Showing 159001 words to 162000 words out of 280244 words

Chapter 54 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1080

kawai ta iya".
Shiru tayi Masa tasan tunda ya ambaci haka babu abunda ze fada Mata akan tambayar ta.
Har doki ya dorata a ranar yayi Mata hotuna da yawa Dan kayan sport suka saka saita kalar fari da ja it's ta Dora hijabi a Kai da suka kebe Kuma ta cire, sunyi hotuna sosai masu matukar kyau bare na garden din sai background din yayi kyau sosai.

Da dare suna zaune a parlour tayi pillow da cinyarsa yana kallon tashar super sport ana nuna wasan realmadrid hannunsa Kuma yana. Wasa da gashin Kanta Wanda ya Sha gyara, sai kamshin hairspray ke tashi duk ya yamutsa Mata shi taga alamar da bayani a tare dashi. Wayarsa ce tayi dauki slow music na wakar wata tshowar mawakiyar America brandy.
Tashi tayi tsam ta nufi wayar ta dauko sunan Habib ta gani Yana yawo akan screen din tana kawo Masa Kiran na yankewa, kiransa yayi gefe ya koma ta Zauna saboda Bata San me zasuyi tattauna ba, tana can tana kallon wani penalty da aka bawa Barcelona suka zubar, sai ji tayi ya tashi da sauri Yana fadar.
"Innailaihi wa Inna ilaihi raji'un! Yaushe ne abin ya faru, subahanallahi gamu Nan zuwa Azaren da safe in Sha Allah".

AUREN HUCE HAUSHI


Naman Fateemah






Page 58.

