Showing 255001 words to 258000 words out of 280244 words

Chapter 86 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1040

yayi min text message na inda Zan raka Bilyinun da address din asibitin da zamuje da number likitan da zamu nema, wallahi Ammah ki yarda Dani bansan gurin waye zamuje a Jos din ba Saida likitan da muka samu yayi Mana jagora zuwa dakin da take sannan Naga itace, Ni kaina mamakin abin yaki bani to meya hada Salma da Ya Mahmud Taya akayi yasan halin da ake ciki, nayi tunanin ko Zahra ce ta fada masa sai Kuma nayi tunanin ai Nima fada tayi lokacin Dana fada Mata".
Nisawa Ammah tayi tana jinjina maganganun magajin, haka Aunty Hassana ma.
"Allah ya kyauta ya rufa asiri, Amma abin da mamaki dai gaskiya".
Dan murmushi Aunty Hassana tayi. "Babu mamaki wallahi Ammah, wannan mijin na 'yarki ba karamin mutum bane ni lamarinsa ya daina bani tsoro idan akace miki yasan abinda mu Bamu sani ba a cikin gidan Nan kada kiyi mamaki Dan Naga Bai dauki Lamarin 'yar Nan taki da sauki ba ze iya yin komai saboda ita kina jifa tun zuwan su Zahra Jordan ita da Abba suke bibiyar yarinyar nan".
Tashi magaji yayi Yana fadin "Allah ya huci zuciyar sirikar masu abun, nifa yace can Zan koma kusa da Zahra tunda Aminiya ta ce, Ina ga fa hijira lahu ta tabbata a gareni, Idan kin shirya Aunty ki fito na kaiki gida".
",Kai dai Allah ya shiryeka wallahi gidan kanwarka zaka tafi ka tare saboda abun kunya gaba ka bashi ba baya ba".
Aunty Hassana ta fada.
Dariya yayi kawai ya fice.


*******

Zahra na kwance tayi pillow da cinyar Mahmud bayan sunyi wanka Yana tunke Mata gashin kanta Daya zare Banda din yana fadin "precious kinsan Allah na yarda da abinda Hausawa ke fadin ta ciki na ciki ta baka na baka, Naga fuska biyu muraran, Bari na dauko Miki abun daga tushe yanda Zaki fi gane abinda za fada Miki"..
Gyara kwanciya tayi tana facing dinsa shi Kuma Yana Wasa da wani zare da ake daure gaban rigar barcin dake jikinta Wanda shi kadai ne ya rufe gaban rigar.
"Sunana Mahmud Muhammad Dange mahaifina general Muhammad Dange Dan asalin garin Dangen shuni ne, local government ce Mai zaman kanta a Nan sokoto, mahifinsu Abbie sunansa Alhaji sa'idu jibrin Dange Mai kudine na gasken gaske su goma Sha hudu ne a gurin mahaifinsu goma uwarsu Daya ubansu Daya sai Sa'id shi kadai uwarsa ta Haifa ta rasu sai Kuma Halisa itama uwarka ita kadai ta Haifa Amma ita uwarta tana gidan, sai Allah ya sakawa Alhaji jibrin tsananin soyayyar sa'id tunda yaro ne mai hakuri da wuya ya Fadi anyi masa Abu Saidai idan Alhajin ya gani ya tsawatar, ko a harkar kasuwa Alhajin yafi son ya tafi da Sa'id ko gidajen man petrol dinsa ze je to da said yake tafiya abinda ya kawo rashin jituwa kenan a tsakanin Sa'id da 'yan uwansa, sannu a hankali Sa'id na bin Alhajin guraren cinikinsu har Allah ya hada sa'id da wani Alhaji sani gada,Wanda shine sila ta samun asalin dukiyar data yad'u har jikoki, Dan tankar Mai ya Ringa sauke masa yana bashi a kan farashin kamfani, kafin wata shida jari ya kankama, kafin shekara sa'id ya hada jari na ban mamaki.
Ganin haka sai 'yan uwansa suka huro wuta akan kasuwarsa.

Sa'id Bashi da tsoro ko alama haka akayi ta juyawa da :yan uwansa.
Zuwa lokacin da zasuyi Aure shi sa'id Allah ya hada shi da Hadiza 'yar Asalin kwantagora ta jihar Niger.
