nutsuwa ta saukar Mata, a tare suka sauke wata ajiyar zuciya, hannunsa ya saka duka biyun ya Kara sakata a jikinsa.
Kamar ance Sameer ya juyo sai Idanunsa sukayi Masa kyakykyawan gani, wani smile yayi ya bace bat daga gurin.
Saida ya samu nutsuwa sannan ya Dan janye daga gareta.
"Preciousss.. you are highly welcome to india, idonki kenan kin manta Dani Ko? Na Zama Kamar narayan Daya rasa uwa".
Hannu yasa ya dago fuskarta Yana Karewa fuskarta kallo yayi Mata wani smile Mai ma'anoni da yawa, handbag din hannunta ya karba ya rike hannunta
"Ok let's go"
Dan waige-waige ta fara Kamar tana neman wani Abu.
"Wai me kike nema ne?"

"Tare fa muke da oga Sameer, Kuma Naga ban gansa ba".
"Ki rabu dashi ze shigo da safe saiya tsaya ya taho Miki da kayan da yace Rukayya ta saka kin dauko".
Ya fada Yana dan Jan tsinin hancinta.
Shi yake driving din motar da hannu Daya, dayan kuma Yana rike da nata hannun.
Ta gajj iya gajiya so take tajita a kwance kawai, ba gidan dasu Habib suke ya nufa ba, directly Leela palace ya nufa da ita, dakine na Alfarma tun a parlour ta Zuba ta gaji da gasken gaske duk Bata Jin dadin jikinta ga yanayin da take ciki duk a tsantsance take jinta.
Kusa da ita ya zauna Yana Dan matsa Mata jiki kadan.
"Wash! Allah, wallahi I am so tired".
"Ok Bari na hada Miki Ruwa kiyi wanka zakiji dadin jikinki ki Dade ne bakiyi doguwar tafiya haka ba".
Hannuwanta ya Kama duka biyun.
"Oya tashi mu shiga kiyi wankan ki huta".
Cikin bedroom din suka tana jikinsa.
Kan hadaddan royal bed din dakin ta kwanta,shi kuma ya wuce toilet din bai Dade ba ya fito, har lokacin tana kwance dagota yayi zip din rigar ya Fara kokarin zugewa.
"Dan Allah ka Bari Zan shiga na cire da kaina".
Ba musu ya bar Mata rigarta ta tashi ta wuce ciki, ta Jima tana gasa jikinta da ruwan zafin daya hada Mata, Bata taba tunanin harta Gama wanka base shigo ba Amma abin mamakin ko a leke bai leko ba.
Duk wani abun bukata ta tarar dashi a ciki.
Daure da towel ta fita hannunta Daya Kuma tana rike da k'arami tana goge gefen gashinta inda ya jike.
Wayarsa yake daddangwala baiko dago Ido ya kalleta ba.
Harta Gama abinda zatayi ta saka kayan barci said lokacin ya kalleta me zaki?i a kawo miki?"
Ya fada Yana kallonta daga sama zuwa kasa.
"Ba komai barci nake son yi".
"Ok. To hauki kwanta Ina wani aiki ne"..
Saida ta hau tsakiyar gadon ta zauna sannan Zahra ta gaishe shi tare da tambayar Mai jiki.
"Jiki Alhamdulillahi, wato har yanzu bazaki daina yi min gaisuwar Hausawa ba ko? Kin Dade baki ganni ba Amma ba irin concerned din nan ko".
Dan juya Masa sexy eyes dinta tayi.
"Nima ai ba wani wani concerned daka nuna min, Kamar ma bakaso nazo ba, bleeding fa nayi da kwana na ya Kare Saida kaje kayi min addu'a a qabarina".
Ta wani turo Baki irin na yaran Nan.
"Subhanallahi wallahi dokin ganinki ne ya sakani mantawa da matsalarki, tunda naji abinda ya kawo Zubar jinin na samu nutsuwa, to sorry Bari nazo ki fada min yanda abubuwan suka faru Kuma naji dumin jikinsa Mai saka min nutsuwa".
Ya aje wayar ya taso ya shigo jikinta yana Dan hura Mata iskar bakinsa a saman idonta sannan ya Kai bakinsa Yana Dan Wasa da cikin kunnenta da harshensa, a hankali ya Fara fada mata.
"I don't have words to describe what I feel for youuu.. I fall deeper in your love with every passing day, pls help me I am madly in love with you mi babe".
Ya karasa fada Yana Bata wasu hot kisses Yana Kuma shawagi da hannunsa a cikin rigarta, wata irin tsuma ta Fara tamkar Wadda Zazzabi Mai rawar sanyi ya Kama.
Bakinta sai rawa yakeyi ta kasa furta ko kalma Daya Dan da zafinsa yake tafiyar da ita sun dauki dogon lokaci Yana sarrafata sai da yayi Mai isarsa ya maida Qishinta da yake tare dashi sannan ya gyara Mata kwanciya ya sakata a jikinsa suna sauke ajiyar zuciya su duka.
Barci sukayi har suka makara sallar Asuba, barcin suka Kara komawa manne da juna, hankalin Zahra a Dan kwance yake tunda tasa iya dai haka za'a tsaya ba inda za'a tafi.
Sai wurin Sha daya da rabi suka tashi duk yanda Mahmud yaso suyi wanka tare kiyawa tayi, ya za'a ta yarda yaga wannan bulbular.
Kafin ta for yayi musu order Abincin break fast, sunci sunyi hani an kafin su wuce Asibiti.
Alhamdulillahi jikin baba Malam din da sauki sosai, kamar ya Goya Zahra Daya ganta, sun Jima a Asibitin, suna Nan su Abubakar ya shigo tunda Habib Yana tare da Baba Malam din tunda mahmud ya tafi dauko Zahra a airport shi ya zauna a gurinsa, sunanan Sameer ya shigo ya duba Baba Malam din, wani kallon kasa kasa yake yiwa mahmud din, da gani magana ce fal a bakinsa, dasun hada Ido saiya sakar masa wani murmushi.
Sai wurin la'asar Baba Malam yacewa mahmud ya Kai Zahra can inda suka sauka ta Kara hutawa.
Tare suka fito da Sameer.
"Sir ga kayan madam Ina za'a Kai su Naje can gidan bakwa nan..
Ok ka kausi Leela palace can tayi nata masaukin".
Yayi gaba ya nufi Zahra dake can gefe tana jiran su Gama su wuce duk ta matsu ta gyara jikinta.
Saida suka dauki hanya sosai mahmud ya riko hannunta Yana Mata kallon da Bata iya jurewa daga idanunsa.
"Preciousss... Wai yaushe abun nan ze tafi ne yafa shigar min rayuwa, naga kamar ya Kara kwanaki fa?".
Wata irin faduwar Baga taji,me yake nufi da wannan tambayar ne Kuma?".
Duk tsoro ya kamata nan da nan

* AUREN HUCE HAUSHI*


MAMAN FATEEMAH.

Page 69.


..........washe gari basuje asibitin da safe ba daukar ta yayi suka fita,boutique suka shiga na kayan sakawa suka loda ita abun har mamaki ya Bata, da farko cewa yayi ta zaba da kanta sai ta dauko kamar set shida sai inner wears data dauka, Yana kallonta Yana ganin haka ya dauko babban basket ya Fara lodar Kaya da na gurinsa ya cika ya dauko wani da taga abun nasa ba Mai karewa bane ta Fara hada shi da Allah akan ya barsu haka bafa aaidawa zasuyi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login