................Da wani irin sauri da sassarfa ta karaso inda Mahmud din yake tsaye rike da wayar Yana salati, hannunsa ta rike tana jijjigawa tana fad'in.
Waye ya mutu a Azaren, wayyo Allah Ammah ta, shikenan Ashe munyi sallama kenan"
Ta rukumkume shi sai kuka.
Da kyar ya banbare ta daga jikinsa yana fad'in.
"Menene haka precious Wai? Waye ya fada Miki mutuwa akayi da Zaki tada hankalinki, Nima ki tada min nawa".
Zaunar da ita yayi, sannan shima ya Zauna suna facing din juna tana matse hawaye daga idonta.
Hannunta ya kama ya rik'e Yana fad'in.
"Ki nutsu ba Wanda ya mutu fa Baba malam ne ya Fadi dazu bayan sallar insha'i a kofar masallaci yazo tsallake kwalbatin da ake gyara ya taka slap ya zame dashi sai Kuma slap din ya biyo shi ya fada Masa a bayansa,bayan an Ciro shi daga ciki sai Kuma sai tafiya ta gagara suka nufi Asibiti to a can ne suka yiwa Su Habib bayanin ya
Samu matsalar data Hana kafafunsa tafiya, yanzu haka Yana F. M. C likitoci na tsaye a Kansa Wai suna tunanin ya Samu Spinal cord injury ne".
Wani irin zaro idanu zahra tayi tana fadin.
"Innailaihi wa Inna ilaihi raji'un mun shiga Tara "spinal cord injury? shikenan Baba malam sai yanda Allah yayi" .
Sai wasu sabbin hawayen.
"Kiyi hakuri kuka baya magani sai addu'a kawai".
Basu Dade a parlourn ba suka koma ciki Dan kallo dai ya tashi, ya Dade Yana lallashinta kafin ta saurara da kukan, ya sani sunyi wani irin sabo da Baba malam Yana kaunarta sosai Dan sauda yawa Yana ganin Yana saka Almajirai Yi Mata Addu'oin na musamman, itama sauda yawa Yana ganinta da Leda a hannu ta kawowa malam din.
Kwana Sukayi ba nutsuwa Kota sisin kwabo a tare dasu Malam ubane na gaske Mai nuna kauna da karamci ga kowa.
Dan Mahmud kusan kwana Sukayi suna waya da Habib sun Kai uku da Rabi Saida likitoci suka gama dubashi sukayi Masa Allurar barci sannan ya samu nutsuwa, zahra ma har lokaci batayi barcin ba.
Bayan ya aje wayar be kwanta ba toilet ya shige ya Jima kafin ya fito da bathrobe da karamin towel a hannunsa Yana tsane ruwa, jallabiya ya zura ya Fara nafila, ganin haka ya saka Zahra tashi itama tayo alwalar ta dosa nafilar itama, suna zaune har akayi Kiran assalatu.
Shi ya fice, sai kuma gashi ya dawo tana niyyar tayar da sallah, tsayawa tayi saboda gurin da take ya nufo.
"Ki shirya kafin na dawo da wuri zamu wuce Azaren".
"To, insha Allah".
Ya juya ya fice ita Kuma ta tayar da sallah zuciyarta fal murna abunda ta cire Rai dashi kenan kwana kusa, Ashe basu sani ba a kusa zasuje garin, ikon Allah Kennan sallar ta tayar.
Babu Bata lokaci ta shirya har ta shiga kitchen tayi simple Abu kamar yanda taga Ammah nayi idan Abba zeyi irin wannan tafiyar takance lusarar Mace ce ke barin mijinta ya fita neman abin breakfast a hanyar tafiya, wadda tasan kanta Bata barin mijinta neman abincin titi yayin sakakkon tafiya.
Kafin ya shigo ta hada basket tsab a bedroom ya sameta tana kokarin saka doguwar rigar abaya 'yar Dubai a cikin kayan dake dakin ta ganta ba karya ta amsa sunanta, a hankali ya karaso da sallama a bakinsa Yana zuwa rigar ya karba ya saka Mata ya dauko veil din ya dauki clip din me zanen heart da stones a jiki yayi Mata rolling, ita har mamaki ya Bata ganin yanda yayi Mata dos ba Wani mistake.
"Kinyi mamaki ko? A gurin Aisha na iya Ni nake Mata idan zamu fita unguwa tunda da Mace aka hadoni ai dole na iya sabgar mata".
Yayi gaba da sauri ya nufi toilet.
Da idanu tabi shi tasan wani wankan ze sake, ita batasan wane irin jikine dashi ba sanyin ruwa baya Masa komai a zamansu dashi ta fuskanci ma'abocin son ruwa ne shi.
Handbag Mai Dan girma ta dauko ta Zuba turaruka da Dan abinda baza'a rasa ba a ciki.
Yana fitowa daga toilet din ya fice Yana fadin ta jirashi a parlourn farko.
Ba tafi minti biyu da Zama ba taji alamun tsayuwar mota a kusa da parlourn, tashi tayi ta shige kitchen ta dauko basket din, ta fito kenan shi kuma ya Gama gangaro steps din kenan, cikin wani yadin filtex ruwan sararin samaniya da hula itama sky-blue din Yana daura agogo a hannunsa, wani irin kyau taga yayi Mata kana ganinsa kasan yarone matashi Maiji da kuruciya ga Wani sirrin kyau da yake fita daga fuskarsa, ganinta da basket ya bashi mamaki karasowa yayi Yana fadar.
"Wannan fa".
Ya nuna Mata abinda ke hannunta.
"Is for you".
Ta fada tana nufar inda ta aje handbag dunta.
"Thanks, wato so kike na koma kamar yaron goye ko?".
Dan juya masa sexy eyes dinta tayi kawai.
Karbar basket din yayi suka jera sun bala'in kyau Kamar ka daukesu ka boye saboda yanda sukayi wata irin dacewa kana ganinsu kasan couple ne da suke cikin ganiyarsu.
Suna fita Zayyan yayo zarya ya karbi basket din daga hannun Mahmud Yana fadin.
"Good morning sir".
"Morning"
Ya amsa masa, sannan ya gaishe da zahra.
Da sauri Zayyan ya budewa Mahmud back seat ya zagaya ya budewa zahra dayan gefen itama, har ze shiga seat din driver Mahmud yace yaje side din da Aunty zilai take ya fada ta shirya zuwa goma Sameer zezo su tafi.
Tare da Aunty zilan suka dawo jiki na Mata tsuma har kasa ta tsuguna ta gaishe da Mahmud sanan Zahra ta gaishe ta, zahrar tayi Mata bayanin halin da ake ciki, cikin nuna jimami ta jajantawa Mahmud din tare da Addu'ar fatan samun lafiya.
Saida aka bude musu gate suka fice sannan Aunty zilan ta koma da sauri tayi abinda zatayi na abincin da take dafawa saboda hadiman gidan ta shirya kada a jirata.
Saida suka bar kano sannan Mahmud ya Danna wani guri jikin kujerar gaba, take wani covering ya raba tsakaninsu da Zayyan da yake aikin tukinsa.
Janyota jikinsa yayi ya kwantar da ita baice Mata komai ba itama batace masa ba sai fuskarta da yake Dan shafawa lokaci zuwa lokaci Batasan sanda barci yayi awon gaba da ita ba, Bata farka ba Saida suka kusa shiga Azare Shima wayar da sukeyi da Habib ce ta tasheta.
Warrr tayi da Ido tana kallonsa.
"Kin tashi?"
Kaita gyada Masa tana janye jikinta daga nasa.
Directly FMC suka nufa a parking space suka tarar da Habib yana tsaye Sam be gane su waye a motar data wuce shi tayi parking a nesa kadan dashi, hundred percent hankalinsa na Kan wata mota Mai shigowa, da sauri Zayyan ya budewa Mahmud kofa ya fito Yana rike da hannun zahra kamar me tsoron kada ta Bata, duk yanda taso ta zame hannunta yayi mirsisi ta qiya, gurin da Habib yake suka nufa kafin su karaso Habib ya juyo da sauri Jin turaren Mahmud daga bayansa.
"Masha Allah"
Ya fada a zuciyarsa, ganin yanda sukayi wata irin dacewa gaba daya gani yayi sun canza Masa tamkar masu rayuwa a kasashen Europe din nan.
Da sauri ya nufo Mahmud Yana fadin "wallahi banyi zaton ku bane a waccan motar kaga wadda nafi maida hankalina a kanta Nan".
ya nuna irin motar Zahra.
"A'a ata yallabai mukazo tare da drivernsa, ya fada Yana tsare zayyan da Ido.
Zasuyi musabiha da Habib Zahra ta samu zare hannunta daga cikin nasa, idan shi bakone ita garinsu ne yanzu da anyi dace idon sani ya gansu zance ze cika unguwa Daman ya lafiyar kusa ita da komai nata a baki yake, ga unguwar tasu ta 'yan gargajiya.
Gaishe da Habib zahra tayi tare da tambayarsa Mai jiki, sannan suka gaisa da Zayyan ma.
Habib yayi musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da Baba malam vip ne Nan Abba ya saka Abdul Hakeem ya biya aka saka shi duk da Abban baya garin.