Cikin ikon Allah 'yan watanni kalilan ciki ya bullo jikin Hadiza sunyi rainon cikin tare, Dan Allah yayi shi mutum ne Mai son 'y'y ga tausayin mace gashi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? daidai k
Lokacin arzikinsa sai Kara habaka yake, abinda ya tsone idanun 'yan uba kenan duk da kowa da nasa rufin asirin sosai tunda Allah ya saka Albarka a cikin neman nasu Amma saboda sa'id ya Zama zakaran gwajin dafi sai yafi tsaya musu a wuya sosai gashi matarsa Hadiza Bata daukar raini duk da itace karama a cikin matan da aka Auro.
Lokacin da cikin yakai wata Tara iyayenta sunso ta koma gida kontagora ta haihu Amma sa'id ya shafawa idnunsa toka ya Hana yace sai dai a turo wadda zata zauna da ita Sai hakan akayi, cikin Rahama ta Ubangiji kafin a kaiga turo kowa cikin Daren wata litinin nakuda ta kamata kafin ya kaiga fad'awa kowa Allah ya sauketa lafiya ta haifi yaronta namiji murna ba magana murna gurin sa'id Kamar me haka mahaifinsa da sauran dangi wadanda suke kaunarsa,'yan uwan Hadiza sunzo ranar suna yaron yaci suna Muhammad Auwal sai ake ce Masa mahummad kawai.
Tun daga Nan haihuwa ta budewa Hadiza ta haifi Maimunatu sai Mustapha, Saminu, tana goyon saminu ne Allah ya yiwa mahaifinsu sa'id Alhaji Jibrin rasuwa sa'id.yayi kuka Kamar ba gobe Amma dole aka dangana, bayan anyi arba"in akayi rabon gado kowa aka bashi nasa rabon sa'id yaso su hada kasuwanci da 'yan uwansa Amma sai mahaifiyarsu tayi tsalle ta dire tace cutarsu zeyi tunda yafisu sanin Kan kasuwa kowa yaje ya juya nasa tunda kowa Yana da nasa nasibin, dole ya hakura sai Kuma zaman lafiya yayi kaura daga cikin family din Koda yaushe cikin tashin hankali ake ga an tsangwani yaran Hadiza saboda duk cikinsu babu masu nagartar 'ya'yan ta kyawawane sosai, ganin zumunci Yana neman ya lalace yasa kanin mahaifiyar sa'id dake sokoto ma'ikacin gidan ruwa ne har yakai matsayin baturen ruwa na jaha gaba Daya yace ya taso daga dangen ya dawo sokoto hakan akayi sa'id ya bada kudi aka saya Masa gida Mai kyau da tsari tunda lokacin harkar petrol ta bude sosai harya mallaki gidajen Mai kusan uku a cikin kwaryar sokoto.
Bai fadawa kowa halin da ake ciki ba sai ranar da zasu bar garin, ba wani damuwa 'yan uwan suka nuna ba ya tattaro Kan iyalinsa suka dawo sokoto, anan yaransu sukaci gaba da zuwa makaranta, bayan an yaye saminu aka haifi Aliyu sai Kuma haihuwar ta tsaya, kafin shekara biyar arzikin sa'id ya habaka sosai Dan Nan da Nan sunansa yayi fice a sokoto ga taimako har 'yan uwansa Bai ragesu ba duk da kowa da nasa rufin asirin, makarantar sojoji aka Kai Muhammad tunda Daman shine ra'ayinsa da taimakon kawun mahaifinsa Allah yasa aka samu a kaduna, Maimunatu Nan kwatarkwashi aka kaita boarding itama sannu a hankali rayuwa na juyawa har Muhammad ya Gama makarantar sojoji lokaci tuni Maimunatu ta Gama secondary dinta ta shiga poly har da maganar Aurenta a gida, shi Kuma Muhammad ya tafi wata makarantar ta sojojin a Jos.
Su Mustapha da saminu da Auta Aliyu kowa Yana nasa karatun.
Lokacin da akayi bikin Maimunatu Muhammad baya Nan ya tafi wani course America, a can Allah ya hada shi da Mr Johnson baturen ingila kuma masanin sirrin kasuwanci sun hadu dashi ne ta dalilin kanwarsa wadda suke course din tare Anita sunyi sabo sosai da ita tana da kirki yawanci tana tambayar Muhammad abinda ya shige Mata duhu, ta dalilin Mr Johnson Muhammad ya Fara business da kudin da suke samu tunda basu zauna a banza ba idan suka Gama bunda zasuyi suna fita suyi aiki Wanda ake biyan mutum par hours.

