Showing 177001 words to 180000 words out of 280244 words

Chapter 60 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1065

Basu dawo ba, da kanshi yake driving din, da Dan hanzari yake tafiya saboda gaba Daya hankalinsa yayi Asibiti.
Lokacin Daya shiga direct office din consultant din ya nufa, be same shi a office ba Yana cikin ward inda yake duba patient dinsa, baifi zaman minti goma ba doctor din ya dawo da zugar wasu dalibai a bayansa Yana ganin mahmud ya gane shi, tunda yaji yana Jin yaransu yake Nan Nan dashi.
A cikin office din wasu hotuna ya dauko ya aje a Kan table dinsa yace mahmud da sauran daliban su matso.Dalla Dalla ya shiga Yi musu bayanin yanda ciwon yake da yanda yake yiwa mutum illah idan har ba'a Farga an kawo mutum Inda za'ayi Masa aikin gaggawa ba saboda yanda spinal cord din ta matse to komai ze iya faruwa za'a iya rasa kafa da amfanin kasan Jiki na har abada, Dan haka daga Nan zuwa Kwana uku za'ayi wannan aikin, Amma dole charges zasu karu tunda sun Kara gani karaya a kashin hakarkarinsa na hagu guda biyu sai kashin mukamikinsa Daya goce".
Take a Nan mahmud ya nemi a bashi bill na Karin charges din da aka samu, yaje ya biya komai ba damar ganin Baba malam haka dokar take,yana tafiya a Kan barandar Asibitin Yana sauri ya Karasa gurin Daya aje mota yaji daga bayansa ance.
"Waye nake gani Kamar Mahmud Dange".
Da sauri ya juya Yana mamakin waye wannan yayi Masa farin sani haka.

Faisal ya gani kanin Aunty Surayya matar uncle Mustaphan zasuyi sa'anni da mahmud din, cikin fara'a Mahmud ya Fara fadin.
"Faisal bungudu Long time, Daman talaka Yana ganinku?".
"Kaji ka da wani magana Kai ganin ku ai sai Mai sa'ar gaske, Nigeria kun Mata tawaye ma kwata-kwata yaushe ake ganinku, meya kawo ka Nan ne haka ko patient gareka".
"Eh wallahi wani Babana ne ya samu spinal cord injury muka kawo shi Nan, Kai Kuma meya kawoka?"

"Wallahi Alhajin mu ne ya samu accident tun kusan wata hudu da suka wuce, karaya ya samu a cinya, anyi gyara har sau uku abun yaki shine, wani doctor da muke gani a wani private orthopedic hospital a Sokoto yayi Mana hanya mukazo nan, kaga jiya uncle Mustapha ya bar Nan kasar tunda shine ya kawo mu sai da ya Gama Mana koma".

Jinjina Kai Mahmud yake kafin yace.
"Allah ya bashi lafiya, ga jikin girma ga lalura muje na ganshi na duba shi".
Tare suka juya Faisal din Yana fadin.
"Wallahi Rabon mu hadu ne nace Bari na koma masaukina nayi wanka na huta tunda ba wata damuwa a tare dashi sunce sai Nan da sati uku zasuyi Masa aiki sai sunyi treating din gurin da infection ya Kama sannan zasu sake Masa aiki"

"Allah yasa ayi aikin cikin sa'a yasa da nasara yasa a dace.
"Allahumma Amin" Faisal ya fada.

Lokacin da suka shiga Alhajin Yana zaune a gadonsa Yana lazimi da casbaha dinsa.
Ganin Faisal ya dawo da wani yasa ya maida hanklinsa a Kansu, har suka karaso yana kallonsu.
Sallama Mahmud yayi masa ya amsa sannan Mahmud din ya gaishe shi da jiki.
Faisal ne ya yiwa mahaifansa bayanin Mahmud, cikin nuna Jin Dadi mahaifan na Faisal ya shiga jorowa mahmud godiyar abinda akayi masa, Basu jima ba Mahmud ya aje Masa Dala dubu yayi masa sallama, Mahmud yasha shi Albarka Kamar ze Bari Baki gurin godiya.
Shima Faisal godiyar ya dunga jerawa Mahmud Kamar me, shiya dauki Faisal ya Kai shi har masaukinsu sannan Shima ya hada shi da dala dari biyar yayi gaba, wani irin shauki ke dibarsa akan yaje gidanta tunda gari ya waye yaji ba abinda yakeso irin yaje ya ganta ita da yaran, amma wata zuciyar na fada Masa kada kaje akwai k'ura Kuma wannan match din bazaka iya playing dinsa yanzu ba, kwabarka ce zatayi ruwa, dole ya karkata Kan motar ya dauke daga direction din da ze Kai shi gidanta, Amma fa dole yaje gareta duk rintsi Dan yanzu ma yasan Yana zuwa wani labarin za'ayi ba wannan ba Dan dole ballin ya tashi.