Lokacin da suka shiga ya koma barci ba kowa a dakin sai Abubakar kadai duk yawanci sai bayan anyi sallar Asuba suka koma gida.
Kai tsaye gurin gadon Mahmud ya nufa, ya tsaya dai dai Kan malam din, gani yayi yayi wata irin rama fuskarsa tayi wani fayau sai qananun raunika a gefen idonsa na dama da gefen kumatunsa.
Kujera Abubakar ya gyarawa zahra sannan suka gaisa tayi Masa jajan jikin malam, gurin Mahmud ya karasa sukayi musabaha tare da jajantawa juna.
Ya Dade a tsaye a gaban gadon daga shi sai mahaliccinsa suka San Abinda yake saqawa a cikin zuciyarsa.
Juyowa yayi Yana facing din Abubakar da Habib.
"A hannun wane doctor case din malam yake?".
Habib ne yace.
"Yana hannun doctor Omole consultant ne a bangaren Orthopedic, yanzu ma ba dadewa suka bar dakin lokacin ma inaga kun shigo garin".
"Ok ba matsala, muje ka rakani na gansa".
Ya fada Yana nufar kofar da wannan azamar tasa, su Abubakar suka rufa Masa baya.
Zayyan ma ya bisu dakin ya rage daga Baba malam da yake barcin dole sai Kuma ita zahrar dake zaune tana duba wayarta.
Office din likitan suka nufa a hanyar suka hadu dasu salisu sun dawo harda Mu'az a cikinsu, tasu batazo Daya ba da shi sam saboda yanda baya iya kauda Kai akan mata, kuma salisu ya taba fada Masa har ciki ya taba yiwa wata yarinya 'yar Mai aikin gidansu finkarfi yasa aka dannesu aka bawa wani marar gata.
Sun gaisa tare da jajantawa Mahmud.
Salisu ne ya kalli Habib Yana fadin.
"Wai Dan Allah a Ina mutumin ya maqale ne? ko wayarsa fa na Dade ban samu ba, ka fada Masa wallahi zamu kwace kanwar mu tunda haka ze Mana gara ta dawo kusa damu yanda zamu ringa ganinsa.? Amma ka dauke yarinya kayi shiru sai wani kyallin jiki kake Kamar Mace".
Dan murmushi Mahmud yayi yana fadin.
"Ka dauki bashi Zan biya, kanwarku Kuma sai yanda nakeso zanyi da abata haka kawai Zan ajeta sakaka kowa Yana gane min ita, Mai tsada ce".
Ya fada Yana tafiya tare da cewa.
"Bari muga doctor"
Har sun Fara tafiya Mahmud ya tsaya ya Dan koma baya gurin Zayyan da suka bashi 'yar tazara.
"Kaje maza kafin zugarcan su Karasa dakin ka Kai precious can gidansu kace Zan kirata".
Ya juyo shima Zayyan ya juya da sauri.
Suna zuwa kofar doctor din wani matshin doctor ya fito da sauri sauran kadan suyi karo da Habin ya danja da baya Yana fadin.
"Sorry".
"Ba komai".
Habib ya fada, sai Kuma doctorn ya kalli Habib sosai.
"Habib Abubakar ko?"
Kai Habib din ya gyada masa.
"Ok. Bismillah daman kiranka zani akan issue din Babanka".
Tare suka shiga ciki Mahmud da Abubakar na biye dasu a Bata.
Sun samu doctors kamar biyar sun zagaye doctor Omolen Yana ta bayani sun saka hoto X-RAY a tsakiya wasu na yin jotting na abinda yake musu bayani.
Matsawa wasu sukayi Habib da wannan likitan suka tsaya suma, doctor Omolen ne ya dago lokacin da doctor Hafeez yake Masa ga yaron patient din Nan harma da wasu yaran nasa ya fada Yana nuna su Mahmud da Abubakar.
Umarnin tasowa doctorn yayi musu, ba musu suka taso.
Bayani ya Farayi musu Yana nuna musu inda ya samu matsalar k'ashin bayansa k'asusuwan ne suka matse sakamakon fadowar da slap din yayi Masa a gadon bayansa, su suka matse spinal cord dinsa har ta samu injury Wanda ake Kira (spinal cord injury).
Yanzu Abu biyu ne zuwa uku na farko ko a turasu National Orthopedic na Dala Kano ko ibadan ko Kuma su fita dashi India wani Asibitin Fortis hospital dake new Delhi ko Kuma Max orthopedic surgeon hospital shima dai a Indian.
Take jikin Habib ya Kama tsuma Saida Mahmud ya zaunar dashi a resting chairs na cikin office din Yana Zama ya fasa kuka kamar mace.
Abubakar ya fita da Habib waje Yana bashi magana akan ya dangana yayi Masa Addu'ar samun lafiya da Kuma mafita.