Da taimakon Mr Johnson din Muhammad ya Fara turowa Dan uwansa Mustapha Kaya idan yayi order sai ya turo Nigeria Kuma cikin Rahama ta Ubangiji Kayan masu da an kawo sai masu sari su sayen ga mahaifinsu ma Yana Kara koyawa Mustapha dabarun kasuwa kafin wani lokacin jarin yayi karfi na ban mamaki abinda yaso ya kawo sabani Kennan tsakanin saminu da Mustapha Dan karara saminu ke nuna Jin zafinsa akan zabar Mustapha da Muhammad yayi ya Dora akan kasuwarsa, Saida Hajiya inna sunan da wani yaron makotansu ya saka mata tayi Jan Ido da fada na tashin hankali sannan abun ya lafa, Dan yanda saminu ke nunawa 'yan uwansa tamkar 'yan uba.
Haka akayi ta juyawa har lokacin dasu Muhammad suka dawo lokacin tuni Maimunatu ta haihu yaronta Tahir har Yana yawonsa ko ina, Basu Dade da dawowa ba akayi masa posting Calabar cross river State da matsayi Mai girma, abinda ya tilasta ya tashi neman Aure kenan tunda Daman akwai wata yarinya 'yar makotansu da suke soyaya da ita Ammaratu yaso ta sosai sai dai lokacin da yake kokarin tafiya course dinsa mahaifinta yayi maganar Aure sai aka fada Masa ga inda zaya shi Kuma yace yarinyarsa ta Isa munzalin Aure, abinda ya Hana Auren kenan a wancen lokacin, akayi Mata auren da wani, abun bai kai ko Ina ba ya lalace Wai mijin yace Bata da lafiya dole aka raba Auren, to dawowar Muhammad suka Kara hadewa duk da Da farko Hajiya Inna taso ta Hana Amma Alhaji sa'id ya nuna Mata tayi hakuri ba'asan abinda Allah ya hukunta a tsakaninsu ba, idan da Rai a gaba Saiya auri budurwar, ba'a dauki lokaci ba aka Sha bikin Muhammad da Ammaratu suka tattara suka wuce calabar, yayi mamaki yanda ya tarar da ita budurwa tunda yasan tayi Aure sai lokaci ta bashi labarin ai Bata tab'a yarda da mijin ba shine yace baze iya ba Bata da lafiya.
Cikin ikon Allah wata buyi da aurensu ciki ya bullo a jikin Ammaratu zokiga murna gurin Muhammad, namiji ta Haifa yaci sunnan Abdullahi, sai Ramlatu sai Habiba, Ibrahim tana goyonsa suka dawo kaduna lokacin Yana da mukamin canal, daga gefe Kuma kasuwanci yayi wani irin karfi.
A kaduna Allah ya hada Abbie da momin Kano 'yar sarautar Kano ce, hutu taje gurin yayanta Allah ya hada su babu Bata lokaci iyaye suka shiga Hajiya Ammaratu tayi tashin hankali Kamar ba gobe dalilin da yasa ta koma sokoto da Zama kenan.
Amarya ta Fara tarewa a sokoto kafin su wuce kaduna, itama da Albarkar haihuwa tazo ta haifi ummu Salma da Jamila, tana goyon Jamila wani aiki ya taso na kasa da kasa lokacin yaki ya barke da 'yan tawayen MALI Abbie ne ya jagoranci tawagar sojojin Nigeria zuwa malin.
Sun dauki wata da watanni suna fafata yaki da 'yan tawayen kafin a karya lagonsu duk da tallafin da suke samu na makamai daga wasu kasashen duniya, ana murna anci galaba sai Kuma suka bulla wani bangare ba na yankin Agadas ta jamhuriyar Niger Daman Suma ana fama da 'yan tawayen Abzinawa.
Dole aka nemi Karin sojoji daga kasashen ecowas aka kara turawa arewacin Niger din, a lokacin ne Abbie ya koma Niger aka Kai wani can MALI din.