__
Har dare Zahra Bata Jin dadin jikinta Sam da mahmud ma ya Kira Basu Dade ba yace Yana da wani uzurin da zeyi sukayi sallama.
Wurin karfe biyu da rabi ta farka sai taji Kamar an Zuba Mata ruwa, da sauri ta yunkura ta tashi zaune abunda ta gani ya sakata tashin hankali ta sauko a zabure tana sallallami jikinta sai rawa yakeyi, period ne yazo abinda Bata taba yiba kenan ai sai kowa yasan da zuwansa Amma wannan sai ganin Abu tayi da wata irin Zuba ta tashin hankali.
"Na shiga Tara mezan gani haka?".
Toilet ta nufa tana cikin rudu ba kadan ba data shiga ta cire nighty din ta sakarwa kanta Ruwa ta wanka Yana bin kafarta Zuba yake sosai har da guda guda, ganin abin bana hankali bane yasa ta fashe da kuka, da kyar ta samu ya Dan tsagaita da Zuba ta hada pad biyu ta saka ta fito ta kunna wutar dakin yanda taga Kan bed din sai hankalinta ya Kara tashi cire bedsheet din tayi tana share hawaye.
Cikin washing machine ta saka bedsheet din ta fito da towel a bucket da detergent ta Fara aikin gurin tana cikin aikin tayi wata irin Zuba wadda har Saida ya biyo kafarta saboda yawa hannu ta Dora a ka ta fasa kuka tana fadin.
"Na shigesu shikenan mutuwa zanyi".
Wayarta da dauko ta lalubo number Muhmud ta Kira ba tayi tunanin ko karfe nawa bane a can.
Yana zaune yana aiki a laptop dinsa yaji Kiran ta ya shigo agogon dake parlourn ya duba yasan yanzu a Nigeria tsakar dare ne to lafiya yasan ba gwanar chart din dare bace bare yayi tunanin kiransa tayi suyi Hira.
Yana dauka yaji shashshekar kukanta.
Cikin kidima ya tambayeta.
"Menene? Meya faru? Keda waye a dakin?" Kiyi min magana Mana ".
Duk ya jero Mata wadannan tambayoyin, Bata bashi amsa ba sai faman fadin ta shigesu take.
"Wai precious so kike Nima na fasa kukan ne? na tambaye ki kinyi min banza kina ta kuka, ko wani ne ya mutu aka fada Miki kike wannan kukan ko wani Abu yake damunki ne?"
Ya fada Yana kwantar da murya Dan so yake tadan samu nutsuwar da zatayi masa bayanin damuwar data saka tayi masa Kiran tsakar dare.