Saida suka fice Mahmud ya fuskanci doctor din Yana tambayarsa wane Asibitin ne yake ganin shine best a cikin biyun Daya fada musu na Indian.
Wani daga cikin doctors din ne yace abunfa ba Mai sauki bane za'aci millions of naira a Kan aikin ga kudin flight.
Dan murmushi Mahmud yayi Yana fadin.
"Ba komai Allah ze rufa asiri, a bani website dinsu duka zamu bibiyesu muga wanne zamuje in Sha Allah".
Ba Bata lokaci aka bashi address din duka biyun da wasu sabbin magungunan da za'a saya da Allurai yayi musu godiya ya nufo kofa likitan da yayi musu jagora ne ya biyo Mahmud Yana fadin.
Idan babu damuwa zanyi magana da Kai,akwai wani Dan uwana da yake zaune can Indian Zan hadaku dashi Dan ku samu saukin abubuwa"
"Ok Nagode in Sha Allah zanyi maka magana idan komai ya kammala".
Sukayi musabaha doctor din ya koma shi Kuma Mahmud ya nufi inda ya hangi su Habib Abubakar nata watsa hannu da alam fada yake yiwa Habib din.
Koda ya karaso Baice musu komai ya zauna kusa da Habib Yana sauke numfashi.
"Ya ake ciki'. Abubakar ya tambayi mahmud.
Ba komai in Sha Allah za'ayi abinda ya kamata jiran zuwan oga Sameer nakeyi baze gagara ba suna aikin da yafi wannan ma ai qungiyoyin suna da kudi sosai. Dan wannan aikin ba wani Abu bane yanzu Kai Habib idan malam ya tashi ka tambaye shi inda za'aga passport dinsa kaima kaida Abubakar sai ayi muku tare da Visa tunda daku ya kamata aje".
Yana Gama fada ya mikawa Abubakar takardun da za'a sawo magani tare da ATM card dinsa yana fadar a karbo wadannan magunganan.
Tunda su zahra suka fito daga Asibitin ta ringa Alla Alla su Karasa gida taga Ammah. Suna shiga harabar gidan Bata jira Zayyan dake kokarin fitowa bude Mata ba ta fito da sauri tamakar zata kwasa a guje, Musaddiq ne ya fito Yana zuburar Baki da gani aikensa akayi baya son zuwa.
Ai Yana ganin zahra ya kwala qara yana fadin.
"Yehhhh! Adda Zahra!"
Ya kwasa a guje ya koma ciki yada kwadawa Ammah Kira.
"Ammah! Amma! Ammah! Ki fito ga Adda zahra tazo".
Mama dake tsaye a balcony din dakinta da waya a hannu ta gangaro da sauri ta nufo part din Ammah, Mama na kokarin shiga su Kuma su Ammah da Musaddiq na kokarin fitowa Ammah na fadin.
"Bana son shashanci wace zahrar Kuma yanzu ko karfe tara Bata karasa ba nasan hal......"
Bata karasa ba zahra ta shigo, ai suna arba da Ammah ta jefar da handbag din ta karaso da gudu-gudu ta shige jikin Ammah sai ta saki wani siririn kuka, tana fadin.
"I missed you Ammata! I really missed you, kinki zuwa ki ganni Ni Kuma ya hanani zuwa".
Tunda zahra ta shigo wani fitinannan kamshi ya doki hanci Mama ta rude ga uwa uba yanda zahrar ta koma ko makaho ya shafata yasan taji dadin masauki, Dan ba karamin kyau da Wani irin fresh tayi ba.
"Ke Kuma menene haka idan koroki yayi ba sai kiyi bayani ba ai kuka baya magani Daman kowa ya sayi rariya yasa zata zubar da ruwa Kuma tsintacciyar mage ai Bata mage".
Mama ta fada tana kallon zahra data shige jikin Ammah.
Dan murmushi Ammar tayi tana fadin.
"Zahra kuje daga ciki gani Nan, ya jikin malam din ko Baku shiga can ba?".
"Munje Yana barci ne, kuma gurin da maza sosai shine yace a kawoni gida zuwa dare sai muje na duba shi".
"Ok, shikenan ku shiga Allah ya bashi lafiya".
Ammah ta fada ta wuce main kitchen dinsu sata dauko wasu abubuwan tunda Alawiyya Bata Nan ta aiketa gidan Hajiya kaltume.
Nan suka bar Mama sororo da tarin kunya wato amsa aka Bata a kaikaice.
Jiki ba kwari ta koma part dinta.
Su zahra suna shiga Musaddiq ya mika Mata Jakarta Yana fadin. Kai Adda kike yarda Jakarki da kudi da yawa Kuma a ciki".
Kansa ta shafa tana fadin "Ni bani da wasu kudi a ciki, Wai Ina zaka Naga kana Bata rai?"