Cikin ikon Allah suka dakile 'yan tawayen, wata rana suka fita zasuje wani kauyen buzaye sayen Kayan dafa shayi, suna cikin tafiya Hilux dinsu ta samu matsala gashi babu gari a kusa sun fito sunyi cirko-cirko sun rasa abun yi gashi babu order order a tare dasu, sunan a tsaye suka ringa jiyo qugin injin mota ba'a Dade ba motar ta nufosu su Abbie suka Zama cikin Shirin Kota kwana tunda guri ne da babu tsaro ganin sojoji yasa masu motar suka rage gudun motarsu maza ne guda biyu a gaba da alamar uba da d'a ne sai Mata biyu a baya babbar mace sai yarinya budurwa Mai wani irin kyau Mai fisgar hankali a kusa da ita, suna tsaywa Abbie ya karasa ya gaishe da Babban mutumin, sannan suka gaisa da Dan nasa anan yake tambayar meya faru da motar? Bayani yayi masa na Suma Basu San abinda yake faruwa ba kawai sun fito ne zasu shiga kauyen dake gabansu sayen Kayan shayi shine motar ta samu matsala.
Dansa Daya Kira ishai ya umarta daya fita su daura igiyar jan mota su fitar dasu daga wannan gurin Mai hadari.
Gurin window din da Hajiyar ke Zaune Abbie ya Dan leka ya gaishe da Hajiyar ya dago idonsa ze juya caraf suka sarke Dana yarinyar dake kusa da ita, da sauri ta juyar da fuskarta Dan ji tayi zuciyar ta kamar zata fito Dan dokawar da takeyi. Ba zato taji mahaifiayarta na fadin "wani irin sakarcine haka zainab kina ganin yaro yazo ya gaishe mu ke ki kasa gaishe shi?"
Shi dai gaba yayi Bai tsaya yaji me zata fada ba Dan kusan Abu iri Daya sukaji lokacin da suka hada a idon.
Basu tsaya a kauyen ba dole suke wuce cikin birni inda a Nan ne za'ayi musu gyaran,Abu kamar Wasa aiki ya Zama Babba dole sukayi waye can camp dinsu kada hankali ya tashi. A gidansa na wannan garin inda ya kasance mahaifarsa Alhaji Haroon ya sauke su da abinci da gurin kwana Mai Rai da lafiya, lokacin Yana ambassadorn Niger a k'asar Rasha sunzo hutun karshen shekara ne suka baro Yamai suka shigo gaishe da dangi Allah ya hadasu, sunga karamci da kyautatawa mutane ne masu karki kamar me, Ishaq a gurinsa ya zauna suna ta Hira a Nan yasa su 'yan Nigeria ne, zainab da wata yarinya suka shigo musu da kayyayakin abinci, tunda ta shigo Abbie keta binta da kallo ita Kuma taqi yarda ta dago saboda taji yanda idanunsa suka yawo a jikinta, serving dinsu zata Fara Abbie yace ta Bari suje kawai saboda yaga yanda abokanen tafiyarsa biyun suke kallonta duk sai yaji ya damu,washe gari ma su suka kawo musu break fast sai kusan goma na Rana sannan masu gyaran suka kawo motar har gida,sunyiwa Alhaji Haroon godiya sosai Dan hanawa yayi su biya ko sisi na gyara sannan yasa akayi musu fulltank na petrol a motar.
Har ciki suka shiga suka gaishe da Hajiyar sun taso zasu tafi Hajjar ta Kira zainab tace tazo suyi sallama Kamar zata fasa kuka ta fito tana sadda Kai kasa da gaske mutumin Nan dodonta ne, daga gefe ta Dan tsuguna tana gaishe su.
Ya ishai ne ya dubeta Yana fadin kunyarwa takeji da take sadda Kai kasa kamar tana gaban sirikinta.
A haka su Abbie suka fice a waje sukayi musanyar number da Ishaq sannan ya karbi ta Alhaji Haroon Wanda suke Kira Abu.
Har suka koma sansaninsu Abbie na makale da tunanin zainab haka yayi ta fama da ita a cikin zuciyarsa har tsawon kwana uku Amma Kullum sai sunyi waya da Ishaq da Alhaji Haroon Ambassador a ranar cikon na hudu ne ya kasa daurewa ya dauko mota da ordily dinsa Daya suka biyo Sahara zuwa cikin gari.