"Pls precious tall me menene Mana?".
Cikin karaya da sallamawa ta bude bakinta da kyar tana shashsheka.
"Wallahi me Amor jinane ze Kare bleeding nake kagan shi Nan sai Zuba yake duk na Bata bedroom din Nan Ni dai ka yafe min nasan mutuwa zanyi ta fada wani kukan Yana kwace mata.
Jin abinda take fada ya daga Masa hankali sosai, saima ya rasa Yaya zeyi Mata wani tunani yayi, saiya aro jarunta ya yafa yace mata.
" Pls haba my angel ki nutsu babu abinda ze sameki kinji maza kirawo Matar nan tazo ki hadani da ita.
Kai kawai ta gyada Kamar Yana kallonta, Kiran number Aunty zilan tayi, tana cikin barci taji Kira figigit ta tashi ta dauka sunan Zahra ta gani da sauri ta dauka cikin kuka Zahra tace Mata.
"Kizo Aunty zilai zan mutu".
"Innailaihi wa innailaihi raji'un! Na zilai na shiga uku meya sameki?".
Shiru tayi mata, da gudu-gudu zilan ta karasa bedroom din Zahra abinda ta gani ya daga Mata hankali.
"Na shiga uku Ni zalaihatu meya sameki wannan ai Bari ne, tun yaushe Kika Fara zubar da jinin nan? Bari na fadawa Mai gadi ya kaimu Asibiti wannan ai ba abun Wasa bane, Kiran Mahmud ne ya shigo Aunty zilai ta mikawa wayar.
Jin muryar Mahmud yasa Aunty zilai Kara risunawa tamkar yana gabanta, magana ya Fara Dan ko gaisuwar da take masa Sam beji ba.
"Dan Allah ki taimaka Mata ta gyara jikinta ga zayyan can Yana jiranku zaku wuca Asibiti.
A&E sukaje anyi Mata tambayi daga karshe sukace sai nayi scanning da safe zasu tantance Dan Zahra ta kafe ita ba miscarriage tayi ba su Kuma sunce babu abinda ze kawo Mata irin wannan heavy bleeding din Sai shi, suna Asibitin mahmud ya sake Kiran zayyan ya tambaye shi me sukace ya sameta.
Yace Masa ance miscarriage tayi Amma da safe zasuyi hoto su duba.
Jim Mahmud yayi Yana tunanin meya hada zahra da barin ciki Kuma? Sai dai wani abun na daban gaskiya.
Sunyi mata duk abinda ya kamata Kuma Alhamdulillahi zubar tayi sauki, wurin karfe hudu da rabi suka dawo gida sai da safe zasu koma za'a Mata scanning a ga menene mu"assasa na kawo zubar jini kuma ayi Mata pcv.
Bayan daqowarsu mahmud ya kirata yafi sau biyar Yana tambayarta ya jikin? Ba wata matsala? Meke mata ciwo?.
Haka yayi tayi ita har Saida ya koma Bata tausayi ma ya fita shiga damuwa ita keda Matsalar Amma ya fita shiga tashin hankali nesa ba kusa ba, ya fada Mata yayi Dana sanin tahowa ya barta,Amma dole yasan abinyi tunda akwai matsala.

*AUREN HUCE HAUSHI*
08055362975
Or

09061432330
My WhatsApp number.



AISHAT ISAH MUSA (Aunty Uwani)

Naman Fateemah.

Page 64.