"Ba Ammah bace ta bada kyautar biscuits dina da chocolates da suka rage ba a kaiwa jikar Haji?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
ya kaltume data aiki Aunty Alawiyya Ni Kuma Ina son All butter Kuma babu a Nan kusa sai naje store Kuma Zazzabi nakeyi".
"Ah gaskiya ba'ayi daidai ba, kayi hakuri na bude opay sai na yiwa magaji transfer saiya sawo maka"
"Kai! Adda ki duba da kudi fa a jakar sosai".
Budewa tayi taga da gaske yakeyi to tana tunani lokacin da tayi barci ya Zuba matasu.

Jeka kirawo Amadun gidansu Aunty mujiba yaje ya sawo maka".
Ya fice Yana tsallen murna.
Ammah ce ta shigo da wasu ledoji a hannunta, da sauri zahra ta tashi ta karba tayi kitchen dasu, da Ido Ammar ta bita 'yar tata ta cika Masha Allah ta cicciko kamar me karamin ciki Amma idan tayi la'akari da duka yaushe suka bar garin a halin ciwo ai ko cikin ne be Isa ya nuna Kansa haka ba, kawai samun hutun Zama guri Daya ne.
Kusa Ammar ta zauna data dawo.
"Ki daina saka turare haka duk kamshinsa ya kashe min nawa na freshner da turaren wuta".
"Wallahi Ammah Wanda nake sakawa ne na saka, yanzu Dan Allah Ammah inata rokonki jki taimaka ki saka Baki ya maidoni gida Amman Kika qiya, nasan badan rashin lafiyar Baba malam ba bazezo Dani garin Nan ba".
Dan murmushi Ammar tayi Tana K'are Mata kallo.
"Meyake Miki da kike son barin kusa dashi ki dawo Nan kina ganin hakan shiya fiye Miki? Ashe har yanzu Baki da wayo kada na qara Jin magana makamanciyar wannan daga bakinki,duk inda mijinki ya saka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login