Sam Alhajin Haroon baiyi mamakin ganin Muhammad ba Dan yasa da walakin goro Miya yanda yake kiransa da yanda yake tambayar su zainab yasa da wata a kasa, Yana zuwa baiya kwauron Baki ba ya fito da bukatarsa ta son Auren zainab inda Kuma ya fad'awa Abu shi Mai iyali ne har buyi a fada Mata idan ta amince zata iya aurensa a haka, Basu bar garinba Saida magana Mai karfi Dan ana tambayar zainab din ta rufe fuska, dariya Hajja tayi tasan za'a rina ita tun ranar da suka hadu a Sahara tasan akwai abinda Allah ya hada Dan taga yanda kowannensu ya nuna da suka had a Ido to abinne na zamani baka zakewa.
Cikin Kankanin lokaci sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki tamkar sun shekara suna soyayya sai yaji tamkar Bai tab'a son wata 'ya mace ba a rayuwarsa Dan yanda yake Jin zainab daban ne da yanda yaji a matansa na baya, kafin wani lokaci zainab sunyi sabo da Hajiya Inna ta waya Kuma kusan kowa a cikin family yasan Muhammad Dange zeyi Aure a Niger Dan tuni manya sun shiga maganar babu Bata lokaci akayi biki Daman ta hada karatunta tun shekarar data wuce, Shima suka dawo gida tunda an samu kwanciyar hankali a yankin da ake fama da tarzomar.
A lokacin ne Abbie ya Gama katafaren gidansa da Kuma wadan da ya ginawa 'yan uwansa duk da kowa ya Kama kasa a lokacin Amma samun ba Daya bane, da yawa Yan uwan Babansu Wanda suke uba Daya sun dawo sokoto kowa Kuma Allah ya saka Masa Albarka a cikin nemansa sai dai sa'id da yaransa sun Zama zakarun gwajin dafi a cikin Families din Dan babu Hadi ko alama tazarar da nisa tamkar Dangote a cikin zuri'ar Alasawan koki ta Kano haka misalin yake a zuri'ar DANGE da iyalan Alhaji sa'id din.
A lokacin Abbie ya dawo gida sokoto da aiki shine musabbabin da momin Kano ta dawo sokoton itama duk abin Jin dadin rayuwa an tanada a gidansa Nan Dan ko daga waje kalli gidan ka Kara kallon komai na furnitures ya zuba Amma dole yasa aka cire wasu Dan iyayen zainab sunce sai sun Mata nasu jeren an kawo Kaya na garari Wanda suka tada hankalin kishiyoyinta da farko ce musu akayi irin 'ya'yan buzayen Nan ne masu yawo suna neman sadaka ya gani a sansaninsu 'yan gudun hijira,Amma ganinta da 'yan uwan ta da irin dukiyar da aka Zubar sai Kuma jiki yayi sanyi Baki ya mutu tanadin wulakancin da akayi tanadi za'ayi ya kau.
Zamane aka Zubar na kishin mimmuge ba fada a zahiri Amma akwai 'yar kasa daga gurin babbar gidan wanda da wuya mutum ya gane lokaci daya, gashi Hajiya Inna da Alhaji sun dauki son duniya sun dorawa zainab, Shima Mai gidan wanda take Kira da general yake Mata wani mahaukacin so Wanda baya iya boyewa a gaban kowa gashi tayiwa sauran zarra a gurin komai na auratayya sai abun ya Zama biyu.
Ba laifi sunyi amarci sosai Dan Saida ta dauki kusan wata shida suna cin amarci sannan ciki ya bullo Mai wata irin fitinar son kasancewa da miji dole tasa ya dauketa ya tafi da ita wani course da zaya a South Africa abinda yaso ya tada hankali a gidan sai da yayi Jan Ido da kurarin duk wadda bazata zauna ba kofa a bude take sannan aka Samu zaman lafiya.
Ya fada Yana Dan Jan tsinin hancin Zahra "kinji yanda Muke muna ciki dan haka dole ki shirya tunda ba rago Kika aura ba tin a ciki ya Sami energy kinsan duk Inna tawa ta bani labarin nan?".
Rike Baki Zahra tayi "har wannan Kuma?." "A'a ba direct ta fada min ba fa cewa tayi Wai cikin rashin hakuri ya sakata, Saida na tambayi Hajiyar makwarari ta fada min kinsanta ita handsfree ce"..

Kina ji Saida sukayi wata uku suka dawo lokacin cikin watansa shida kuma tun a can a asibitin da take zuwa ante-natal clinic suka fada Mata twins ne mace da namiji Amma Tayi shiru ko Mai abun Bata fad'awa ba saboda abune cikin duhu kada ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login