.............Sun koma asibitin sunga consultant g
Gynecology doctor sabuwar ce tazo daga federal medical center Birnin kudu, Dr Hajara yqrinya ce karama Amma tasan aikinta, so sai ta duba zahra ta turata ayi Mata special scanning saboda taga history na ciwonta a cikin file dinta.
Basu Dade a gurin scanning din ba suka dawo, tunda doctor din ta bude take jinjina Kai abun yayi matukar Bata mamaki, Saida ta aje result na scanning din sannan ta cire eye glasses din idonta.
"Dan Allah sister me ki kayi amfani dashi akan matsalarki ta fibroid? Ma'ana kin Sha wani magani na hausa Kona Islamic chemist haka akan matsalarki?".
Kai zahra ta gyada mata alamar eh.
"Pls my friend talk to me".
Ta fada tana murmushi.
"Eh nayi amfani da wani magani Amma Ina ganin black pepper ne kawai da kakata ta bani tace na ringa Sha da ruwan zafi Amma sai yayi twenty minutes Zan tace na Sha safe da yamma tace ze narke basai an yanka an cire ba, tace ma Yana maganin haihuwa Wanda baya haihuwa idan Yana amfani dashi eggs dinsa zeyi producing a samu haihuwa, tace min Yana magani sosai a bangaren ciwuwwukan Mata da suka shafi mahaifa, ko macen da bata haihuwa shima idan tana amfani dashi In Sha Allah zata Samu haihuwa, abinda ta fada min kenan".
Zahra ta fada tana kallon Dr din.
"Masha Allah, batayi karya ba Babu komai a cikin mahaifarki yayi dissolving ya wuce a cikin jinin da Kika zubar, Naga sun rubuta miscarriage irin haka ne yake kawo a batawa yarinya suna alhalin ba haka bane".
Ta fada tana kallon Aunty zilai.
"Kinga sister dina budurwa ce dal babu wata alaka data taba hadata da wani namiji na gani Dan haka ku bani number din Mama nayi Mata bayani nasan ba Karamin tashin hankali ta shiga ba a jiya nasan har yanzu Bata da nutsuwa da wata ce ma tana Nan tare damu ayi komai a gabanta".
Kallan kallo ake tsakanin Aunty zilai da zahra.
Me maganar likitan ke nufi da tace zahra budurwa ce? Tsatstsare Aunty zilai zahra tayi da Ido kafin ta juya ta kalli doctor Hajara kamar yanda ta gani a jikin Dan siririn freme a Kan table dinta.
"Nagode doctor Amma ba sai kin Kira Ammatah ba Bata kasar taje ganin likita tana da hawan jini ne Batasan ma bani da lafiya ba, ya pcv din Naga 48% ya Isa kenan?.
Murmushi tayi doctor din.
"Sister zahra ai yanzu haka sai ki bada jini,me 27% ma is ok basai an Kara masa jini ba sai dai a bashi maganin Karin jini".
"Ok tom shike Nan nagode kwarai sai an Jima" zahra ta fada tana tashi tsaye, har sun Kai Bakin kofar fita taji doctor din na fadin.
"Sister zahra bazaki bani number wayarki ba idan an tashi bikinki nazo Miki, bansan kowa ba a garin Nan daga Jigawa mukayi transfer nida mijina shima doctor ne pediatric banu Dade da Aure ba Ina son nayi kawa a nan".
Dawowa zahra tayi tana fadin.
"Ai kuwa na gode kwarai da gaske kawo na saka Miki number dina sai ki kirani Naga taki".
Ita dai Aunty zilai mamakin duniyar Nan ya cikata, har gurin mota doctor Hajara ta raka zahra saboda Bata da patient a ranar zata shiga ante-natal zasuyi awo.
Address din gidan Ammah ta bawa doctor din, sukayi sallama suka wuce, suna hanya mahmud ya Kara Kira yanda yaji muryar ta cikin nutsuwa yasan lamarin yayi kyau.
"I will call you later, we are on the way".
Ta fada Masa a hankali.
"Ok"
Kawai yace ya yanke Kiran.
Tunda suka shigo motar zahra ta hade gabas da yamma yanda Aunty zilai ma ba zatayi Mata wata magana ba, don taga yanda ta zaro Ido lokacin da doctor ke bayani.
Har kofar parlour zayyan ya kawo su ya sauke Yana fadin.
"Ranki shi dade Allah ya Kara lafiya".
"Allahumma Amin"
Zilai ta fada.
Ita ta bude kofar Zahra ta shiga, suna shiga ciki zahra ta juyo tana fuskantar zilan.
"Aunty zilai wannan maganar ta Zama sirri yarda da Aminci yasa nake yin abubuwana a gabanki tunda bamu taba samunki da wani abun ashsha ba, ko Ammah bana son taji labarin wannan abun Daya sameni Kinga dai ance babu ya wuce to zancen ya tsaya ya junan mu".
"In Sha Allah babu Mai ji uwar dakina, Amma wani hanzarin ba gudu ba, ko kuma dai a fadawa Ammah mijin naki bashi da lafiya sai a nemar Masa magani ai irin wannan ba'ayin shiru kada karamar matsala ta Zama Babba, yaro har yaro Amma babu lafiya".
Ta fada tana Jimamin abun.
Dariya maganganun ta suka bata ita bilhaqqi da gaske take maganar ta.
"Ki daina dariya wallahi ba abun dariya bane, yanzu saboda Allah kuja Baki kuyi shiru Dan yarinta, ai wannan ba Karamar matsala bace ba fa".
"Wai Aunty zilai waye yace Miki bashi ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da lafiya? Lafiyarsa kalau wallahi".
"Eh Daman lafiyar kalau Mana azahiri Amma a badini kuma ai Mai tsananin ciwo ne".
"Allah Ina fada Miki ba abinda ya sameshi fa".
Wani kallon Amma Baki da lissafi zilan tayi mata.
"Eh Naga lafiya a tare dashi tinda akace har yanzu kina nan a buduwarki Kinga kuwa ai lafiya ta tabbata a gare shi, yo ko waliyi ne aka aje Masa danyar yarinya kamar ki ya aje walittakar ya Raya sunna Amma shi yaro sharaf dashi ace ya Zuba Miki Ido tsawon watanni ai kinsan da matsala".
Ganin ba zata fahimce ta ba yasa Zahra fadin.
"Kinga Aunty zilai babu ruwan ki da shiga sangarsa ki Zuba Masa ido idan ma bashi da lafiyar ai ya sani ze nemarwa Kansa magani".
"Gaskiyarki Kuma fa babu ruwanw kada na dauko ruwan dafa kaina da kaina".
"Da dai yafi".
Bedroom Zahra ta wuce barci takeji sosai.

Tana shiga ta cire rigar jikinta wani wankan ta sake, fitowa tayi daure da towel sky blue a jikinta, jinta take wani iri Bata taba samun irin wannan bleeding din ba shi yasa duk ta takura.
Zama tayi tana shafa lotion na razac tana sonsa sosai, tana cikin shafawa taji ringing din wayarta a Kan bedside tashi tayi tsam ta nufi gurin sunansa ta gani Yana yawo Kan screen din, wallahi tausayi yake Bata ya kasa samun nutsuwa Kota sisin kwabo.
Video call ne, dauka tayi tana Masa sallama.
Tsura Mata Ido yayi yana tasbihi ga ubangijin da yayi wannan surar, wani yawu ya hadiye ba shiri, kashe mata Ido Daya yayi Yana dage girarsa ta hagu.
"Precious..,"
Ya kirawo sunanta in a deep voice, lumshe Ido tayi Dan sai taji yau sunan ya zamar Mata wani so special.
Gefen bed ta zauna ta Dan jingina da pillow a jikin gadon, sexy eyes dinta ta Zuba Masu kamar Zaiba a ciki kafin ta amsa Masa gently.
"Na'am.. meu Amor....".
Saida ya lashe lips dinsa saboda wani abu ya tsirga Masa cikin mararsa har Saida ya rufe Idanunsa, a hankali ya sauke su a kanta fal fitina Yana Mata wani kallon kasa-kasa.
"Kin tashi hankalina fa ba kadan ba, na rasa nutsuwa ta, hakurin zamanki nesa Dani ya Kare gaskiya bazan iya wannan jarumtar ba, gangar jina ke Nan Amma zuciyar tana Nan Kinga kuwa mutum ba zuciya ai babu mutum, ya jikin naki? Me suka fada da sukayi scanning din? naji zayyan na fada min wai sun ce miscarriage kikayi, nace a'a sai dai wani abun badai shi ba".
Gyara kwaciyarta tayi.
"Nima da farko haka suka fada Aunty zilai ma haka tace data gani, na fada musu bashi bane Amma Basu yarda ba, sai doctor din data dubani da safen Nan tace fibroid din ne yayi dissolving ya biyo period shine ya kawo heavy bleeding din, Kuma fa da har number din Ammah ta nemi na Bata Wai zatayi Mata bayanin abinda ya faru Dani tasan hankalinta ba a kwance yake ba ance 'yarta budurwa tana dauke da ciki tayi bari, gara ta fada Mata Babu wani Daya taba sanin yarta a matsayin mace lalura ce kawai, kasan muna dawowa Aunty zilai ta tsareni da maganar bamu da wayo Ashe baka da lafiya muke zaune bamu fadawa kowa ba ita zata fadawa Ammah a nemar maka magani tunda Amana ta turota gurina, da kyar fa na fashimtar da ita nace babu ruwanta ta barka ka nemi maganinka".
Dan cute pink lips din ta yake bi da kallo harta Gama bashi statement din.
Kankance Idanunsa yayi Yana Mata wani kallo.
"Gaskiya Kam maganar doctor gaskiya ce, Ni nasan har yanzu rainon a Bata nake yi koba haka bane? Kice da Auntyn ki ta Kira Mana Ruwa? da bazan Kara yarda mu hada ido da Ammah ba ai tonon sillil ne wannan shikenan na Zama ragon maza a idanunta".

Ai zahra Bata gane ta saki layi ba Sai daga baya, kunya taji ta rufeta.
"Nifa labari na baka ba Wai wani Abu ba".
"A'a gara na saka shimma kada a zaci da gaske ne, yanzu ita ta yarda bani da kuzari fa sai dai tayi ta kallona a haka koba haka bane?.

"Pls dan Allah mubar zancen Nan yafi karfina".

Murmushin nan nasa yayi mata yana fadin.
"Bayani zakiyi da yaren garinku yarinya gashi nan kin jamin ana min kallon wani lusari ko?".

Kira ne ya shigo Masa daga Asibiti, da sauri ya yanke Kiran Yana fadin.
"Bari na daga kirane daga Asibiti.

Yana sauka daga online tayi ajiyar zuciya Allah ya taimaketa, da Allah kadai yasan meze baro Mata taga alamar kamar hakurinsa Yana neman karewa, Dan wannan idanun nasa abinda suke fitarwa Yana Bata tsoro.

______

Maganar canza lokacin aiki sukayi masa saboda wasu dalilai da suka saka za'ayi Masa aikin gobe Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login